Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 3 complete

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 3 complete

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 3 complete

 https://chat.whatsapp.com/JHMyJEdouzG4wqpr7BvZzE

𝑇𝐻𝐸 𝐷𝐸𝑆𝑇𝐼𝑁𝐸𝐷 𝑃𝑅𝐼𝑆𝑂𝑁💋

𝐾𝑢𝑟𝑘𝑢𝑘𝑢𝑛 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎

Boss Bature✍️

_the Writer Of Abban Sojoji and Now  the destined prison_

TAKUN FARKO Episode 3

Taj kuwa tuni jikinshi yayi sanyi,duk da basuyi zaman lafiya da benazir ba,hakan bai sauya komai ba,na daga son da yake Yi mata,Yana jinta sosai acikin ranshi,tun ranar data gudu,kusan kullum saiya kira layinta da daddare ko Allah zaisa ta buɗeshi,Amma kullum akashe yake samunshi,


Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi"Ka sawwaƙe mata kawai,da taje tayita aikata zunubi da auranka akanta,don nasan ba dawowa zatayi ba,"


Girgiza kai taj yayi"baba bazan Iya ba,zan jirata ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita,nasan zata dawo ne,duk mun daran daɗewa"


Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi"Abunda nake fata kenan,Yanzu ina jikar tawa take ne?Inaso na ganta,'


"Tana hannun Inna kulu,Ƙanwar matar maigadinace,itace ke shayar da ita"


"Allah sarki,Amma naji daɗi sosai,ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi,da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana"


Amsa mashi yayi da toh,kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sadashi da ɗakin inna kuluwa,Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci,angel kuma na kwance gefenta ansanya mata kayan sanyi ajikinta,sai  faman tsotar yatsanta take yi,Murmushi ya saki tare dakai hannu ya ɗauketa,Ya fito da ita,


Ƙarasawa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita,Wani irin farin Cikine akan fuskarshi"Tabarakallahu ahsanul khalikin,Taj kaga ikon Allah,Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai,wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world,


Murmushi taj ya saki yana kallonshi,addu'o'i ya shiga tofa mata,Taj na amsa mashi da ameen ameen,har ya kammala yi mata addu'ar,Fira sosai sukayi da surukin nashi,har lokacin Angel na a hannunshi,Sai daya tashi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita


"In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata,Yanzu ka tura mun account number dinka,In sha Allah zakaga saƙona"


"Ngde ssae Allah ya kiyaye hanya,idan Anji wani labari game da benazir dan Allah a sanarmun"


"Kada ka damu surikina,duk inda take nasan tana sane da ƴarta da ta bari,kodan saboda ita zata dawo ne"


Har wajen da sukayi parking na motocinsu guda uku,Taj ya rakoshi da sauri wani bodyguard Ya buɗe mashi mota ya shiga,A jere motocin suka fuce,


Fitarsu keda Wuya,ba zato ba tsammani Sai ga alert na Miliyan 20 ya shigo wayarshi,Yayi farin Ciki sosai da kuɗinnan,dama yana ta tunanin yadda zai tafiyar da rayuwarshi da kuma rayuwar ƴarshi,ga kuma Iyayenshi da yake taimakamawa ga kuma albashin baba mai gadi,Salary ɗinshi basu isa ya dunga ɗaukar duk wani responsibilities nasu,A ranar yayi kwanan farin Ciki,


Bayan Wani LokaciAlamu sun nuna cewa Angel ba ƙaramar fitinanniya bace,don tun bayan wata ɗaya da aka haifeta,Taj yayi bankwana da yin Bacci cikin kwanciyar hankali,Saboda tsabar kukanta,da yake a ɗaki ɗaya yake kwana da ita saboda tsabar son da yake yi mata,Kona seconds baison rabuwa da ita,sai suna bacci Idan ta tsala ihu tamkar wadda za'a zare ranta,har asibiti ya mayar da ita don aduba Lafiyarta,Still bincike ya nuna tana da ƙoshin Lafiya,


Inna kuluwa kuwa dake shayar da ita lokacin da ta fara Haƙora biyu agaba,Ba ƙaramar azaba take sha ba,gartsa mata Cizo take Yi,baiwar Allah Bata ta6a sanar da taj halin da ake ciki ba,kullum sai tayi zazza6i,duk da tana samun kulawa a wurinshi,Duk wani nauyi nasu ya ɗauke masu shi,Hatta Abincin da take ci wanda ke gina lafiyar jikinta,Aneelarh ce ta rubuta masu shi,taj ya siya masu komai,


