https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥
Har ta kusa Fita palourn ta tuna da wayar Mommyn nan Nokia,Sehrish zata iya kira Kuma in har tabar wayar za'a samu matsala,Juyawa tayi ɗauke dashi ta koma saman Sofa ɗin ta ɗauki nokia ɗin ga wayar Junaid duka ta haɗasu Sae faman nishi takeyi,tana ƙoƙarin kama Hanya ta fuce,Hajiya Sarat ta bude Ƙopar A fujajan ta fito,waro ido waje Amrish tayi a wani irin Firgice ta watsa da gudu tamkar ba mutun ta ɗauko a kafaɗarta ba,Lokacin Da Hajiya Sarat ta ankare da Junaid dake sa6e a kafaɗar Amrish,Wani irin kukan Kura tayi da dukkan ƙarfinta ta watso a guje irin gudun nan na fitar hayyaci,Cikin Rashin sa'a tana Sanya ƙafarta saman benen,Tamkar an ja ƙafarta gaba ɗaya ta burkice,a jirkice ta sulalo daga saman benen,kanta yayi Mugun buguwa,Qugunta kuwa sae dai muce Allah ya kyauta,
Amrish kuwa tsabar tsoro ko waiwaye batayi ba,lokacin data faɗo entry hall na gidan,Da gudu ta nufi gate,A lokacin baba mai gadi yana yin alwalar sallar Azhar da aka fara kira,Koda yayi arba da Su Amrish Baiyi tsammanin mutane bane,Wurgi yayi da butar hannunshi ya watsa da gudu zai shige ɗan ɗakinshi Ya ɗauko sandar shi,
Daƙyar Amrish ta iya buɗe baki tace"Baba Mai gadi ni ce,Dan Allah kataimake ni,Ka tsaida mana Taxi mu kaishi asibiti kada ya mutu,"dakatawa baba mai gadi Yayi a sukwane ya juyo yana kallonta,Sae lokacin Ya gane ta,kuma ya gane yaron nan ne na jiya ta ɗauko,ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta fashe da kuka tana faɗin"Baba mai gadi kashe mu zatayi,In har bamu bar gidan nan ba,"
A hanzarce Baba mai gadi ya buɗe mata ƙopa suka fita,har zai tsaya ya tuna cewa Shine yaba Amrish Labarin Yaron,kenan shima Yana cikin hatsari,aikuwa da gudu ya bi bayan Amrish suka miƙi hanya suna neman Abun hawa,A ƙarshe daya ga ta jigata shi ya kar6i Junaid ya ɗaura shi a kafaɗarshi,Babban tashin hankalin tunda suka fito Unguwar babu kowa wayaam dama haka unguwannin ƴan gayun nan suke,Da ace irin geto ne da tuni jama'a sun agaza masu,ɗaiɗaikun mutanan dake wucewa duk wanda yayi arba dasu Amrish saiya watsa da gudu kamar sunga Aljanu,saboda ƙurar da ta 6ata masu jiki,
Da iya ƙarfinta Na ƙarshe ta daddage ta miƙe,ɗago kan da zatayi keda Wuya haƙorinta ɗaya ya 6allo jaga jaga da jini,qugunta ya ruƙe sosai,wani irin azababben raɗaɗi,daƙyar ta samu ta fara jan jiki a galabaice ta nufi wayarta dake ajiye saman sofa,jikinta sai tsuma yake yi,daƙyar ta iya cire password ɗin wayar,Call log ta shiga ta kira wani layi da akayi mashi saving da ƙare kukanka,Daƙyar take magana saboda ciwon bakinta,
"Duk yarda za'ae karku bari yarinyar nan tabar cikin unguwar nan,Nasan zaiyi wuya su samu abun hawa,da ita da yaron Gawarsu kawai nakeso ku kawo mun...."tana magana tana goge zufar goshinta,ga wani irin huci dake fita abakinta,.
"Akwai ƙaramar nokia ɗita a hannunta,Zan tura maku Lambar wayar kuyi tracking ɗinta,"ta ƙarasa maganar tare da yin rejecting ɗin kiran,Gaba ɗaya Amrish ta ɗaure mata kai,saboda ta ɗauketa Shashasha,A irin rainon da tayi ma Amrish irin sangartattun nan ne,bata da wayau haka,Sai gashi yau ta bata mamaki,wai har tasan ma inda suka 6oye shi,koya akai duk tasan wannan?
