Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 26

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 26


 BossLadiesWriters           💋KURKUKUN ƘADDARA💋Middle step  


          سجن القدر❤🤍❤              THE PRISONERS E26🔥💫
Daga alƙalamin Boss Bature
Confusion of the heart💫
Tun da Aneelerh ta turawa numbar saƙo har yau ba'a tuntu6eta ba, abun ya dame ta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kullum ne sai ta ƙara jaraba kiran layin ko za'aci sa'a mamallakin wayar ya ɗaga amma wani iko na Allah a kashe take samun layin duk ta damu da son jin wanene.  Fitowa ta yi daga cikin ɗakinta hannunta ruƙe da wayarta, ɗakin zahra ta nufa da niyar ta faɗa mata halin da take ciki wata'kil ta bata shawara akan abun da ke damunta.


  A bakin ƙofar ɗakin ta fara yin sallama, shiru ba'a amsa mata ba, kusan sau uku tana kwaɗa sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata'ƙil kuma wanka ta shiga.


  Haura ƙafa ta yi ta shiga ɗakin zahra, tun abakin ƙofar room din ta fara cin karo da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba ɗaya ta watso su saman floor, nan take hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta ɗago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta da pillow dinta duk ta watso su ƙasa, Komai na ɗakin ta tarwatsa shi.


Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai tsafta dagangan dai bazata ta6a barin ɗakinta a  hargitse ba.


  Cikin tashin hankali ta soma ƙwala mata kira"Zahra! zahra!!" shiru babu amsa, ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga ɗakin ummi, da sauri Aneelerh ta fuce daga ɗakin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami da ummi zaune suna fira, juyawa tayi da sauri ta nufe su, babu wanda Ya lura da ita acikinsu har saida ta furta"ummi mami Ina zahra" kusan atare suka ɗago suna kallonta, gaba daya sun fahimci babu kwanciyar hankali atattare da ita.


  Ummi tace"kin duba ɗakinta baki ganta ba"?

Kafin ta bata amsa mami tace"Aneelerh wai lafiya? Ya akai naga kamar bakya acikin natsuwarki"

 Muryarta na ɗan rawa ta furta"bakomai, na duba ɗakin zahra ne ban ganta ba"


  Mami tace"shine duk kika ɗaga hankalin ki? Sai kace yau ta fara fita daga gidan, kema kinsan zahra idan har ba wurin aiki taje ba toh tana acikin gida"


   Ummi tace"tun ɗazu fa ta dawo, ki kwantar da hankalin ki, bata wuce cikin ɗakinta, Ki koma ki sake dubawa"


  Juyawa tayi da sauri ta nufi ɗakin donta ƙara dubawa.


  Bayan tafiyarta ummi ta dubi mami"ƙawancen Aneelerh da zahra ba ƙaramin burgeni ya ke yi ba, har mamaki nake yi idan naga yadda Aneelerh take jan zahra a jiki, duk da ta girme ta"


  Mami na murmushi tace"ai shi ƙawance ba a shekaru yake ba, indai mutum Ya mallaki hankalin shi ko da ya girme ka zaka Iya ƙawance da shi, Ni kaina ba ƙaramin burgeni suke Yi ba, Allah dai Ya bar zumunci"


 Ummi tace Ameen ameen.

Daga haka su ka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.


 Afujajen Aneelerh ta faɗo ɗakin zahra tana faman Yin haki, ta kware murya tana ambaton sunanta"Zahra! zahra! Nasan kina jina, Dan Allah kiyi mini magana"


 Still babu alamar za'a tanka mata, ranta ne ya bata cewar wata'ƙil ta fita ne ba tare da sanin kowa ba, Har ta juya zata fuce daga ɗakin ba zato ba tsammani ta soma jin shessheƙar kukan zahra, da sauri Aneelerh taci burki, a sukwane Ta juya tana bin ko'ina na ɗakin da kallo, a ƙoƙarinta nata gano inda zahra ta 6uya, hankalinta yafi karkata akan toilet din ɗakin, da sauri ta ƙarasa bakin kofar ta kara kunnanta, sosai take jin kukan zahra mai matuƙar tsuma zuciya.

