Wa ya Kashe Rukayya? Page 8

Wa ya Kashe Rukayya? Page 8

Wa ya Kashe Rukayya? Page 8

*WA YA KASHE RUKAYYA

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

8️⃣

"Yeah! Ni ne dai *ALIYU YUSUF ALKALI WAZIRI* ɗa ɗaya tilo wajan iyayansa kamar dai yadda ki ka kasance a naku gidan"

ALKALI WAZIRI former president namu da ya sauka shekara biyu a baya? To ai naga babu wanda yasan ɗansa har ya yayi shekara takwas ɗin sa ya sauka, ance ɗansa gaba ɗaya rayuwarsa a turai ya yi babu wanda ya sansa....."

   Cike da rawar murya ta ke maganar mamaki fal fuskarta.

Murmushi ya sakar mata wanda yasa ta kusa sakin Amatulla a ƙasa, ihu ya rinya ta tsala ganin zata sha ƙasa da sauri Amal ta sake rungumeta a jikinta kamar zata mai da ta ciki.

"Ina ki ka samo baby mai kama da ke yarinyar waye".

  Ya yi mata tambayar yana mai tsareta da idanuwansa masu bala'in kaifi.

Daburcewa ta yi ta soma in ina....."ɗiya ta ce".

  Bakinta ya bi da kallo yana sake kusanta kansa da jikinta.

Rawar jikinta ne ya karu ita kam yau ta shiga uku da wannan mutumin meye haka ne wai.

  Ta yi maganar a zuciyarta fuskarta na sake haɗewa.

"Ina ki ka samo baby Amal?"

  Ya sake watsa mata tambayar yana ɗan ja baya daga jikinta.

Wani ajiyar zuciya ta sauke irin na wace ta samu salama ɗin nan.

"Ƴa tace, ni na haifeta".

  Daga haka ta juya ta nufi ɗakinta da wani irin sauri ba tare da ta sake sauraran abinda zai ce ba.

Yafi minti biyar a palon sannan ya juya ya tafi yana saƙe-saƙe a zuciyarsa.

    ***

Batai ƙasa a guiwa ba wajan bayyanawa Aminan nata abinda ya faru ba gaba ɗaya sun cika da mamaki banda Laila da dama ta riga ta sani harma da son da ya ke wa Amal ɗin.

Sun taya ta murna dan acewar su wannan wani abu ne na farinciki da zai ƙara ɗago da martabar group ɗin nasu da kuma sake zama manyan yara ababen kwatance.

Washe gari tunda safe suke ta shirye shiryen party da suka haɗa wanda duk suka gayyaci ƴan ajin nasu saboda murnar gama karatun nasu, babban taro suka shirya sosai irin na yaran da basa ji.

Wajan karfe takwas na dare suka gama shiri cikin wasu irin arnan shiga sai kace ba ƴaƴan musulmi ba ko wacce tasha makeup sai kyalli ta ke.

Message ne ya shigo wayar Amal da ke hannun Ruky ta nai masu hotuna budewa ta yi tana karanta masu saƙon a bayyane

   *"Ban baki izinin fita ko ina ba, kar ki sake ki yi gigin fita ko bakin gate ne, idan ki ka yi hakan ranki zai yi mummunar ɓaci*"

Dariya suka kwashe da shi gaba ɗaya Laila tace"Yau ni naji wata lukutar masifa, sai kace wani mijinki wai karki fita, yo Allah na tuba yanzu in ba Father bane ya bugo yace kar ki fita ba ai babu ubanda ya isa ya hana".

Ahmad yace "To ke ina ruwanki wannan tsakanin masoya ne, in ta so bin umurnin masoyinta babu inda zata"

  Ya kwashe da dariya yaci gaba da faɗin "amma fa Amal wlh da mutumin nan ya sha da ke wollah".

"To wai shi da ke niman kafa gwamnatin sa shi ne yake bada wannan umurnin lallai zamu sha kallo nan gaba kenan da alama kulle zaiyi gaskiya ya rafto dan nan dai babu hurumin hakan".

"Bangane babu hurumin hakan ba" Ruky tace tana hararar Rahman,

  "Ni da zata bi shawarata da zamanta ma ta yi abinta muka tafi muka watse mu kaɗai idan mun dawo tasha lbr ".

"Dallah muje lokaci na tahiya kuna ta zance mara ma'ana".

Taro ya yi taro ƴan mata da samari ta ko ina masu rawa na yi masu shaye shaye nayi masu iskance iskance nayi kowa na aikata abinda yai masa dai dai da muraɗin ransa sai ga masu gayya masu aiki sun iso nan danan kallo ya dawo kansu saboda shigar da ke jikinsu da kuma yadda suka jero a layi su biyar ɗin cike takama abin burgewa a wajan sauran yan mata da samarin da ke wajan kasancewar su kadai ake jira a fara shirye shiryen.

