Kurkukun Ƙaddara episode 40 Complete

Kurkukun Ƙaddara episode 40 Complete

Kurkukun Ƙaddara

 💋KURKUKUN ƘADDARA💋


E40


By Boss Bature writer of Abban sojoji❤


Saboda tsabar firgicin da azeeza ta shiga nan take ta saki fitsarin da take ji  ya soma gangarowa ta cikin wandonta,        an rasa me lallashin wani acikin su, kowa sai kuka yake yi, Kuma har lokacin Batool bata saki wuyan rigar azeeza da ta shaƙe ba, bayin Allah su kaɗai suka san Fargabar da suke aciki, babban abunda suke jima tsoro shi ne azo araba su da ƴan uwansu, Basu da tabbacin za'a dawo dasu ko baza a dawo dasu ba, 


Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita azeeza ta kware maki tana faɗin"Wayyo Allah na, Na shiga uku, batool kin shaƙe min wuyan rigata, Ki sake Ni, inji da abunda ke damu na....."daƙyar ta kai ƙarshen maganar, tana kiciniyar ƙwace wuyan rigarta da ga ruƙon da batool tayi mata, wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, Sun yi jawur, idanuwansu  sun kumbura luhu luhu saboda tsabar tashin hankalin da suke aciki.


Waɗan da ke acikin ɗaki basu san meke faruwa ba, babu alamun zasu farka daga bacci, Wata irin gigitacciyar ƙara batool ta saki sakamakon Cizon da Azeeza ta gartsa mata a hannunta, kaitsaye sautin ƙarar ya daki dodon kunnuwan su, Aikuwa a firgice kowannan su Ya farka, at same time suka ya ye bargunansu tare da yin wurgi dasu, Kowa yana faman zazzare ido, fuskokin su da alamun ruɗani, lokacin da suka ankara daga inda sautin ke fitowa, Jiki Na rawa kowannan su Ya sauko daga saman gadonshi, da gudun gaske suka nufi sashen toilet ɗinsu, kamar an jeho su suka faɗo Ciki, Kowa yana faman baza na muzurinsa, Angel ce farko sai Hanna da hibba, kaf matan da mazansu hada danish da haris, 


Hankalin su yai matuƙar tashi, ganin Jinin dake ɗigowa daga hannun batool sai yarfa shi take Yi, ta runtse idanuwanta sai kuka take yi kamar ranta zai fita, Tun da suke a rayuwar su basu ta6a ganin batool tana kuka mai sauti ba irin na yau, saboda tsabar hakurinta da juriyarta, Ita kanta azeeza data gartsa mata Cizon, duk tabi ta ruɗe jikinta sai kerma yake yi, ta manne jikin bango, Sai zazzare idanuwanta take yi fuskarta sharkaf da hawaye,


"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool meya faru dake? Me kuke yi anan keda azeeza? Badai faɗa kuke yi ba"? Angel ce ta jefa musu tambayar, a yayin da take matsawa kusa da batool, takai hannunta tare da ruƙo hannun batool dake bleeding, Hanna tace"ashe dama kune kuke faɗa? Tun ina bacci nake ta jin hayaniya cikin kunne na, amma kun bani mamaki, yanzu batool ki rasa da wa za ki yi faɗa sai azeeza"? Hannah na rufe baki haris yace"Ku faɗa mana meya haɗa ku da har kuke ƙokarin illata junan ku, wannan wani irin abun kunya ne, " Lamarin duk bai yi musu daɗi ba, sai tambayar su suke yi akan su faɗa musu dalilin yin faɗan na su amma sun kasa tanka musu, saboda kukan da suke yi.


"Hannunta yana zubar da jini, Ya zamu yi? Ko dai muje mu faɗa ma tsohuwa"? Mubeen ne yai maganar, muryar danish da alamun bacci bai ishe shi ba yace"Basai an faɗa mata ba," ya ƙarasa maganar tare da matsawa ya tsaya gefen angel dake a tsaye gaban batool, ya miƙa hannu ɗaya ya damƙo hannun batool dake zubar da jini, tare da kaishi saitin bakinshi tamkar zai gartsa mata cizo, ya kama wurin, kamar yana tsotsar jinin, duk suna kallon shi, Musamman angel da mamaki ya kamata ganin wani sabon salon treatment da bata ta6a gani ba, 


