Rumbun Qaya Page 41

Rumbun Qaya Page 41

Rumbun Qaya  Page 41

RQ

     Page 41

Wani irin k'amewa Lamido yayi saboda yadda maganar ta bige shi, aure kuma? Aure a sati daya? Juyawa yayi da sauri ya kalli wajen da Raihanan take zaune, ta chusa kanta a tsakanin kafafunta, tana kuka sosai duk da ba'a jin sautin kukan nata. Sake maida da kallon sa kan Abbyn yayi sai ya hangi tsananin tashin hankali da damuwa cike a idon sa. Yanayin sa ya nuna irin na wanda yake tsoron wani abu wanda ya sha matukar wahalar sa. Sauke kansa kasa yayi dan be kuma san me zai ce ba.


"Ku tashi ku bani waje." Yace yana zama cikin kujerun falon. Muhd ne ya fara ficewa da sauri, sai Lamido da ya kama hannun Raihana ya mikar da ita dan ko motsi ta kasa yi. Suka fita a tare Abbyn ya bishi da kallo. Me yasa soyayya zatayi masa haka? Me yasa a duk fadin duniyan nan zata rasa wanda zata so sai dan gidan mutumin da yake jin baya burin zama inuwa daya dashi balle har wani abu ya hada su. Mutumin da ya ruguza masa rayuwa ya lalata komai. Ya gwammace yayi mata auren yasan dole dole zata hakura ta zauna wataran tunda shi ma Muhd din bashi da makusa ko kad'an, sannan a kalla shi na gida ne. Duk da a k'asan zuciyar sa yana cike ds tausayin ta amma kuma ba zai bari ta cutar da kanta ba, dama musulunci shi ya bawa damar zaba mata miji a yanzu, dan haka zai yi iyakar kokarin sa wajen ganin be barta ta cutar da kanta ba.

  Dadah na zaune suka shigo, ta mike da sauri dan dama tunda taji kiran nan tasan na lafiya ba.


"Menene ya faru?"


"Hmm, ita da Abby ne."


"Laifin me tayi masa?"


"Maganar Aryan ce dai, yace ba zai bashi ba, har ma ya sanar da Muhd ya shirya sati me zuwa za'a daura musu hannu."


Salati Daadah ta rakfa tana rike Raihanan da take kuka wiwi.


"Anya wannan hukuncin kuwa? Anya Ibrahim?"


"Sai hakuri, nasan ba lallai ya sakko ba tunda yayi wannan hawan."


"Kowa yasan ba'a kyauta masa ba, kuma yana da duk right din da zai yi fushi, amma ya za'a yi da hukuncin Allah? Rabo ba kisa yake fa, wallahi har lahira."


"Bari na je masallaci, naji ana kiran sallah."


Ya juya ya fita. Rike da hannun Raihanan suka wuce dakin ta, tana zuwa ta kwanta a gadon ruf sa ciki tana cigaba da gursheken kuka.


"Wallahi Daadah bana son shi, wallahi bana son shi ko kad'an zan mutu idan aka daura min aure dashi."


"Rufe bakin ki, kiyi shiru. Zan tursasa Lamido lallai ya hanashi abinda yake niyya, idan kuma yaki ni nasan ta in da Zan bullo masa, itama Maimunan zan kirata zan ce ta bawa Muhd hakuri, yayi hakuri dan ba'a aure haka, ba zai yiwu ba."


"Dan Allah dadah karki bari yayi min auren dole, wallahi bana son shi."


"Daina kukan toh, ba sati daya yace ba? Barni da su."


Share hawayen take kokarin yi amma sam yaki tsayawa, da ta share sai wani ya hau zubowa. 


***Ana kiran sallar magriba suka shigo unguwar, basu karaso gidan ba suka tsaya a masallacin kan layin suka fara yin sallah sannan suka nufi gidan. A kofar gidan suka tsaya kamal ya kira Lamido yace masa sun karaso Amma be daga ba, suna nan a tsaye sai gasu sun dawo daga masjid din tare da Abby, da Babbo Sadeeq da shima dawowar sa kenan ya tsaya sallar. Abby be lura dasu ba ya shige gidan sai Lamido da Sadeeq suka karaso wajen su, suka gaisa da Sadeeq din sannan Lamido yace su shigo gidan. Duk da yana cike da tsoro da taraddadin irin karbar da Abbyn zai musu amma kuma ba zai ce kar su shigo ba, dole dai zasu shigo din su ganshi tunda suna tafe da sakon Daddyn.

   Ya zauna kenan yana son kiran mijin Adda Maimunan sai gasu sun shigo da sallama Lamidon na jagorantar su, suka zube a tsakiyar falon nasa cikin girmamawa suka gaishe shi. Ajiye wayar yayi ya fasa kiran ya amsa gaisuwar tasu babu yabo babu fallasa. Kamal ne ya dan sake russunawa ya mika masa envelope din da Daddyn ya basu sannan yace


"Daddy ne yace mu kawo maka wannan sakon, jibi zasu tashi idan ya dawo in sha Allahu zaizo takanas har gida kuyi magana."


