Rumbun Qaya Page 42

Rumbun Qaya Page 42

Rumbun Qaya  Page 42

RQ

     42

****Tunda suka koma hotel din Aryan be ce komai akan abinda ya faru ba, kashe wayar sa kawai yayi ya kwanta akan sofa bayan ya rage kayan jikin sa. Duk maganar da sukayi da Raihana kawai karfin hali ne shi kadai yasin abinda yake Ji. Dole yaje yaga Dr Mahfouz gobe in sha Allah. 


"Aryan?"


Kamal ya kirashi ganin ya juya bayansa gashi bashi da tabbacin idan bacci yake ko idon sa biyu. Be amsa ba duk da yaji amma ba zai iya amsawa ba dan baya son maganar kawai.


"Aryan kana jina? Please Let's talk mana."


"Bana son maganar please."


"Na sani, amma yana da muhimmanci muyi maganar."


"Kasan me? Babu amfanin maganar, ya riga yayi making mind dinsa. A duk abinda yake faruwar nan nine nake daukar blaim din, ni ke biyan dukkan mistakes din su, no one cares about yadda nake ji."


"Ba haka bane ba, duk abinda ya faru ya faru ne for a reason, don't let abinda ya faru yanzu yayi weighing naka down."


"It's ok, ba komai kawai. Goodnight."


"Shit, you are hurting your self, kasan condition naka so be kamata kana rike abu haka a ranka ba."


Mikewa yayi kawai dan maganar Kamal din sake tunzura zuciyar sa take,ya isa wajen kayan sa ya ciro farar jallabiya ya zura, ya fice kawai daga dakin. Kasa ya sauka ya zagaya chan baya ya zauna a wata kujera yana kallon yanayin wajen. Daga sama ta hango sakkowar sa, ta biyo shi bayan da dan saurin ta. Ta zauna a gefen sa tana satar kallon fuskar sa da take a dinke. 


"Hi." 


Kallon ta yayi kad'an, ya dauke kansa da sauri yana dan matsawa dan sake bayar da tazara a tsakanin su.


"Handsome saurayi kamar ka, be chanchanci zama anan ba, all alone."


"Who are you?" Ya tambaya yana tsare ta da ido


"AYUSH, and you?"


"Please kije bana son doguwar magana."


"Menene matsalar ka? Zan iya taimaka maka."


Wani banzan kallo yayi mata ya sake juyar da kansa daga gareta. Tasowa tayi ta dawo dayan side din inda face dinsa take kallo ta tallafi fuskar ta tana kallon sa. Mikewa yayi kawai ya soma barin wajen, ta mike itama da sauri tabi bayan sa, suka haura saman a tare har kofar room dinsu. Ganin tana biye dashi yasa shi jan tsaki ya tsaya ya juyo yana facing dinta


"Karki kuskura ki biyo bayana wallahi."


"Toh ka saurare ni mana, ko ka bani number ka muyi magana."


"Ba zan iya ba." Ya murd'a kofar ya shiga tayi kamar zata bi bayan sa yayi saurin banging kofar yana jan tsaki. Kamal da yake zaune yana waya ya bishi da kallo.


"Kai da wa kuma?"


"Wata stupid yarinya ce, ta dauka ma kowa irin ta ne. Nonsense."


"Babe zamuyi magana."


Ya katse wayar yana kallon shi ya zauna ya dafe kansa da hannu biyu


"Da zan iya barin garin nan a yanzu da na bari wallahi."


"But ba shine solution ba, ba zai yiwu mu kyale Barr yayi amfani da ego dinsa ya cutar da ku ba, abinda mukayi magana da Sadeeq da Lamido kenan,duk abinda ma zamuyi sai munyi kawai."


"I don't think it will work, so ba zan takura masa ba, yar sa ce yana da right din yayi abinda yaga dama."


"Kai kuma fa?"


"Waye ya damu dani kuma?"


"Ni mana,Daddy ,Ya Nabee.


"Ok."


"Ok?"


"Me zance toh?"


"Shikenan kawai."


"Zan kwanta, but please karka yi min magana."


"Naji, ba zan ba, sai da safe."


***Akan hannun ta, tayi bacci rike da waya tana jiran kiran sa, da asubah ta farka da sauri tana duba wayar amma sai taga be kira ba. Tashi tayi a sanyaye ta shiga toilet ta yo alwala ta fito, ta fara raka'atanil fajr sannan tayi sallar asubah ta roki Allah ya sassautar da zuciyar Abbyn nata. Tana zaune a wajen har gari yayi haske, ta tashi ta hau saman gadon ta kwanta lamo ta dora kanta akan pillow. Wajen bakwai da rabi Hydar yayi mata knocking, ta tashi ta bud'e masa ya kalli rinannun idanun ta wanda suka jeme saboda kuka, yi yayi kamar be gani ba yace


"Kizo Muhd zai tafi."


"Na'am?"


"Eh, kizo kuyi sallama kafin ya dawo."


