Rumbun Qaya hausa Novel Page 9

Rumbun Qaya hausa Novel Page 9

Rumbun Qaya hausa Novel Page 9

 RUMBUN QAYA*


  

           Page 9


©️®️ *_Hafsat Rano_*


ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥


****Karfe tara ya farka daga nannauyan baccin da ya dauke shi, bashi karfin zuciya da na gangar jiki amma hakan ya tashi da k'yar, yayi wanka ya shirya sannan ya kira Kamal yace yazo ya dauke shi dan baya jin zai iya driving. Ba'a dau lokaci ba sai gashi ya iso, ya fito yana tafiya wadda ya sa Kamal din karasowa da dan sauri yana kallon fuskar sa


"Are you ok ?"


Gid'a masa kai yayi, ya wuce shi zuwa wajen motar, bin sa yayi cike da mamakin karfin hali irin nasa. Bud'e masa motar yayi ya zauna a hankali sannan ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar gidan. A hanya be ce masa uffan ba, kansa jingine da jikin kujerar ya rufe idon sa ruf dan ma baya so Kamal din ya ishe shi da tambaya, he's so weak dan hatta heartbeat dinsa ya sauya.


"Aryan!"


"Um." Yace ba tare da ya bud'e idon ba


"Baka jin dadi, let go back please."


"Haka nace maka? Na gaji ne kawai."


"Gajiya? Me kayi da safen nan da zai saka ka gajiya,?"


"Ba sai ka sani ba."


"Ai saboda babu shi din ne ma, sanin da nayi maka baka kwana a gidan nan idan har ba wani abu bane ya faru ba, kai da Daddy ne ko? Dan nasan baka saka damuwar Adam a ranka balle har ta dame Ka."


"Kamal please, let talk about it some other time."


"Ok, be strong please."


Yace masa cike da tausayawa, kafin ya maida kansa kan titin ya cigaba da tukin sa ransa duk babu dadi.


   Ko da suka isa company be fito daga motar ba, har sai da ya dauki wasu yan dakiku saboda yadda yake jin kansa na juya masa, da k'yar ya cije ya zuro kafar sa ya fito dan yayi ma kansa alkawarin ba zai taba bari hakan yayi affecting dinsa ba, amma kuma daga yadda yake ji yasan yana gaf da breaking alkawarin da yayi ma kansa nan kusa. Jerawa sukayi zuwa cikin building din Kamal na biye dashi a kusa kusa dan tsoron yanayin da Aryan din yake ciki. Har sai da ya kaishi office dinsa ya tabbatar ya zauna sannan ya wuce nasa da niyyar kiran Dr ya samu bayanin abinda ya faru dan yasan ta yadda zai iya kulawa da Aryan din. Be taba jin da gaske Aryan yana bukatar mace a tattare dashi ba sai yau, yana bukatar macen da zata zamar masa tamkar bangon da zai jingina dashi, tabbas zai rage abubuwa da yawa yasan, sai dai wacece zata iya zama da Aryan din da halin sa? Da ciwon sa? Da damuwar sa? Da shariyar sa? Wacece zata jure duk wannan? Dole sai dai wadda take tsananin so da kaunar sa fisabillillah, ba wai dan wani abun duniya ko fame ba, wadda take jin da gaske yana da bukatar a jashi a jiki, a nuna masa tsantsar soyayya, irin wadda ya rasa, wadda zatayi masa soyayyar uwa da danta, tayi masa soyayyar miji da mata. Tunanin sa ne ya katse sanda yaji Dr Ma'aruf din ya daga wayar, suka gaisa ya tambaye shi abinda ya samu Aryan din, yasan waye Kamal a wajen Aryan din shiyasa be boye masa komai ba, har ma da abinda ya kasa fadawa Daddyn, wanda ya sake tsoratar da Kamal din sosai. 


   System ce a gaban sa yana rike da mouse yana scrolling sai dai har ga Allah be san abinda yake dubawa ba, ga tarin bayanai nan da duk wani abu da yake da bukata a ranar amma ya kasa aiwatar da komai, lekowa Kamal yayi ganin sa a haka ya sashi zuwa office din su ya tarar da Raihana tana zaune babu abinda take dan babu aiki sosai a ranar saboda rashin zuwan Aryan din da wuri, dole sai ya gama dubawa idan ma akwai aikin zai aiko mata dashi ta mail ko ya kirata tazo ta karba. Gaishe shi sukayi dukka a karo na biyu sannan yace ta taso ta dan dafa musu shayin nasu. Ok tace ya fita ita kuma ta wuce kitchen din. Akwai komai da zata bukata nan da nan ta hada abinda zata hada ta dora, ta tsaya a kitchen din har ta gama sannan ta dauka zuwa office din Kamal din, tayi Knocking kad'an a kofar sannan ta tura, waya yake ya kalle ta sannan ya kalli kayan hannun ta


"Kai mana office din Aryan please, thank you." 


