Wa ya Ksahe Rukayya? Page 9

Wa ya Ksahe Rukayya? Page 9

Wa ya Ksahe Rukayya? Page 9

*WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.



9️⃣



Sai ta tazo tsakiyar Palon sannan ta anke da shi kame bisa kujerar da ke fuskantar ɗakinta gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika palon fuskar nan tasa a ɗaure babu annuri.


Cike da mamakin kasancewarsa a gidan nasu da sassafen nan ta ke kallonsa tana ƙara haɗe rai itama.


Kamar haɗin baki gaba ɗaya ƴan matan ko wacce ta fito daga ɗakinta sanye da Abaya sun yane kansu da mayafin sai kace waƴanda sukai meeting akan abinda zasu sanya a yau ɗin.


Cike da mamaki suma suke kallonsa kafin suka haɗa baki wajan cewa "Good morning sir!"


Kamar mai ciwon baki yace masu "Morning"

  Yaja baki yai shuru abinsa.


Kai tsaye suka nufi dinning dan karyawa suka barsu nan cirko cirko.


Ahmad ne ya shigo cike da mamaki shima ya gaida malamin nasu ya nufi dinning shi ma.

  Bin bayan Ahmad ta yi zata wuce da kakkausar murya yace "ina zaki?"

  

Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba.


Rukayya na buɗe kulolin abincin ƙamshi ya cika dinning area ɗin nan da nan Laila ta soma yamutse fuska lokaci ɗaya ta soma yunkurin Amai da gudu ta miƙe ta nufi ɗakinta suka rufa mata baya gaba ɗyansu hankali tashe harda Ahmad sai faman tambayar ta su ke ko lahiya.


Hankali tashe Amal ma tabi bayansu tare da mancewa da wanzuwar wani Aliyu a gabanta.


Ƙaƙarin amai laila ke ta yi gashi babu komai a cikin ta gaba ɗaya ta galabaita.

  Ruwa suka zuba mata ta wanke fuska da baki nan Ahmad yace su wuce Asibiti da ita kawai dan gaba ɗaya ta yi yaushi sai numfarfashi ta ke.


Sai da suka fito palon Ahmad ya dubi Amal ya ce "Amal ke ki tsaya a gida kawai tunda kina da bako muje mu dawo".

  Kasa musa masa ta yi saboda yadda Aliyu ya tsare ta da idanuwa kamar zai haɗiye ta.


Ba haka ta so ba dan ita wani shakkar Aliyun ma ta ke yi. 

  Tana ji tana gani suka fice suka barta da shi a palon yanai mata wani mugun kallo.

 Gaba ɗaya ta ji ƙafafunta suna rawa bata san sanda ta zube a kujerar da ke gefenta ba.


  Tsawon mintuna biyar suna zaune shiru kamar daga sama taji shi yana fadin "Raina ni ki ka yi dana ce kar kije party jiya ki ka tafi? Ko kuwa rashin tarbiyya ne da rashin sanin darajar na gaba da ke?"

 "Amal kinsan abinda ki ke aikatawa kuwa? Kinga irin shigar da ki kayi kika je ko wani kare da doki yana ƙare maki kallo kuwa?"

  "Wai dan Allah meye matsalarki Amal meye ke damun kwakwalwarki ne wai"

 Ya kare maganar a tsawace yana tasowa daga inda ya ke.

  Da wani irin gudu ta miƙe zata gudu amma ga mamakinta ko inda take bai kalla ba kai tsaye ɗakinta da yaga ta fito daga ciki ya nufa kansa tsaye.

  Da sauri ta rufa masa baya dan bata san me zai je yi a dakinta ba.


 A tsakiyar ɗakin ya tsaya yana karewa ko ina kallo kafin ya kalleta a fusace yace "Wuce ki hada kayanki mutafi karki batan lokaci"!


A razane ta kallesa  bakinta na rawa tace "haba mana Aliyu wai ya ka ke min haka ne ni dai dan Allah ka rufa min asiri ka kyale ni, Allah yasani ka takurawa rayuwata Wlh".