Lokacin da baby ta fara rarrafe A wata na shida,Tayi 6arna kamar zata haukata masu gidan,da rarrafe take 6aro da kaya su zube kasa,ta kacaccalasu,akwai ranar da Ta samu wasu mahimman takaddu na Taj,Ta kekketasu into pieces,Ranar Har zazza6i yayi saboda muhimmancinsu,kuma idan tayi 6arna taga ya zabga tagumi Yana kallonta,Sai ta 6a6aka dariya kamar babban mutun haka sautin dariyarta yake,a lokacin da takai shekara ɗaya da rabi, 


Da kanta ta daina shan nono,hakan yasa inna kuluwa ta yayeta,a washe garin ranar data yayeta,ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyensu,yayi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan,Ba don yaso ba ya sallameta,Yayi mata alheri sosai,baiwar Allah ita kanta ba don taso ba,tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi,Game da Ƴarshi,to fah


Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji,har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta,a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna,Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo,sam bataso Yana ɗaurata asama,tuntana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daurata da zarar Ya bar wurin saita faɗo kasa,Taci gaba da 6arna,Abun Ya ɗaure mashi kai,Yarinya sai kace aljana,ranar da ta ƙureshi Keji yasa akayi mashi mai girma,hada mukullin rufewa,Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe,A tsakar falo ya ajiyeta,shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta,ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancinta har takai ga fashe mashi da kuka,tausayinta Ya kamashi,har baisan lokacin daya  fiddo da ita daga cikin kejin ba,Ya rungumeta yana lallashinta har ya samu tayi bacci,A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha'e,Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita,idanuwanshi sukayi jawur,gashi bai iya koda yi mata tsawa,A fusace ya ɗauketa yakaima Su aneelarh ita,Yace ya basu kyauta su ruƙeta awurinsu,ba ƙaramin farin Ciki sukayi ba,hannu biyu suka kar6eta,ashe xaune bata ƙare ba,A tunaninshi Ya samu hutu,Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccinshi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari,


Wuraren ƙarfe 12:30 na dare,Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi,hakan yasa shi farkawa daga bacci,Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon,


Kamar ance Ya dago karaf idanuwanshi suka sauka akan  baby Angel dake kwance ajikinshi ta ƙanƙameshi,wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarshi,a firgice Yake kallonta,Har wani murmushi take sakar mashi,yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba,Abun yayi mugun ɗaure mashi kai,taya akai har Tayi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake akusa da gidanshi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba,


Jiki asanyaye Ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata asaman kanta,Wai koda shaidanun aljanune suka shigeta,sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi,Babu yadda ya iya,haka ya ƙankameta akirjinshi Yana shafa sumar kanta,Sae gashi bacci Ya ɗauketa,bada jimawa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi.


Wuraren Sallar asuba,Uzair da aneelarh suka buga uban sammako,Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace,Duk sun ruɗe,Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel  zaune saman Dining Chairs Hannunshi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha,


A ruɗe suka kalli Juna,saboda tsabar mamaki,kafin ma Taj yayi masu bayani,Uxair Ya rufe shi da faɗa yana cewa'Don me zaije Ya dauki yarinya batare daya fada masu ba,Yasa duk sun tashi hankalinsu,'sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,

  Tukunna Taj yace"Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo,

A sukwane Aneelarh tace"Wai dagske ita tadawo da kanta"?

 Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa"Eh da ƙafafuna na dawo,kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba,ni na buɗe dakaina"tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba,

  Tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!cike da tsantsar mamaki suke kallonta,Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?


  Girgiza kai Taj yay"Lamarin Baby sai addu'a,Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu  da rabi na dare,naji motsin mutun ajikina,Ashe itace ta dawo,Ba ƙaramin tsorata Nayi ba"


Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba,


A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya,Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar saiyazo,kuma duk in yazo saiya kashe ma angel kuɗi kamar hauka,kafin tafiyarshi,


A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number,Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj,kuma kada yayi tunanin zata dawo,ta tafi har abada,Abunda yasa yayi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye,Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba,Har bibiyar Number data tura saƙon yayi amma akashe ya sameta,Yaji takaici sosai,tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwarshi harya fidda rai,ba don yaso ba,Ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani,Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata....,......


