Rumbun Qaya Page 40
Health College

Rumbun Qaya Page 40

Rumbun Qaya  Page 40

RQ

      Page 40

***Babu sallama ba komai ya fada ciki,fuskar sa a tamke. Dagowa Aryan yayi jin an shigo ganin wanda ya shigo yasa shi cigaba da abinda yake ba tare da ya bada wani attention din sa ba, tunda shi sam guy din be masa ba dama tun farko.


"Malam magana nazo muyi." Yace ganin Aryan din ya share shi 


"Pardon?" Ya fada yana tsayawa da danna wayar da yake yi ya kalle shi a kaikaice


"Naji duk abinda kace da duk take taken ka ma, Raihana tawa ce ni zan aureta, tunda gida be koshi ba, ba za'a bawa dawa ba." 


Kamar be ji abinda yace ba, dan idan ya motsa sanadin maganar Muhd din toh wajen nan ya motsa. wani kululun abu ne ya tsayawa Muhd din na wulakancin Aryan din,.


"Lallai ma, Malam magana fa nake maka."


"Oh haba? Ban ji abinda kace ba ko zaka iya maimaitawa."


"In maimaita?"


"Yes please, ina jinka." Ya zare airdrop din kunnen sa ya juyo yana bashi attention dinsa


"Wasa kake wallahi,na maimaita kamar bani da abun yi? Na tabbatar kaji abinda nace kawai dai ka nuna..."


"Hello baku kusa ba?" Ya d'aga wayar sa kamar ba magana Muhd din yake masa ba, 


"Ok, ni zan wuce ma hadu a chan."


"No sai mu dawo ko bayan magriba ne, ko ka dawo kai kadai."


"Ok." Ya katse wayar yana mikewa, ya dan kalli gefen da Muhd din yake a tsaye yace


"Sai anjima Malam, ka dan shiga da kayan ciki."


Ya fice ya barshi da tarin bakin ciki, tunda yake ba'a taba ci masa mutunci irin yadda Aryan din yayi masa ba. Rasa me ma zai yi yayi, ya dinga zagaye a dakin yana jin kamar ya bishi ya shako shi ko dai yayi masa wani abun da zai ji haushi sosai. Kafa yasa ya daki kujerar dake kusa dashi ya juya ya koma cikin gidan.


   Kuka Raihana ta fashewa da Dadah, kukan bakin cikin abinda yayi mata. Iyakar kureta yayi ya kaita karshe. Ba haka ake ba, bata taba jin inda ake soyayya dole ba, tunda ta nuna masa bata so me yasa ba zai hakura ba, har zai wani zo ya sakata a gaba kamar wani ubanta. Hakan da yayi ya kara mata tsana da haushin shi a zuciyar ta.


"Kiyi shiru haka na, kinsan zuciyar yan maza da kishi, kishi ne yake dawainiya dashi."


"Toh fisabillillah amma ya dace ya saka ni a gaba yana titsiye ni? Naga ai ba'a dole ko?"


"Ba'a yi, kiyi masa uzuri da ciwo kana son mutum yana shareka sai kaga wani yazo an kula shi, ko waye kuma dole yaji haushi, kawai kowa da yadda yake nuna fushin shi ne akan kishi, ni tausayi ma yake ban, son masu wani akwai wahala wallahi, be yi sa'a ba sam."


"Baki ga yadda yake min fada ba Dadah?"


"Na gani, menene toh? Hakuri zakiyi."


Wasu hawayen ne suka sake biyo fuskar ta, har ga Allah taso kaiwa Aryan tea din nan, duk da tana jin nauyi da kunyar sa, tasan a yadda Muhd din yake cikin fushi da k'yar idan ba zuwa zai ya gaggaya masa magana, tasan kuma fushin Aryan zai yi yin zuciya ya tafi ma gaba daya. Dalilin kukan ta kenan, da k'yar Dadah bata baki tayi shiru sannan taje ta wanko fuskarta ta dawo dakin ta bud'e bedside drawer dinta ta ciro wayarta ta kunna ta, fita Dadan tayi ta ja mata kofar. Wani tunani ne yazo mata ta tashi ta fita, ta shiga kitchen din sai taga kayan tea din a ajiye akan freezer din, babu alamun an taba su daga yadda ta ajiye su. Falon chan ta nufa tayi sallama jin shiru baa amsa ba yasa ta tura kofar ta shiga, baya nan da dukkan alamu ma tafiya tayi, da sauri ta juya ta koma cikin gidan tana kwalawa Dadah kira. Dakin ta, ta shiga ta samu Hamma Muhd din a zaune idonsa ya yi ja sosai suna magana da Dadah, juyawa tayi da sauri ta koma dakin ta, ta shiga number sa tayi dialing. Alwala zai yi yana nannade hannun rigar sa kenan wayar sa tayi kara, daga in da yake tsaye ya leka wayar yaga me kiran. Ganin itace ya sakashi tsayawa da abinda yake yi, ya mika hannu ya dauki wayar sannan ya zauna a gefen gadon ya d'aga.