Lokacin da Su Amrish suka haura saman titi,suna neman abun hawa,duk mai motar da suka tsaida sai yaƙi tsayawa,Baiwar Allah duk tabi ta ruɗe gashi sam taƙi tunanin yarda nokia ɗin Hajiya sarat data ɗauko,kuma ta hanyar bin diddigin layinne kaɗai za'a san Location ɗin da suke,
Suna cikin wannan tsayuwar,wata danƙareriyar mota ta shawo kwana da gudu,bata tsaya a ko'ina ba sai agabansu Amrish,mutuwar tsaye tayi lokacin,shi kanshi baba maigadi ya firgita da ganin motar,Jim kaɗan mamallakin Motar ya fito jikinshi sanye da fararen kaya hatta takalmanshi,Facemask ɗin fuskarshi Ya hana Amrish ta gane shi,
Yayi mamakin ganinsu cikin wannan halin,bai tsaya tambayarsu Lafiya ba Kawai ya buɗe masu bayan motar,badon ta yarda dashi ba hakanan dai kawai suka shiga cikin Motar tunda ba yarda zasu yi,a back seat na motar ta shiga baba mai gadi ya jinginar da junaid a tsakiya kafin shima ya shiga,Mai motar ya fusgi motar da gudu,a dai dai Lokacin motoci guda uku masu blank tunted ƙirar Range rover suka bi bayan motar shi,da wani irin mahaukacin gudu mutumin ke tuƙa motarshi,yarda kasan filin ƴar tseral haka motocin nan suke gudu asaman titi,
Amrish sai kuka takeyi tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na ranar,ba komai ya ƙara tsoratar da ita ba fa ce Harbin bindiga da taji a bayan motarsu,Ya salam!gashi hanyar da suka biyo babu ƴan sanda balle su samu taimako,
Ɗaya daga cikin Ƴan ta'addan da suka biyosu wanda ya buɗe murfin motar ya miƙe a tsaye hannunshi ruƙe da irin wannan bingidar mai fitar da bullet kamar bomb,kwakkwaran Saiti Yayi ma Motarsu,Yana sakin Bullet ɗin mai girman gaske nan take Ya hau saman motarsu Ya fashe gaba ɗaya Wuta ta kama ci a bayan boot ɗin Motar,Hakan yasa motar ta dakata da tafiya,ganin sun ci nasara akansu yasa suka tsayar da motocinsu,Suka diddiro daga cikinta kusan Su takwas ne,Ƙirar jikinsu gwanin ban tsoro,babu ɗigon imani akan fuskarsu,kowanne hannunshi ruƙe da manyan makamai,
Suna ƙarasowa gaban motar,ɗaya daga cikin samudawan nan ya damƙi murfin motar ya 6alleshi,hannu yakai tare da damƙo rigar mutumin dake acikin motar ya wurgoshi waje,basu tashi ankara ba,Sae da Mai tuƙin motar ya fito yana faman ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una,Leƙa cikin motar sukayi Wayaam basu ga Amrish da yaron ba,Ashe Ba motarsu bace,Sunyi mistake Saboda mai wannan motar da suka kama iri ɗaya ce da motar da suka bi su Amrish,
Da sauri Suka koma cikin motocinsu,A guje suka ja motar,Sunbar bayin Allah da aikin neman taimakon kashe masu wutar motarsu,don ma Allah yasa babu wanda ya raunata acikinsu,
A 6angaren Su Amrish kuwa,mutumin dake tuƙa motarsu ne ya umarce ta data jefar da wayoyin hannunta gaba ɗayansu,nan take ta zuge glass ɗin motar ta wurgar dasu waje,Bayan ta jefar dasu sai ya Canza hanya da wani irin gudu yabar titin,Su kuma waɗannan miyagun da suka fara yin tracking ɗin Layin wayar Hajiya sarat na ƙaramar nokia ɗin da aka basu,Ta hanyar laptop ɗin dake a hannun wani kwararre acikinsu,Sae location ɗin ya dinga nuna masu hanyar da Amrish ta jefar da wayoyin,Nan fa suka miƙi hanyar cike da sa ran zasu kamasu,Lokacin da motarsu ƙare kukanka ta ƙarasa inda Location ɗin Ya basu,Sai suka tsayar da motocinsu,A zafafe suka fito suna waige waigen neman inda suka ajiye motarsu,Sai da suka gama shan wahalar nemansu a Area ɗin wurin abun takaici sai ga wayoyin sun tsinta yashe a ƙasa,Rai a matuƙar 6ace suka hanzarta komawa cikin motocinsu batare da sun ɗauki wayoyin ba,Nan fa suka ruɗe saboda hanyoyi ne guda uku,Ta hannun dama da kuma ta hannun hagu,Ga kuma wadda ta mike straight,To fa sun ruɗe a wannan lokacin,Basu san ta wace hanya su Amrish suka bi ba,A ƙarshe kawai suka raba motocinsu dama guda uku ne ɗaya tabi straight,ɗaya tabi Left ɗayar kuma tabi Right,Don sunsan Dole a ɗaya daga cikin hanyoyin suka bi,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 2 na rana,
Wayar Ishaq ta soma ringing,A lokacin dawowarshi kenan daga wurin aiki,Buɗe mashi mota sergeant Yayi Ya fito daga cikin motar hannunshi ruƙe da wayarshi,picking call ɗin Yayi tare da kara wayar a kunnanshi,
Fuskarshi ɗauke da murmushi ya soma magana"Mutanan Damaturu,Sai yau ake jinku"?
