Kukan Zuci page 4 - Novels Elite
Health College

Kukan Zuci page 4 - Novels Elite

 

Kukan Zuci page 4 - Novels Elite

💔💔 Kukan Zuci 💔💔

Written by Novels Elite.


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da wata manufa ba sai don nishaɗi. 


Page 4.


Kamal da yan uwansa hankali ya kwanta, sun sami abinda yake so, sai yadda suka so yi da dukiyar Alhaji. Haka rayuwar Kabiru ya cigaba da tafiya cikin ƙunci da wahala wajen Hajiya Rabi, hatta da wanki shine yake yi.


Kwanan Hajara biyu a asibiti jikinta yayi kyau sosai sai dai ciwon kai ne kawai yafi samun ta, cikin kwana biyun da tayi Prof. Umar tare da iyalan sa suke zuwa duba ta domin ya ce ba zai bar ta ba domin bai san hannun wa zata faɗa ba, ahaka ne matarsa ta ce ya Kaita gidan su ta zauna tare dasu har zuwa lokacin da zata iya tuna wacece ita, sai ta koma inda ta fito, Prof. Umar yaji daɗin shawarar matarsa sosai saboda ta nuna masa tana da tausayi.


Alh. Mahi dai sunan shine mijin amma Hajiya Rabi ita ke da ikon faɗa aji a gidan sai kuwa babban ɗan ta Kamal wanda a yanzu shine Shugaba a wajen kasuwanci mahaifinsa da Umarnin Hajiya Rabi, a haka ne shima ya shigar da nashi kasuwancin na miyagun ƙwayoyi, dukiyar Alh. Mahi kuwa. kuwa sai yadda suka yi dashi, sune gidan mata da wajen shaye-shaye sai ƙarfe 1 na dare ko biyu yake komawa gida hakan ne yasa baya tashi da wuri, sauran ƴan uwan nasa kuwa tare suke komai.


Wata ranar juma'a da rana bayan ya dawo daga masallacin juma'a, Kabir ne da abokinsa tun na yarinta Muntari suna zauna a ƙofar gidan su Muntari yana bashi shawarar yayi ta haƙuri da yawaita addu'o'i komai yayi farko yana da ƙarshe, a anan ne har akai la'asar da magriba kafin Kabiru ya koma gida ya ci ɗan abincin da aka bashi wani lokacin ma da yunwa yake kwana amma duk da haka bai taɓa kwana da su a zuciyarsa ba, Kabiru ya gama cin abincin ba daɗewa yayi karatun da ya saba yi duk dare tare da addu'o'i da mahaifiyarsa ta koyar dashi tun yana yaro.

Misalin ƙarfe 10 na safe, a ranar da Hajara ta cika sati biyu a asibiti,  likita ya shiga ɗakin da take ya sake duba ta da kyau ya tabbatar da ba abinda ke damun ta, sannan ne ya sa a rubuta mata takardar sallama, ta warke sosai matsalar ɗaya shine ta rasa tunanin ta. Dr. Habib ya kira Prof. Umar ya faɗa masa an sallami patient ɗinsa, cikin ƙan ƙanin lokaci direba ya zo ya ɗuki Hajara zuwa gidan Professor Umar.


Tafiyar da bai wuce mintuna 30 ba suka isa cikin farfajiyar gidan Professor, gida ne gini irin na zamani wanda an kashe manya-manyan kuɗaɗe wajen gina shi wanda manyan masu tsara gini sukayi hadda mai gadi ɗakin sa yana da kyau sosai masu aiki ma ɓangaren su da ban. Ɓangaren baƙi aka wuce da Hajara inda aka kaita ɗakin da zata zauna tare da haɗa ta da wanda zata dinga kula ta ita, matar Professor kuwa da yaran ta sukan zo wajen Hajara akai-akai domin kada a barta ita kaɗai, sannan Professor ya sa akayi mata addu'o'i a masallatai daban-daban tare da cigiya ko Allah zai sa a sami yan'uwanta amma shiru ba'a samu ba, Haka ta cigaba ta zama a gidan Professor ba tare da tsangwama ba domin tana samun kulawa sosai a gidan.


Washe garin asabar Kabiru ya tashi da zazzaɓi mai tsanani amma a haka Hajiya Rabi yace sai yayi mata wanki, Alhaji Mahi ne yace haba Rabi ki dinga tausayin yaron nan baki san wa zai zama ba nan gaba, kika sani ma ko shine zai cigaba da riƙe ki? Yi min shiru idan bazai yi min wanki ba kuwa saidai kai kayi min wankin a maimakon shi, ba yadda zai yi hakan dai Alhaji Mahi ya yi shiru domin babu yadda ya iya ita ce mai gidan, Kabir da ƙyar ya gama wankin, abokinsa Muntari ne ya ya kaishi Chemist ya aka bashi magani ya sha ya kwanta bai daɗe da kwanciya ba wani bacci mai nauyi ya kwashe shi.

