💦💧💦💧💦💧💦💧
🛑 *IYAYENA*🛑
💦💧💦💧💦💧💦💧
*By NUSAIBA ALKAMAWA*
*PROFICIENT WRITER'S* *ASSOCIATION*
*PAGE 📄 7
******
_________Saida Waheed yayi wa khamees wajen 3 missed call Bai daga ba, kallon wayar Waheed yayi cike da takaici anya kuwa baxaije yasamu abokin nasa ba? yafada masa damuwar sa kar kuma naje bansame shiba yana cikin tunanin nan yaji wayanshi tana ringing aikuwa da saurinsa yadaga ganin khamees ne.
"hello abokina sorry bana kusa Da wayar ne, Waheed yace OK kana inane yace ina gida ganinan zuwa khamees yace to amma fa kayi sauri yau Daddyna yace xan rakashi unguwa Waheed yace OK ganinan zuwa ya kashe kiran yanayin gaba safwan yace yaya kodai naxo na rakaka ne naga surikar momy ne?"tsaki kawai yayi tare da harararsa yayi ficewarsa yana isa gidansu abokin nasa ya tarar da Daddy da momyn khamees ya tsaya suka gaisa.
_______ Daddy yacewa Momyn khamees kinganshi ko, haka suka iya babu abinda suka iya sai yawo amma sun kasayin aure ai nakusa maganin khamees wlhi Daddy yayi ƙwafa" shidai Waheed bece komai ba yasosa kai yashige part din khamees ya tarar dashi yana shiryawa" abokina yana ganka hakane kamar kana cikin damuwa ?
Waheed yace abokina ina cikin damuwa wllh" subanahallah wace irin damuwa ce haka take nema ta gigita tunanin abokina haka?
Hmmn Daddy ne yace na fitar da matar daxan aura kuma kasan ni ayanxu banida wacce nakeso sabida bana kula yanmata duk basa gaba na wai yabani nan da three month inba haka ba yazabamin da kanshi.
Khamees yayi shiru yana tunani can yace yauwa abokina ko dai jidda zaka zaba ne nima Daddyna yayimin mata sunanta Yusra kuma tana da kanwa Jidda wllh abokina Jidda tana da hankali sosai ga tarbiyya zakaji Dadin zama da ita wlhi" Waheed yace kai abokina rabani da yanmatannan wllh bana ra,ayin naje nacewa budurwa inasonta senaga kamar zata rainani nikuma bana son raini kainifa auren ne bana sonyi gaba daya fa.
" Khamees yace ahaba abokina ai aure shine cikar mutumcinmu tun wuri gwara muyi tunkafin su xabo mana da kansu kanaji Waheed kodai nayi mata magana ne ,ko kuma muje ka ganta ne ?
Waheed yakamata fa ace yanxu mun ajiye iyalifa yawanci classmate dinmu sunyi aure amma mu muna zaune yakamata ace yanxu mun maida hankalinmu akan maganar auren mu.
Waheed yace owk abokina karka damu zamuyi wannan maganar insha Allahu,nandai suka fita khamees suka fita da Daddynsa shikuma Waheed yanufi asibiti.
Aunty kuwa tunda tabar Daining ta shiga daki take tunanin mafita amma takasa samu hakika yanxu tana cikin damuwa duk shekarun da tayi tana shirya shirinta Gashi yana Neman ya lalace gashinan mommyn yara tana Neman bata matsala amma mafita dayace kawai ta kirawo kawarta hajiya saratu ta bata hakuri daga nan se su samu mafita ,dan ita sam atsarinta bataso Waheed yayi Aure.
_______wayarta ta Dakko ta bugawa Hajiya saratu aikuwa bugu biyu tayi aka Daga, Daga Daya bangaren naji ance waye yake magana?
"Aunty tace hajiya Aunty ce tsaki naji anja sannan aka katse wayar ta sake kira amma ba,a Dauka ba haka taita kira amma ba,a Dauka ba can kuma sai Aunty taji wayarta na kara cikin rawar jiki ta Daga tace hello kawata Dan Allah kiyi hakuri komai yawuce Dan Allah yarinyarma Da akeyin abin akanta ta mutu mudawo kamar da kinji Aminiyata.