On the other hand Hafsat tace"Wlh Daddy fushi nake dakai,you forgot about me,"
"Nima ae fushi nake dake,tunda na baro damaturu kin ƙara kirana ne?Ko irin Morning message ɗin nan babu ko,Yanzu da ace ban kiraki ba da shikenan bazaki neme ni ba,"ya ɗanyi maganar yana ɗaure fuska kamar tana agabanshi,
"Shikenan na ɗauki laifin,Am so sorry,Amma daddy meyasa ka canza Layinka?in na kira wancen Mtn ɗin bana samun shi"
"Kinga yanzu na dawo daga wurin aiki,Agajiye nake,bari na ɗan samu natsuwa I will call u later,"
A ɗan shagwa6e tace"dan Allah Daddy,idan ka huta kada ka manta ka kirani akwai maganar da nakeso nayi dakai,"
"Toh,"ya amsa tare da kashe kiran Ya nufi cikin gidan aranshi yana faɗin"yanzu haka saboda Mommynta ne yasa ta kira ni,lokacin daya shiga gidan ya yi mamakin yarda aka gyara mashi ko'ina fess,murmushi ya dinga saki don ya san cewa aikin hajjaju ne,wani irin ƙamshi ke tashi acikin palourn,
Ga lafiyayyen abinci An jera mashi asaman dining,Dama da wata matsiyaciyar yunwa ya dawo,A hanzarce ya haura upstairs ya shige Bedroom ɗinshi,Bayan ya rage kayan jikinshi ya faɗa cikin toilet,Within mins Ya fito Ya kimtsa kanshi cikin jallabiya,Saukowa Downstairs Yayi kaitsaye ya nufi dining ya zauna,Da kanshi Yayi serving ɗin abincin ya zauna yana ci yana murmushi kamar wani zautacce,Sai da ya kammala cin abinci,tukunna ya koma saman Sofa ya zauna tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,
Wayarshi ya ɗauko ya lalubo Layin Hafsat ya danna mata kira,Kamar jira takeyi ta ɗaga kiran,
"Daughter ina sauraronki!maganar menene kikeson Yi dani"?
"Daddy dan Allah ka taimaka,Nasan zaiyi wuya ka fahimceni,wlh Mommy tana cikin mawuyacin hali,Ta zama abun tausayi,ta kira ni da wani layi jiya tana kuka tana rokona cewa inyi maka magana ka yafe mata,Ta gane kuskurenta,Rayuwarta ta wulakanta Daddy a gefen bishiya take kwana zaune ba bacci,dare da rana a wurin nan take Yini......."
Tunkan Hafsat takai ƙarshen Maganarta,Ishaq ya katse ta"ke yanzu kin yarda da maganarta?Kodai kun haɗa baki ne da ita?
Da sauri hafsat tace"Wlh daddy da gaske take,Ae nasa ta ɗauko mun video ɗinta,Wayarma fa aronta takeyi don ta kiramu,Zan tura maka video ɗin ta whatsapp yanzu,zaka shaida abunda nake faɗa maka,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da cewa"its okey,Am waiting for the video,"yana kai ƙarshen maganar ya katse kiran,Kafin Ya kunna wifi ɗinshi ya shiga whatsapp,Messages ne suka fara shigowa cikin wayar,can sai ga saƙon hafsat ya shigo,
Chat ɗinsu Ya shiga,Anan ya samu video ɗin data tura mashi,yatsanshi yasa ya ɗan ta6a video ɗin nan take Ya soma loading,ƙura ido Ishaq yayi akan Screen ɗin wayar yana kallon video ɗin,
Bai ta6a tunanin zaiga laila a irin wannan ƙasƙantacciyar rayuwarba,a gefen bishiya take zaune,gefenta kwanon bara ne,ƙafarta ɗaya ta lalace babu kyan gani wani irin ruwa ke fita acikinta,Sae kuka takeyi tana magana
"Don Allah Ishaq ka taimaki rayuwata,ba don halina ba,dan Allah da manzonsa zakayi,Nasan nina jefa kaina cikin wannan halin,Ku kalli irin wurin da nake rayuwa,kowa ƙyamar taimakona yake yi,babu mai son zuwa wurina saboda warin da nake yi,"_
Saboda tsabar tashin hankali,Da sauri Ishaq ya kashe video ɗin tare da yin wurgi da wayar saman sofa ɗin,
Jingina bayanshi Yayi ajikin kujerar,tabbas Yaji tausayinta amma abunda ya ɗaure mashi kai shine taya akai taje Enugu!Uban me yakaita?don a iya saninshi bata da wata alaƙa da garin,Ya jima a haka kafin Ya ɗauki wayar Ya sake kiran Hafsat,
Tana ɗaga kiran Yace"Naga video ɗin,wlh hafsat ba don zuciyar musulunci ba,babu abunda zaisa na taimaki Laila!ke bari in faɗa maki zan taimaketa ne kawai Saboda Allah!Taci albarkacinki hafsat!Zansa a ɗaukota akaita asibiti,Inyaso ko ƙafarce su cireta A maidata maiduguri,Amma ni bazan sake rayuwa da laila ba,"
Fashewa hafsat Tayi da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,daƙyar ta samu ta tsagaita da yin kukan tace"Nagode sosai Daddy,koma miye laifinta ne,ita taja ma kanta,naji daɗi sosai Daddy Am really proud of u,"
"Yaushe zaki dawo gida!kinsan cewa hutun aikin da kika ɗauka ya qare ko"?