Sosai batool ta runtse idanuwanta, tana faman cizon brownish lips ɗinta, a hankali danish ya zame bakinsa daga saman hannun batool, wani iko na Allah jinin ya tsaya da zuba, sai dai a bunda ya ɗaure ma angel kai, ganin bai zubar da jinin daya sha ƙasa ba, A ruɗe take bin fuskarshi da kallo batare daya lura da ita ba, Sauran ƴan uwan babu wanda Ya kawo komai aranshi sai ita data ankara da abunda ya yi, zuciyarta ta shiga ruɗanin, taya akai ya ke iya swallowing ɗin jini!? 


Muryar azeeza cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah batool ki yafe ni wlh bada son raina na gartsa maki cizo ba, ke ce kika shaƙe mini wuyan rigata har naji zafi na cije ki," wani irin jiri batool take gani acikin idanuwanta, biji biji take bin kowannan su da kallo, Angel tace"Batool meke damunki? Wai baza ku faɗa mana me ya haɗa ku ba? Meyasa ku ke yin kuka? Ga zufa duk ta wanke jikin ku," matsawa batool ta yi kusa da angel ta kwantar da kanta saman kafaɗarta, da sauri angel ta sanya hannayenta biyu ta rungumeta sosai ajikinta, cikin muryar kuka batool ta zayyane musu abunda ke faruwa, Hankalinsu yayi matuƙar tashi, deeja dake a gefen haris ta fashe da kuka tana faɗin"mun shiga uku, abunda nake gudu sai da ya faru, wannan wace irin masiface? Fuskarta a yamutse takai kai ƙarshen maganar, haris yace"gaskiya bazaiyiyuwa ba, nidai bazan bari atafi da wani daga Cikin ku ba, sai dai a haɗa dani," cigaba da magana deeja tayi yayin da hawaye ke bin fuskarta tace"Dan Allah mu hada  kanmu, wannan karan kada mu bari atafi da ƴan uwan mu, ina matuƙar tausayin azeeza da batool, bazan so su ɗanɗani irin raɗaɗin azabar da muka sha ba, musamman azeeza zamu iya rasata,"  maganar deeja ba ƙaramin tsorata azeeza ta yi ba, jikinta ya hau 6ari, haƙoranta har kakarwa suke yi kamar wadda sanyi ya kamata, da sauri javed ya janyota jikinshi, kamar jira take yi dama ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka, lallashinta ya shiga yi, yana ɗan bubbuga bayanta da hannun shi,


  Zuciyoyinsu duk sun karaya, Fuskar Rubina ɗauke da matsananciyar damuwa tace"Wai shin Jinin wanene acikin su? Ta ya zamu iya ganewa? ɗagowa azeeza ta yi daga jikin javed tana faɗin"I just know it's not my blood, wlh ba jini na ba ne, sai da na faɗa ma batool cewa banawa bane, Saboda ni ko da na shiga toilet ɗin ban kai ga cire wandona ba, na yi tozali da shi" 


cikin shessheƙar kuka batool tace"Nima banawa bane, ba daga jikina yake ba, har na shiga na fito daga Cikin toilet ɗin ban ganshi ba" koda batool tae maganar bata raba jikinta daga na angel ba, ta ƙanƙameta, ji take kamar in ta raba jikinta daga nata za'a zo arabasu ne, 


Hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar angel. Har cikin zuciyarta tana jin wani irin mummunan faɗuwar gaba, muryar na ɗan rawa ta ambaci sunayensu Batool azeeza, "duk suka natsu, suna jiran jin me zata ce musu,


  "Since we were all confused, we couldn't figure out whose blood was in the toilet, abunda yakamata muyi zamu shiga toilet ɗin mu duba jinin da kyau, idan muka tabbatar jini ne, Azeeza da batool kowannan ku zai shiga cikin toilet ya bincika jikin shi, ta hakanne kaɗai zamu Iya gane daga jikin wa jinin ya ɗigo" gaba ɗaya kowa yayi amanna da maganar angel, koda suka shiga toilet ɗin suka duba dakyau, jini suka gani har ya ɗan bushe  a ƙasa, Hankalinsu ya ƙara tashi, angel tace abunda ya rage yanzu, su shiga su duba jikinsu, Batare da 6ata lokaci ba,  azeeza da batool suka shiga cikin toilet, kusan atare suka fito daga Ciki, Har suna haɗa baki wurin faɗi "Ba daga jiki na yake ba" Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, To wai jinin wanene toh? dole dai acikinsu ne wani ya zubar dashi, kuma azeeza ta tabbatar musu da cewa sabon Jini ne, domin kuwa lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin, da ruwa ruwa jikinshi, kafin yakai ga bushewa,


