Rumbun Qaya Page 38
Health College

Rumbun Qaya Page 38

Rumbun Qaya  Page 38

Rumbun Qaya

     Page 38


***Tashi Ya Nabeela tayi ta kwashe kayan wajen da taimakon househelp suka kaisu kitchen, sama ta haura itama dan duba su Amna dan sun tashi tun safe sunyi breakfast dinsu sai tasa suka koma saboda an saba tashin wuri saboda school. Su uku ya rage a falon Malam Hassan yace wa Daddy zai tafi, duk da Daddyn be so ba amma dole ya barshi ya tafi amma da sharadin zai dawo nan kusa ya sake duba jikin Daddyn kafin su tafi. Shi ma kuma Daddyn zai zo har ranon da ya kara samun karfin jiki. Driver daddy ya kirawo yace ya shirya mota, dan da Kamal ne zai maida shi sai kuma Daddyn yace driver ya maida shi yana so zasu dan tattauna da Kamal din. Baba Rabi'u ne ya karaso ya kira Daddyn Kamal ya bud'e masa kofar tunda dole sai ta ciki za'a iya budewa idan basu yan gidan ba. Yana shigowa suka gaisa da Malam Hassan a sake sannan suka dingumo suka yo waje don rakashi, da waya Kamal ya kira Aryan yace yazo Baba zai tafi sai gashi ya sakko ya same su a compound din. Hannun sa zube a aljihun sa ya tsaya yana kallon su, daddy ya fito da Debit card dinsa karamin ya bawa Habu driver yace su fara tsayawa yayi ma Baban siyayya kafin su wuce. Godiya sosai. Malam Hassan yayi, ya zauna a gaban motar Kamal ya gyara masa rigar sa da ta dan fito sannan ya rufe masa kofar


"Allah ya kiyaye hanya Baba, cikin satin nan zamu shigo in sha Allah."


"Allah ya kawo ku,sai anjima Alhaji, nagode da karamci."


"Ni ne da godiya, zan zo har gida ma in sha Allah."


"Allah ya kiyaye hanya."


"Amin Aryan, ka tabbata kaje kaga likita kaji?"


"In sha Allah zanje."


"Allah ya kara sauki."


"Amin." 


Suka hada baki suka fada. Sai da suka ga fitar su daga gidan sannan suka juya suka koma cikin gidan. Saman Arya  ya haye, Kamal kuma ya zauna tare da Daddyn da Baba Rabi'u a falon k'asa.


"Kaga dan uwanka ko Kamal?"


"Daddy ayi hakuri dan Allah."


"Ai ba laifi yayi min ba, ni tausayin sa nake kawai, yaushe zai yi farin ciki shima?"


"Ya kusa daddy, in sha Allah kwanan nan zaka ga sauyi."


"Ta yaya Kenan?"


"Dama akwai maganar da nake son sanar dakai daddy."


"Ina jinka."


"Aryan yana son yar gidan Barrister Matawalle."


"Raihana?" 


"Eh ita."


"Tirkashi, a wannan yanayin da ake ciki? Kana ganin Nasir zai taba amincewa?"


"Toh, shine dai ba zamu ce ba, amma dai zamu gwada. Shine kawai hanyar da za'a bi wajen dawo da tsohuwar alakar da take tsakanin ku Daddy."


"Kayya, ban ki ta taku ba Kamal, amma Nasir yayi fushi, fushi me munin gaske, bana jin Nasir zai iya daukar yar sa ya bawa d'ana, abu me me kamar wuya,."


"In sha Allah zai yarda."


"Toh, shikenan amma dai, shikenan dai toh bari mu gani, ka bani number sa ina so na fara kiran shi ma dai, kafin naje har gida."


"Ok."


"Amma sai nake ganin kamar ya tsawwala, Allah muna masa laifi ya yafe mana, me yasa ba zai zama cikin masu yafiya ba?"


