Rumbun Qaya Page 39

Rumbun Qaya Page 39

Rumbun Qaya  Page 39

RQ

      Page 39

***Kansa da ya kwanta luf ya kalla a cikin mirror sannan ya dauko designer perfume dinsa ya feshe jikinsa dashi. Kananan kaya ne a jikin sa brown chinos da riga long sleeve wadda ta dan matse shi kad'an. Ya gama saka two set na kayan sa a cikin suitcase dinsa. Turo kofar Kamal yayi ya shigo bayan ya dan kwankwasa. Dawowar sa kenan da ajiye Ya Nabeela da Khadija a gidan Ya Nabeelan ya gama shiryawa shima har ya karbi duk takardun da Daddyn ya bashi su kaiwa Matawallen.


"Kar muyi missing flight muje ko?" Yace daga jikin kofar, 


"Ok." Aryan yace ya dauki wayoyin sa ya makala airdrop a hannun sa sannan ya shiga jan suitcase din tasa ya fito ya rufe kofar. A k'asa ya tarar da Daddy tare da Kamal a tsaye suna magana, ajiye kayan yayi a gefe ya karasa ya durkusa a gaban Daddyn ya gaishe shi


"Har an fito?"


"Eh."


"Ok, Allah ya kiyaye hanya, Kamal ka dai ji me na fada maka ko? Akan wannan maganar."


"Eh Daddy, in sha Allah zamuyi abinda kace."


"Ok, sai kun dawo, Allah ya kiyaye."


"Amin Daddy." Suka hada baki a tare.  Fita sukayi aka saka kayan nasu a booth sannan driver yaja suka nufi airport. Suna zuwa basu samu delay ba suka tashi sai Adamawa-yola. Duk abin nan Aryan be san daddy yasan da maganar shi da Raihana ba, be san Kamal ya gaya masa ba kawai a zuwan zasu je kai sakon Daddyn ne. Maganar da Daddyn yakewa Kamal din kenan dan yace kar su matsa idan yaki amincewa dasu suyi hakuri dan shi babu abinda zai iya.

  Suna sauka a airport Kamal ya kira Lamido yace sun sauka, dama ya sanar dashi zuwan su tunda dama suna communicating, address din ya turo musu saboda lokacin yayi nisa baya kusa, sannan ya kira Raihana ya gaya mata akwai baki zasu zo amma sai yaji wayarta a kashe. Baya so ya kira daddy dan yasan yadda yake ciki dasu ita kuwa dadah wayar ta sai kayi ta kira bata dauka ba bata ma san anayi ba. Tunowa da yayi Muhd yazo kuma yana nan yasa ya kirashi ya sanar dashi baki zasu zo ya sauke su a falon baki kafin ya karaso, sannan ya tura wa Kamal din number Muhd din yace su kirashi idan sun karasa. Kasancewar zuwan su kenan na farko garin yasa suka dan samu delay kafin su isa, dan sai da suka fara neman hotel wanda yafi kusa da unguwar su Raihanan suka ajiye kayan su, suka huta ma sannan kowannen su ya sauya shigar sa zuwa manyan kaya fararen shadda rika da wando. Rigar Aryan irin 3quarter din nan ce me gajeran hannu, haka yake son rigunan sa mafi yawancin lokuta shi kuma kamal nasa tazarce ne har kasa ya fito a magidanci sosai me aure while Aryan kana ganin sa kaga matashin saurayi.


"Dan Allah Aryan don't mess up, kaga dai abinda ya kawo mu, ba wai iya sakon Daddy bane kawai, munzo yada jam'iya ne, kayi abinda ya dace dan Allah."


"Ni ai ban iya komai ba kasan."


"Bance ba, kawai dai nasan halin ka ne, kar kaje kayi ma yarinyar mutane dunkum itama tayi shiru a rasa me magana."


"Wai me ka maida ni ne?"


"Me tsoron mata."


"Hmm, toh ai shikenan."