A ranar Uncle abdallah ya dawo Nigeria,Uzair ne da kanshi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu,tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa yayi,Musamman Taj,hajiya adama tayi murnar ganinsu Cikin ƙoshin lafiya,Ranar yini tayi da angel awurinta,tun dawowarsu Angel awurunsu take kwana,Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar  take natsuwa agaban mutane,Amma idan shi da itane tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida,


****Boss Bature******


A kwana atashi,Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea,Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya,duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita,Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi,Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki,ko 6ari bata ta6a yi ba,Abun ya dameta sosai,Shi kanshi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa,har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu,Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi,Lokacine baiyi ba,ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalinsu harya basu Labarin Iyayenshi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa,Tunda sukaji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,


A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji,Ashe Yanzu wasan Ya fara,


Tun tana da shekara Uku Ya sanyata A nursery,hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata,rana ta farko data fara zuwa makaranta,ta samu ƴa'ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo,Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta,saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta,Saboda bazasu Iya Control ɗinta ba,gashi Ya hana a dukar mashi ƴa,ko tsawa Baiso Ayi mata,sai dai bayan idonshi,


Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa'ƴan mutane,tun da yayi mata fada abunda bai ta6a Yi mata ba,Aranar har fushi tayi taƙi cin abinci,daƙyar Ya lallasheta ya samu suka shirya da ita,


Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece,tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado,A tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba,bayan fitarshi Da rabin awa,ta farka tana Jin yunwa,gashi Sam bata da juriyar Yunwa,Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki,Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din,Dama tasan Yadda yake kunneshi,Saboda wasu lokuttan atare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki,To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta,Yana Wurin aiki Aka kirashi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi,Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan,Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi,Duk yabi ya ruɗe,babban tashin hankalinshi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta,da gudun gaske Ya fada Ciki,Su uzair suka bi bayanshi dama sunzo hada aneelarh,A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo,Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,


Sai da suka gama shan wahalar nemanta,Ba zato ba tsammani suka same ta acikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha,


Da gudu suka nufeta gaba ɗaya suka rungumeta,kowa na faman sauke ajiyar Zuciya,Abunda Ya faru,Ashe bayan ta kunna gass,ta sauko daga saman Chair ɗin,Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha,Sam ta manta da tabar gass a kunne,duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita bataji ba,Baba maigadine Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Cikin gidan don yaga meke faruwa,koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi,Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman Agaji,


Angel tasha fada awurin Taj,kuma duk da laifin da tayi mashi ko dungurinta baiyi ba,kadan daga Cikin munanan halin angel shine,Bata barinshi yayi bacci muddin ta farka,to shima dole ya farka baccinshi Ya qare,Idan suka fita Yawan shakatawa,komai ta gani tana so,koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi,idan ba haka ba hmmm xa'aga tashin Hankali,Bayan wannan Ta iya jan faɗa,idan suka Je anguwa,komai ta gani saita dauka ta jefar,Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka,duk duniya babu wanda bata Jin tausayinshi Irin mahaifinta,azabtar dashi take Yi,Shi kuma Ya mutu akan sonta,Bai iya rabuwa da ita,gashi ta tsani taga yana karatul Alqur'ani,da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun,kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba,idan uziri ya hanashi zuwa masallaci,Kamar shaiɗaniya haka take,har malami aka dauko yayi mata addu'a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu,tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta,ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi,Ita lafiyarta qalou


,Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya,Ta sace takalmanshi ƴan madina,sai daya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗaukesu,sukayi ta nema kasa ko sama babu su,bayan tafiyarshi,Ta fiddo takalman data 6oye a karkashin gadonsu taba Taj,wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta,haushi kamar Ya rufeta da bugu,yaji kunyar abun nan,haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abunshi,Babban abunda zai baka mamaki da ita,sam bata da tsoro,yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon harta Iya kunna kallo,tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radionsu,Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe,Tasa key ta rufeshi,dalilin dayasa Tayi mashi haka shi ne,Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair,Ita kuma bata son zuwa gidan,tafi son duk inda zaije ya tafi da ita,Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakinshi,bayan ya shiga wanka,Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai,Ta murɗa mashi key,ta datse ɗakin,Ƙarfin Hali,