"Kayi hakuri Hamma Hydar, amma ba zan iya zuwa ba." Ta juya ta koma ta kwanta ta barshi a tsaye baki hangame cikin tsananin mamakin ta, tunda suke bata taba masa musu ba, ko ya sakata abu taki yi sai yau, kasa magana yayi ya juya ya ja mata kofar kawai dan idan ma yayi maganar bata da amfani. Tunda har ta furta masa ba zata ba, toh ba zata din ba kuwa.

  Muhd na tsaye yana jiran fitowar ta sai ga Hydar din ya fito shi kadai


"Muje na sauke ka, bata tashi ba."


"Oh ok, dadah ni zan wuce."


Ya juya wajen Daadah da take zaune a falon, 


"Allah ya tsare, ya kiyaye hanya." Tace kawai dan a cike take dasu dukkan su, shiyasa ma taki sakar musu fuska musamman Hydar da ya zake sosai akan maganar. Fita sukayi sai ta tashi ta shiga ciki, idan sun san wata ai basu san wata ba, Muhd jikan tane kamar Raihanan, amma tunda tace bata so sai a bata zabin ta tunda dai bashi da wani aibu ya ma fi Muhd din nagarta ta kowacce fuska.


   ***Akan hanyar su ta zuwa airport Kamal sukayi waya da Lamido, Aryan dai be san me suke tattaunawa ba shi dai kawai burin sa ya ganshi a Kano,kunnen sa a toshe yake ma gaba daya yana sauraron karatun alkurani,sai da suka shiga ciki sannan ya kashe. Suna zuwa basu dade ba suka tashi, ya sake maida karatun ya kwantar da kansa a jikin kujerar har suka iso. Sauri sauri ta dinga yi tun a cikin jirgin ta ganshi amma yana dan nesa da ita, shiyasa da aka fito tayi sauri ta biyo su ta same su a wajen shiga mota. Shi Aryan be gane ta ba ma kwata-kwata suka gaisa da su ya fada motar sai Kamal ne ya tsaya ya saurare ta, ya bata abinda ta tambaya sannan shima ya shiga motar.


"Kayi kasuwa mutumi na." Yace yana dariya


"Kana da matsala."


"I'm serious, yarinyar nan kai ta biyo, har na bata number dinka ma, irin yaran nan ne ajeboters wanda basu san wani abu wahala ba ko kunya, idan sun ga namiji yayi musu kawai suna magana ne."


"Lallai aiki ya gansu, Allah ya sauwake."


"Amin, kaga shikenan ka samu replacement."


"She's too cheap."


"Wa din?" 


"Ita yarinyar." 


"Gashi nan kuwa tana kiran ka."


Kallon wayar yayi da sauri sai ya tuna a kashe take ma tun jiya, kunnawa yayi ya kira Dr Mahfouz yace zai shigo yanzu. A asibitin aka ajiye shi, Kamal yace zai shigo yace a ah ya wuce ciki shi kuma ya wuce gidan Ya Nabeela.


***Yau kwanan Daddy uku da tafiya, washegarin da suka dawo shi kuma ya tafi, basu fada masa abinda ya faru a chan din ba sun dai ce masa ya karbi sakon. Ya dan ji dadi yana kuma fatan ya duba sakon a lokacin da ya dace.

   Suna zaune a office din Aryan din Kamal na shigar da wasu ayyuka a cikin computer Aryan kuma yana signing wasu takardu Zainab ta kwankwasa ta shigo rike da takardu ta ajiye su, tun da suka dawo daga yolan aiki kawai Aryan yake yana so a lallai sai yayi keeping kansa busy saboda ya dauke hankalin sa daga abinda yake shirin faruwa. Hakan bata yiwuwa dan duk abinda yake tunanin kara kusanto shi yake ga wani irin fargaba da tsoron rasa abu me matukar muhimmaci a gare shi. Be kara tabbatar da yana son ta da gaske haka ba sai da kwanakin nan suke ta karatowa. Be kirata ba tun maganar da sukayi ranar yaki bari kuma itama ta kirashi dan baya so ya taka dokar Allah tunda akwai maganar aure a tsakanin ta da wani. Amma fa ba karamin dauriya yake yi ba, dauriyar da take neman kaishi k'asa sosai. 

  Gefen kirjinsa ya dafe yana cikin aikin ya tsaya chak da komai ya yi shiru yana jin yadda gudun zuciyar ya karu sosai. Dagowa Kamal yayi ya dube shi ya ture system din da sauri yana tashi tsaye


"Are you ok?" Ya dafa shi


"Bani ruwa please." 


"Ok." Ya dauko masa ruwa me dan rangwamen sanyi ya bud'e masa ya mika masa ya karba yasha kad'an sai yaji kamar an kara masa gudun bugun zuciyar. Saurin ajiye ruwan yayi yayi baya akan kujerar yana runtse idon sa


"Ya Allah, bari na kira Dr Mahfouz."


"No ba sai ka kirashi ba, zai daina haka yake min."


"Haka yake ma? Tun yaushe?"


"Zai daina fa, don't worry."


"Ba maganar zai daina bane ba, bari kaga."