"Ko na rubuta maka abinda zaka ce idan kaje a waya? Sai ka faki idonta ka dinga karato Mata."


Wata dariya ce ta tasowa Aryan din, gaba daya Kamal ya gama maida shi wani bita chan, shine har sai an rubuta masa abinda zai ce din? Dariyar da ya dade beyi irinta ba ya dinga kyalkyalawa, Kamal ya tsaya yana kallon sa da mamakin sa.


"Allah ka ma maida ni wani iri, yanzu har sai na rubuta min abinda zan ce?" 


Dariya Kamal din yayi shima sai lokacin maganar ta bashi dariya


"Toh ai kaine wallahi, nasan halin ka."


"Hmm, toh muje dai, na matsu na ganta wallahi."


"That's my guy, haka nake son ji, be romantic."


"Muje toh, Mr Romeo."


"Sunana kenan, ko kace laila majnun, yaro ba zaka gane ba ne, aure yayi wallahi."


"Nifa kanin ka ne, don't spoil me."


"Zaka ce na fada maka, muje." Ya dauki wayar sa dake saman gadon suka fito. Uber sukayi har unguwar tasu, sannan suka duba house number din suka tsaya a daidai date din gidan. Number da Lamido ya turawa Kamal ya kira Muhd yana ganin kiran ya fito waje ya same su, da kallo Aryan ya bishi dan be manta fuskar sa ba, sallama yayi musu suka bashi hannu suka gaisa sannan yace su shigo. 


"Wannan gayen shi na gani ranar fa ya kawo ta office."


Ya fadawa Kamal k'asa k'asa. 


"Da alama a gidan yake shima."


"Ok." Yace yayi shiru suka bishi ya bud'e musu kofar falon suka shiga sannan yace yana zuwa. Suna zaune ya dawo da bottle water da cup ya ajiye musu sannan suka sake gaisawa


"Lamidon yana hanya ya kusa karasowa."


"Ok mun gode, Alhaji yana gida?"


"A ah, ya fita dazu."


"Ok, Raihana fa?"


"Tana nan." 


"Ok. Mun gode." Fita yayi ya bar su, kusan mintuna biyu da zuwan su Lamido ya karaso gidan. Sauri ma yayi sosai dan wani aiki yake gashi da nisa yake. Falon ya wuce direct ya same su, dan sun yi waya da Muhd yace sun karaso. Gaisawa sukayi da tambayar aiki tsakanin sa da Kamal sannan suka gaisa da Aryan.


"Abubuwa biyu ne suka kawo mu Sir, na farko sakon me gidanmu ne yace a kawo wa barrister wasu takardu gasu nan."

Ya daga envelope din, 


"Sai kuma magana ta biyu wadda na fara maka maganar a waya, maganar Aryan ce dama, munzo neman izinin a bamu damar ganin Raihana"


"Ok,Masha Allah, abinda ya kamata muyi kenan bayan wannan case din, ina da niyyar ganin family dinmu sun hadu sun dawo kamar yadda muke a dah, yanzu kalli Aryan ni dashi kamar strangers haka ma Abby da Alhajinku. Dole muyi wani abu a matsayin mu na manya, duk abinda ya faru ya faru ne bisa kuskure,kuma bawa baya taba wuce kaddarar sa."


"Naji dadi sosai daka fahimce mu sir, Allah ya bar zumunci, aikin yanzu na mu ne mu karasa shi dan dama mune muka fara shi, daddy bashi da matsala so yake ma Abbyn ya yafe masa laifukansa, ko ya samu ya karasa rayuwar sa cikin kwanciyar hankali."


"Ka bar komai a hannu na, duk da nasan abu ne me matukar wuya amma dole zamuyi nasara a karshe."


"Godiya muke Sir, Allah ya kara girma."


"Yanzu mu shiga gidan ku gaisa da Daadah, sai muci abinci mu fita akwai wani abu da nake son nuna maka."


"Ok sir."


"Muje Aryan." 


