Rumbun Qaya Page 44


Health College

Rumbun Qaya Page 44

 

Rumbun Qaya Page 44

RQ

     Page 44

***Hydar na fita ta kalli falon sosai da sauri ta mike tsaye domin ta tabbatar da ba wai idon ta ne yake mata gizo ba. Fitowar sa kenan daga toilet din, hannun sa daya yana goge sumar kansa da dan karamin towel sai bathrobe dake daure a jikin sa, sai da ya tsane ruwan kan nasa sannan ya cire bathrobe din da towel din ya wurga su a laundry basket ya zura short trouser ya shafa mild oil perfume. Kwanciya yake so yayi ya dan yi bacci dan har lokacin jikin nasa is weak, dan haka ma be tsaya saka wata riga ba ya fada saman gadon. Yana kwanciya sai ya tuna da wayar sa a falon kuma yana so ya duba ta sannan ya kashe dan kar ma a kira shi. Mikewa yayi ya zura bedside slippers dinsa ya nufi falon kansa tsaya sanin shi kadai ne a gidan. Tana tsaye tana son gasgata in da take tana kuma son gano dalilin da ya kawo ta gidan ya fito. Da karfi ta kwalla kara ganin mutum daga shi sai gajeran wando ya fito, karar da tayi ce ta bashi tsoro dan ko da wasa be yi tunanin ganin ta ba. Juyawa tayi da sauri ta bashi baya tana runtse idon ta kam-kam. Tsayawa yayi chak daga in da yake yana son tantance me yake faruwa? Tunanin zuwan da tayi a wanchan lokacin ya fado masa, me take yi anan? Ya tambayi kansa. Tunowa da yayi da yanayin da yake ciki yasa shi juyawa da sauri zai koma ciki, sai kuma wani tunani ya fado masa, taku daya biyu yayi ya juyo ya shiga takowa zuwa wajen da take tsaye ta juyar da bayan ta ta runtse idonta jikin ta na rawa sosai. A daidai saitin bayanta ya tsaya, har tana jin hucin numfashin sa a saitin wuyanta.  Wayar sa ce tayi kara alamun shigowar sako, hannu yasa ya dauki wayar dake daidai saitin sa ya bud'e sakon ya karanta


_"She's your wife man, taka ce halak malak. Sender Babban wa uba."_. Yasa emoji din wink a karshe. Wani irin murmushi ne ya subcewa Aryan, be san lokacin da ya dire wayar ba, sai ji kawai tayi ya rungume ta baya baya da karfi. So tight da har tana iya jin ragowar danshin dake jikin sa


"Na shiga uku." 


Ta furta jikin ta na cigaba da rawa sosai, 


"Alhamdulillah zaki ce."


Ya rada mata a kunnen ta a hankali. Har cikin kwakwalwarta maganar ta shigar mata, ta haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassarawa. Juyo da ita yayi gaba daya suna facing din juna, idon ta a rufe yake har lokacin ya tsurawa fuskar ta ido da tayi fayau daga ranar da ya ganta.  Hannu ya kai ya shafa saman idon nata, yace


"Bud'e idon ki please." Girgiza kai tayi da sauri tana sake runtse idon ta


"Pleaseeeee kinji? Wani abu nake son gani."


"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na Hamma Hydar zai kawo ni ba." 


Ta fada muryar ta na rawa gashi ya rik'e ta kam kuma very close da jikin sa.


"Hydar ne ya kawo ki?" Yace cike da mamaki, da kai ta amsa masa, sai yayi murmushi kawai ya tauna kasan lips dinsa ya tallafo fuskar ta


"Batan hanya yayi kenan, yanzu ya za'a yi? Ni kuma gaskiya kinzo kenan." 


"Dan Allah dan Allah kayi hakuri."


"Um um, ba zan iya ba gaskiya, sai dai idan zaki bud'e idon ki."


"Toh kaje kasa kaya."


"Zafi nake ji, idan kika bud'e kad'an naji zan je nasa amma."