Kowannan su ya shiga ruɗani, in a low voice danish yace"ku daina wahalar da kanku, Idan ma dagaske jinin ne, Giants ne zasu banbance wanene acikin su," harara angel ta watsa mashi tare da cewa"danish har fata kake yi azo a ɗauke su"? duƙar da kanshi ƙasa yai batare daya bata amsa ba, haris yace"yanzu duk ba wannan ba, ku zo mu koma ɗaki mu jira mu gani me zai biyo baya" muryar azeeza a rauna ce take fadin"Ni wlh bazan fita daga nan ba, ku rufa mana asiri mu yi zaman mu acikin toilet mu datse ƙopar, ta yadda ba zasu Iya shigo wa su ɗauke mu ba" la66anta har shaking suke yi saboda tsabar firgici.


Tsananin tausayin su ne ya kama ƴan uwansu, haris yace"Azeeza ta kawo shawara mai kyau, mu rufe su kawai acikin toilet, kun ga shikenan munyi maganin Giants ba zasu Iya shiga su ɗauke su ba"  Jinjina kai angel ta ɗanyi alamar gamsuwa da bayanin Haris, ta ƙara da cewa"Ni zan zauna a atare dasu cikin toilet ɗin" 


  Girgiza kai danish yayi yana binsu da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa yace"that cannot be possible, if you say you will stop the giant from taking her you'll  bite off more than u can chew........." daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da suke watsa mashi asaman fuskarshi, Tsabar takaici ya hana Haris furta komai, Sai angel ce tai ƙoƙarin cewa"Kome zamu yi be shafe ka ba danish, u should stay away from us, tun da ba ka supporting ɗin mu that's mean baka da amfani awurin mu, ka koma saman gado ka kwanta zai fi maka kwanciyar hankali. If not wlh zan yi maka abunda baka tsammani,"  angel na rufe baki deeja tace"Danish baya atare damu, na fara zargin cewa Yana atare dasu, shiyasa ko jiya da aka dawo dani duk irin baƙar wahala dana sha, Kowa Yana yi mini sannu duk da bata maganin ciwo amma ina ji daɗi, atlease ƴan uwana sun nuna sun damu dani sun yi kewata, amma danish ko kusa dani baizo ba, sai kace wata maƙiyiyar shi.


hawaye na bin fuskar deeja takarasa maganar, Ran haris ya 6aci sosai, a fusace ya kai hannun shi ya damƙi damtsen hannun danish ya fusgo shi ya ja shi da ƙarfi ya fitar dashi daga cikin sashen toilet din. har cikin ɗakin su bakin gadon shi  ya kawo shi, anan ya dakata Ya ɗago suna kallon juna ido cikin ido shi da danish, 


"Ba ka da amfani a wurin mu, duk da haka bawai ina gudun ka bane, ko Ina fushi dakai a'a ko ɗaya, har yanzu kana nan a yadda kake cikin zuciyata, sai dai bama buƙatar ka a halin da muke ciki yanzu, Gado shi ne ya dace dakai ka hau ka kwanta" ya ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki, kafin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin. Jikin danish  ya yi sanyi, slowly ya ɗan juya baya yana kallon haris dake ta sauri har sai da ya shiga ƙopar tukunna danish ya ɗauke idonshi daga kallon bayan nashi da yake yi, 


Kamar yadda suka ce ya hau saman gado, aikuwa gadon ya haye ya kwantar da kanshi saman pillow, shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, ganin yadda ƴan uwanshi suke nuna rashin amfanin shi acikin su, abun yana mishi ciwo acikin zuciyarshi. Daurewa kawai yake yi dan ba yadda zaiyi, 


Bayan haris Ya koma cikin toilet ɗin, atare da angel suka tsara yadda zasu shirya ma Giants don su hana atafi da ƴan uwansu, Bayin Allah sun damu da ƴan uwansu sosai, babu mai tunanin abinci acikinsu ba don basu jin yunwa ba, sai dan damuwar da suka shiga, na fargabar kada azo a ɗaukar musu ƴan uwansu,