"Ok." Suka bi kofar dake cikin falon wadda kai tsaye zata kaika cikin gidan. A main falon suka zauna ya shiga ciki ya kira Dadah yace tazo su gaisa da baki, ta fito tana tambayar su waye. Sai da suka gaishe ta sannan Kamal yayi mata bayanin su, aikuwa nan da nan ta hau murna. Ta tashi tace musu tana zuwa ta nufi dakin Raihana. Fitowar ta kenan daga wanka ta gama busar da dogon gashin kanta da hand dryer tana daure shi waje daya Daadah ta shigo.


"Wai ke lafiyar ki kalou kwana biyun nan baki da walwala bakya sakewa ko yaushe kina daki, bayan mun riga munyi magana nace kiyi addu'a."


"Hamma Muhd ne bana son gani, kuma kinga tunda yana gidan be kamata na dinga fita any how ba, kinsan ni da jin zafi bana son saka kaya masu kauri takura nake wallahi"


"Toh yanzu sai ki tashi ki zura ko doguwar riga ce muje ki gaida baki a falo."


"Baki akayi? Su waye?"


"Idan kika fito zaki gansu."


"Ok, bari na saka doguwar riga."


Ta bud'e closet din ta, ta ciro wata doguwar ta zura ta dora mayafin rigar akanta da ta tufke jelar ta sakko ta bayan ta.


"Ki dan kara fesa turaren ko?"


"Nasa roll on fa Daadah, wannan wanne baki ne haka da har za'a ce nasa turare."


"Zaki gani ai,maza fesa wanchan din chan sannan ki dan murza powder da lipstick."


"Toh, ko dai Hamma Muhd ne yace kizo ki fito masa dani."


"Kinji ki, maza dan Allah ni kin barni tsaye."


Powder ta shafa kad'an tunda ita dama ba ma'abociyar powder bace ba, ta saka lipstick kadan ta murza lips din nata sannan tace


"Yayi?"


"Saura kwalli, bakwa san saka kwalli yaran yanzu, ido firkai firkai "


"Kai Daadah." Ta dauki kwallin ta saka. Kallon ta Daadah tayi 


"Ya kunnen ba dan kunne?"


"Daadah wai zance zani? Nifa dan kunne takura min yake."


"Saka dai, ko kanana ne, mace sai da kwalliya."


Bud'e wajen da take ajiye su tayi ta dauko ta saka.


"Ko ke fa, muje toh." 


Tasa ta gaba suka fito. Dan corridor ne ya raba falon da dakin Raihanan. Dariya take suna magana da Dadah tana tsokanar ta kawai taga mutum a zaune, shine yake facing direct ta inda zasu fito sai Kamal da Lamido da dayar kujerar. Wani irin shock tayi, ta tsaya chak ta kasa karasawa saboda tsabar rud'ewa. Kasa k'asa yake kallonta, kallon da yasa taji kamar na bige mata guiwar ta, taji kamar ta juya saboda tsabar yanayin da ta shiga.


"Raihana, karaso mana kika tsaya anan." Kamal yace yana mata murmushi. Da k'yar ta iya maida masa murmushin ta karaso ta zauna kusa da Daadah ta manne mata kamar zata shige jikinta ta gaishe shi.


"Lafiya lou, ya gida ya kwana biyu?" 


"Lafiya lou sir, ina wuni Sir?" 


"Lafiya lou."  Aryan yace yana kallon centre table din dake gaban sa. Ganin ta gaba daya ya sauya masa lissafi, ga wani irin nauyin Dadah da take wajen kuma yasan kowa yaga irin kallon da yayi mata.


"Mikewa Lamido yayi yace


"Oga muje ko, Raihana ki kai mana abinci falon baki yanzu."


"Ok." Tace ta mike da sauri tayi hanyar kitchen har tana hardewa. 


"Ba yau zaku koma ba amma ko?"


"Eh sai sun ga Abby."


"Ok, shima ya fita ne ya shiga gari, kila sai magriba zai shigo."