Baba Rabi'u yace


"Rabi'u ba zaka gane yanayin ba, ni bana ganin laifin Nasir, ko nine abinda zan yi Kenan, karshen rashin kyautawa an masa,."


"Amma ai da sai yayi hakuri ko? Tunda dai yanzu kusan komai ya wuce."


"Ba zai taba wucewa ba ai, tabon nan yana nan a zuciyar s, dan haka ni dai bana ganin laifin sa, idan ya amince ya yafe min ya kuma bawa Aryan Raihana toh, idan yaki sai Aryan yayi hakuri ya nemi wata."


"In sha Allah ma zai hakura, in sha Allah." 


"Toh Allah yasa."


"Bari muje muga Dr Mahfouz Daddy."


"Ok, ya aikin naka?"


"Ina hutu ne, karshen next month Zan koma watakila kuma ayi min transfer ma."


"Toh Allah yasa muji alkhairi, da zaka bar aikin ka dawo ku cigaba da kula da companyn nan naku, Aryan kadai ba zai iya ba."


"Yanayin aikin namu ne daddy, amma zan duba in sha Allah."


"Yawwa, Allah ya baku sa'a, ya taimake ku baki daya yayi muku albarka."


"Amin ya ALLAH."


   Saman ya hau ya samu Aryan yace ya taso suje wajen Dr Mahfouz, be ce komai ba ya chanja kayansa zuwa jeans da shirt sannan suka fito tare. Kamal din ne yake driving Aryan na gefen sa, yaki cewa komai har suka karasa, suka same shi a office sukayi magana sannan ya kara rubuta wasu drugs din ya basu suka fito suka siya a pharmacy sannan suka dawo gidan. Suna dawowa gidan ya sha magungunan ya kwanta saboda wani irin azababen ciwon kai da yake, wanda yake da alaka da abinda ya faru dazu. Yayi regretting duk abubuwan da yayi, zafin zuciyar shi tayi yawan da yake kasa controlling dinta mafi yawan lokuta, sai yayi abu yazo yayi ta regretting. Dole sai yayi kokarin rage fushin sa idan yana son Jin dadin rayuwar sa. Fita Kamal yayi ya ja masa kofar ya nufi gidan su Khadija don dauko ta.



****Kamar yadda Muhd yace zai zo ranar, sai gashi ya iso da yamma. Raihana na daki Daadah tazo kiranta, dama tun jiya da ta kashe wayarta bata sake kunnawa ba. Ta dauka da wasa yake da yace zai zo, ashe da gaske yake. Kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu haka taji, ta bud'e wardrobe dinta ta dauko wani zumbulelen Hijab dinta tun na islamiyya ta zura sannan ta fito. Yana zaune a falon an kawo masa ruwa da abinci Dadah na gefen sa a kujerar sai Hamma Hydar da yake zaune a dayar kujerar suna magana. Da kallo ya bita ta kamar tsohon maye, ta turo baki ta hade rai ta zauna ta gaishe shi ya amsa yana kallon yanayin dake fuskar ta 


"Yasu Mama da Amina?" Tace kamar dole


"Lafiya Lou, sun ce a gaishe ki, Amina taso biyo ni toh amma jibi zasu fara exams shiyasa."


"Ok, Allah ya bada sa'a."


"Har yanzu bakya jin dadi ne?" Hamma Hydar yace ganin yadda take magana.


"Kasan sai a hankali dama jikin zai ware." Daadah tayi saurin kareta


"Kin shanye dose din magungunan ki?"


"Eh na shanye."


"Nasan halin ki dakin magani, karki min karya."


"Allah Hamma na shanye. Ko Dadah?"


"Ta shanye."


"Ya karfin jikin?" Muhd yace


"Alhamdulillah."


"Allah ya baki lafiya."


"Amin." 


Sai ta mike


"Karatu nake Daadah, bari na karasa."


"Toh." Tace bayan ta gano ta tsaf zaman ne ba zata iya ba.