Ƙawar Hajiya Rabi kuwa, Saratu tana da yarinya mace wanda ta sha alwashin ganin ta haɗa su da yaron ƙawar nata Kamal Dan gidan Hajiya Rabi ta ko wani hanya, amma zata fara jin ta bakinta tukuna. Hakan ya sa Sarari zuwa gidan kawar na ta domin faɗa mata abinda ke ranta, ta sami Hajiya Rabi zaune a falo tana kallo tare da ɗiyarta Safiya,  bayan sun gaida ne Hajiya Rabi ta umarci Safiya da ta basu waje zasu yi magana, Sarari ta ce "Kawata kin san abokin kuka shi ake gaya masa mutuwa, wata shawara nazo dashi wanda nasan zai amfane mu gaba ɗaya tare da 'ya'yanmu, ni sai nake ganin kawai mu haɗa A'isha da Kamal aure ko"  a firgice Hajiya rabi ta miƙe tare da cewa " gaskiya wannan maganar taki bana tunanin zaiyiwu domin ba yadda za ayi na haɗa ɗa na da ƴar ki aure, ke fa kin san duk abinda muke yi tare da ke ko, gaskiya ki canja wannan shawarar ki kawo wani abindai, idan ta sami miji dai zanyi mata duk abinda uwa zatayi ma yarta, amma ba zan bari ta auri ɗana ba. A guda ce saratu ta miƙe tace " tunda kin ƙi zan bi kowani irin hanya ne don ganin anyi wannan auren" mu zuba Ni dake. Ta fice ba tare da yi mata sallama ba, wannan maganar ya yi matuƙar bata mata rai sannan yayi mugun bata tsoro don tasan halin ƙawar na ta, duk wani lungu da saƙo na zuwa gidan boƙaye.


Tun dawowar Hajara daga asibiti har kawo yanzu bata iya tuna wacece ita ba, kyawawar halayen Hajara yasa Professor da iyalansa suke sonta sosai tun bata saukewa har ta sake sosai ta zama kamar dama a gidan take hakan ya sanya farin ciki sosai a cikin wannan ahali tana taimaka musu sosai wajen tarbiyyar yaran su. Haka rayuwar Hajara ya cigaba da kasancewa cikin farin ciki da walwala ba tare da sanin wacece ita, a ina take ba, har kawo wannan lokaci ana cigaba da addu'a don Allah ya dawo da hankalin Hajara saboda ta faɗi daga ina take da abinda ya faru da ita ba.


Rana tayi sanyi don Ba'a daɗe da yi sallar la'asar ba, ya farka daga bacci da ya ɗaukeshi, daƙyar Kabir ya tashi yayi Sallah sannan yayi wanka yayi karatun Alqur'ani mai tsarki, amma bai dade ba sakamakon zazzaɓin bai gama saninsa ba ga tunanin ɓatar mahaifiyarsa, da wannan tunanin ne har magriba tayi ya tashi ya nufi masallaci yayi Sallah ya tsaya saidai akayi sallar Isha sannan ya dawo gida, ya ci abinci sannan ya koma ɗaki ya kwanta sai bacci.

Wasu mutane ne guda biyu manya sosai  fuskarsa rufe ta yadda babu yadda za'a gane su, sashin Alhaji Mahi suka nufa wanda dama tun shigowar su Kabir ya ji motsin su sakamakon dama baiyi bacci sosai ba, ahankali ya bi su a baya har cikin sashin ba tare da sun san ana bin su ba, sunyi Sa'a ɗakin kuwa ba'a kulle yake ba suka shiga ciki shidai yana biye dasu, sun sameshi yana bacci, ɗaya ya danne kansa da matashi ɗayan kuma ya riƙe ƙafafuwarsa ganin haka ne Kabir ya yanka ihu a nan ne suka san ana kallon su nan da nan suka nufi inda Kabir ya ke, yadda ya ga sun nufo inda yake nan take ya juya da gudu ya fita suna binsa da makamin da ke hannunsu.


Shin za suyi nasarar kashe Kabir ko zai tsira? Mu haɗu a shafi na gaba. Domin faɗin ra'ayoyin ku, kuyi magana a comment. Ko


  Whatsapp Group .

Novels Elite

08062334828

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post