"Eh daddy,Ina nan ina shirin dawowa amma yanzu gidan bazaiyi mun daɗi ba,nafison na zauna a wurinsu Abba,tunda ga ƴan uwana acikin gidan inyaso sai ka nema mun transfer na dawo aiki a Abuja,"
"Idan kika koma Abuja,ni kuma fa?nikaɗai akeso inyi ta zama a kaduna "?
A ɗan shagwa6e hafsat tace"idan zaka ƙara aure,Sai in dawo nan,"
Murmushi ya saki anzo dai dai inda yafi so,
"Calm down ur mind,just ki dawo gida kawai,Cikin ƴan kwanakin nan Nima zanyi aure,"
Yana jiyo sautin dariyarta,alamar taji daɗin maganarshi,sun jima suna waya kafin suka Yi sallama,
*Boss Bature*
*AMANI*
Tana kwance saman gadonta,Amal ta faɗo cikin ɗakin Hannunta ruƙe da wayarta,hawa saman gadon tayi har zuwa inda Amani ke kwance tana sharar bacci,Hannu tasa tana bubbuga ƙafarta,
"Aunty Amani!ki tashi ana kira,"
Daƙyar ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,sun ɗanyi jawur dasu,rai a6ace ta kalleta"Bana hanaki tashi na daga bacci ba in aka kira ni"?
Sunnar dakai Amal tayi"Am sorry,dama Aunty hayaam ce ta kira tana kuka......"hankali aɗan tashe Amani ta yunƙura tare da mikewa zaune tana faɗin"kuka kuma!Allah yasa lafiya,"ta ƙarasa maganar tare da kar6ar wayarta da Amal ke miƙo mata,
Call log ta shiga,Anan taga kiran da hayaam tayi mata,
Calling ɗin layin tayi,bayan Hayaam ta ɗaga kiran Amani ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi sallama taji shessheƙar kukan Hayaam
"Subhanallahi!wai meke faruwa ne?hayaam ki buɗe baki kiyi magana mana,"a ɗan ruɗe tayi maganar,
"Kodai Wani ya rasu ne"?
Sai lokacin Hayaam ta soma magana"Aunty amani muna cikin masifa!munga rayuwa,rayuwarmu ta wulaƙanta a idon jama'a......"anan hayaam ta kwashe dukkan abunda Ya faru bayan komawarsu maiduguri ta sanar da ita,
Saukowa Amani tayi daga saman gadon tana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,.
"Allah yajiƙan Mammy,Allah ya gafarta mata zunubbanta,Amma banji daɗin irin mutuwar da tayi ba,ƙaddara ta riga fata,da kunsani tun farko baku barota ba,
Cikin shessheƙar kuka hayaam taci gaba da magana,
"Munaji muna gani,zama gidanmu ya gagaremu,Mutane sun ɗaura mana karan tsana,Yanzu haka a gidan Malam limam muke,matanshi sun tsanemu,suyi ta tseguminmu suna zaginmu,Abinci basu bamu sai in liman yana acikin gidan,Abra ma sai addu'a domin kuwa ta fara samun ta6in hankali,sai sambatu takeyi tana faɗin duk ita taja,Itace tayi silar mutuwar Mammy...."kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya cuyota,
Daƙyar Amani ta lallasheta"kuyi haƙuri ku rungumi ƙaddara,in sha Allah komai zai wuce,Yanzu nidai zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka maku,Ko gidan ne a gyara maku shi,kafin Allah ya kawo maku mazajen aure,don kuwa yin auren shikaɗaine rufin asirinku,in ba haka ba mutane bazasu daina tsangwamarku ba,"
(Wlh matsalar mutananmu kenan,idan mutun Ya aikata zunubi arayuwarshi yazo ya yi nadama ya shiryu,Sai su dinga tseguminshi suna ƙyamatarshi,Shi kanshi Allah daya halicce mu yana son bayinsa waɗanda suka Tuba daga aikata zunubi,Amma wasu mutanan da ruƙo, shiyasa wasu ko sun shiryun daga baya sai su koma ruwa saboda mutane,Wannan babban kuskure ne saboda mutane ka koma kana aikata barna,Makomarka zaka duba,In zaka tuba dan Allah zakayi,Dan kuma kanka,ba don mutun ba,a karshe ina mai jan hankalinmu da mu kiyaye harshenmu don zai iya jefamu a halaka,aduk lokacin da wata mummunar kaddara ta fada ma wani muyi Addu'a mu nemi tsarin Allah kada mu rinka zundenshi don muma bamu fi karfin Allah ya jarabemu ba,Allah ubangiji ya rabamu da mummunan kaddara yasa mufi karfin zukatanmu,Amin )
Sosai Hayaam ta shiga yi mata godiya,kafin daga bisani Su kayi sallama,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 6 na marece,Sehrish na kwance saman gadonsu abun duniya ya isheta,duk ta shiga damuwa saboda rashin samun kwakkwarar hujjar da zasu kama Azmee,tana cikin wannan zancen zucin taji an banko kopar ɗakin,A firgice takai idanuwanta kan mai shigowa,Jahad ce ta faɗo ɗakin fuskarta sharkaf da hawaye,a ruɗe Sehrish ta shiga tambayarta Lafiya,
"Bakisan meke faruwa ba,Ga Abba can ya yanke jiki ya faɗi rai hannun Allah,"jin wannan maganar yasa Sehrish ta sauko daga saman gadon jikinta na kerma ta nufi hanyar fita ɗakin,atare da jahad suka fita,