Yace bayan ya dan zare wayar daga kunnen sa yayi maganar sannan ya cigaba da wayar, bata so ba dan ita bata ma san ya shigo yau ba duk da tasan babu abinda zai hanashi shigowar amma rashin jin duriyar sa yasa ta sakankancewa da be zo din ba. Tana kokarin karasawa office din nasa zainab ta taso da sauri ta tare ta


"Oga yace baya bukatar kowa a office din sa yau."


"Oga Kamal ne yace na kai masa."


"Bani na kai masa da kai na."


Wani kallo Raihana tayi mata,ta rasa dalilin takura mata da yarinyar tayi, gashi ita kuma sam ba'a nuna mata iko da gadara, wanda taga alamun dabiar Zainab din ce, murmushi tayi mata kad'an sannan tace


"Karki damu bari na mika masa."


Tayi wucewar ta, ta barta a tsaye a wajen cike da mamakin yarinyar. 

   Kan sa ya dora a saman table din bayan ya dan ture system din, sai da ta shigo sannan ya dago, tayi saurin janye idon ta daka kallon sa ganin yadda nasa suka kad'a sosai, kallon kayan hannun ta yayi har ta karaso ta dora su saman dan madaidacin table din dake gaban couch din.


"Good morning Sir." 


"Menene wannan?" Yace bayan a amsa gaisuwar a ciki ciki dan ita bata ma ji ba


"Sir Kamal ne yace a kawo nan."


Juyar da kansa yayi gefe da yaji kamar ya makale masa, sannan ya sake dawo dashi tunanin taimaka masa ya fado masa


"Have a seat."


Ya nuna mata wajen zama, dan jim tayi kafin tazo ta zauna a daaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table din nasa ta dayan side din, turo mata system din yayi gaban ta, sannan a hankali yace 


"Ki duba min wannan." 


Kallon screen din tayi, sai taga same aiki ne da wanda ya saka ta kwanaki .


"In kin gama dubawa ga mails dinsu nan kasa sai ki tura."


"Ok."


Tace ta shiga aikin, yanayin maganar sa tayi mata kama da ta mara lafiya sosai, dan babu wannan zafin a maganar haka kuma babu nacaccen kamshin nan nasa da kullum yake mamaye baki daya ilahirin building din. Kamar ta bud'e baki ta tambaye shi ko akwai matsala ne? Dan tana jin sautin numfashin sa na fidda wata yar kara, sannan tana jin kamar jawo numfashin yake ta karfin gaske. Amma kuma tace masa me? Tasan yanayin sa zai iya bata amsar da zata gwammace dama bata yi tambayar ba. Wayar sa dake saman table din ce ta dinga kara amma yayi biris kamar bashi ake kira ba, so take ta dago taga yanayin da yake ciki amma sai ta kasa dan cike dake da shakkar sa. Tura kofar ya sakata kallon kofar, sai dai ganin wanda ya shigo ya saka gabanta faduwa, fuskar sa ce ta washe ganin ta, ya karaso yana maida kallon sa kan Aryan din da shigowar sa ta saka shi yunkurin mikewa amma kasancewar bashi da karfin jiki sai ya kasa.


"Me ya kawo ka?" Yace muryar sa a shake wadda take kara tabbatarwa da Adam weakness dinsa, shafa saman kansa yayi yaja kujerar dake gefen ta Raihanan ya zauna sannan yace


"Baka duba wayar kane? Daddy yana ta kiranka tun asubah, shi ya turo ni, na duba masa kai."


"Tunda ka ganni sai ka tafi ko"


"No ai ban gama ba,zai kira yanzu sai na hada ku." Yace yana zaro wayar sa da ta soma ringing ma tun kafin ya dire maganar, dagawa yayi


"Eh daddy yana office, eh toh gashi nan dai bari na bashi."


Ya cire wayar ya mika masa, wani kallo Aryan din yayi masa kafin ya karbi wayar ya saka handfree ya dorata a saman table din


"Aryan kana jina?"


"Ina kwana?" 


Yadda yayi maganar ya saka Raihana kokarin mikewa ta bar musu office din dan ita bata gane yadda abubuwan suke ba.