“Hello.”


“Hi, ka tafi?”


“Yes,na tafi. Baki kawo min tea din ba.” 


“Nazo naga baka nan.”


“Kinyi latti, amma zan dawo anjima. Ki ajiye min idan nazo sai ki bani nasha.”


“Ok.” Tace tana sauke ajiyar zuciya jin muryar sa tar alamun babu abinda ya faru tsakanin sa da Muhd, amma kuma me yasa ya tafi haka kawai ba sallama?


“Don’t think hard, wani abu ne urgent ya taso min Shiyasa ana tafi.”


Yace jin tayi shiru yasan kuma dole tunanin da take kenan, idan ba haka ba ma yasan da wuya ta kirashi.


“Sai anjima tom, sai ka dawo.” 


“Ok see you then.” Ya ajiye wayar, dan sosa kansa yayi yana son figuring abun baki daya, dama tun farkon ganin muhd yasan son raihana yake, ya kuma sakè tabbatarwa yau, sai dai be sani ba, mutual relationship ne ko one side? Sannan menene stage din da suke kai, baya son yayi abu da ka Shiyasa be biye masa ba duk da yayi masifar mata masa rai amma ya danne dan ba a irin sa yake bata energy da yawon bakin sa ba, ko Adam sai yayi masa abu sau nawa amma sai yaga damar kallon sa ma, ko ya bashi amsar da zata dade tana sosa masa rai.


“I need to find out ko ma menene.”


   Tafiyar da Aryan yayi yasa Kamal ma yace zai wuce kawai zasu dawo idan Abbyn ya dawo da magriba, sauke shi Lamido yayi a kofar hotel din sannan ya juya ya tafi gida. Knocking yayi a kofar Aryan yazo ya bude dan yasan shine , matsa masa yayi ya shiga yana kallon shi daga shi sai gajeran wando babu ko riga a jikin sa, shiryawa yake Kamal din ya dawo Shiyasa.


“Fita zakayi ne?” Yace yana kare masa kallo


“A ah, ruwa na dan watsa kaji garin zafi da na dawo alamun zaa iya yin ruwa.”


“Eh akwai hadari da alama.”


“Kun dade, ina kuka yi ne?”


“Aikin mu ne, baa ji.”


“Oh okh.” 


“Me yasa ka dawo wai? Nayi mamaki da kace zaka dawo.”


“Aikin mu ne, baa ji.” Ya kwaikwayi same amsar da Kamal din ya bashi ya fada.


“Haha, kana da matsala. Please fada min menene?”


“Gayen nan ne, wanda ka kira shi da muka karasa gidan, yazo yana faffada min maganganu, ban ma dai saurare shi ba, ganin zai bata min rai ya tunzura ni yasa na taho kawai.”


“Muhd, munyi maganar sa da Lamido. Cousin dinsu ne kuma saboda raihana yazo gidan takanas daga kano. Infact har Abby ma yasan da maganar kuma yana supporting dinsa sosai da hydar ma.”


“I know, dole kayi mentioning hydar a karshe. It’s like kamar yafi kowa daukar zafi akai, da ni ma yake fushin naga alama.”


“Eh gaskia. Shima irin ka ne da Zafin zuciya sannan abinda ya faru a office da kana ma raihana fada da Ya gani ya sake lalata komai.”


“Yes na tuna, har yana cewa sai nayi nadamar abinda nayi mata. Amma ai na bata hakuri ta hakura ma. Shi menene Nasa?”


“Gani yake baka dace da ita ba ko? Kamar zaka wahalar musu da kanwa.”


“Hmm. Zan bashi mamaki. Shi zan fara kira nace yazo ya rakamu asibiti idan nayi ma kanwar tasa ciki.”


“Hahaha! Kai ko? Baka fa da m wallahi aryan.”


