Rumbun Qaya page 34

Rumbun Qaya page 34

Rumbun Qaya page 34 Hausa novel by Hafsat Rano

Rumbun Qaya

           Page 34


_*©®HRano*_

  

***Turo kofar akayi aka shigo, Adam ne ya karaso da sauri ganin idon Daddyn a bud'e, kujerar da Aryan ya tashi daga kai ya zauna yana kallon Daddyn cike da farin ciki. Juyawa Aryan yayi ya fice ya rufe musu kofar dan baya son ganin abinda zai bata masa rai, duk da ya yarda da soyayyar da Adam din yake wa Daddyn ganin yadda ya damu sosai akan rashin lafiyar. Be san wani a matsayin uba ba, face Daddyn kuma shine kadai gatan sa. Shi ma Daddyn yana yi masa soyayya irin ta d'a ne da mahaifi yana jin shi sosai.


"Ya ka fito?" Ya Nabeela tace tana mikewa daga wajen da take zaune


"Adam ne yazo."


"Ban ga shigewar sa ba kuma, ko lokacin muna waya da Daddyn su Amna ne."


"Eh may be, bari na wuce idan Baba Rabi'un ya dawo sai kuyi maganar, zan yi kokarin fara processing tafiyar ina hadawa da sauran aikin."


"Ok, nima tafiya zan naga dare ya fara, yace zai biyo sai mu tafi."


"Ok, Baba Rabi'un shi kadai zai kwana yau?"


"Eh ina jin tunda jikin da sauki. Kaje gida ka huta, kayi bacci sosai please."


"Baccin ne ma baya yiwuwa ai, akwai ayyuka a gabana masu yawa."


"Still dai, ka huta yau dai, kayi tafiya kana bukatar hutu."


"Zan gwada."


"Yawwa, ya labarin Kamal?"


"Muna magana a chat,yana sane ya kyale ni sanda nake matukar bukatar sa."


"Yayi min daidai ai, da ace kana da matarka ba zaka yi wani missing dinsa sosai ba, yanzu haka da yadda ka gajin nan kana komawa za'a tare ka a kula mun da kai."


"Zan gudu, sai gobe."


"Baka son gaskiya dai." Tasa dariya


"Inaso mana, kawai maganar kara min pressure zatayi, amma dai I'm planning something, hoping yayi muku yadda kuke so."


"Akan wannan maganar?"


"Eh." Ya daga mata kansa


"Good, haka muke son ji, Allah ya bada sa'a ya taimaka."


"Amin, goodnight."


"Goodnight,." Ta daga masa ya fice cikin takun sa me cike da nutsuwa.


"Allah ya tallafi rayuwar ka Aryan ya hada ka da abokiyar zama me son ka." Ta daga hannu tayi addu'a sannan ta koma ciki.


•••••••Raihana bata tashi tunawa da sakon Hamma Muhd ba sai da safe bayan tayi breakfast ma tana kitchen tana wanke kwanukan da aka bata abun ya fado mata, da sauri ta dauraye hannun ta, ta goge da kitchen towel ta dauki wayar ta bud'e whatsapp din ta shiga kan chat din nasa. Saura kasan wayar da subce daga hannun ta, ta fadi kasa saboda abinda ta karanta.


_"Ni kuma? Soyayya?" 


Ta furta tana sake kallon tsararren sakon wanda ya tsaro da kalaman kokarin kafa kai. Ko kad'an bata ji son sa a zuciyar ta ba, hasalima baya cikin jerin mazajen da take jin zata iya zaman aure dasu kwata-kwata, ya tsaya dai a iya yan uwantakar amma ita dai a'ah, bata shirya ba sai ta kara wayo da hankali. Rasa me zata ce masa tayi, ba zata iya ce masa a ah kai tsaye ba, babu dadi duk tsiya wanda yace yana son Ka yafi makiyinka ai, ba kuma zata iya amsa goron gayyatar soyayyar tasa ba, dan ita gaba daya ba abinda ma yake gabanta ba kenan, Kar taje tana zaman zaman ta a hada bikin ta da na su Hamman ta, tafi so ta fara rakashewa a bikin su daidai gwargwado kafin a fara maganar ta. Jin ta take har lokacin yar karamar yarinya ce ita, bata isa aure ba, dan bata san ta yadda zata fara kula da garjejen saurayi ace ita zata masa kusan komai ita din da ba'a wani dade sosai da su Hamman ta suka daina goya ta ba.