 Muryarta na rawa ta furta"Zahra meya faru dake? Wanene ya ta6a min ke? Dan Allah ki faɗamin zahra, ashe kina jina shine kika ƙi tanka mun ko?" cikin shessheƙar kuka zahra tace"...Aunty Aneelerh babu abun da ke damuna,  kawai bana son kowa ne a kusa dani"


  "Ki fito daga cikin toilet din muyi magana zahra, ni bana so inganki acikin damuwa, kema kin sani har farin cikina zan Iya sadaukarwa saboda ke, don haka ki fito muyi magana" cikin kwantar da murya Aneelerh take yi mata magana.


 "Zahra ke nake jira ki fito muyi magana, wlh idan kika bari na haura ƙafa ta daga cikin ɗakin nan to kada ki yi tsammanin zan waiwaye ki, haba dan Allah, ina amfanin irin hakan? Ashe dama baki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki ba? Har zaki Iya ke6e kanki cikin damuwa ba tare da kin neme ni ba"? 


  A faɗace Aneelerh ta ambaci hakan, duk don ta samu zahra ta buɗe ƙofar toilet din.


  Bugun ƙofar tayi da hannunta"kada Allah yasa ki buɗe ƴar rainin wayau" ta faɗa tare da juyawa ta nufi ƙofar fucewa daga dakin, Buɗe ƙofar toilet din zahra tayi, Fuskarta sharkaf da hawaye idanuwanta har sun kumbura, kumatunta sunyi jawur dasu, Short ne a jikinta tare da farar vest, Sumar kanta kamar ta mahaukaci sabon kamu.  Da gudun gaske ta nufi Aneelerh dake ƙoƙarin fita daga ɗakin, Gaba ɗaya ta faɗa saman bayanta ta rungume tana cigaba da yin shessheƙar kuka.


   Ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, tare da kai hannu ta ruƙo damtsen zahra ta zagayo da ita, har saida gabanta ya faɗi ganin yadda hawaye suka wanke mata fuskarta tamkar ba zahra ba, damuwace ƙarara akan fuskarta, kwantar da kanta Aneelerh tayi saman kirjinta, a hankali take shafa sumar kan zahra da yatsun hannayenta.


  "Ya isa zahra, ki daina kuka bana son ganin hawayenki,' cikin murya kuka tace"Aunty Aneelerh ba zaki gane ba, Ni kaɗai nasan halin da nake aciki, Allah ji nake kamar in haɗiyi zuciya in mutu kowa ya huta"


  Kalaman zahra sun ƙara ɗaga mata hankali, tabbas akwai gagarumar matsala, Yarinyar da koda yaushe fuskarta dauke da murmushi komai zaka yiwa zahra a duniyar nan baka isa ka 6ata mata ranta ba, sai gashi a yau itace take Yin kuka har tana faɗin kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.


  "Kiyi haƙuri zahra, bai kamata kina yin wannan furucin ba, Idan ma wani abune ke damunki meyasa ba zaki kai kukan ki ga Allah ba? sai kawai ki kulle kanki a toilet kina kuka? Hakan ya dace? Kina tunanin shine mafita a gare ki? Ga ummi ga mami, ga mahboob, ga abie da uncle uwa uba ga kuma ni meyasa ba zaki tuntu6i ɗaya daga cikin mu ki faɗa masa damuwarki ba? Kin tsaya kina yin zurfi ciki a ƙarshe ki yi wa kanki illa amma faɗamana da zakiyi shi zaisa ki samu maslaha na abunda ke damunki, ko da ace bamu da abun da zamu taimaka maki wurin yaye damuwarki zahra zamu Iya baki shawara ko mutayaki da addu'a akan Allah ya yaye maki"


  Faɗa Aneelerh tayi mata, sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, ruƙo hannunta Aneeleeh tayi"wuce ki shiga toilet ki wanke fuskarki Ina jiranki" ta faɗa tare da sakin hannun zahra, baiwarAllah jikinta duk ba ƙwari tana tafiya tana waiwayon Aneelerh, yayin da hawaye ke cigaba da fita a idonta.