"Ok Allah ya dawo dashi lafiya."


"Amin." Ta amsa suka fita ita kuma ta bi Raihana kitchen din da sauri


"A tsaye ta ganta jikin fridge bata taba komai a kitchen din ba, shigowar dadah tasa ta motsa ta kalleta tayi murmushi


"Lallai dole yarinyar nan kiki dan uwanki,."


"Kai Dadah, wai dama sune suka zo amma baki fada min ba, wallahi naji kunya."


"Toh ba gashi kin gani ba, ni kuma naga abinda nake son tabbatarwa."


"Nifa babu wani abu fa, ni ba ruwana wallahi."


"Munafuka,ni zaki wa karya? Ban ga abinda ya faru bane ba? Maza wuce ki kai musu abincin kizo muyi magana."


"Kai shikenan na shiga uku." Tace tana dora kayan akan wani babban tray sannan tasa plate uku da spoons ta dauka ta fita ta bi ta kofar da suka shigo din. Sallama ta fara yi a hankali ya amsa ta shigo kirjinta na faduwa. A tsaye yake dama tun shigowar su bayan su Kamal sun ce masa zasu dan je su dawo. Shigowa tayi tana kallon kasa, saura kad'an ta zubar da kayan hannun ta yayi saurin tarewa yana kokarin saka idanun sa a cikin nata da take ta kokarin boyewa. Sakar masa tray din tayi ya ajiye shi a tsakiyar falon. Juyawa tayi ta nufin barin dakin yayi saurin tare gabanta ya hanata fita.


"In...a...wuni?"


"Ai mun gaisa." Yace idon sa a kanta.


"Gani a gidanku, nazo takanas na baki hakuri akan laifin da nayi miki."


"Ai nace na hakura."


"Ban yarda ba, me yasa kike avoiding idona."


"Ni kawai, ba komai."


"Oya, look at me." 


Dagowa tayi kamar munafuka ta kalle shi, tayi saurin maida kanta k'asa.


"Please ki kalle ni... Yadda nake kallon ki."


"Ba zan iya ba."


"Are you shy?"


Da ka ta amsa da eh ta juyar da kanta. Murmushi yayi me taushi sannan yace


"Wannan gashin ki ne?"


Da sauri ta juyo ta manta ma shaf bata rufe gashin ba ta baya, ta hau tura shi a cikin dan kwalin.


"Rowa ake min? Idan kana neman aure ai ya halatta a barka ka kalla ko sau daya ne."


"Aure?" Tace tana dagowa


"Umm, aure. Ko ba zaki aure ni ba?."


Bagatatan maganar tazo mata, dan haka bata ma san me zata ce ba, kamar wadda ruwa ya cinye haka ta yi tsit ko kwakkwaran motsi ta kasa yi. Tana jin idanun sa akanta. 


"Please, kice wani abu, will you marry me?"


Hadiye yawu tayi da ya tsaya mata, ta daure tace


"A ah."


"Me yasa? Bakya so na?"


"Nima ban sani ba?"


"Ni na sani, amsar kuma yes ce."


"La'ila,haka nace?"


"Action dinki ne yace."


"Karfin hali." Tace a zuciyar ta, haka kawai mutum kai tsaye be ce yana son ta ba, babu wata magana a tsakani sai yace ta aure shi? Haka akeyi dama?"


"Zamuyi maganar a waya, karki kashe wayarki yau i will call you, zo ki zuba min abinci yunwa nake ji, sannan zan samu tea din nan?"


Duk yana tafiya yake maganar ya karasa gaban tray din ya zauna ya barta a tsaye a wajen. Sai da ya kara maimaita abinda yace sannan ta karaso ta durkusa ta dauki plate ta soma zuba masa abincin cike da mamakin gut din sa. Tana ta zubawa yana kallon ta sai da ta cika sosai sannan ta ajiye masa a gaban sa ta saka spoon zata mike ya hanata


"Wannan abincin ina zan kaishi? Ko tare zamu ci?"


