Rumbun Qaya hausa Novel Page 8

Rumbun Qaya hausa Novel Page 8

Rumbun Qaya hausa Novel Page 8

 RUMBUN QAYA*


  

           Page 8


©️®️ *_Hafsat Rano_*


ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥
________••••••••••••••••***A gajiye likis ta koma gida, ga uwar yunwa ga ranta da yake a chunkushe, ko abincin kirki kasa ci tayi duk da yunwar da take ji ta zauna shiru tana bitar abinda ya faru dazun. Wajen la'asar ta tashi ta je dakin Adda Maimuna ta tambaye ta abinda za'a dafa da daddare duk da ba ko yaushe ne take shiga kitchen din ba amma in dai tana nan, tana taimakawa sosai ayi duk aikin da za'a yi da ita, ba zata zauna ta lafe komai sai dai ayi mata ba, irin wannan zaman gundurar masu gidan kake yi shiyasa take shiga ayi duk abinda za'a yi da ita, ta lura kuma hakan na faranta ran Addan shiyasa ma take sake dagewa wajen ganin ta zauna lafiya dasu a dan zaman da zatayi.

  Tuwo tayi miyar kubewa daf da magriba ta gama ta gyara kitchen din tas, sannan ta dora indomie dan bata jin cin tuwon kawai gashi kuma tana jin yunwa tunda da rana bata wani ci abincin ba. Tana cikin cin indomie din Oga Kamal ya kirata, ta daga da yakinin dalilin da ya saka shi kiran nata. Hakuri ya bata akan abinda ya faru dazun ya kuma yi kokarin nuna mata sam hakan ba halin Aryan din bane ba, shi kansa be san dalilin da ya saka yayi acting haka toward her ba,amma sam tsakanin sa da ma'aikatan ba haka bane ba. Ta dai ji shi ne ba wai dan ta yarda ba, dan ita bata ga duk abinda ya fada din ba,tunda dai ita be mata ba.

   Tattare wajen tayi ta kai plate din kitchen ta dauraye shi sannan ta dawo falon ta samu su Muhammad suna kallon ball ta zauna kawai dan idan ta koma dakin ma babu abinda zatayi, ga Amina yau ba ta dawo ba ta tsaye gidan Anty Saliha babbar yayarsu watakila ma ta kwana a chan.***Rashin neman sa da Daddy be yi ba jiyan sai ya zata ya manta ya cigaba da sabgogin gaban sa, yana raba kafa yaje nasa office din yaje na gida, baya shigowa gidan sai dare sosai kuma dan baya son abin magana, haka kuma da safe da wuri yake ficewa ya wuce gidan sa ya karasa shiryawa a chan daga nan ya tafi aiki, haka yakeyi a kwana biyun sai dai yau yana shigowa sai ga Daddy a falon k'asa shi da Adam da tarin takardu a gabansu daga gani wani muhimmin aikin sukayi tunda har suka kai wannan lokacin, ji yayi kamar ya juya amma babu hali dan sun riga sun ganshi. Karasowa yayi ciki ya durkusa ya gaida Daddyn wanda ya amsa masa idanun sa na kan wata takarda sannan yace ya zauna. Kallon juna sukayi shi da Adam kafin ya zauna yana zubawa takardun ido yana son fuskantar dalilin zaman nasu.


"Kai da nace ka sameni da daddare shikenan sai kayi batan dabo? Yau kwana uku."


Shafa saman sumar kansa yayi, ya dan yi yak'e kad'an


"Ya tabbata a gidan dai kake kwana, ni ne dai baka son haduwa da, sai ka shigo late ka fice da safe ko?"


"Ba haka bane ba." 


"Toh Ya ya ne? Har yanzu maganar nan ce Muhd? Ba zaka hakura ba ko?"


Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, dan be zaci Daddy zai dauko wannan maganar ba a irin wannan lokacin, be taba kawo hakan ba da ya gwammace ya fasa shigowar da ya gansu, ko yayi wata karyar da zai samu ya zille.


"Ya kamata ka sani, ban amince kayi wani abu akai ba, na fada maka ba tun yau ba, ka bar wannan maganar kawai amma na lura kamar baka ji, abinda ya riga ya wuce ya wuce, tsaurara bincike ba zai taba haifar d'a me ido ba."