Shiru tayi ya cigaba da kallon ta zuciyar sa cike da farin ciki kal kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha haka yake ji. A hankali ta dan bud'e idon kad'an ta kalle shi, dama shi ita yake kallo, idon ta ne ya shiga cikin nasa ya wani narke mata su, da sauri ta maida idon ta kulle kirjinta na wani irin fat fat. Dariya yayi kad'an ya sake matso da ita jikinsa gaba daya, ya kai bakin sa saman forehead dinta ya sakar mata light kiss sannan a kai bakinsa kunnen ta yace


"Tsoron kallon mijinki kike ji?"


Kalmar mijin ta shiga kunnen ta zuwa brain dinta amma sai ta kasa gane ma'anar abinda yake nufi ma baki daya.


"Ok zauna ina zuwa." Yace yana sakin ta, sai kuma ya dawo da sauri yace


"Muje tare kar naje na fito naga bakya nan" 


Ya kama hannun ta suka shiga ciki har lokacin taki yarda ta bud'e idon ta, gaba daya ta kasa nutsuwa ta kuma kasa fahimtar ma abinda yake faruwa gaba daya, shi kuwa a nutsen sa yake komai. Ba tare da ya nuna tsantsar mamakin sa ba, yanayin sa kenan. Bedroom dinsa ya shiga da ita ya zaunar da ita a gefen gadon ya wuce wajen kayan sa ya dauki jallabiya ya zura sannan ya dawo in da take zaune ya zauna a kusa da ita sosai yace ta bud'e idon ta. Budewa tayi a hankali amma taki kallon sa tana dan zamewa kad'an ta matsa daga zaman da yayi kusa da ita sosai. Sake matsowa yayi ya kama hannun ta ya juyo da fuskar ta bangaren sa ya cigaba da kallon zagayayyar fuskarta zuwa dan karamin lips. Gaba daya kallon da yake mata ya hanata sakat, gashi da ta dauke kai sai ya juyo da kan nata. 


"Please ki bari nayi ta kallon ki, kamar mafarki haka nake ji, how come? Ya akayi hakan ta faru?"


"Oya bani labari, yaushe Abby ya chanja mind dinsa? Tausayi na yaji ko?"


"Nima ban sani ba, bansan nan zamu zo ba."


"Ok wait, bari na dauko wayata na kira kamal, shi zai fada mana komai. Just wait for me yanzu zan dawo kinji?" 


Duk yadda ya kware a iya boye mamakin sa ko damuwar sa ya gaza a yanzu, jin sa yake kamar a saman gajimare saboda tsabar farin ciki. Falon ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal din. Dagawa yayi ya kwashe da dariya


"Ango kasha kamshi." Yace yana kokarin rage dariyar tasa


"Please kun saka mu a duhu, muna bukatar bayani."


"Muma compound din gidan ai, bari mu shigo ciki."


"Ok, kai da waye?"


"Ni da surukinka, bari mu shigo."


"Ok." Yace ya sauke wayar ya isa kofar falon ya bud'e ta, suka karaso Kamal na kallon shi ya sake kwashewa da dariya


"Kasan kuwa angwaye akwai saka jallabiya wallahi, ko me yasa?" 


Yace cikin sigar tsokana suka yi dariya dukkan su har Aryan din, sannan ya matsa musu suka shigo. Zama sukayi, Hydar ya mika masa hannu suka gaisa sannan Kamal din ya soma yi masa bayanin duk abinda ya farun da kuma yadda akayi da zuwan da sukayi ya kare da


"Gata nan mun kawo maka ita, sai ku daina ciwon love din ku mike aiki na jiranku."


"Saboda mune agogo sarakan aiki ko?"


"Emana, kaga ba shikenan sai ayi mata new seat a office dinka ba."


"Ni duk ba wannan ba, wato duk kun sani har Ya Nabeela amma babu wanda ya fada min."


"Toh Mr korafi, ai ka fara godiya kafin korafin."


"Surprising naku muka yi ai." Hydar yace yana murmushi


"Mun gode amma kad'an."


"Wallahi idan ban sa ta fito mun tafi ba, babu fa wata wahalar da kayi ta aure ba lefe ba komai kawai aka kawo maka mata amma ba godiya ba komai?"