Hmmmmn dama nafada miki Ni kujerace dole axo azauna akaina sai abu ya ƙwabe miki xakixo gurina ko "a'a wllh kawata ba haka bane ba nidai ina baki hakuri akan abunda yafaru abaya.
To ai shikkenan na hakura Amman idan kika kuskura kika kara nidake har abada"baxa ayi haka na kawata ,nandai suka cigaba da tautaunawarsu.
Kiran wayar khamees ne yatashe Ni daga barci dagawa nayi tare da yin sallama,amsamin yayi yace dan Allah abokina idan kana kusa kaxo ka rakani wata unguwa in anjima ,ohk kawai nace masa na kashe wayar domin inaso nacigaba da yin barcina .
Da yamma bayan nadawo daga gurin aiki na biya gidansu khamees ina shiga kuwa natarar dashi yasha kwalliya tambayarshi nayi ina zamu ?saice min yayi rakashi gidan su budurwarsa xanyi,hade rai nayi sbd Ni bana son xuwa irin guraren nan to kenan ma yamayar dani dan rakiyarsa?nace masa dama sbd hakane ka katse min aikina aikuwa da nasan hakane da baxanxoba nafada ina mai galla masa harara,murmushi yayi min yace min ai dan nasan idan nafada maka baxa kaxoba yasa ban fada ba nidai dan Allah kaxo muje,ba yacce na iya haka na bisa sbd ya hadani da Allah .
Muna Isa muka yakirata awaya yace gamu a Kofar gida .
Yusra ta karaso tace sannunku cikin sakin fuska suka amsa yusra tace lalala yaya Waheed yau kainake gani Waheed ya kuramata ido yana kokarin tuna wacece?
yace kai kaddai Yusra ce ta girma haka Yusra tayi murmushi tace itace wlhi yaya, Waheed yace ah lallai London ta karbeki kinga yanda kika girma kuwa cikin barkonci yake tsokanarta yace wlhi dole nema Abba yasamo mana siriki mu aurar dake wannan irin girma haka yafada cike da xolaya.
" Yusra tace kaima Dai kafada yakamata ma a aurar damu tare tunda tazararmu shekaru biyu ne " hakadai yayi ta tsokanarta , khamees wanda yaxuba musu ido yana mamakin dama sunsan juna ne ?wai kardai kuce min kunsan juna ?munsani ma dear dan abokin aminin babanmu ne shi to London din dana tafi yasa Bama ganin juna sai yanzu,Bara na kira muku Jiddah da feenart suxo sugaishe ku , Waheed yace a'a ba sai ankira suba,Amman khamees yace a kirasu,aikuwa Yusra ta kirasu,saigasu sunxo kuwa kyawawan ƴammata,gaishe su sukayi suka amsa musu
Yusra tace yaya Waheed to ga Jiddah nan ga feenart nan autan momy ,kallansu Waheed yayi yana mai mamakin girmansu kamar basune wa'yannan yan kananunba,Masha Allah yanxu sune suka girma haka ,su kuwa su feenart sun kuyar da kansu sukayi wai sunji kunya,Yusra tace eh w'lh ga Jiddah ma ansaka ranar ta da Dr Jamal dan yayan babanmu ,kai Masha Allah Allah yasa ayi damu khamees yafada .
to sai anjima to kugaishe da su momy ,insha Allah xasuji.
Waheed kuwa sai satar kallon feenart yakeyi harsuka shige gida bayan sun shiga gida ne su Waheed sukayiwa Yusra sallama suka nufi mota harya shiga motar sai kuma ya fito ya kwankwaso kofar gate Gidan, mai gadi yana budewa ya mika masa Leda yace Dan Allah baba kabawa Yusra "baba mai gadi yace to" khamees yazaro kudi yabawa baba mai gadi " baba mai gadi yadinga yi masa godiya yatafi " yana tafiya baba mai gadi yakaiwa Yusra sakonta " aikuwa ta bude tana budewa taga sarƙa mai Dan karan kyau ta gold kirar Dubai Yusra sabida tsabar murna batasan sanda tace wow my Dear Thank you Thank so much I love you my lovely khamees.