Tun yana lallashinta ta buɗe mashi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar maiyin magana da babban mutun,Ya zazzageta Da masifa,duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba,har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki,ya kawo mashi taimakon gaggawa,batare da 6ata lokaci ba saiga  uzair Yazo gidan,A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo,aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe mashi ƙofa,koda ya fito baibi ta kanta ba,Ya fuce daga falon yana huci,Uzair dai yaci dariya,shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,Saboda bala'in angel Saida yakaiga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayinshi,bawan Allah duk yayi duhu ya rame,ita kuwa Babyn tashi har kumatu tayi saboda rayuwar Jin daɗi,yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita,gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yadda,saboda kowa Mamakin shekarunta yakeyi,Just 5 years fa,


Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani,Shine girka mata abinci,Yayi mata wanka,Ya wanke mata gashi,Yayi mata kitson kalaba,har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi,Amma yarinyar nan Idonta sun makance,idan kana son Ganin Dariyarta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,Lokacin da takai Shekara 7 a duniya,Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi,mai suna Muhsin,lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba,musamman dayazo masu da angel,yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta,Allah yayita da farin Jini,


Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe,Taƙi ci,da suka tambayeta meyasa bazataci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane,a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba,ƙiri ƙiri tayi mashi ƙarya,Muhsin Ya rokeshi akan yayi mata magana taci abinci,Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci,da buɗar bakinta sai cewa tayi"Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,"


Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki,Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗinshi akan maganar angel,har suka tashi tafiya Bata Ci komai ba,tun lokacin yaci alwashin saiya  yi mata fada in suka je gida,Ashe da zasu Baro gidan,Ta sace warin Takalmin matar gidan,Mai tsadar gaske,Babu wanda Ya lura,sai bayan Da sukayi nisa da tafiya,Ta ɗago takalman tana nuna mashi Wai Yakai amayar mata dasu Na yara,Sun burgeta,hankali atashe Yayi parking ɗin motar,dama a ƙule Yake da ita,wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,a karshe yace"Banasonki,kin fita araina,Ke ni ba mahaifinki bane,bansanki ba,ki fita arayuwata"Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi,buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje"Kije ki nemi wani uban"Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri,Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama'a,fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta,yana faman ƙwala mata kira,Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin"Wayyo Allah,taimako,wani mutun zai sace ta,ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta,kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu,Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora,Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba,Ya soma bleeding,don mutane su ɗauki abun serious,sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa"Ba mahaifinta bane,Sace ta yayi yana gana mata azaba,Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta,dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi,Jin wannam maganar yasa ran mutane Ya 6aci,Musamman ƴan ƙato da gorar nan,sun fusata sosai,Kamar jira sukeyi dama a harzuƙe suke,Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki,ita kuwa ko ajikinta,har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba,Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba,tafi kama da ƴa'yan larabawa da turawa,shi kuma yana da ɗan duhun fata,ga kuma Launin idonta ba kalar nashi baBa don Allah yasa ansamu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba,da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen,daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu,Sunyi mashi jina jina,rashin sani yafi dare duhu,dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sunsanshi,saboda sanannan Ɗan jaridane,babbar matsalar da aka samu,mafi akasarinsu Fuskarshice dayawa basu sani ba muryarshi kawai suka sani,A wannan lokacin kuma ba wanda ya ankara kuma basu bashi damar da zaiyi masu bayani ba,


Police station suka wuce dashi,A cikin Cell suka turashi,tare da garƙameshi,Sam baya acikin hayyacinshi,Ya galabaita sosai,A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali,Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c,ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,

Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta,Tace mashi sunanta Angel ,ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta?da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba,Akwai abokin aikinshi Uzairu,atare suke sace ya'yan mutane,


A lokacin taj ya dawo hayyacinshi,Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su bashi waya Ya kira amininshi da matarshi zasu bada shaida akanshi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya,Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,


Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki,Saboda tsabar sauri Ko aneelerh,bai jira ba,yaja mota Ya nufi station din da taj yayi mashi kwatance,


Bayan yayi parking ɗin motar,Ya fito ya shiga Ciki da azama,Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyarshi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj,Suka Hankaɗa shi ciki,Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskarshi duk Sahun naushin mutane,bakinshi da hancinshi duk sun fashe,baisan Lokacin daya fashe da kuka ba,kamar ƙaramin yaro,rungumeshi yayi ajikinshi, sosai,Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel akayi daga  office din Dpo,Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne,Tace Eh shi ne

*Yanzu Wasan Ya fara,Kada ku bari abaku Labari🤩*

*Mu haɗu a Next Page On Monday don Jin yadda zata kaya*💃....................

_Paid Book ne,Amma Ba'a fara payment ba,Sai an kammala free tukunna👌_

_Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i wannan numbobin_

08103884440

08169856268

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post