"Ba komai duk zan yi mata duk abubuwan da ya kamata ne fiye da wanda ake ma kowa ma. Godiya kuma Daadah kawai zan shikenan."


"You are not serious, a gaban Hydar din?"


"Shima ya sani ai, yasan gaskiya."


"You are not nice." 


Kamal ya dauki pillow ya jefa masa ya chafe suka sa dariya gaba daya, kallon Hydar kawai Aryan yake amma ya shirya masa rashin m, dole ne ma ya rama abinda yayi masa ta cikin ruwan sanyi.


"Yanzu sai maganar biki, ya kamata ayi biki kamar yadda ake ma kowa ko?"


"A bari hada da na suna nan da wata tara." 


Ya basar bayan ya fada kaamar ba shine yayi magana ba, wani pillow Kamal ya sake jefa masa ya mike tsaye cike da mamakin Aryan din


"Muje Hydar."


Yace sai kuma ya kalli Aryan din da shima ya mike tsaye


"Gida zaku koma saboda a fara gyaran nan din ko?"


"Ok hakan yayi, amma ba yau ba."


"Idan kun ga dama karma ku koma, shima a hada da na sunan nan da wata taran ayi."


"Eh hakan ma dai duk shawara ce." Ya fada yana dariya.


"Gobe ma rana ce wallahi, kirawo ta Hydar zai mata sallama."


"Komawa zai?"


"Eh amma sai gobe ko?"


"Eh in sha Allah."


"Ai zaku sake haduwa, idan kace mata sallama yanzu zaka rikita min ita ne."


Kama baki Kamal yayi wanda shi no a jikin sa maganar sa kawai yayi kuma tsakanin sa da Allah har a zuciyar sa haka ne.


"Wai dan Allah Aryan yaushe bakin ka ya bud'e haka?" 


"Daga sanda kayi min aure."


"Wato ni na jawo ko? Na karba maka mata yarinya me hankali amma da abinda zaka saka min kenan?"


"Sorry sir." Ya fada yana dariya


"Oga Hydar please ka bari sai gobe dan Allah."


"Ok ba damuwa, zan shigo kafin na wuce."


"Yawwa thank you."


"Inaga kai ma fitowa zakayi kawai mu duba office din chan dan naga ka warke garau, sako kayan ka kawai mu wuce akwai ayyuka masu yawa, kasan kuma next week zan tafi." 


Kamal ya tsokane shi yana son Jin abinda zai ce 


"Tab wallahi ba zan je ba." 


Yace ya juya ya bar su a tsaye kawai suna dariya. Fita sukayi suka rufe kofar ya dawo ya saka key a kofar dan kar ma su dawo sannan ya nufi dakin cike da karsashin sa. Tana zaune a in da ya barta, ta kara jawo mayafin ta sosai ya sakko saman fuskar ta ya rufe fiye da rabin fuskar. Wuce ta yayi ya nufi wajen kayan sa, ya zare jallabiyar ya maida ita inda ya dauko ta dan duk ta takure shi, ya dauko wani wando ash colour da rigar sa masu laushi,wandon ya kai masa wajen guiwar sa sai rigar da take armless ya saka ya dawo wajen ta ya janye mayafin da ta rufe fuskar ya cire shi gaba daya ya ajiye shi akan bedside sannan ya jawota jikinsa ya sakata a tsakiyar kafafun sa ya dora kansa a saman kafardar ta yana shakar kamshin jikinta.


"Naje munyi magana da Kamal yanzu, kina so kiji me muka ce?"


Da sauri ta daga kanta sama alamar eh dan gaba daya ya na neman rikita mata tunani, hannun ta na cikin nasa yana murzawa a hankali ga shi ya dora kansa a jikinta duk maganar da zai yi direct cikin kunnen ta take zuwa. Yanayin yadda yake maganar so deep ma kawai ya isa ya rikitar da ita. Kamar bashi ba, kamar wani ne na daban aka chanja shi ba ainahin Aryan din da ta sani ba, gaba gadi kawai yake koman sa tun farko baya tsaya nuku nuku ko magana ce zai fade ta kawai ko ba zata maka dadi ba shi ba ruwan sa. 