"Seat down!"


Yace mata yana zare idon sa akanta, komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta. Yadda yake maganar da yadda yake amsawa wanda aka kira da Daddy ne ya daure mata kai, shi kowa haka yake masa kenan? Har mahaifin sa ma?


"Yan mata aiki ake yi ne?" 


Adam ya fada yana karyar da kansa hade da wani irin kallo, kallon da yake hana mata sakat idan yayi mata shi dan ta tsani a rayuwar ta yawaan kallo musamman irin wannan da kana gani zaka tabbatar da abinda mutum yake nufi. 


"Umm." Ta bashi amsa tana sake kankan da kanta dan ita gaba daya zaman wajen ya ishe ta.


Wayar sa Aryan din ya garo masa bayan ya gama maganar, ya dauka yana mikewa


"Babu kyau wulakanta mahaifa dai, baka ga yadda hankalin sa ya tashi ba, amma kamar ko a jikin ka."


Uffan be ce masa ba, yayi masa wani banzan kallo kawai ya ja siririn tsaki, dama kuma Adam din yasan ba zai tanka masa ba, kuma dama be yi don ya tanka masan ba, yayi ne duk dan saboda aikin da suke kokarin dora Raihana akai ne, shiyasa ba karamin dadi yaji ba ganin ta zaune a office din Aryan din,hakan ya sake tabbatar musu da aikin su zai tafi yadda ya kamata.

  Rankwafowa yayi ta saman kujerar da Raihanan ke zaune, ya dora kansa daidai saitin kunnen ta a hankali yace


"Ki kula dashi sosai, kinsan yana da matsalar kwakwalwa."


Daga kanta tayi da sauri ta kalle shi, ya kashe mata ido daya sannan yayi murmushi.


"Get out!" Aryan yace a zafafe, daidai lokacin Kamal ya shigo office din, da saurin sa ya karaso ganin har Aryan din ya mike tsaye, ya kalli Adam din sannan ya kalli Raihana dake zaune da system din Aryan din a gabanta


"Sannu da zuwa Malam Kamal, yau na kawo muku ziyara gashi har zan tafi, sai mun sake haduwa ko?"


Yayi gaba ya bud'e kofar hade da banko ta a lokaci daya. Dafe kai Aryan yayi da yake jin kamar ya cire shi yayi wurgi dashi ya huta tsananin ciwon da yake masa.


"Calm down please." Kamal yace yana matsawa gefen sa


"Raihana, please excuse us kinji?"


Tashi tayi da sauri ta fice sum-sum-sum dan dama hanya take nema. 


"Na gaji Kamal, na gaji wallahi, Adam yana so ya kai ni bango, yana so ya kai ni karshe."


"Dan Allah ka kwantar da hankalin ka, yau ne karo na farko da ya fara irin haka? Kasan shi kasan abinda zai iya, kasan kuma komai akan dalilin da yasa yake maka hakan, ya riga yasan weakness dinka, dashi yake amfani wajen bata maka rai."


Dafa jikin table din yayi da hannu daaya, dayan kuma ya rike kansa ya shiga jujjuya shi, yana ganin a karshe sai Adam ya haukata shi sannan zai kyale shi. Dafo shi Kamal yayi yace


"You need some rest Aryan, baka da lafiya."


Zame hannun yayi ya zauna yana sakin kan a hankali


"Me yasa kake punishing kanka haka ne wai? Me yasa ? You are sick tun daga yanayin maganar ka har facial expression dinka ya nuna, amma ka dage sai kayi aiki? Akan me?"


"Bani shayin chan please, mu bar maganar nan haka nan Kamal."


Matsawa yayi ya zubo masa shayin a cup ya mika kasa, ya kafa kansa ya shiga sha a hankali dan zafin na ratsa makoshin sa wanda yake a matukar bushe. Shanye wa yayi tas ya sake kara masa shima ya shanye, sannan ya dan dora kansa a saman table din ya kulle idanun sa. Babu yadda Kamal ya iya face ya fita ya barshi, ya je ya dauki wayar shi ya kira Ya Nabeela yace ta shigo office din, cikin kankanin lokaci sai gata tazo a cikin yanayi, ta same shi kamar ma bacci yake a zaune dan har ta shigo be dago ba, sai da ta taba shi sannan ya tashi. Dole ta tilasta masa bin ta, ta dauke shi daga office din zuwa gidan ta, sannan ta kira Dr Ma'aruf din tun a hanya yace zai same su a gidan.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post