Rumbun Qaya Page 43

Rumbun Qaya Page 43

Rumbun Qaya Page 43

Rumbun Qaya Page 43


***Tare suka dawo da Abbyn ya shigo falon ya durkusa har ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa sannan yace


"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri."


"Ni ai ba laifi akayi min ba sam, abinda kake ganin daidai ne ka zartar akan yar ka, bani da wani iko akai na hana balle a nemi shawara ta."


"Subhanallah, kiyi hakuri Hajiya wallahi ba haka bane ba, abubuwan ne suka zo a baibai, amma ba anyi hakan bane domin a bata miki rai, yaran nan gaba daya dani kaina a karkashin ikon ki muke, kece mahaifiyar su kuma kece mahaifin su, dan Allah kiyi hakuri Hajiya."


"A ah, babu komai fa, tunda har an riga an yanke hukunci magana ta kare, zan tafi zamana ya kare a gidan nan, Allah ya bada zaman lafiya"


"A ah Hajiya, ba za'a yi haka ba, dan Allah kiyi hakuri."


"Toh..."


"Yanzu me kike so ayi Hajiya?"


"Ka saurari yarka, kaji damuwar ta, kaji abinda take so sannan idan be sabawa shari'ar musulunci ba kayi mata, Raihana yarinya ce karama wadda ba zata dorar da rayuwa tare da soyayyar uwa ba, ta girma a karkashin kulawa ta data yan uwanta gasu nan, bata taba bijire musu ko yi raina su ba, bata taba batawa kowa rai ba, yarinya ce me cike da walwala da farin ciki, akan me za'a dakushe ta? Akan me za'a bata mata rayuwa ta hanyar yi mata auren dole, kunsan illar sa kuwa? Kunsan abinda zai jawo? Me yasa ba zaku yarda da kaddara ba, KU zama masu hakuri? Allah ma muna masa laifi amma ya yafe mana, me yasa abinda ya faru ba zai wuce ba? Rayuwar gaba daya nawa ce? Sannan duk abinda ya faru ya faru ne tsakanin ku, ku iyayen yaran nan, menene nasu su? Me yasa abun zai shafe su? Me yasa ba zakuyi kokarin gina sabuwar rayuwa ba? Bansan dalilin ka na zafafa wa har haka ba, nasan an bata maka, an zalunce mu ciki har dani, wanda har yanzu bansan shin da gaske Aisha ta rasu ba, ko tana wacce duniyar? Bamu ga gawarta ba duk da mun samu tabbacin tana cikin motar da tayi hatsari, me yasa ni ba zan rike abun ba? Me yasa ba zamu fawwwalawa Allah komai ba? Mu zama masu karbar kaddara a duk yadda tazo mana, sai mu hau fushi muce mu sam ba zamu zama masu yafiya ba? Rayuwa zata yiwu a haka? Muna so kuma muma Allah ya yafe mana zunuban da muke aikatawa, bayan mun kasa zama masu yafiya da jin kai ga sauran mutanen da kaddara ta hada mu dasu. Ni dai nasan ban isa nasa dole ayi ba, ko na hana ayi ba, shawara ce dai a matsayi na na babba, ga Raihana nan, zabi ya rage naku, ku zaba mata rayuwa me inganci ko ku dakushe ta, ta hanyar tursasata tabi abinda bata so."


"Ayi hakuri Hajiya, ayi hakuri." Abby yace maganganun sun yi mugun shigar sa. Juyawa tayi kawai ta bar musu falon ta koma ciki. Abby ne ya fara fita ya koma part dinsa, ya bar su a zaune cikin wani irin yanayi. 