"Menene a ciki?"


"Sako ne dai, yace idan Ka duba zaka gani."


"Ok, karbi Lamido, ka mika min shi cikin daki ka saka shi kasan drawer."


"Ko na bud'e maka ka gani?"


"A ah, kayi abinda nace kawai."


"Ok." Ya tashi ya shiga ya kai masa ya saka a inda yace sannan ya dawo. Still dai Kamal din ne ya sake yin magana akan abinda ya kawo su na biyu, Abbyn na jinsa sarai sai da ya gama sannan yace


"Sai dai kuyi hakuri Raihanan dai na riga nayi mata miji, sati daya ya rage a daura auren. Sai kuma me yake tafe daku?"


Shiru sukayi gaba daya tamkar ruwa ya cinye su, Aryan da ya rasa a wacce duniyar yake saboda yadda yaji tana juyawa dashi ga wani irin abu da ya zo nan da nan ya tokare masa makoshi. Zufa ce ta shiga karyo masa ta ko ina da wani irin faduwar gaba.


"Akwai wani abun ne kuma?"


"Babu komai Alhaji, mun gode Allah ya kara girma."


"Amin, na shiga ciki idan kun gama ku gaida gida." Ya mike yayi shigewar sa ya bar su a wajen. 


"Muje falon chan muyi magana Kamal." Lamido yace bayan tashin Abbyn. Aryan ne ya fara mikewa ya fice da sauri, sai suka bi bayan sa suma. Zuciyar sa ce tayi zafin gaske, irin wadda bata taba yi masa ba, ga wani irin ciwo da take masa irin wanda yake fama a duk lokacin da ya tuna ya rasa abu me muhimmanci a rayuwar sa. Niyyar sa kawai ya fice daga gidan, ya bar garin ma baki daya a daren dan a yadda yake ji komai zai iya faruwa. Amma sai Kamal yayi saurin tare shi, yace su tsaya suyi maganar dan Allah. Be iya bud'e baki ya amsa ba, sai bin su kawai da yayi ciki wanda ya tabbatar sai dai ya zauna kawai ba dan zai gane abinda suke cewa ba. A tsaye ya tsaya bayan duk sun zauna Lamido ya kira Sadeeq a waya yace ya zo sannan yace da Aryan din ya zauna dan Allah. Be magana ba yaje ya zauna ya dafe kansa kawai. Sadeeq din ne ya shigo ya zauna a gefen Kamal yana kallon Lamidon


"Me yake faruwa ne? Yanzu nake samun labari a cikin gida wajen Daadah, ga Raihana chan kuka kawai take wallahi."


Da sauri Aryan ya dago, dan be yi tunani ace masa tana kuka ba, ya dauka ma abinda ya faru da izinin ta ne, ko kuma da yardar ta. Kenan auren dole zai mata? Saboda kawai laifin da Shi bashi ne ya aikata ba, idan aka duba ma yana cikin wanda abun ya shafa.


"Wallahi Sadeeq issue din ne babba ne, kasan haka kawai Abby baya fushi kuma ko yayi ma baya lasting, amma akan maganar nan wallahi baka ga ni kaina yadda yayi min kacha-kacha ba, sannan ya yanke hukuncin nan."


"Subhanallah, abun yayi tsamari gaskiya, ni wallahi kasan rashin zaman da banayi ba komai nake sani ba, amma yanzu ya za'a yi? Baka ganin mu sake samun sa dai da maganar"


"A yanzu dai ba zai yarda ba wallahi."


"Ina ganin mu bari zuwa da safe,ko?" Kamal yace


"Eh hakan dole za'a yi, amma please Aryan ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah komai zai wuce, shaanin aure dole ne sai anyi irin wannan."


"No ba komai." Yace kamar har zuciyar sa haka ne, nan kuwa abinda yake ji yayi tsanani sosai.


"Oga bari mu wuce, zamuyi waya kawai."


A tare suka tashi zasu fita, Lamido ya tsayar dasu ta hanyar kiran Aryan.


"Please ina zuwa." 


Tsayawa sukayi, ya bi kofar cikin gidan ya shiga ciki, ya wuce kai tsaye dakin Raihana. Har a sannan bata daina kuka ba, ita kadai tasan abinda take ji idan har ta tuna aure za'a mata auren ma na dole, da k'yar tayo alwala tayi sallar magriba shine take zaune har lokacin akan sallamar tana cigaba da kukan bakin ciki. Tsayawa yayi daga kofar yana kallon ta, kallo me cike da tausayawa, baya son duk abinda zai bata mata rai, yana jin kamar idan suka sakata kuka be rike kalaman karshe da Ammy ta fada masa ba, akan yan uwansa da kula dasu, shiyasa be taba bari tayi kuka dashi ba, ba ya jin kuma zai iya zuba ido ta cigaba da zubar da hawayen. 