  Tana shiga dakin ta cire Hijab din tana jan tsaki, bata son naci a rayuwar ta, menene na zuwa kuma? Kenan dadewa ma zai yi tunda yake maganar da zasu zo da Amina Amma jibi tana da exams, gaskiya zai takura mata zai shiga rayuwar ta da yawa. Cigaba tayi da kwanciya a dakin kawai dan ko fita bata son yi. 

  Falon Abby Hydar yaja Muhd domin ya gaishe shi, Abbyn na zaune suka shigo Muhd yayi saurin zubewa a k'asa ya gaida Abbyn ya amsa a sake sannan ya tambaye shi mutanen gida.


"Duk kowa lafiya Abby, suna gaishe ku."


"Madallah, sannu da hanya."


"Nagode Daddy." Yace a ladafce. Wayar Abbyn ce kira ya shigo, Hydar ya dauko masa ya mika masa ya daga bayan ya kalli number


"Assalamu alaikum." 


Daddy yayi sallama daga dayan bangaren. Wani irin dauke wuta Abby yayi, ya sake kallon number sannan ya saka wayar a handfree yana matsar da ita daga kunnen sa


 "Barka da rana Alhaji Nasir."


"Da wa nake magana?"


"Ibrahim ne Nasir, baka dau muryar ba?"


"Wanne Ibrahim din?"


Dan jim daddy yayi cikin yanayin ba dadi yace


"Ibrahim Mukaddas."


"Ok, ina sauraron ka."


"Ya gida ya aiki?"


"Kasan bana aiki ai, gida lafiya Lou."


"Na kira ne na baka hakuri akan abinda ya faru..."


"Muje Muhd." Hydar yace yana mikewa suka fita


"Abinda ya faru ai ya riga ya faru, babu amfanin dawo dashi." Abby ya amsa bayan ya tari numfashin sa


"Haka ne, amma dai ka daure ka saurare ni,nasan ban kyauta maka ba..."


"Ina ganin da zamu jingine wannan maganar, kowa ya fuskanci rayuwar sa da yafi, gaskiya bana son dawowa da abinda ya wuce."


"Na sani, na sani amma dan girma Allah ka saurare ni, akwai maganganu masu tarin yawa da nake so mu tattauna, sannan ka fuskance ni."


"Ni ka fuskance ni sanda nake cikin matukar bukatar taimakon ka? Ka dubi halin da zan shiga da wanda iyali na zasu shiga? Ka tuna wannan? Ka kore su ka kwace musu muhalli sannan ka hau kan dukiya ta ka zauna daram."


"Ko sisi ban taba maka a kudin ka ba, wallahi duk abinda Ka mallaka a lokacin yana nan, ya ninka kansa saboda kasuwancin da nake maka dashi."


"Menene amfanin su, a lokacin da suke bukatar su me yasa baka neme su ka basu ba? Kasan wahalar rayuwar da suka sha? Kasan yadda akayi suka so nan?"


"Ban kyauta ba, na sani wallahi ban kyauta ba, Dan girman Allah Nasir kayi hakuri ka yafe min, dan Allah."


"Ba zan iya ba, ba zan taba yafewa duk wanda suka jefa rayuwata da ta iyalina a bakin kunci ba."


"Ka saurare ni dan Allah."


"Karka sake kirana dan Allah, ka rike girman ka na rik'e nawa, mun riga mun manyanta yanzu rayuwar yaranmu ce a gaban mu."


Sai ya kashe wayar kawai yana kaiwa karshe. Dama dai Daddy yasan zaa yi haka, ko ma fiye da haka dan yasan iya karshen bata masa yayi, ya kuma cutar dasu. Baba Rabi'u dake kusa dashi a zaune ya girgiza kai kawai


"Ina ganin ka barshi ya sake warwarewa."


"Ba zan warware ba , kafin tafiyar nan zan aika yaran nan da komai da nasan nasa ne, bansan me Allah zai yi ba achan, ko rai zai yi halin sa, kar na mutu da hakkin sa."