Haris ne yace da angel ta shiga Cikin toilet ita da batool su datse ƙopar ta yadda giant ba zasu Iya shiga Ciki ba. ita kuma azeeza a ƙarƙashin gado zasu 6oye ta, hanna tace ae zasu Iya gano azeeza tunda suna kallon komai suke Yi, amma ita a ganinta, abar azeeza ta shiga cikin toilet ɗin tare dasu angel, Haris yace su yi hakan kawai, toilet ɗin ƙarshe suka buɗe angel da su azeeza suka shiga Ciki, kafin su rufe ƙofa haris yace"su kwantar da hankalin su, idan an kawo abinci zasu kawo musu nasu su ci," suka amsa mashi da toh, daga bisani angel ta datse ƙopar da Jam lock, 


Kallon juna suka shiga yi atsakaninta dasu azeeza dake a tsaitsaye, fuskokinsu sharkaf da hawaye, sam babu kwanciyar hankali atare dasu,


Tsananin tausayinsu ne ya kamata, gaba ɗaya ta sanya hannayenta biyu ta rungumesu ajikinta, Cikin sigar lallashi take Yi musu magana,

  "In sha Allah giants bazasu raba mu da ku ba, bazan bari a cutar mini da ku ba, ina ji ina gani, wlh sai inda ƙarfi na ya ƙare, koda kuwa zan rasa raina ne, amma wannan karan ashirye nake dana fuskanci kowani irin tashin hankali ne"  with Confidence angel tayi maganar, babu wasa akan fuskarta.


Hankalin su batool ya ɗan kwanta, saboda jin abunda tace, ɗagowa batool tayi daga jikin angel, idanuwanta sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, cikin sanyin murya tace"Angel, bana so wani ya cutu acikin ku ta dalilin mu, idan har giants sun zo zasu tafi damu, kada kuce zaku shiga huruminsu, " girgiza kai angel ta ɗanyi tare da cewa"ki daina faɗin hakan, batool da ace kinsan me suke Yi maku idan suka ɗauke ku, da baki ce haka ba, ke kanki bazaki so atafi dake ba, mutanan nan basu da imani basu da tausayi, kashe mana rayuwa suke son yi ta yadda ba zamu ta6a amfanuwa ba, burinsu shine su ƙarar damu," tamkar zata fashe da kuka ta kai ƙarshen maganar,  azeeza dake kwance jikin angel, taƙi ɗagowa baiwar Allah, Jikinta sai kerma yake yi, ta ƙanƙameta tamkar zata koma cikin cikinta, wani irin faɗuwar gaba take ji, ita kanta angel tana iya jiyo sautin bugun zuciyar azeeza, fargabatar kada tsoro yasa zuciyar azeeza ta buga harta mace kafin ma su ƙaraso, 


  "Mu samu wuri mu zauna, nasan kun gaji da tsayuwa"  daga jikin bango suka zauna, still azeeza bata saki jikin angel ba, hannu bibbiyu ta ƙanƙameta koda suka zauna, itama batool ta ɗan kwantar da kanta saman kafaɗar angel, toilet ɗin yai tsit ba ka jin hayaniyar komai, tsawon lokaci kafin angel ta fara faɗa musu addu'o'in da zasu karanta na neman tsari, saboda tsaro,


Lokacin da angel ta datse ƙopar toilet ɗin, Ajiyar zuciya kowannan su Ya sauke, Haris yace dasu su koma ɗaki su zauna su jira su ga waye zaizo ɗaukarsu azeeza, Hada ja musu kunne akan karsu kuskura su bari tsoro yasa su faɗa ma giants inda suka 6oye su azeeza, duk runtsi duk wuya suja bakinsu su yi shiru, Suga iya gudun ruwansu, suka amsa mashi da toh,


atare suka nufi cikin ɗakin, Idanuwansu akan danish dake kwance saman gadonshi, haushin shi duk ya kama su, wani sullu6iyo dashi,


Suna yunƙurin haurawa su zauna saman gadajenshi, kwatsam suka soma Jin motsin buɗe kofa tacen saman bene, wa'Iya zubillahi zoka ga tsantsar tashin hankali akan fuskokinsu, A matuƙar ruɗe suke kallon matattalar benan , 