Fita tayi daga kan chat din sai tayi nazarin me zata ce sannan zatayi masa reply kar tayi a take ta kwafsa. Cikin chat din Aryan ta shiga kamar munafuka dan dama tunda ta tashi take son budewa amma ta kasa. Murmushi tayi ta tura masa hi a kasan hello din da yace mata, sannan ta dora da waye? A gaban sakon. Tana sane tayi hakan ta ajiye wayar tana murmushi ta cigaba da aikin da take yi. Sai da ta gama tas ta gyara kitchen din ta fito ta koma daki ta zauna a saman gadon ta sannan ta sake shiga whatspp din. Blue tick din da ta gani akan chat din Aryan yasa ta tabbatar ya karanta sakon ta, typing taga yanayi ta yi baya ta kwanta akan pillow tana jiran amsar sa.


"Ghost ne!" Ya yi reply ya sauka a take ya kira wayar ta. Wani irin harbawa zuciyar ta, tayi da karfi ganin shine yake kira, ta rasa dalilin da yasa take jin hakan game dashi da duk wani abu da ya shafe shi. Kamar ba zata daga ba, amma kuma bata da wannan karfin zuciyar, sakata tayi a kunnen ta bayan ta daga tace hello. Ajiyar zuciya ya sauke me dan karfi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi sannan yace


"Baki da number na?"


"Na'am, mmm.. eh bani dashi."


"Oh okh, baki saving bane ba?"


"Eh." 


"Ok, do it now, please."


"Why?"


"Just. Kiyi saving bana so na kira mutum ko nayi masa magana yace be gane ba."


"Ok zanyi."


"Good, how was your night?"


Gwalalo ido tayi waje, how was your night Yake tambayar ta? Lallai


"Alhamdulillah." Tace 


"Masha Allah, me kike yi yanzu?"


"Ba komai, just laying down."


"Can i join you?" 


Ya fada kamar me rada, kame wa tayi a wajen cike da mamakin sa. Ta jishi sarai amma sai ta nuna bata ji me yace ba.


"Na'am?"


"Baki ji ba?"


"Umm, banji ba."


"Ok, yaushe zaki dawo, we need you here,."


"Ka manta? Kaine kace na tafi,baka son sake gani na, you hate me!"


"Shhhhh!!!" Ya dakatar da ita da karfi


"Please Raihaana." Yayi lowering voice dinsa sosai sannan yace 


" Duk abinda na fada ba har zuciya na bane, and I said I'm sorry, I'm sorry kiyi hakuri."


Bata ce komai ba, 


"Kinji? I'm sorry, kuma nayi regretting duk abinda nace."


"Ok." Tace da k'yar


"Kin hakura? Kin yafe min?"


"Umm."


"Serious?"


"Umm..."


"Thank you so much, nagode."


"Uhum."


"Are you coming back?"


"A ah."


"Pleasee dan Allah ki dawo, Kamal ya tafi, kema kin tafi I'm so lonely, please come back."


"Hamma na ba zasu yarda ba."


"Why? Me nayi musu ne har haka?"


"Ban sani ba nima."


"Shikenan, bari nayi clearing abubuwan da suke gabana, zanzo har nan din, sai muyi magana naji, menene laifi na."


"Okh."


"Na gaji, aiki yayi min yawa kwanan nan bana samun enough sleep."


"Ayya sannu, it's not easy." 


"Thank you, bari na shirya na fita, sai anjima."


"Ok sai anjima."