"Abby yaji tausayi na ya bani ke, halak malak, naji dadi na gode wa Allah, daga ranar zuwa yau jini na ya hau yafi sau dubu, na rasa me ma zanyi, idan na tuna wannan sahoramin Abby zai bawa ya hanani sai naji duk babu dadi, nasan na fishi chanchantar ki, na fishi bukatar ki kuma na fishi son ki..."


"Tun kina baby, tiny little baby nake son ki Raihana, tun bansan menene son ba ma, ashe ban sani ba matata ce aka haifa min." 


"Zan sha ruwa." Tace da sauri tana jin yadda yake shinshina wuyan ta yana saukar mata da wani irin numfashi me dumi a saman wuyan nata 

"Um um." 


Yace dan ya gano su take ta gudu, ya sake matse ta sosai a jikinsa ya saka hannayen sa ya makaleta ta yadda duk motsin da zatayi a jikin sa zatayi. 


"Zanje toilet." Ta sake fada cikin neman hanyar tserewa


"Pleaseeee ki barni, na dade ina mafarkin wannan ranar, ki barni naji dumin jikinki, kiji nawa please."


"Allah toilet nake son zuwa."


"Ok, muje na rakaki."


Zaro ido tayi da sauri, toilet din zai rakata?


"Tashi muje toh." Ya dan cikata yana bata damar mikewa. Kasa tashi tayi dan har gwara su cigaba da zama a hakan da ya rakata toilet din


"Um um na fasa zuwa." 


"Bakya so na raka ki?"


"A ah na fasa ne kawai." 


"Ok, na fasa raka ki din, jeki ina jiranki, amma idan kika dade zan shigo."


Kallon sa tayi ya daga mata kai


"Na fasa da gaske, jeki."


"Ok." Tace ta mike ya nuna mata toilet din da hannun sa. Kasancewar babu Hijab babu mayafi a jikin ta yasa ta kasa tafiya. Baya yayi shi kuma yana kallon ta yana jiran yaga abinda zatayi. Mayafin da ya cire mata ta saka hannu zata dauka yayi saurin daukewa yana tsare ta da idanun sa masu kashe mata jiki.


"Haka zaki je, ko na rakaki."


Sakin mayafin tayi ta wuce a hankali ya bita da kallo yana sakin murmushi. Tana karasawa toilet din tayi saurin shigewa ta saka lock din jikin kofar ta dafa kirjin ta da yake harbawa da karfi. Wayar sa ya dauka zai kira Kamal yayi masa maganar abinci dan yasan zata ji yunwa sai yaga missed calls din Ya Nabeela,fasa kiran Kamal din yayi ya kirata tana dagawa ta fara gud'a. Murmushi kawai ya dinga yi suka gaisa tayi masa Allah sanya alkhairi sannan tace zata turo driver ya kawo musu abinci zata shigo gobe, godiya yayi mata ya kashe wayar gaba daya tunda dama abinda zai tambayi Kamal din kenan. Dan kishingida yayi sai ya tuna tace zata sha ruwa, sai ya tashi ya dauko mata ya ajiye ya sake komawa yana jiran fitowar, kusan minti goma da shigar ta amma shiru kuma shi be ji alamar motsin ruwa ba. Mikewa yayi ya karasa jikin kofar toilet din ya kwankwasa kad'an. Tace tana tsaye gaban mirror tana kallon idanun ta da sukayi wani irin kodewa saboda kuka, fuskarta kuma tayi wani jaja jaja itama abin ka da farar fata. Sake knocking yayi sannan yace


"Zan shigo fa."


Bata dauka da gaske yake ba, dan tasan kofar a rufe take shiyasa taki amsa masa, sai da taji kamar ana murd'a kofar kafin ta yi aune har ya bud'e ya shigo. Hannun ta kawai ya kama ya fito da ita, dan dama yasan babu abinda take yi a ciki. Kan gadon ya maida ita ta zauna sannan ya mika mata ruwan ka karba tasha kadan ya rufe ya ajiye. Fita yayi ya barta a dakin ta dauki mayafin da sauri ta sake yafawa, ta takura sosai da rashin sa dan riga da skirt ne a jikinta rigar kuma fitted ce wadda ta dan kamata musamman ta sama. Tana zaune ya shigo rike da basket me kyau an rufe shi da wani farin kyale me kyau. Dire shi yayi akan carpet din dake gaban gadon ya zauna ya mika mata hannun sa yace ta taso. 