   Direct wajen da ya ajiye envelope din da Daddyn ya aiko masa yaje, ya bud'e ya dauko dan tun ranar be bude ba, ya zauna a gefen gadon sa ya bud'e a hankali bayan ya zura medicated glass dinsa. Takardun filaye ne da gidajen da ya mallaka tun a wanchan lokacin, sai kuma takardar share din da yake dashi a company Mukaddas oil and gas. Duk bayanan da ya kamata ya samu suna ciki. Ajiye su yayi a gefe ya sake fito da wasu takardun wanda suke dauke da bayanin health condition din Aryan, wanda suka kasance na shekarun baya a lokacin da ya shiga matsalar PTSD at a very young age. Ajiye su yayi suma a gefe bayan ya gama dubawa cike da tausayawa. Wani dan karamin flash ya fado daga ciki. Ya dauka ya jawo system dinsa ya jona a ciki. Maganar Daddyn ce cikin muryar dake nuna jikin sa babu dadi yake rokon Abbyn ya yafe masa sannan ya taimaka ya bawa Aryan Raihana, yasan be kamata ya tambayi alfarma a wajen sa ba, kuma shi kansa Aryan din be san ya nemar masa alfarmar ba, amma idan yaga da takura shikenan babu komai. Ajiye flash din yayi bayan yayi copying maganar akan system dinsa sannan ya dauko takardar karshen. Wadda take kunshe da bayanan dalilin fitar Abbyn daga prison wacce ke dauke da sa hannun Daddyn. Jikinsa ne yayi wani irin sanyi sosai, hankalin sa ya tashi, yanzu idan wani abu ya samu Daddyn ya zaiyi? Me yasa be danne zuciyar sa ya saurare shi ba? Me yasa shi be rama sharri da alkhairi ba, ya nuna masa ya fishi ko a wajen Allah. Amma sai ya biye wa dokin zuciya ya aikata abinda sam ba halin sa bane, gashi har yana neman ya gurbata rayuwar yarsa kwaya daya tilo saboda wani dalili nasa na daban. Tashi yayi ya hau zagaye a tsakiyar dakin yana tuna maganar da sukayi da Alhaji Kabir akan maganar auren. Be goyi baya ba sam dan dai Abbyn ya matsa ne ya amince saboda kar yaga kamar ya ki yarsa. Amma daga shi har Adda Maimunan basu zama masu son kai ba, sun kuma nusar da Muhd yayi hakuri amma ya nuna musu shi dai ya amince. Tausayin Raihanan suke ji dan su ba zasu iya aikatawa Amina hakan ba. Zagayen ya cigaba da yi cikin son neman mafita, gashi saura kwana biyu kachal ta ina zai fara? Ya dade yana sakawa da warwarewa kafin ya tsaida shawara guda wadda yake ganin itace zata zama maslaha ga kowa da kowa. Alhaji Kabir ya fara kira, ya sanar dashi komai ya kuma basu hakuri, be damu ba, duk da yasan Muhd zai ji babu dadi amma yasan zai hakura a karshe tunda shi namiji ne. Ganin ya sauke wannan ya sa ya kira Lamido a waya yace suzo dukkan su part dinsa yana son ganin su, dama suna tare basu riga sun tashi ma daga falon ba dan ko aiki babu wanda cikin su yayi yunkurin tafiya saboda daga Daadah har Raihanan sun rufe kofar dakunan su sun shige ciki suna kuma tsoron wani abu ya same su. Part din Abbyn suka nufa suka same shi a falo yana zaune yana jiran isowar su, zama sukayi ya kalle su daya bayan daya sannan yace


"Na yi tunani na kuma yanke shawarar bawa Raihana zabin zuciyar ta, zan kuma cika alkawari kamar yadda na dauka sai dai na dawo da daurin auren gobe ba sai jibi ba, inaso Lamido ka kira Kamal ka sanar masa, idan mutum daya ne ma ya samu zuwa ya wadatar, idan ba'a samu me zuwa ba, ni nan zan zamar masa wakili sai kawun ku ya yi waliccin uwata. Idan yaso ku dauke ta ku kai ma mijinta ita, ni kuma sai ku fara nemar min visa domin zan bi bayan aboki na."


Wanan karon har Hydar maganar tayiwa dadi, suka yi murmushi dukkan su sannan suka ce alhamdulillah. A take Lamido ya fita daga falon ya kira number Kamal a lokacin yana tare da Aryan din da ake kara masa drip jikin nasa ya sake rikicewa sosai fiye da dah dan ma yana da masifar karfin hali da dauriya. Ba dan sun nuna masa dole dole ba da babu abinda zai sa ya yarda ya kwanta wanda kuma yake da matukar bukatar hutun. 


"Lamido ne yake kira."