Suka ajiye wayar a tare. Wani fresh Aryan yaji akan sa kamar an janye masa wani abu me nauyi da ya tokare shi. Nine kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Be zata zai iya wannan long conversation din da ita ba, sai gashi yayi, har yana jin kamar su dawwama a haka suna magana. Murmusawa yayi ya tashi daga zaman ya tattare takardun sa sannan ya fada toilet dan yin wanka. Yana wankan yana tunanin abinda ya faru, shi kadai kawai sai yayi murmushi, ya gama ya fito daure da towel ya shirya a tsanake cikin shigar suit baka yasa bakin takalmin sau ciki sannan ya dauki abinda zai dauka ya watsa su a brief case dinsa hade da notepad dinsa ya fito. A falo ya ajiye komai ya shiga kitchen ya samar wa kansa tea ya dawo falon ya zauna yana sha yana kallon TV har zuwa lokacin da Habeeb ya karaso ya mike ya maida cup din kitchen ya dauraye shi sannan ya fito yana jin sa sakayau. Kansa da a kullum yake masa nauyi yau sai yaji kamar an cire masa ciwon an maye masa gurbi da wani irin mixed feeling me tafiya hade da farin cikin zuciya.


Tunda suka gama wayar take blushing, wani yanayi wanda bata taba jin irin sa ba take ji a yanzu. Muryar sa me cike da amo ta haddassr mata da wata irin kasala. Chusa kansa tayi a cikin filon tana murmushi k'asa k'asa, a haka Dadah ta shigo ta same ta. Tashi tayi zaune ta tankwashe kafarta tana kallon ta


"Na zata bacci kike ai da naji shiru."


"A ah, waya nake."


"Ok, yanzu mamanku Maimunatu ta kirani da wani labari."


Gaban Raihann ne ya fadi cike da tsoro tace


"Wani abun ne ya faru?"


Girgiza kai Daadah tayi


"Babu komai, sai alkhairi. Wai Muhammadu ne ya sameta da maganar ki,."


"Ni kuma Dadah?"


"Akwai wata a dakin ne da muke magana bayan ke? Kaji min shiririta."


"Toh ai Daadah maganar ce naji ta banbarakwai."


"Kinci gidan ku, ace ana sonki kice maganar ce banbarakwai."


"Ni dai gaskiya Daadah bana son shi."


Tafa hannu tayi ta hau salallami


"Menene laifin shi Raihana? Menene aibun sa? Yaro saurayi kyakkyawan gaske, me jini a jika, gashi dan dangi gashi kuma dan uwanki, me kike nema?"


"Allah ni Daadah son shi kawai ne bana yi, son yan uwantaka nake masa."


"Tirkashi, haka zaki mana Raihana? Har ina murna na sanar da yayyanki? Suma kuma murnar suke gasu chan a falo."


"Allah ni Dadah bana son shi, Allah kuwa."


"Toh wa kike so?fada min sai naji ai."


"Ni ba wanda nake so."


"Kinci gidan ku,ko aljanune dake ni jikar mutum hudu,eh?"


"Ba komai fa Daadah, na zata zaki fuskance ni, ni kawai bana son kowa ne, zaizo ne soon, amma banda Hamman gidan su Amina."


"Toh ni dai babu ruwana, kiyi tunani sosai sannan ki duba abinda zai faranta mana rai, idan kuma akwai wanda kike so ne ki fada min ni zan wuce miki gaba, amma idan har babu toh fa ba ruwana."


"Shikenan zan fada miki shi, amma yanzu ki hana su Hamma maganar toh, yanzu sai su dauka su fadawa Abby."


"Ki dai yi kokarin bashi dama ku fahimci juna."


"Toh Dadaah,zan bashi dama."


"Yawwa haka nake son ji, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi."


Sai ta mike


"Bari na samesu nace su bar maganar zuwa sanda kuka daidai ta kanku, amma dai zaa bashi damar zuwa wajenki, idan Allah yayi zaa yi dashi toh, idan kuma Allah be yi ba shikenan."


"Ok tam." Tace dan so take a bar maganar haka nan shiyasa ta amsa mata da yadda take so. Tana fita ta kulle kofarta ta koma ta kwanta rigingine tana kallon saman dakin. Daga chan bangaren hankalin Muhd duk ya tashi, gashi ta duba message dinsa amma babu reply gashi yayi ta kiranta dazu yana jin user busy duk sai ya kasa nutsuwa, yaje ya sanar da Adda Maimuna shine ita kuma ta kira dadah dan ba karamin farin ciki ta shiga da labarin ba, dan dama tana ta fargabar wadda Muhd din zai dauko, sai gashi ta kwana gidan sauki.


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261
TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post