"Dan haka bana so, ka bar maganar nan na fada maka, ka barta tunda ba akan ka aka fara mutuwa ba, ba kuma zai zama na karshe ba, kana gani nayi iyakar kokari na akan case din, kuma an tabbatar da kanta ta kashe kanta, binciken Yan sanda, likitoci da duk kwararru akan fannin ya tabbatar da haka, akan kishi? Toh me kake so nayi kuma akai? Ko ban iya ba kaine ka iya?"


Kansa a k'asa zuciyar sa na wani irin harbawa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, ya dinga jin wani irin tashin hankali na bijiro masa, maganganun da ya tsani ji a rayuwar sa, ace wai ta kashe kanta da kanta, wanne marar tunani ne zai yarda da hakan? Ta ya ya kishi zai saka ta kashe kanta? memory din abinda ya faru ne ya shiga dawo masa filla filla. Muryar ta radau tana neman taimako, cikin tsananin wahala da galabaita. Sunan sa da take kwalawa ya shiga yi masa amsa kuwwa, tamkar a lokacin take kiran sa, tamkar a lokacin komai yake faruwa, idanun sa ya runtse, ya hango ta kwance a cikin jini, cikin tsananin jinin da be taba ganin irin sa ba, Ammin sa a kwance, an mata yanka irin wanda ake wa rago! Jikin sa ne ya hau rawa sosai, gumi ya shiga keto masa, Adam ne ya fara lura da halin da yake ciki, yayi saurin ankarar da Daddy dan tun sanda ya fara masa magaar be ko kalle shi ba, zabura yayi cikin tsananin tashin ya watsar da takardun hannun sa, sukayi kan Aryan din suna kwalla kiran sunan sa.

   

"Kira Dr, kira likitan sa Adam, innalillahi."


Wayar sa ya ciro da sauri ya shiga dialing number likitan da yake duba shi, ringing daya ya dauka dan har yana shirin kwanciya ma dan be dade da shiga gida ba. 


Suna tsaye akan sa suna kokarin bashi taimakon gwaggawa Dr ya karaso, ya taimaka musu aka karasa saka masa nebuliser dan dama gashi asthmatic toh da irin hakan ta faru sai numfashin ya soma yin sama. Kusan minti talatin zuwa awa daya sannan ya fara samun daidaituwar numfashin sa dama kan sa. Rufe idon sa yayi ruf, yana jin maganganun su akan sa da yake masa wani irin ciwo.

    Har kusan ukun na dare suna tare a dakin sa harda Hajiya Zeenat, dan nan aka maidashi, yana jin yanayin damuwar da Daddyn yake ciki fiye da duk wata damuwa da ya taba shiga akan ciwon nasa, me yasa yanzu ya nuna damuwar sa sosai? Me ya sauya daga sanin da yayi wa Daddyn na rashin kulawa da damuwa da abinda ya shafe shi? Be san dalilin nuna masa soyayyar ba, bayan be same ta a lokacin da yake da matukar bukata ba, a lokacin da ya chanchanci a jashi a jiki a nuna masa soyayya, sai yanzu? Da ya girma ya mallaki hankalin kansa? Baya bukatar wannan soyayyar, baya bukatar kulawar zai iya kula da kansa tamkar yadda yayi a baya. Suna fita daga dakin ya tashi da k'yar dan jikin sa baki daya babu kwari ya fice daga dakin ya sakko k'asa, ya isa dakin masu gadi ya taso daya daga cikin ma'aikatan gidan yace ya kaishi gidan sa, a daren nan da komai haka suka tafi. Suna isa ya ce masa ya zauna ya karasa kwana anan kawai ya shige ciki yana jin kamar ana daddatsa masa cikin jikin sa saboda wani irin mugun sanyi me hade da zazzafan zazzabi da ya rafke shi a lokaci daya. Gabannin asubah zazzabin ya dan sake shi kad'an, ya tashi da k'yar dan dama ba baccin yake ba. Alwala yayi yana fitowa daddy na kiran wayar sa, be daga ba dan yasan kila dakin sa yaje duba shi da asubah yaga baya nan shine dalilin kiran, bashi da wani bayanin da zai bawa Daddy bama shi da karfin jiki da na zuciyar da zai iya magana dashi, musamman da ya zama duk abinda ya fada ba zai iya ce masa a ah ba. Raka'atanil fajr yayi ya zauna a saman daddumar har zuwa lokaci ya tashi yayi subh sannan ya koma ya sake kudundunewa a cikin blanket. Bacci ne ya dauke shi me karfi cikin yanayin da shi kadai yasan abinda yake ji.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post