Yace yana nunawa Aryan din wayar, juyar da kansa yayi Kamal ya d'aga suka gaisa sannan ya tambaye shi idan suna tare da Aryan ne, ya amsa da eh sanann yace ya dan fita waje zasuyi magana. Chan compound din gidan ya fita sannan sukayi maganar, wani irin dadi ne ya lullube Kamal din, ya dawo dakin da Aryan din yake ya tarar dashi kamar me bacci, be fada masa ba dan dama plan dinsu kenan shi da Lamido. Zama yayi a gefen gadon ya hau duba available flight da zasu yolan gobe, yaci sa'a ya samu na safe amma da yar tsada, haka ya siya musu sannan ya dauki key din motar sa ya fita. Yana driving din suna waya da Baba (Malam Hassan) ya sanar dashi abinda yake faruwa sannan ya kira Ya Nabeela ya sanar da ita itama, lokacin tana hanyar zuwa gidan Kamal din saura kiris ta saki steering motar saboda murna. Rokon ta yayi kar ta fadawa Aryan din surprise zasuyi masa kawai. 


   Su uku suka shirya, Malam Hassan, Dr Farouk mijin Ya Nabeela sai wani cousin din Daddy. Da sassafe driver ya kaisu airport ko tashi Aryan din ma be yi ba suka lula sai Adamawar yola. Duk abin nan dake faruwa Daadah bata sani ba haka ma Raihana, suna dai tare Daadan na bata baki dan ta lura kaamar abinda tace be shige su ba, ganin yadda suka cigaba da sabgar gabansu a ranar. Dangin Ammyn ne suka zo gidan bayan Daadah ta sanar dasu, duk sun dauka ma Raihana sun daidaita kansu da Muhd din ne ashe ba haka bane ba, sai da suka zo sai duk jikin su yayi sanyi haka dai aka cigaba da zama a gidan kamar ba aure za'a yi ba. 

   Hydar ne yaje ya taho dasu daga airport din suna sauka, ya kawo su gidan suka hadu da Daddy a falon sa suka zauna har lokacin ya kusan karasawa sannan suka dunguma zuwa masallacin. Asabar ce sai kuma tazo da daurin aure da yawa, sai da aka fara na wadanda suka riga su sannan aka shiga daura auren Raihana Nasir Matawalle da angon ta Muhammad Ibrahim Mukaddas bisa sadakin dubu dari da Kamal ya bayar. Kasancewar anyi daurin aure da yawa ya saka ma ba zaka gane wannan mutanen wannan bane haka ma wannan, haka aka gama aka watse suka dawo gidan cikin farin ciki da annashuwa. Matan gidan na zaune aka shigo musu da alawa da goro.


"Kar dai zargi na ya tabbata auren nan aka daura yau?"


"Eh Dadah, an daura auren Raihana da angon ta Muhammadu."


Lamido yace yana murmushi. 


"Yanzu har da kai Lamido?"


"Muje ciki zan miki bayani Daadah."


"Me zaka fada min?"


"Muje dai, sirri ne."


Da k'yar ta bishi cikin ya sanar da ita abinda ya faru, sai kuma ta hau murna tana saka musu albarka, ta juya zata je ta sanar da Raihana ya hanata


"Angon yana chan kwance babu lafiya, karki fada mata dan Allah suprise za'a mata."


"Akan me? Yarinya na chan na ciwon so Allah ya share mata hawayen ta za'a ce ba za'a fada Mata ba."


"Dan Allah Dadah, dan Allah."


"Gobe da safe zasu wuce da Kamal, sauran da suka zo dai yau zasu koma."


"Haka da wuri? Me yasa ba za'a bari muyi biki ba."


"Kai Dadah, da fa bakuyi niyyar bikin ba dama."


"Wannan ai auren soyayya ne, wanchan kuma na dole, kai Allah ma yaso na jima ina gyara Raihana, da irin wannan auren bagatatan haka za'a kaita dakin miji ba wani gyara."


"Wannan maganar ku ce Dadah, bari na koma waje."


"Allah dai yayi maka albarka kaji, bari naje na sata tayi wanka ta ci abinci dan wannan ramar da tayi ma Allah yasa kar kasusuwan su ciji mijin."


Dariya ya kwashe da ita, ya barta a ciki yayi waje, ta fito ta nufi dakin Raihanan ta same ta tare da wata kanwar Ammy da tazo ta fada mata an daura auren. Tsabar kukan tayi ta gaji ya ma ki zuwa, ta hakura kawai duk yadda sukayi da ita. Sata taje tayi wanka Dadah tayi babu musu taje tayi ta saka kaya ta zauna da kudaddiyar fuskar ta da ko mai bata saka mata ba bare ta samu arzikin powder. Abinci aka kawo mata taaci kad'an ta koma ta kwanta tana tunanin rayuwar da zata shiga da yadda abubuwan suka faru a dan kankanin lokaci. Tabbas Muhd ba zai taba jin dadin zama dashi ba, tayi biyayya ta aure shi amma ba zata taba son sa ba, har abadah gangar jikinta kawai ya aura.