"A ah, ni naci abinci."


"Toh ni ina naga cikin da zanci wannan abincin?"


"Gashi nan."


"Rage toh, idan ba haka ba sai dai ki zauna muci tare, ina ci ina kallon beautiful face dinki kinga bansan sanda zanci da yawa ba."


"Na shige su." Tace a ranta, wai me yake damun Aryan din ne yau. Dauka ta sake yi ta rage ta ajiye masa a hankali yace


"Wannan soft hands din naki, i can't wait to touch it again." 


Ai bata san sanda ta mike zumbur ba, tayi hanyar barin dakin da sauri, murmushi yayi ya dan daga muryar sa


"Please ki kawo min tea din."


Karasa ficewa tayi, tana fita ta dafe kirjinta da hannunta da yake wani irin harbawa, sai kuma ta samu kanta da yin murmushi. Salon sa daban ne a komai, maganar sa me sanyi da aji ta dinga yi mata yawo a cikin kunne. Kitchen din ta koma ta dauko kayan dafa shayin dan basa taba rabo dasu ta dora ta tsaya a kitchen din ta jira ya gama ta zubo a kettle din ta dauro cups uku zata fito daga kitchen din Muhd ya shigo ya tsare ta ransa a bace.


"Waye wannan da yazo?" Ya tambaye ta yana kallon kayan hannun ta


"Oga Kamal ne da Aryan, na wajen da nake PPA dina."


"Amma sune har sai sun biyo ki har nan? Me suka zo yi toh?"


"Waje na suka zo? Wajen Hamma Lamido suka zo ai, sun san juna tun da Baban su abokin Abby ne."


"Wanda ya zalunci Abby ya tarwatsa muku rayuwa shine har zaku kawo su cikin gidan nan har kina dafa musu tea zaki kai musu?"


"Hamma, ni menene nawa? Sani fa akayi."


"Still dai, a gabana baban su ya kira Abby ya kuma ce ba zai taba yafe masa ba, amma me zai kawo yaransa gidan nan just two days da maganar, tun farko ma be kamata ku tarbe su ba."


"Wannan dai toh Hamma Lamido zaka fadawa tunda shi yace suzo, ya kuma san abinda yake faruwa da Daddyn yace su zo din."


Ta wuce shi zata fita yayi saurin tare kofar


"Ba sai kinje kin kai masa ba, bani na kai."


"Please Hamma ka matsa na wuce."


"Why? Saboda kina son shi ko me?"


"Zan wuce please."


"Sai kin fara sanar dani amsata, kwana nawa ina binki kina min hanya hanya, akan ki na bar aiki na nazo garin nan, duk baki gani ba, amma wasu daban da suka wulakanta mahaifinki kin saurare su har kina dafa musu shayi, sai ki sanar dani nasan matsayata."


"Me yasa kake irin wannan maganar?"


"Kin fi kowa sani, kinsan komai tunda ke ai ba yarinya bace ba."


"Me yake faruwa ne anan?" Daadah da tazo wucewa ta dan jiyo su ta karaso da sauri


"Ya tare hanyar wai ba zan wuce ba, ni bansan me nayi ba."


"Daadah shayi ne ta dafawa bakin chan, shine nace ta bani na kai musu da kai na ba sai taje ba."


"Me yasa ba zan je ba? Me yasa zai hanani zuwa?"


"Saboda gaba nake dake." 

  Yace cikin bacin rai da kishi dan gaba daya ya kasa controling kishin sa, dan ya dan saurari wasu maganganun da yaji Aryan din yanayi, abinda ya tunzura shi kenan ya biyo ta.


"Bashi ya mika musu toh ke Raihana, bashi kiyi hakuri."


Akan deep freezer din kitchen din ta dire masa, ta fice daga kitchen din da sauri. Bin ta Daadah tayi shima ya fice daga kitchen din ba tare da ya dauki kayan ba, ya nufi falon da Aryan din yake ciki.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post