Wani mugun tsaki yayi ya wuce ta ya nufi wajan ajiyar kayan nata wanda dama da riga ta gama haɗa komai waje daya wani empty akwati ya jawo ya shiga loda kayan a ciki duk wanda hannunsa yaje kai kawai ya ke jawowa, saida ya cika shi tam ya rufe sannan ya juyo yana watsa mata harara baki ta tura masa tare da juya masa baya.


Sai da ya gama ƙare mata kallo sannan ya jawo akwatin da hannu ɗaya ya sa dayan hannun nasa ya fisgota da k'arfi tana fisfisgewa amma bai kulata ba sai da ya dangana ta da motarsa wanda ya shigo da shi har cikin gidan.


Kuka kawai ta fashe dashi tana kallon irin wannan karfin hali da Aliyu Haydar yake gwada mata, k'atuwar budurwa kamarta amman yake yi mata duk yanda yaga dama ita kam gaskiya ya takurama rayuwarta.


"Wai ina zaka kai ni ne ba tare da ƴata ba? Ka barni inje in ɗauko ƴata".

    Ko kulata bayi ba ya turata a motar ya rufe sannan yasa akwatin a baya ya zagaya ya shiga.

  Babu wanda ya dakatar da shi a cikin masu tsaron nasu tunda sunga jiya yazo yauma yazo kuma ya jima a ciki.


Kai tsaye hanyar Kano ya ɗauka yana ta faman falfala uban gudu bisa titi kamar wanda zai tashi sama.


A tsorace ta ke dubansa ganin fuskar tasa babu annuri ya sata saka fuskarta a cikin cinyoyinta tana ci gaba da kuka ƙasa-ƙasa, wlh ji ta ke kamar ta shake shi har sai taga baya numfashi.


Wani irin burki ya taka ji kake kuuuuuu!!!!!!

 "Cikin tsananin firgita Amal ta fad'a jikinsa ta kankamesa jikinta sai rawa ya keyi.


 Wani irin shock ne ya ziyarce shi tamkar wutar nepa ya jashi, da sauri ya hankaɗata yana mazurai.

"Ke bakida hankali ne? Bakiga tuki nake ba?" 


"Bakaji yadda ka taka burki ba? Na sani ko hatsari zamu yi yanda ka ke ta falfala wannan gudu, ni dai kar kaiwa ƴata asara ba tada kowa a duniyar nan sai ni".


Bai ce mata uffan ba yaci gaba da tukinsa.


Babban gida ne mai tsarin gaske a GRA dake nan cikin jahar Kano 


Gidan farin fenti ne da shi, inda gate din gidan ya kasance baki, kana shi gowa cikin gate din gidan titi ne a mik’e santal shimfid’e da kananan duwatsu irin na titi dinnan amnan farare masu surki da baki, wannan titi idan ka mik’e shine zai kai ka har ma’ajin motocin gidan, idan kayo gaba kad’an grass carpet ne malale kore shar da shi abin sha’awa wanda zai sadaka da palon baki mai kama da d’akin taro guda, daga gefe kuma matattakalar bene ce wanda zai sadaka da babban palon gidan, idan ka kai kallonka gabas kuwa wata matattakalar bene ce kuma wanda zai sadaka da d’akunan baccin mutan gidan, d’akuna uku ne kacal a saman, d’aya na Amal ne yayinda sauran biyun babu kowa a ciki.


 falon k’asa kuwa anan d’akin mai aikin gidan yake watau sabuwa amintacciyar mai aikin gidan kenan.

 Daga can kusurwa kuma idan ka mike anan site din Father yake wanda ya kunshi palo da komai.


Daga gefe guda kuwa wajan cin abinci ne watau dinning table kujeru ne reras a wajan gashi an kayata wajan abin gwanin ban sha’awa, tsayawa fadin haduwa da k’ayatuwar wannan gida bata lokaci ne.


Da kakkausar murya Aliyu ya buga mata gargaɗin cewa karya sake yaga ƙafarta a waje bayan ya kawo ta har gida wanda ko tambayarta unguwar da gidan baiyi ba sai dai kawai ta gansu sun iso.

 Izuwa yanzu ta daina jin mamaki da lamarin nasa illa ma tsoro da ya koma bata dan ya zame mata kamar wani Aljani.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post