Abunda ya faru,Alex na zaune gefen gado tana jiran fitowarshi daga toilet,tun da ya shiga shiru bai fito ba,tun tana sa ran fitowarshi harta fara tunanin ko lafiya kusan Awa ɗaya da rabi yana acikin toilet ɗin nan,Miƙewa tayi ta nufi toilet ɗin tasa hannu ta kwankwasa ƙopar"Abban Junaid!"ta kira sunanshi da ƙarfi,Shiru bai amsa mata ba,a ƙarshe dai ta yanke shawarar shiga ciki,tana tura ƙopa ta same shi kwance saman tiles,idanuwanshi sun jirkice,jikinshi sai kerma yake yi,Fasa ƙara Mommy tayi anan ta zube tana jijjigashi,Ganin cewa dagaske fa baya acikin hayyacinshi yasa ta miƙe da gudu ta fito daga ɗakin tana kuka,
A lokacin Abusufyan da abu suna zaune a main palour tare dasu Hosana da Jahad,Tun daga kan yarda ta faɗo falon Yasa su miƙewa suna tambayar lafiya,Kasa buɗe baki tayi sai dai nuna masu hanyar bedroom ɗinshi da tayi duk tabi ta ruɗe,da gudun gaske Abusufyan ya nufi ɗakin tare da abu,suna shiga ciki dama ƙopar toilet ɗin abuɗe Mommy tabarta,nan suka sameshi cikin mawuyacin hali,sunyi matuƙar girgiza,Cuccuboshi Abusufyan yayi ya fito dashi daga cikin toilet ɗin,Ya janyoshi zuwa saman gadon ya kwantar dashi,jiki na rawa Ya curo wayarshi saboda ruɗu daƙyar ya iya lalubo Layin Sgr ya danna mashi Kira,Sai daya bi kowannansu Ya sanar dashi halin da Mahaifinsu ke ciki,
A lokacin dasu Sehrish suka faɗo falon Ya yi dai dai da shigowar Omar da Sgr,da gudun gaske suka shigo kaitsaye suka nufi bedroom ɗin Abbansu,wucewarsu keda wuya Kanal yousouf ya faɗo falon da gudu shima Ya wuce part ɗin,gaba ɗaya sai da matasan gidan suka hallara a ɗakin,wasu tuni sun fara zubar da hawaye,tsoransu kada su rasa mahaifinsu a wannan halin da suke ciki,sae faman ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un suke yi,
Fawan dasu twins kuwa tuni sun fara kuka kamar wasu ƙananun yara,
"Addu'a zakuyi mashi ba kuka ba,in sha Allah zai samu lafiya,"acewar Abusufyan shi kanshi dauriya kawai yake yi,don kada suga rauninshi,hakan zai ƙara tayar masu da hankali,
yanke shawarar kaishi Asibiti suka yi,Sgr ne ya ɗauke shi asaman kafaɗarshi,Sauran suka bi bayanshi,
Suna fitowa entry hall ɗin gidan,da gudun gaske armstrong ya buɗe mashi mota ya kwantar da Abbansu aciki,Sannan ya bude mashi front seat ya zauna,Jan motar yayi da gudun gaske motar Marshal tabi bayansu,Motocinsu Kanal yousouf suka rufa masu baya,hada Oummansu Sehrish aka tafi asibitin a motar fawan ta zauna tare da Jahad da Hosana,Mommynsu Junaid kuwa tana a motarsu Abusufyan sai lallashinta Yake yi,duk ta shiga damuwa alokacin motocinsu suka fita daga babban gate ɗin gidan,mutun uku aka bari a gidan Aunty Azmee dake kumshe a ɗakinta,Sae Haroon dake kulle a medical room dinsu,
Sehrish bata samu tabisu ba,daga komawa ta ɗauko mayafinta sai dai tajiyo tashin motocinsu,kamar tayi hauka lokacin da ta fito waje bata samu motar ɗaya daga cikinsu ba,anan ta zuƙunna gaban ƙopar palourn tana kuka,ga tsoron shiga gidan da takeyi,
Da wata irin jiniya motocinsu suka hau saman titi a jere,Lokacin da suka ƙaraso Katafaren Asibitin Sgr,Sai suka tsaida jiniyar,a hanzarce bayan sunyi parking ɗin motocin nasu,Sgr ya fito Ya ɗauki Abbansu,sauran ma suka fito gaba ɗaya suka wuce cikin asibitin,Zo kaga taron nurses da likitoci,Ai tunda suka ji isowar Sgr kuma suka ji cewa Mahaifinshi ne baida lafiya,nan fa sukayi dandazo domin duba lafiyarshi,
A wani katafaren ɗaki suka kwantar dashi,kusan likitoci shida ne akanshi daga cikinsu hada Doctor Emran,
Sgr baisamu shiga ba,saboda a halin da yake ciki a yanzu bazai iya duba Abbansu ba,yana cikin matsananciyar damuwa saboda yasan dalilin ciwon Abban nasu,dama yace su fara ƙirgen kwanakin mutuwarshi,in har basu dawo mashi da yaronshi ba,
A saman waiting seat suka zazzauna suna jiran tsammani,Omar da Sgr suna a tsaye,Kowa ka kalli fuskarshi gwanin ban tausayi,
"I can't forgive my self,idan har Daddy ya mutu silar 6oye mashi mutuwar Junaid da mu kayi,"Ya ƙarasa maganar yayin da idanuwanshi suka cicciko tab da hawaye,
Ruƙo hannunshi Omar yayi"bakai kaɗai ba Rafayet,nima bazan yafewa kaina ba,in har muka rasa shi,wlh i ave regretted already,Da mun sani tunfarko mun sanar dashi gaskiya kawae tunda dama gudun hakan yasa muka 6oye mashi,"gaba ɗaya duk sun sha jinin jikinsu,
"Dan Allah kukan ya isa haka,twins,fawan da irfan,in na sake jin shessheƙar kukan wani acikinku wlh zaku koma gida ne,"kanal yousouf ne keyi masu faɗa,.