Takun tafiyar giants suka soma Jiyo wa acikin kunnuwansu, kafin su bayyana su uku masu kawo musu abinci hannayen su ruƙe da farantai, wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke ganin basu zo da shirin tafiya da wani ba, Bayin Allah hada murmushin su, saboda sun sa ma ransu cewa  baza a ɗaukar musu ƴan uwansu ba,


Da ido suka bi giants da kallo har suka sauke musu farantan abincin, da sauri suka nufi saman dining carpet ɗin suka zazzauna, babu wanda yae tunanin yayi ma danish magana akan yazo yaci abinci,  sai ma ta ƴan uwansu suke yi dake acikin toilet, ƙasa ƙasa da murya suke yin magana don kada giants su ji su, 


 "A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai musu"? hibba ce tai maganar, hannah tace"ku daina magana kada Giants su ji mu, abunda za'ae mu ɗauko kwandon batool mu ɗibi abinci, sai mu ajiye, bayan sun tafi sai muje mu kai musu acikin toilet ɗin," haris yace"kin kawo shawara mai kyau," batare da 6ata lokaci ba, hanna ta miƙe taje ta ɗauko kwandon daga ƙarƙashin gadon batool ta dawo ta zuƙunna gaban farantan, ta yaye jan ƙyallan da aka rufe faranti na farko dashi, fried fishes ne aka kawo musu, manya manya sun soyu sai maiƙo suke Yi, a ƙalla kowa zai samu ɗaya, Kifin akwai tsoka jikinshi sosai, A hankali take kai hannu tana ɗaukar kifin tana ajiyewa acikin kwandon, ganin ta ɗauki uku, yasa haris yace"Ki ƙara ɗaya kodan saboda danish" duk da fushi da yake yi dashi hakan bai hana shi jin damuwa dashi ba, Hanna tace toh, tasa hannu ta ƙara ɗaukar ɗaya ta ajiye, Ta ɗibar musu fruits tare da robar ruwa guda uku ta ɗauka, miƙewa tayi hannunta ruƙe da kwandon taje bakin gadon batool ta ajiye shi ta dawo ta zauna, a tsanake suke Cin nasu fried fish ɗin, Suna ci suna satar kallon giants dake atsaye sun goya hannayen su saman ƙirjinsu yadda kasan  Gumaka,  ko gajiya da tsayuwa basa yi,


A 6angaren su angel dake acikin toilet, Tuni bacci yai awon gaba da azeeza da batool, duk suna akwance saman jikinta, itama angel ɗin wani irin bacci take ji ga yunwa dake addabarta, sai faman lumshe idanuwanta take yi, 


Daga wajen ƙopar toilet ɗin ta soma Jin ana yi musu knocking ras taji gabanta ya faɗi, hatta su azeeza dake baccin jin bugun ƙopar yasa suka farka a firgice suna faman zazzare idanuwan su, 


  Muryar hanna suka jiyo tana faɗin"Ni ce angel, ku buɗe mini kopa, breakfast ne na kawo maku" Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, duk sunyi tsammanin ko Giants ɗin ne suka zo tafiya dasu,


 "Ku jira na amso mana abincin" tai maganar tare da zame jikinta daga nasu ta miƙe ta nufi ƙopar, ta cire jam lock ɗin, ta janyo ƙopar tare da leƙo da kanta waje,


Hanna ta gani atsaye ita da haris, kwandon Yana a hannun hanna ta ruƙo shi,


  "Angel Giants sun zo kuma sun tafi, Ni ina ganin kamar ɗigon jinin nan ba jini bane. Tunda da ace shine, Giants zasu tafi da su azeeza ne, Amma kinga har sun kawo mana abinci sun tafi" shiru angel ta ɗanyi tana nazarin maganar Hanna. Ita gani take kamar jini fa ne, kawai dai bai kai ga zuwa bane gaba daya shiyasa basu zo sun ɗauke su ba 