"Taso." Yace mata, sai a lokacin tasan yana tsaye a wajen. Dagowa tayi tana kallon sa yayi mata alamar ta tashi, ta mike da k'yar, ta karaso wajen da yake tsaye.


"Please ki daina kukan nan kinji?"


"Hamma Abby baya so na."


"Yana sanki mana, duk abinda yake yi a yanzu saboda son naki ne."


"Toh ni bana son Hamma Muhd, wallahi bana son shi."


"Aryan kike so?"


Da sauri ta daga mishi kanta


"Toh kiyi shiru ki daina kukan nan kar kanki yayi ciwo." Goge hawayen tayi da bayan tafin hannun ta, sannan yace


"Zo muje."


Bin sa tayi har waje, ya bud'e motar sa yace mata ta zauna sannan ya koma ciki ya samu Kamal da Sadeeq suna magana Aryan kuma yana tsaye kawai hannayen sa zube a cikin aljihun sa. Kana gani kasan yana cikin yanayi amma kuma he calmness dinsa yana nan a tattare dashi. Kiran sa Lamido yayi yace Kamal ya jirasu dan Allah, yace toh suka fito tare ya kaishi har gaban motar tashi sannan ya bud'e masa mazaunin driver. Kamshin turaren sa ne ya fara sanar da ita yazo wajen ta dago da sauri sai a lokacin ya gane abinda Lamidon yake nufi. Motar ya shiga ya zauna ya karkato da jikin sa yana facing dinta sosai. Wani irin chakudadden yanayi ya shiga zagayawa a tsakanin su, kukan ta na fita kasa kasa, kukan da ya sake haddasa masa wani irin yanayi a zuciya da gangar jikin sa. Hannun sa ya mika ya kamo nata ya sakasu a cikin nasa, kukan ta ne ya tsaya chak kamar an dauke ruwa. Motsa bakin sa yayi a hankali cikin muryar sa da tayi wani irin dashewa yace


"Please ki daina kuka, kina hurting dina, my heart is burning, tana min ciwo kamar zata fado."


Bata cigaba da kukan ba sai ajiyar zuciya da take saki a hankali har sai da ta daina gaba daya, har lokacin hannun ta na cikin nasa yana kallon ta. sai da ya tabbatar da tayi shiru gaaba daya sannan yace


"Bansan me yasa Abby baya so na ba, banyi laifin komai wallahi, I'm innocent, dan Allah yayi hakuri, I can't take it, ba zan iya jure rasa ki ba, I love you raihana, I love you so much ban taba son wata ba sai ke. Please karki bari na rasaki."


Kuka tasa masa, abinda take ta so da burin ji daga bakin sa, yace yana sonta, sai gashi ya fada a yanayin da ita kanta bata san me zatayi ba. 


"Oh Ya Allah." Ya dan daki steering motar, hannun sa ya bude kamar zai jawota jikinsa sai kuma ya dunkule hannun yana girgiza kansa.


"Kina so nayi hugging dinki? Please ki daina kukan nan bana son nayi abinda ya sabawa Shari'a, please ki daina dan Allah."


"Na daina."


"Yawwa, promise me ba zaki kara kukan nan ba."


"Bazan kara ba."


"Good girl, mu barwa Allah komai."


"Are you ok?" Tace jin yadda yake numfashi har yana making sound 


"I can't say, already ina da tabo a heart dina raihana, my heart is so weak right now wanda bansan me zai faru ba, I don't know ko zan iya."


"Zaka iya." Tace tana goge kwallar da ta zubo mata


"I went through alot, may be time din da heart din zata daina bugawa ne yayi, I don't know."


"Ka daina fadan hakan dan Allah."


"Tom na daina, kema kiyi min alkawarin ba zaki kara kuka ba, idan kika cigaba da kuka zuciya ta zata cigaba da zama weak."


"Ba zan sake ba."


"Thank you so much."


"Komawa zakayi?"


"In sha Allah, gobe zan koma."


"Dan Allah karka tafi."


Kallon ta yayi, ba zai iya zama ba bayan yasan chanja raayin Abbyn ba abu ne me sauki ba. 


"Ki shiga gida toh, i will call you idan na koma."


Bude gate din akayi, muhd ne ya leko kamar me neman wani abu, wani tunani ne ya fadowa Aryan, ya kalle ta da sauri


"Don't tell me wannan sullutun Abby zai bawa."


"Umm, shine."


"Me? No ina ba zai yiwu ba, wannan din?"


"Eh Hamma muhd ne."


"I think bani da wani option da ya wuce na sace ki kawai, da dai a bawa wannan dan iskan yaron wallahi gwara na gudu dake."


"Dan Allah kayi hakuri."


"BA zaki bini ba?"


"A ah, kawai dai."


"Wasa nake miki, ki shiga gida kar Abby yayi fada."


"Ok tom, sai da safe."


"Sai da safe." 


Yana kallon ta har ta shige cikin gidan, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ciro wayar sa ya kira Kamal yace su tafi.*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261
TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post