   Kafin fitowarta Aneelerh ta bar ɗakin ta nufi falo, fridge ta buɗe ta dauko mata ruwa me sanyi. 


 Cikin tafiyar sauri ta nufi ɗakin.


 "Aneelerh kinga zahran ne"? Muryar mami ce ta katse mata hanzarinta, ba tare da ta juya ta kallesu ba ta bata amsa da cewa"Eh mami, ashe toilet ta shiga" 

 Bayan ta shiga ɗakin, ta daura ruwan a gaban mirror, ta koma bakin door din ɗakin ta soma tattara kayan da zahra ta watsar ta maida su a ma'ajiyarsu.


 Ba ta jima da zama a gefen gadon ba, Zahra ta fito daga toilet, ta wanke fuskarta kamar mara gaskiya ko haɗa ido da Aneelerh bata son yi, saman mirror chair ta zauna tana fuskanta  Aneelerh, sai dai ta taƙi ɗagowa su haɗa ido da ita.


  "Ga ruwan nan ki sha" ta faɗa tana nuna mata robar ruwan, data ajiye mata, Yatsun hannunta na kerma ta ɗauki bottle water din ta cire murfin ta soma ɗaɗɗakar ruwan kamar zata haɗa da robar duka ta shanye, bayan ta gama sha ta maida murfin robar ta daurata gaban mirror.


  "Zahra ina sauraronki, Ki natsu ki fadamin meya faru dake? Da har yaja kika kulle kanki a toilet, bana so ki furta mun kalmar babu komai! Ranki zai Iya 6aci" fuskarta a ɗaure tamau tayi mata maganar.


  Zahra na faman sunnar dakai, idanuwanta akan yatsun hannunta muryarta adabarbarce ta soma magana.


  "Aunty aneelerh zan faɗa maki amma kada ki faɗa ma kowa dan Allah," jinjina kai Aneelerh tayi"in sha Allah"


  Cigaba da yin magana tayi"dama akan decorating company dinmu ne, ban ta6a faɗa maki cewa banawa bane, mallakin mamansu ƙawata ne, Ni a lokacin dana kammala karatu ina neman aiki bansamu ba, Nayi ma daddy magana akan ya taimaka mini in buɗe Beauty saloon nawa nakaina, amma sai yace min shi baida halin da zai Iya taimaka mani, bayan ni nasan yana da arziƙin shi kawai baison bani ne kusan halin shi ɗaya da mahboob in dai wurin maƙone ko mami fama take yi dashi, dawowar ku gidan nan ne ma ya fara sakin hannunshi gudun kada ku gane halin shi,' Aneelerh ta natsu tana sauraranta.