"In sha Allahu ma babu abinda zai faru, ka tura su din hakan ma shawara ce."


"Abinda za'a yi kenan."


"Toh maganar yaran fa? Wa zai shiga masa gaba?"


"Rabi'u kana ganin Nasir zai saurare ni da maganar auren Yara? Ai a yadda ransa yake a bacen nan ba zan iya masa maganar ba."


"Shikenan, Allah yasa muji alkhairi." 


"Toh Amin ya ALLAH."



    ***Kwana biyu da zuwan Muhd duk in da Raihana tasan zata hadu dashi bata zuwa, zaman da take a falo ma ta daina sam ko yaushe tana daki idan akayi mata magana sai tace kawai tafi son zaman hakan ne. Hydar ne ya sanarwa da Abby dalilin zuwan Muhd din da izinin fara magana da Raihanan da yake nema a take Abby yace ya amince masa farin ciki fal zuciyar sa dan dama baya son wata magana ta taso akan Raihanan dan ba zai iya chanja alkawarin da yayi ma kansa ba. Har daki Hydar yazo ya sameta da maganar yace ta zo Muhd din yana falo zasuyi magana. Kamar wadda aka watsawa tafashshen ruwan zafi haka taji maganar. Ranta duk ba dadi ta sake zunbudo Hijab din ta fito babu kowa a falon, juyawa tayi ta nufin komawa Hydar ya kwala mata kira daga waje. Fitowa tayi yace taje falon su Muhd din yana chan yana jiranta. Zumburar baki tayi ba tare da ta bari ya gani ba, ta nufi shashen nasu fuskar ta a turbune tana cika tana batsewa haka kawai take jin wata irin tsanar shi na shigar ta, bata son naci gashi nema yake ta karfi da yaji sai yasa an mata dole. 

  Yana zaune ta shigo ya mike yana karyar da kai murmushi kwance a fuskar sa. 


"Alhamdulillah, tunda na samu Hydar ya fito min dake, wai Raihana gudu na kike ne?"


"A ah." Tace a kufule


"Toh bismillah, zauna magana zamuyi, kinsan fa dan ke nazo garin nan amma kike ta share ni."


"Ni ba share ka nake ba, kawai bana jin dadi ne."


"Wai har yanzu zazzabin be tafi ba?"


"Umm."


"Toh ko zamu koma asibiti."


"Bobbo Sadeeq ne yake bani magani."


"Oh na tuna fa Sadeeq likita ne, toh bari na masa magana ko?"


"AI zan masa da kai na."


"Ok, sannu, zamu iya maganar yanzu? Saboda gobe nake so na koma na bar aiki a gabana."


"Kai na ke ciwo bana son yawan magana."


"Toh, yanzu ya za'a yi?"


"Nima ban sani ba."


Shiru yayi duk sai yaji babu dadin yadda take amsa masa, wanda ta nuna masa clearly bata raayin sa, gashi shi kuma da gasken gaske yake son ta, har yana jin idan ya rasata zai iya shiga babbar matsala. Be zata abun zai zama haka ba, ganin yadda suka saba ta sake dasu sosai ya dauka da ya kawo kokon barar sa zata amsa. Toh ko dai tana da wanda take so ne? Ya tambayi kansa. Toh amma idan akwai ai Hydar zai fada masa. Toh ko dai be mata bane ba?


"Raihana ko dai ban miki bane ba??"


_"Eh."_ tace a zuciyar ta, amma a zahiri sai taki magana kawai ta cigaba da wasa da gefen Hijab dinta.


"Ciwon kan ne?"


"Umm."


"Ok shikenan, ki koma ciki amma ki bar wayarki a kunne dan Allah, zan kiraki."


"Toh." Ta tashi tayi ficewar ta,ba tare da taji komai ba, ko rashin kyautawar ta. Tana zuwa daki ta zare Hijab din tana jan siririn tsaki.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post