 Muryar haris ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi,


  "Nima ina tunanin ba jini bane gaskiya, tun da ga shi har zunzo sun tafi batare da sun buƙaci tafiya dasu ba" abunda za'ae yanzu ku fito  mu koma cikin ɗakin ku zauna ku yi breakfast ɗinku" Gyaɗa kai angel tayi badan taso ba tace"Allah yasa abunda muke hasashe ya zama gaskiya,  bari nayi musu magana su fito mu koma daki amma kafin nan, zan taimaka musu su wanke fuskokinsu," haris ya amsa mata da toh .kafin ya kalli hanna yace"Mu jira su acikin ɗaki" juyawa suka yi atare suka koma ɗaki, 


Badajimawa ba, Sai ga angel ta fito hannayenta ruƙe da nasu azeeza, Bayin Allah har faɗa wa sun ɗan yi saboda damuwa, Ƴan uwansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, da su kayi tozali dasu, 


A saman dining carpet suka zauna su uku, Hanna ta ajiye musu kwandon. Angel da azeeza suka ɗauki fried fish ɗinsu A hankali suke Ci,  Sauran ƴan uwansu duk suna a kewaye dasu suna kallonsu, ganin batool ta kasa ci ne yasa haris yi mata magana yace"batool meyasa baki ci? Muryarta na ɗan kerma tace"Hannuna Zafi yake yi mini"  sai lokacin suka tuna da cizon da azeeza ta gartsa mata, Zuƙunnawa haris yai agabansu, ya kai hannu cikin kwandon ya gutsiri tsokar kifin ya mika mata abaki, ta ɗan buɗe shi tana Ci, sai ƙara kwantar musu da hankali ƴan uwan nasu suke Yi, bayan sun kammala Ci, suka sha fruit ɗinsu, tare da ruwa, 


Angel tace yakamata suje suyi wanka, jikinsu duk zufa, suka amsa mata da toh, har tana cewa idan bazasu iya yin wankan ba zata taimaka musu suyi, batool tace ita zata Iya, azeeza kuma tace tafi son angel tayi mata wankan, hannun su aruke dana juna suka nufi toilet, bayan tafiyarsu, Haris ya ɗauki kwandon yana kallon sauran Fried fish din daya rage na danish tare da Rabin gwanda, Ta6e baki ya ɗanyi kafin ya nufi gadon danish, Ya ajiye mishi kwandon daga gefen shi yace"Idan kaga dama ka ɗauka ka ci, breakfast ɗin ka ne" ko motsi danish bai yi ba, ya runtse idanuwanshi, kuma ga dukkan alamu idonshi biyu ba bacci yake yi ba, 


Watsa hannu haris yai alamar bai damu ba, Ya wuce abunshi,  bayan wani lokaci, angel tafito daga Cikin toilet tare dasu azeeza, Wani irin sanyi suke Ji, asaman gadajensu suka kwanta, angel ta lullu6esu da bargunansu, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yai awon gaba dasu, 


Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, yanzu sun ƙara tabbatar da cewa ba jinin gaske bane suka gani acikin toilet tunda har marece ya doso amma ba'a zo an ɗauki wani daga Cikin su ba, 


Ita dai angel ta kasa samun natsuwa acikin zuciyarta, abu biyu ne ya dameta, na farko Jinin batool da danish yasha da niyar ya taimaka mata wurin dakatar da bleeding ɗin da yake yi, amma wani abun mamaki bai zubda jinin ba sai ya shanye shi, hankalinta bai kwanta da hakan ba, abu na biyu daya tsaya mata arai shi ne wannan ɗigon jinin dake acikin toilet na wanene? Dole akwai wanda ya zubar dashi, 


Zuciyarta cike fal da tunani ta ɗan kishingiɗa saman gadonta, da niyar ta samu ta runtsa, juyawa ta ɗanyi tana satar kallon danish dake kwance saman gadonshi, yatsun hannunshi dana ƙafarshi sai kerma suke Yi, hakan ya tabbatar mata da cewa idonshi biyu, ta6a baki ta ɗanyi aranta tace"Haka zaka ƙare, mutun sam baya gajiya da hawan gado, mai matacciyar zuciya kawai" takarasa xancen zucin tana mai jan tsoki, ta ɗauke idanuwanta daga kan jikin shi, ta mayar dasu kan kwandon da haris ya ajiye mashi daga gefen gadonshi, yau kuma kowa zai lallashe shi yaci abincin shi? murmushin takaici ta dan saki, wani lokacin in yana abu kamar ƙaramin yaro, har mamaki yake Ba ta 