"Sai kace ba musulmai ba!maimakon ku tayashi da addu'a amma kun dage sai kuka kukeyi,"ya ƙarasa maganar tare da jan guntun tsoki,idanuwanshi cike tab da kwalla,
Abu kuwa sai faman lallashin Mommy takeyi,ganin yadda take ta shar6ar kuka,
Abusufyan ne yace"don Allah Aunty kidaina,kina ƙara tayar masu da hankalinsu,keda yakamata ace kina lallashinsu,"hannu tasa tana share hawayen fuskarta,juriyarce bazata iya ba,ita kaɗai tasan yarda take ji acikin zuciyarta,
Fitowa Doctor emran yayi daga cikin ɗakin da aka kwantar da Abbansu,Aikuwa da sauri suka tunkareshi,kowa yana tambayar ya jikin nashi,
"Ku kwantar da hankalinku,Yana samun sauƙi,Addu'ar ku kawai yake buƙata,"yakai ƙarshen maganar tare da aza idanuwanshi kansu Sgr da Marshal"ina son ganinku a office,"
Tunda suka ji haka sai jikinsu ya ƙara yin lakwas,gaba Dr emran Yayi suka bi bayanshi,har izuwa Office ɗinshi,Wuri ya samu ya zauna,kafin suma suka zauna suna fuskantarshi,
A tsanake ya soma yi masu bayani"nasan kunsan meke damun mahaifinku,damuwa ce akan rashin Junaid,Yanzu haka dana baro ɗakin,Sambatu yake yi yana ambaton sunan shi,"dakatawa ya ɗan yi da bayani yana kallonsu,jikinsu sai tsuma Yake yi,
"Jinin shi ne ya hau sosae,Ga kuma Ciwon zuciya dake barazanar kamashi..."
Tunkan emran yakai ƙarshen maganar,Omar ya dafe kai jikinshi na kerma,jikinsu Ya gama mutuwa,
"Yanzu ya zamuyi kenan?menene solution"?Sgr ne yayi tambayar,
"Akwai matsala fa,saboda ya ƙwallafa ranshi akan son yaron,Idan har ba ganinshi Yayi ba,tofa sai dai abishi da addu'a,"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"miƙewa Sgr yayi da sauri ya fice daga Office ɗin,gaba ɗaya sun rasa inda zasu tsoma ransu suji daɗi,
Miƙewa Sehrish tayi daga zuƙunnan da take abakin ƙopar palourn,Hannu ta zura acikin aljihun rigarta,ta curo wayarta don ta kira Jahad taji Ya jikin Abban nasu,
Tana kunna wayar,ta shiga Call log anan ta samu missed calls da baƙuwar number,har kusan sau 10 aka kira,Batasan number ɗin wanene ba,Har jaraba kiran Layin tayi wayar nata ringing ba'a ɗaga ba,
Bayan kiran ya katse ne,ta lura da message ɗin da aka turo mata,Da sauri ta buɗe saƙon ta soma karanta shi kamar haka,
__Sehrish na kira layinki baki ɗaga ba,Amrish ce inason magana dake game da ɗan uwan nan naki,dan Allah idan kinga saƙon nan ki kira ni_
Abun ya ɗaure mata kai,tunani ta shiga yi wani ɗan uwanta ne Amrish ke magana akai,sake kiran Layin tayi wayar ta dinga ringing amma ba'a ɗaga ba,
Katse kiran tayi,tana ƙoƙarin juyawa ta koma cikin gidan kira ya shigo layinta da baƙuwar number,da sauri ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta,tunkafin tayi sallama muryar Amrish ta katse mata hanzarinta,
"Sehrish kina ina ne!ina ta kiran Layin wayarki amma baki ɗaga ba,magana ce akan Junaid na tura maki Address ta message,kibar komai kikeyi kizo ki same mu"tana kai ƙarshen maganar ta katse kiran,
Wani irin faɗuwar gaba Sehrish taji,Abun ya matukar ɗaure mata kai,musamman data ambaci sunan Junaid,
Hannunta na kerma ta shiga duba message ɗin da aka turo mata,kwatancen inda zata same su ne,
Tarasa ya zatayi,ita dai ba mota gareta ba,gashi babu wanda ya rage acikin gidan balle ya kaita,kama hanya tayi ta miƙi titin da zai sadaka da babban gate ɗin gidan,Sae faman zumbula sauri take yi,Sai da tasha wahalar zuwa babban gate ɗin,Sojojin dake tsaron gidan suka hanata fita,kamar ta fashe da kuka,
A dole ta shiga kiran layin matasan gidan,Duk wanda ta kira bai ɗagawa,har Abusufyan ta kira shima bai ɗaga kiran ba,
Sai da ƙyar ta samu Hosana ta ɗaga kiranta,da sauri ta kara wayar a kunnanta,
"Hosana Ya jikin Abban"?