Ya zaro wayar sa ya kira Dr Mahfouz, suka gaisa yake tambayar sa jikin Aryan din


"Naso bashi gado amma yaki wallahi, amma abinda yake rikewa a ransa yayi yawa, he is holding alot hakan kuma yana kara damage din, last da yazo nayi masa bp it was high, na bashi drugs nace idan yaji any slight change ya dawo ko ya kirani nazo gidan."


"Ya salam, wallahi be fada min komai ba, yanzu haka abun yana neman worst."


Yace yana kallon yadda yake numfashi da k'yar


"Subhanallahi, gani nan zanzo yanzu."


"Ko mu hadu a gida na?"


"Ok hakan yayi."


"Thank you Dr, sai kazo." Ya ajiye wayar ya zagaya wajen Aryan din


"Tashi muje please."


"Kaima kamar mace, zai tsaya ba. Haka yake yi amma zai tsaya."


"Allah baka isa ba." 


Tashi yayi kawai dan baya son su cigaba da musu, ya yi gaba Kamal din ya bishi rike da wayoyin su. Khadija na zaune suka shigo ta tashi tana kallon su, gaisawa sukayi da Aryan din ta shiga daki ta dauko mayafin ta sannan ta dawo falon. Karasowa Dr Mahfouz yayi Kamal ya shigo dashi falon yana shigowa ya kalli Aryan din ya girgiza kai


"Ok kana da matsala wallahi, akwai wanda yake wasa da lafiyar sa irin ka kuwa?"


"I'm fine fa."


"Yes gashi nan, look at you daga ranar da kazo office zuwa yau, haba mana."


Murmushi kawai yayi, Dr Mahfouz ya ciro abun auna BP ya gwada ya zaro ido da sauri yana kallon Kamal


"You see, BP dinsa ya kara high sosai, a wannan stage din mutum zai iya collapsing."


"Hmm, me ya kamata ayi yanzu kenan?"


"Abinda dai baya so din shi za'a yi, dole ya kwanta coz yana bukatar hutu."


"No Dr, dan Allah karka kwantar dani a gida."


"Wallahi sai ka kwanta, bari kaji ma."


Kamal yace kai tsaye, dariya ma ya bawa Aryan din ya murmusa kad'an be sake magana ba, an ce fadan da yafi karfin ka sai ka maida shi wasa kawai.


****Ana saura kwana biyu kamar yadda Abby ya tsara, dadah ta fito janye da akwatin ta katuwa da ta lodawa kaya, Hydar na zaune a falon yana breakfast ta fito ya mike tsaye da sauri


"Daadah wannan kayan fa?"


"Gidan ku zan bar muku."


"Kije ina?"


"In da naga dama, ina ruwan ka?"


"Wasa kike Amma ko?"


"Da yake ni sa'ar kace da zan maka wasa ko?"


"Me ya faru? Munyi laifi ne?"


"Akan me zan cigaba da zama daku? Tunda kun girma kun isa kuyi wa kanku hukunci abinda kuka ga dama. Bani da amfanin zama AI."


"Me yake faruwa?" Lamido yace suna shigowa shi da Sadeeq


"Tafiya zanyi, na bar muku gidanku tunda abun haka ne,."


"Me mukayi Daadah? Dan Allah kiyi hakuri "


"Ba zan hakura ba, gwara na tafi ai duk kun gama mallakar hankalin ku ya ci ace ma kun ajiye Yaya bibiyu ko uku ma"


"Dan Allah kiyi hakuri, ki zauna muyi magana dan Allah."


"Kasan bani da amfani a gidan nan, tunda har za'a yanke shawara ba za'a sanar dani ba,na zuba ido amma babu wanda ma yake yin maganar."


"Wai maganar Raihana ce Daadah?"


"Fisabillillah haka zaku zuba ido a cutar da yarinyar nan, marainiyar Allah, ina tausayin ku? Ina son da kuke mata? Yarinya a dan kankanin lokaci duk ta fige ta lalace."


"Wallahi Dadah Abby hana mu maganar, wallahi ko da wasa kaje masa da maganar sai kaga bacin ransa, nayi iyakar kokarin ganin ya fuskance ni amma yaki fahimta ta."


"Toh ai shikenan, sai ayi duk abinda aka ga dama, ni zama na ya kare, Allah ya bada sa'a ya taimaka."


"Dan Allah kiyi hakuri, ki zauna ayi maganar nan dan Allah."


"Kasan Allah Lamido, ba zan zauna ba, in dai ba za'a fasa auren nan ba ko a bata wanda take so ba toh zama na ya kare."


"Hydar yiwa Abby magana."


"Akwai munafuki sama da Hydar? Uwar me zaka amfana idan ka assasa abinda bata so?"


"Kai Daadah."


"Karya nayi? Ba duk kaine ka assasa ba."


"Ku bani waje na tafi dan Allah, kuna bata min lokaci."


Rike jakar Sadeeq yayi, Hydar kuma ya tafi bangaren Abbyn ya kirawo shi. 


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261
TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post