*after some hours💔*


Kafin marece ya yi sai da kowan nan su ya yi wanka, Suka koma saman gadajensu suka kwanta, har lokacin danish bai motsa ba, Yana ayadda yake lafe saman gado, 


Angel tana ƙoƙarin nutsawa cikin baccinta, ta soma jin motsin mutun a jikinta, aɗan firgice ta ware manyan idanuwanta akan fuskar wanda ke zaune saman gadonta, Tayi mamakin ganin batool, fuskarta duk a yamutse. Idanuwanta sun ƙanƙance, tunkafin ma batool tayi mata magana taji wani irin faɗuwar gaba,


Muryarta na ɗan rawa tace"Lafiya? Batool meke damunki"? Cikin sanyin murya ta soma magana"Bana jin ɗaɗin jikina angel, gaba na sai faɗuwa yake yi, na gaza jurewa, shiyasa nazo wurinki, don kiyi mini addu'a, ko na samu naji sanyi araina" ajiyar zuciya angel ta sauke a yayin da take yunƙurin mikewa xaune tace"Wlh har gabana ya faɗi dana ganki nayi tunanin ko jinin ne kika gani yazo miki ashe bashi bane" jinjina kai batool ta ɗanyi alamar eh, tace"Bashi bane, bana jin daɗi ne kawai" 


"Tun da nake dake batool ban ta6a ganin ki cikin damuwa ba, irin na yau, kin canza sosai, duk sai naji ba daɗi jikina," daƙyar batool ta ɗan ƙaƙalo murmushin dole akan fuskarta tace"kada ki damu sister, zan dawo dai dai ne, just fargabar abunda ya faru ɗazu ce tasa duk na canza, Amma yanzu da ɗan sauki" 


Ido cikin ido suke kallon juna. angel ta ruƙo hannayenta acikin nata tare da cewa


"Zanyi maki addu'a, amma nafi so naji ki ajiki na, don naji daɗin kwantar miki da hankali kamar yadda kika saba yi mini" murmushi suka sakar ma juna atare, 


A saman chest din angel batool ta kwantar da kanta, tare da sanya hannayenta, ta zagayo dasu ta bayanta, sosai tayi tighting ɗinta, wani irin tsananin ƙaunarta take ji, suna matuƙar son junansu fiye da tunanin mai tunani, addu'o'i angel ta soma karantowa tana tottofa mata asaman kanta, har cikin zuciyarta take jin wani irin daɗi yana ratsata, har tana fadin"sister kada ki daina yi mini addu'ar nan, ki cigaba, ina jin wani irin sanyi acikin raina," murmushi angel tasaki, tare da ɗaura hannayenta saman sumar kan batool dake a dumbuje babu gyara, ta shiga shafata tana faɗin"indai akanki ne, zan iya kwana batare dana runtsa ba, wurin yi miki addu'a, ina matuƙar ƙaunarki my batool, " muryarta asanyaye ta karasa maganar, 


  "Mu kwanta mu yi bacci, mu ma, " acewar batool, a manne da juna suka kwanta saman mattress ɗin, angel taci gaba da yi mata addu'a har sai da bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu,"


To jama'a, ɗaki fa ya yi shiru baka jin hayaniyar komai, hankalinsu kwance sai sharar baccinsu suke yi, kamar waɗanda aka yanka mutuwa agabansu, 


(Last posting da nayi wata tayi comment cewa ita data biya kuɗin littafi ƙwara tayi sadaka🤔 saboda rashin wayau har zata iya 6ata lokaci ta zauna ta karanta taji dadi, amma saboda tsabar. Baƙin ciki da hassada na wasu mutanan da basu ɗauki marubuta abakin komai ba, duk irin wahalar da suke yi su basu gani,  mutun ya 6ata lokacin shi ya zauna yayi typing yayi editing, yabi kuma ya tura maku, ciwon kai, ciwon ido ciwon wuya duk akan typing. Shima fa sana'a ce, menene 300 Ko500 wlh bazasu ta6a biyan marubuviya wahalar daya sha ba, munayi ne dan Allah yayi mana baiwar👌 duk wadda ta ƙara yi mini comment na jakkanci zanyi removing dinta daga group, Da masu hankali nake hulɗa, waɗanda suke da cikakken hankali da tunani.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post