“Toh Allah ya zafafa da yawa. Ni kuma da gaske nake ba wasa nake ba, yadda mukayi ta rigima a kanta da yarinta shi yake so mu dora, ya manta ko da din nike winning, cox ni take zaba akanshi.”


“Match made in heaven kenan.”


“I’m serious, ni da shi ne.”


“Ba kara? Soon to be in-law dinka ne fa.”


“Lamido ba? Da sadeeq amma hydar sam. Su karata shi da dan iskan yaron chan da Ya gama gaggaya min magana.”


“Yanzu dai haushin Muhd takwaran ka, zaka huce shi akan hydar.”


“Duk su karata.”


“Yanzu duk ba wannan ba, yadda zaa shawo kan Abby ya amince kawai ake nema, Lamido yace kafin mu koma anjima zai fara masa maganar, idan yaso sai muje masa muma da maganar.”


“Ok. Go ahead dinsa kawai nake nema. Shi yasa nake bin komai a sannu saboda hakan shine daidai.”


“In sha Allahu komai zai zama normal. Ka fara babbar magana ai dole ayi abinda Ya dace.”


“Kar ayi ma.” Yace yana murmushi. Shi kansa maganar tashi ta bashi dariya.


*****Fada sosai Abby yake wa Lamido, ta in da yake shiga bata nan yake fita ba. Tun da ya same shi da maganar zuwan nasu da kuma maganar raihana ya saka masa full stop dan baya son zancen ma. Da kyar aka samu yayi shiru da fadan ya zauna yana huci.


“Kira min ita maza, idan bata da hankali ni Ina dashi. Idan kuma zaku nuna min iyakata ne toh.” 


“Ba haka bane Abby. Suna son junan su ne wallahi, mu kuma farin cikin ta muke nema.”


“Kana nufin na dauke ta na kaita gidan nan? Kana da hankali kuwa Lamido? Ko dai girman ne kawai na hankali!?”


“A ah, Allah ya huci zuciyar ka. Kayi hakuri.”


“Sa waya ka kirata tazo maza ta same ni, akan wannan maganar zan yi mummunan sabawa kowa wallahi, har kai din kuwa.”


“Ayi hakuri Abby. Kanwata Kizo Abby na son ganin ki.” 


“Tunda ita shashasha ce bata da hankali. Mutumin da ya wulakanta ku, Ya kore ku daga gida Ya kwace muku komai , shine dan rashin hankali zaka dauki kanwar ka, ka kaita gidan tayi rayuwar aure. Lallai kuwa sannun ka.”


Shigowa tayi kamar Munafuka ta zauna daga bakin kofar ta gaida abbyn ya amsa a ciki ciki sannan yace 


“So nake ki fitar da miji, idan kuma babu kowa ni zan zaba miki mijin. Sati daya kuma yayi yawa na daura miki aure. Daki saka ni bacin rai gwara Kiyi na dan lokaci ne.”


“Abby dan Allah kayi hakuri,wallahi ni ba wanda nake so.”


“Karya ne, ba yaron nan Aryan kike so ba? Kin dauka ban sani ba? Bayan ni dake munyi magana na gaya miki bana so amma baki ji ba, shine kika cigaba da kulashi har yayan ki yana da bakin zuwa yayi min maganar bayan duk abinda Ya faru dashi ne akayi komai.”


“Abby dan Allah kayi hakuri.” Ta fada muryar ta na rawa dan har ta soma kuka.


“Naji, wa kike so toh?”


“Ba kowa.”


“Har Aryan din?”


Shiru tayi, ya kara maimaitawa Amma batayi magana ba sai kuka da take yi 


“Kira min Muhd maza yazo yanzu.”


Tashi yayj zai fita abbyn yace


“Baka da number shi ne? Ka kirashi mana.”


Dawowa yayi ya zauna ya kira muhd din yace yazo. Ko minti daya baa yi ba sai gashi. Ya durkusa ya gaida Abbyn


“Kana son raihana?”


“Naam?” Ya d’ago da sauri


“Da gaske kake kana sonta zaka aurerà kuma?”


“Eh Abby.”


“Shikenan, zan kira Alhaji Kabir din muyi magana, na baka raihana nan da sati daya zaa daura muku aure.”




*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*



*ZAFAFA BIYAR BACTH A*



1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*



2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*



3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*



1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*



_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________*



*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*



_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*



_Duk biyar 1500_


*______________________________*



*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_





*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma



_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261

TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post