Bayan su Waheed sun tafi suna mota khamees ya dinga bawa Waheed labarin gidansu Yusra amma Waheed jinsa kawai yakeyi shidai tunanin feenart yaki barin zuciyarsa har suka rabu da khamees tunani yakeyi tunowa yayi da maganar khamees inda yake cemasa mutumina kodai ka fada ne naga tunda su feenart sukaxo suntafi da imaninka" cikin sauri Waheed yace haba Dai sai kace kai murmushi yayi yace nasan ma ba sonta nakeyi ba wata zuciyar kuma tace masa to meyasa kake damuwa da ita nanma yace inajin tausayinta nakeji sai kuma yace to ai ba abin tausayi tazama ba yakasa bawa kansa amsa Don haka ya kawar da tuninta ta hanyar cigaba da tukinsa,har yakai khamees gida sannan shima yajuya xuwa gida .
yana isa gida yayi horn mai gadi ya bude masa yashiga kai tsaye part dinsu ya wuce seda yayi wanka cikin kananan kaya ya fito yayi kyau sosai kamar ka saceshi yana shiga ya Darect Daining yawuce yafara zuba abinci alala akayi da miyar ganyayyaki wacce taji kifi da nama yafara cin abincinsa.
Aunty kuwa bayan sunyi waya da hajiya saratu daxu akan yau zata zoo Amma tace ta kirawo Rukayya aikuwa ta kirawo ta (yar kanwar aunty ce).
Waheed yana cikin cin abinci yaji karar takalmi dan juyowa yayi ,suka hada ido da Rukayya kallo daya yayi mata ya Dauke kansa daga inda take, ita kuwa farin cikine ya mamaye zuciyarta aranta tace wow ya Allah ka mallakamin wannan bawan naka tana karasawa tace la yaya abinci kakeci ɓata rai yayi yace Eh karasowa tayi tace yaya xanci shidai Waheed yana mamakin hali irinna Rukayya ace mace batada kamun kai aransa yace kai wannan mijinki yashiga ukunsa tashi yayi yabarmata gurin ya haye sama Dakin mommy, yana hawa ya tarar da Abdallah akan cinyarta yanata shagwaba bai kulashiba yafara gaishe da momy ta amsa sannan su cigaba da hirarsu duk Dai Rabin hirar da takeyi masa akan yayi kokari yayi aure CE.
Bayan hajiya saratu ta iso Aunty tajata part dinta suna shiga seda ta huta Sannan,Suka fara magana Aunty tace hajiya yanxu menene mafita hajiya saratu tayi murmushi tace...................?
tace mafita ɗaya ce shine aure yakamata mu hada Waheed da Rukayya ta wannan hanyar CE kawai zamu samu abinda mukeso" Aunty tace wai tsaya hajiya aure dawa wace rukayyan? Hajiya saratu tace Rukayyar ki mana" taya kike ganin zan hada Rukayya jinana da Dan maƙiyata karfa ki manta Rukayya yar kanwatace ciki daya kuma muna ji da ita taya zan hadata aure da Waheed mutumin da nafi tsana kuma Dan kishiyata" hajiya saratu tace dadina dake kenan baƙyabin shawara kinsan mene ma,anar yin haka ne ? to yakamata kisan cewa ta wannan hanyar ce kawai zamu iyayin yaki da mahaifiyar Waheed dakuma yaranta " Aunty tayi murmushi tace to ƙawata inajinki" hajiya saratu tace yauwa ƙawata kinsan meye hiki mata tayin hakan inason mu hada Rukayya da Waheed aure ne Domin musamu cikon burinmu da mukayi shekara da shekaru muna son cikashi ta wannan hanyar na tabbatar zamu samu cikon burinmu hajiya saratu taciga da magana tace abinda za,ayi shine dolene sai kin sakko kin lallaba kishiyarki ta amince da aurannan sannan zaki cusawa Rukayyar son aurennan Domin karta bamu matsala" Aunty tayi Dariya tace kawata inajinki to me zamuyi musu" hajiya saratu tace idan muka hadasu aure zamu bari har sai ta samu ciki ta haihu daga nan saimu kashe alhaji da Waheed ta ruwan sanyi wato zamusa azuba musu guba acikin abin shansu su duka ukun harda kaninsa bayan mun kashe su saimu haukata Momyn su Waheed tabi Duniya shikenan Dukiya ta dawo hannunmu.
Daga taskar Nusaiba Abdullahi alkamawa ✍️
Masuson cigaban wata sakayyar kofa abude take suyi min mgn .
Share