"Nima bansani ba,Sun shiga dashi ciki,"
"Dan Allah idan akwai wani kusa ki bashi wayar,"
"To"ta amsa mata,jim kaɗan taji muryar Kanal yousouf,
Sai da ta fara tambayarshi jikin Abban nasu,Ya sanar da ita cewa da sauki,tukunna tace"Gani nan zan fito gida an hanani,dan Allah ka taimaka kasa su barni na fita,nima asibitin zanzo,"
"Ki basu wayar,"Cire wayar tayi daga kunnanta ta miƙa ma ɗaya daga cikin sojojin,ya kar6a su kayi magana dashi sannan ya miƙa mata wayar,"Zaki iya tafiya,amma yace kada abarki ki fita ke kaɗai,don haka wani daga cikinmu zai ɗaukeki a mota ku fita,"
Ba ƙaramin daɗi taji ba,dama ƙarfin hali ne kawai,ko kuɗin abun hawa bata dashi,
Anan ta tsaya,wani sergeant ya ɗauko mota ta buɗe ta shiga ciki ya tashi motar,saida suka hau saman titi sannan yace"Madam ina zuwa"?
Karanto mashi Address ɗin wurin tayi kamar yadda Amrish ta rubuto mata a saƙon,
Wani private hospital ne suka shiga,sojan ya fito ya buɗe mata ƙopa ta fito daga ciki,a bakin ƙopar shiga ciki ta samu Amrish a tsaye hannunta ruƙe da waya,wani irin farin ciki ne ya lullu6e Sehrish da gudun gaske ta nufeta,rungume juna sukayi nan take Amrish ta fashe da kuka,
Ɗago da ita Sehrish tayi tana tambayarta lafiya,
"Amrish dama kina nan?layinki kona kira bana samu,meya sameki ne?me kike yi a asibitin nan ne"?
Cikin shessheƙar kuka Amrish tace"mu shiga daga ciki ki gane ma idanuwanki,"
Ta ƙarasa maganar tare da janyo hannun Sehrish suka shiga asibitin,A A&E aka kwantar dashi,a bakin ƙopar ɗakin Sukayi kici6us da Ya Mu'allim malamin da take ta nema,
Cike da mamaki ta ambaci sunanshi"Ya mu'allim,"fuskarshi da alamun damuwa atare da ita,Ya amsa mata"Na'am,kina ta nemana ko"?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh
"Naga saƙon da kika turomin,idan muka samu natsuwa zamuyi magana,Yanzu dai ga ɗan uwanki can kije ki duba jikinshi,"
Gabanta ne ya faɗi rasss!,kawar da idanuwanta tayi daga kallon fuskar Ya mu'allim ta mayar da idanuwanta kan ƙopar ɗakin,mutun ta hango kwance an sanya mashi oxygen a hancinshi,yayin da hannunshi ke sanye da robar ƙarin jini,zuciyarta na harbawa a haka ta nufi cikin ɗakin,lokacin data ƙarasa gaban gadon tayi arba da fuskar Junaid,Sai ta yanke jiki ta faɗi a sume.......
Shigowa Cikin ɗakin Ya mu'allim yayi tare da Amrish,ruwan dake ajiye saman drawer din dake gefen gadon Ya ɗauka,Ya cire murfin ya tarfa ruwan a tafin hannunshi Ya watsa mata akan fuskarta,Nan take ta farfaɗo tana faman Sauke ajiyar zuciya,Yayin da take ambaton Sunan Junaid abakinta,Miƙawa tayi agaban gadon ta zube saman guiwowinta,kamar a mafarki haka take ganin Junaid,bazata Iya jurewa ba,fashewa tayi da matsanancin kuka yayin da take kallonshi,Dama sai da ranta ya bata cewa Junaid bai mutu ba,Yana araye,Ashe dagaske ne,tasha kuka ta gode ma Allah,Cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana kallon Ya mu'alim da amrish dake a tsaye,
"Taya akai junaid daya mutu ya dawo?a ina kuka same shi,A iya saninmu junaid yayi hatsarin mota Ya ƙone ƙurmus"
Jin wannan maganar yasa Ya mu'allim da Amrish suka kalli Junaid,har suna haɗa baki wurin cewa"Junaid Yayi hatsarin mota'?
Jinjina kai Sehrish tayi"Babbar motace tabi takan Motarsu,Wuta ta kamaci,ba'a samu komai daga sassan jikinshi ba,wannan Shi ne abunda muka sani a game dashi....."tana kuka ta Zayyana masu Komai daya faru har 6oye mutuwar junaid dasu Marshal Su kayi,Da kuma Halin da abbansu ke ciki na rashinsa,.