“Nakoshi” wani kallo yayi mata ya bude basket din yana kallon abinda aka rubuta a jikin farin kyallen. HML Aryan and Raihana. Murmushi yayi me dan sauti ya sauke warmers din masu kyau ya bude ya zuba abincin ba da yawa ba ya rufe ya dauki plate din ya dora shi a saman drawer sannan ya kama hannun ta ya gyara mata zama ya zauna yana facing dinta yace ta ci abincin ko ya bata. Duk da tana jin yunwa ga kamshin abincin da yake shigar ta amma kunyar sa ba zata barta ta iya ci ba, ganin ya tsare ta da ido yasa ta ci kadan tace ta koshi, be ce komai ba, ya karbi plate din ya ajiye ya duba duba time yaga lokacin sallar azahar tayi, yace ta yi alwala ya sakè ficewa daga dakin ya hau sama. Tashi tayi taje tayi alwalar tazo ta matsar da kayan ta  tada sallah. Turo kofar ya yi sai yaga tana sallah sai kawai ya ja mata kofar ya fita sukayi jam’i tare da babà maigadi yayi amsa Allah sanya alkhaiiri sannan ya dawo ciki. Motsin sa taji tayi saurin sakè gyara mayafin jikinta ta kame waje daya. Shigowa yayi suka hada ido ya sakar mata murmushi ta sunkuyar da kanta ya karaso ya zauna a gefen ta


"Kinsan siesta?" Ya tambaye ta, girgiza kanta tayi


"Ok, bari ki gani." 


Yace yana mikewa, ya dan karo karfin AC dakin sannan ya kashe hasken dakin ya saki curtains din da suke bud'e. Rigar jikinsa ya zare ya ajiye a saman sofa ya karaso wajen da take tsoro duk ya gama cikata ya kama mayafin ya zare shi ya je ya saka shi a wardrobe din sa ya rufe ya dawo ya mikar da ita.


"Zo muyi siesta, nasan kwana biyu bakya wani baccin kirki."


"Bana jin bacci" Tace tana zaro ido, da tsakar ranar nan ace tazo ta kwanta, akan me?


"Allah sai kin kwanta, hutawa zamuyi."


"Wallahi wallahi bana jin bacci, rana ce fa?"


"Siesta kenan, bakiyi boarding school ba?"


"Ban yi ba." 


"Shiyasa toh, zaki chanja wannan atamfar? Na baki kayana kisa?"


"Um um, ni zan je falo idan ka gama sai na dawo."


Tayi hanyar fita, da sauri ya riko ta, ya sakata a jikinsa gaba daya ya jata zuwa saman gadon, ya kwantar da ita ya kwanta a gefen ta ya saka hannunsa yayi mata rumfa dasu ta yadda ba zata iya ko motsi ba. Zatayi magana ya saka hannun sa a saman bakin ta


"Shssh, don't say anything, ba abinda zan miki so nake kawai naji heartbeat dinki."


Ya dora kansa a saman chest dinta.


"Na shiga uku." Ta furta da dan karfi ganin yadda ya dora kansa a saman kirjinta ya rufe idon sa. Dago kansa yayi yana kallon ta


"Relax please, kinji yadda heart din ki take gudu? Menene ? Tsoro na kike ji?"


Gid'a masa kai tayi da sauri, ya matso da fuskar sa daidai tata a hankali yace


"Babu abinda zan miki fa, heartbeat dinki kawai nake ji. dan Allah ki kwantar da hankalin ki kinji?" Sake gid'a masa kai tayi yace 


"Good girl." 


Rufe idon ta tayi shi kuma ya cigaba da kallon fuskar tata zuwa lips din nata da yake ta fuzgarshi, yana son ya ji shima yadda ake ji.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post