  A ranar Malam Hassan, Dr Farouk da kanin Daddy suka dawo wajen karfe taran dare, shi Kamal sai gobe zasu taho tare da Hydar dan Lamido ranar zai koma bakin aiki Sadeeq kuma yana da abubuwan yi a clinic.

  Da duku-duku Daadah ta sakata ta hau shiryawa, tana shiryawar tana kuka sosai har wani jan numfashi take saboda kuka, har ga Allah Dadah taso ta fada mata da ainahin wanda aka daura amma Lamido ya hanata dole ta hakura amma tana matukar tausayin Raihanan ganin har zazzabi ya kamata ga jijiyoyin kanta da suka fito sukayi rado rado saboda kuka. Part din Abby aka rakata ta same shi a bedroom dinsa ya kira sunan ta, ya shiga yi mata nasiha me ratsa zuciya sannan ya rufe da saka mata albarka. Fitowa sukayi zasu tafi airport din wajen sha biyu, mota suka shishiga ita da Daadah ta kwanta a jikinta tana cigaba da kuka k'asa k'asa. Sai da suka zo airport din sannan kukan ta ya karu sosai, ta rik'e Dadah da itama kuka take dan bata taba kawo rabuwa da Raihanan a wannan lokacin haka katsaham ba. Da k'yar aka banbareta daga jikin Dadah Lamido ya rike Dadah ita kuma Hydar ya riketa suka nufi cikin wajen, sai da suka ga shigar su sannan Kamal yazo yayi musu sallama yace sauran kayan Raihanan zasu turo driver ya daukar mata idan an gama hadawa.Daga chan bayan su Kamal ya zauna hakan yasa Raihana bata ganshi ba, ta dora kanta akan kafadar Hydar din bayan ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take saukewa a jere. 

   Ko da suka iso Kanon ma ba mota daya suka shiga ba, driver ne yazo ya dauke su shi kuma Kamal yayi Uber ya bi bayan su, suna sauka ya Aryan wanda yaga missed calls dinsa tun a chan amma be kira shi ba saboda baya so ma ya samu wani clue akan abinda yake faruwa. Yana kishingide a bayan mota kiran Kamal ya shigo wayar tasa. Ya kirashi na dama ya sanar dashi ya tafi gidan sa idan ya dawo sai ya dawo be daga ba,kawai sai ya kira driver Daddy yace ya zo ya dauke shi ya kaishi. Toh suna saukar ne ma Kamal din ya kira ya tambaye shi yana ina dan yaji karar hanya yace ya tafi gidansa, ok kawai Kamal yace ya kashe ya kira driver da ya dauki su Raihanan yace ya kaisu chan gidan Aryan din. Kasancewar daga inda Aryan din yake yafi kusa da gidan akan daga airport din  yasa ya riga su zuwa. Har ciki driver ya shigar da motar bayan Baba me gadi ya bud'e masa tunda already ya riga dama yasan motar gidan. Suna shiga Kamal yazo shima a Uber ya sauka ya sallama shi. 

  Aryan ya riga ya shige ciki amma kofar a bud'e take be rufe ta da key ba kawai murd'awa zaka yi ka shiga. Kofar driver ya nunawa Hydar din ya ce su shiga, ya murd'a kofar rike da hannun Raihanan suka shiga. Kayan Aryan din ne zube akan kujerar wanda ya cire yana shigowa ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa ko zai rage nauyin da yake ji musamman idan ya tuna daga gobe shikenan bashi da sauran hope. Kasancewar ya kuna ruwa ya hanashi jin shigowar su kwata kwata. 


"Ina zuwa kanwata, ki zauna yanzu zan dawo kinji?"


"Dan Allah Hamma karka barni anan, dan Allah."


"Ai ba tafiya zan ba, waje zan je na sallami wanda ya kawo mu."


"Toh dan Allah karka dade." Tace tana share kwallar da ta sakko mata.


"Ba zan dade ba." Yace ya fito ya ja mata kofar ya nufi wajen Kamal da ke zaune tare da Baba mai gadi suna magana.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post