Amrish tasha kuka hada majina,Shi kanshi Ya mu'allim jurewa kawai yake yi,rashin imanin Yayi yawa
"In sha Allah komai Yazo ƙarshe,duk wanda keda sa hannu a wurin cutar da family ɗinku,Zai gane kuskurenshi,don wannan karan da shirina nazo,"Babu wasa a fuskarshi yayi maganar,
"Dan Allah ku faɗamun ya akai kuka samu junaid"?tayi maganar yayin da take share hawayen fuskarta,
Anan Amrish ta kwashe dukkan abunda Ya faru daga farko har ƙarshe
Miƙewa Sehrish tayi tana kuka,Ta rungume amrish tana Yi mata godiya,bawan Allah ashe shine Yake tura mana saƙo da layinki,muka kasa gane wanene,da yake ni ina da numberki,Shiyasa saƙon Ya bayyana da sunanki,nayi tunanin ko kin yada wayarki ne,Ashe junaid ne ya ɗauketa,Bawan Allah,wlh da ace zan iya mayar da ciwonshi jikina da nayi hakan,junaid bai ta6a shan wahala rayuwarba,Sae wannan karan da ƙaddara ta rutsa shi....."
"Mu gode ma Allah junaid yana raye,duk yarda suka so su cutar dashi,basu ci nasara akanshi ba,domin kuwa junaid kainuwa ne dashen Allah,badai mutun ba,lokacin da muka kawo shi asibitin nan,jinin jikinshi Yayi ƙanƙanta,cikin sa'a likita ya gwada jinina,kuma aka dace yayi dai dai da nashi,gashi nan ana ƙara mashi,Amma yana bukatar jini sosai,"
*ƙarin Bayani*
Abunda ya faru lokacin da Sehrish ta tura saƙonnin nan cike da saran Ya mu'allim zai gani,malaman da ta tura ma saƙon daga ciki akwai numbar Ya mu'alim,Yaga Saƙonta saƙonta sai kuma Aka kirashi a waya ana sanar dashi cewa ɗalibarsa na nemanshi,Sauran malaman data tura ma sakone suka sanar dashi,An turo masu saƙo ana nemanshi,Wannan dalilin ne yasa Ya mu'alimm Ya shirya zuwa gidan,tun lokacin baya ya ta6a zuwa gidan security guards ɗin gidan suka hanashi wuce wa,baisamu shiga ba a wannan lokacin,Sai yau daya samu saƙonnin nemanshi da sehrish keyi,Shi ne ya yanke shawarar Ya fara zuwa gidansu Amrish don tayi mashi jagora zuwa gidansu sehrish ɗin su tafi atare,Da yake ya ta6a zuwa gidansu Amrish lokacin da tayi jinya,kuma cikin sa'a ya zo adaidai lokacin da suke buƙatar taimako,Kunji yarda akai Allah ya hadasu dashi Har ya ɗauke su,
Saboda halin da Abban junaid ke ciki,Ya mu'allim Ya basu shawarar su ɗauki junaid su koma dashi Can Sgr hospital ɗin,Don A haɗashi da mahaifinshi in yaso sai acigaba da jinyarshi acan asibitin,Sai da suka tsaya Jinin ya ƙare sannan Likita ya sallamesu,Suka ɗauke shi a back seat ɗin motar Ya mu'alim Aka shigar da junaid,Sehrish ta shiga ta ruƙoshi ajikinta,bawan Allah ya zama tamkar lagwanin filita jikin sae kerma Yake yi sam baya acikin hayyacinshi,Mazaunin driver Ya mu'allim Ya shiga,Amrish ta zauna gefenshi,Ya tashi motar,a tsanake yake driving ɗinsu,Amrish sae faman zabga murmushi take yi,burinta Ya cika,junaid zai koma wurin ƴan uwanshi,Sehrish kuwa ba'a magana,Bakinta yaƙi rufuwa,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,Tsabar farin ciki ne kawai,Ta ƙankame junaid ajikinta kamar ta mayar dashi cikin cikinta,Saboda tsabar ƙaunar da take yi ma ɗan uwanta,A ranta tana ayyana irin farin cikin dasu Babban Yaya zasu yi idan suka ga junaid bai mutu ba,
Slowly motarsu ta ƙaraso cikin katafaren asibitin SGR................
*akwai yiyuwar littafin Abban Sojoji yakai farkon march,Ba kamar yarda nace ba ƙarshen February,Amma idan kuna son ayi maku after 3 years,kuyi mun magana,sai mu katse shi,ra'ayinku nakeson ji,littafin yazo ƙarshe masu tunanin zai kai azumi,Aniyarku tabi ku😂*
*masu son karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6i layina,Message za'a tura mun ta whatsapp banda phone call*
Masha Allah farkon littafin hausa dana fara karantawa kenan Allah ya kara basira
ReplyDeleteAnd I lyk it dan Allah boss ki kara kokari gurin sake mana na kagu na gama karatun littafin nan 1014 please
ReplyDeleteMasha Allah d book is nice
ReplyDelete