    Hamida ce ta taho cikin wani irin salo mai d’aukar hankali, tana tafiya gaba daya jikinta rawa ya keyi, har ta k’araso gaf da su kafin ta sanya  hannuwanta gaba ɗaya ta rungume Ahmad cikin sigar shagwaba tace "Ina taya mu murna gwani na

meya tsaida ku har zuwa wannan lokacin ku kalla ku gani fa yanda gunnan ya cika duk ku kaɗai ake jira".

   Duk wannan maganar ta na yin sa ne cikin harshan turanci kasancewar ta bayarabiya hausar bai wani zauna a bakin taba,  dago kanta yayi yana kallon cikin idonta a hankali ya manna mata kiss a goshinta yana fadin 

   "kinyi k’yau sosai Hamida me zan samu ne?"

fari tayi da manyan idanuwanta, tace 

  "Harma na kaika ne Ahmad?"

  murmushi yayi wanda yasa kumatunsa lotsawa, ɗan yatsanta ta tura a cikin ramin tana wasa da shi.

  "Ahmad ina k’aunar wannan abin naka". murmushin ya kuma sakin mata ya janyeta daga jikinsa.

Wani mugun tsaki Laila ta saki tana yin gaba abinta.

  Bayanta suka bi suma.

   Tallafo Hamida Ahmad yayi suka bisu a baya, nanfa DJ ya canza kiɗa ya sake kure ƙarar, ihu aka soma yi a na yi masu tafi saboda irin haduwar dasu kayi, nan dai aka shiga gudanar da komi yanda ya dace cikin tsari irinta yan boko, ko kuma ince irinta manyan yan bariki wayanda suka san kan duniya.

    Anci ansha an cashe son rai ansha an bugu sam baka iya tantance dan musulmi da akasin hakan a cikin su, hidimace irin ta yayan bariki wayanda suka san hannunsu, daga k’arshe kowanne yaja hannun budurwar sa suka kara gaba.

Wajan ƙarfe biyu da rabi na dare suka dawo gida a bige ko wanne a cikinsu ɗakinsa ya nufa.

            ****

Tun asuba Amal bata koma bacci ba cike da farinciki ta ke yau zata ga Father kamar ma ta yi tsuntsuwa ta ganta a garin Kano ta ke ji.

 kai tsaye _kitchen_  ta nufa in da ta shiga shirya _breakfast_ kala-kala gaba d'aya gidan ya ɗume da ƙamshi.

Ƙarfe takwas dai-dai Asabe ɗaya daga cikin masu aikinsu ta fito ta sameta ta na ta faman aiki bilhaƙƙi, ta yi mamaki ƙwarai da gaske na ganin Amal ɗin nata faman aiki haka dan sabon abu ne a wajanta.

Asabe ita ce babba a ƴan aikin nasu ta ɗan manyanta shi yasa suke bata girma sosai.

Cikin tsokala tace "A'a uwar ɗakina yau ke ce da kanki a kitchen da sassafe haka, lallai yau mu wasa bakinmu zamuci daɗi kenan, tubarkalla irin wannan ƙamshi haka".

"To Asabe yau ne fa zamu koma gida gaba ɗaya kin sani na kasa hakuri in jira har ku tashi ku ɗora girkin na matsu in ganni a gida wollah, kinga har na gama kawai shiryawa za kiyi bisa dinning ki tafi da naku bangarenku".

"To uwar ɗakina mungode kwarai yau kin hutashe mu Allah ya bada lada".

  Kai tsaye ɗakinta ta tafi in da taga har Amatulla ta tashi tana zaune tsakiyar gadonta tana ta wasa ita kaɗai.

  "Hello my beautiful daughter har kin tashi?"

  Ta daga ta tare da cilla ta sama tuni yarinyar ta soma kyalkyala dariya itama uwar na taya ta.

  "Uhmmm ana ta cewa muna kama bana yarda amma jiya Aliyu ya sake shaida min kamanninmu meye sirrin ne daughter?"

  Ta faɗi tanai mata cakulkuli tana ta faman dariya.

 Wanka tai mata tas ta shiryata kafin ta miƙa ta wajan Asabe dan a bata abinci itama ta shiga wanka.

Tsawon lokaci tana dirje fatar jikinta, ta fito tana goge jiki da wani ɗan tawul mara girma banda wanda ke ɗaure a jikinta.

Sai da ta tsane jikinta tas sannan ta shafa mai, ta feshe jikinta da turaruka masu ƙamshin daɗi sannan ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga har ƙasa ta yane kanta da mayafinsa ta fito palo riƙe da wayarta a hannu tana taku ɗai-ɗai tamkar bataso ta taka ƙasa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post