  Numfasawa zahra tayi kafin taci gaba da cewa"akwai wata rana da naje gidansu ƙawartawa, muna zaune a falo muna fira akan yadda zamu buɗe beauty saloon da zamu gudanar da kasuwancin su, har take ce min mommynta tana da kuɗi sai dai itama maƙone da ita ba ta Iya fidda kuɗi ta bata hakanan idan ba abun da ya shafi karatunta bane, amma da zata amince mana ko da bashine ta bamu idan muka samu kuɗi tun da kusuwancin ana samu sosai indai mutun ya samu kar6uwa awurin mutane, sai na zaro ido nace mata a'a ni bana so muci bashi muzo mu kasa biya, na faɗi hakanne saboda sanin halin mahaifiyarta masifaffiyace bata da mutunci in dai akan kuɗin ta ne, Aunty Aneeleh fatima ta matsa mini akan muje muyiwa mommynta magana tasan idan na sanya baki zata bamu tallafin da zamu buɗe, saboda muna mutunci da ita, duk cikin ƙawayen fatima tafi sakewa dani har idan nayi kwana biyu banzo gidan su ba takan tambayi fatima ina ƙawarnan taki mai dimple da yake haka take kira na, sai tace mata zata kira ni idan tana son ganina, Aunty aneelerh tsautsayi ne ya kai ni ga amincewa da maganar fatima, muka kwasa muka je wurin mommynta, muka fada mata dangane da beauty salon din da muke so za mu buɗe gashi bamu da kuɗi, matar nan tayi dariya tace mana ai ba wani abu, ta ji daɗi da mu ka yi tunani mai kyau, ita tana son mutun me burin ya nemi na kansa, don haka zata buɗe mana company da zamu dinga gudanar da kasuwancin mu harma mu zuba ma'aikata acikin sa da zasu dinga taya mu aiki, idan yaso zamu dinga raba riba da ita, a lokacin munyi mamakin jin zata buɗe mana company mu da muke maganar buɗe ƙaramin beauty saloon, ni bansan da wata manufa a ƙasa ba, Ni da fatima munyi murna muka dinga yi mata godiya da addu'o'i, tun da ta buɗe mana companyn bata ta6a kar6ar ribar da muke rabawa ba, duk in muka kai mata kasonta sai tace mana mu ruƙe a hannun mu zata nema yanzu bata buƙatar kuɗi, Aunty Aneelerh tun muna tara mata kuɗin har dai fatima tace min mu kashe kudin ai mommynta bata buƙatarsu shiyasa bata kar6a ba, in yaso daga baya in muka tara wasu kuɗin sai mu biyata, zuciya ta ɗebeni muka haɗu ni da fatima mu ka kashe kuɗin, acikin su na cika da nawa kuɗin na sayi mota, Na canza wayata na sayi iphone 15, wayar da kika ga ina ruƙewa a hannuna, Na ciri dubu ɗari uku naba ummin mu nace gashi nan tasa mun albarka kasuwanci yayi kyau, ummi taji daɗin kuɗin nan, dama tana buƙatarsu daddy baya bata kuɗin da zatayi hidindimu dasu, duk nice fa nake taimaka masu idan na samu kudi, shi kawai ta 6angaren abinci ne yake yi mana ƙoƙari, sai kuma kayan sallah idan tazo amma inba sallaba babu abunda daddy yake yi mana, kudin shi sai dai muga wasu suna ci, acikin kuɗin naba mahboob dubu hamsin shima yai ta yi mini godiya hada ƴar ƙwallar shi saboda daɗin da yaji....' dakatawa ta ɗanyi da yin maganar hawaye nabin fuskarta, tun kafin ta ƙarasa jikin Aneelerh yai sanyi don tasan ƙarshen zancen bamai daɗi bane.


   Jinjina kai zahra ta ɗanyi kafin ta daura da cewa"Aunty aneelerh saida na tabbatar kuɗin sun ƙare tukunna hankalina Ya kwanta, sai kwanan nan da Hajiya saratu ta kira awaya suna buƙatar ayi masu decoration da kitso da ƙunshi, lokacin dana duba asusun mu, ba mu da isassun kuɗin da zamuyi order na kayan da za'ayi masu amfani, dama dai ita hajiya falmata itace take yi mana hanyar da ake shigo mana kayan adon daga dubai, muka zauna nida fatima mukayi shawara sai tace min zatayi ma mom dinta magana, bayan sunyi magana da ita, sai ga fatima tazo wurin aikin mu idanuwanta jawur dasu, hankalina atashe na tambayeta lafiya meya faru da ita, cikin shessheƙar kuka tace min mominta tace idan har muna so tayi mana order din kaya mu fara tura mata ribar da muka tara mata a hannun mu, tana buƙatar kuɗin da gaggawa, tun anan fatima tace mata ai babu kudin nan mun kashe su, tsabar 6acin rai ta zazzaga mata masifa tamkar ba ƴar ta ba, hada mari ta kwasa mata a fuska, ko lokacin da tayi mini magana fuskarta da sahun yatsun hannun mahaifiyarta, Hankalina ba ƙaramin tashi yai ba, saboda ni bansan inda zan samu kuɗi na biyata ba, daga ni har fatiman bamu da kuɗin a hannun mu, Aunty Aneelerh nasan bamu kyauta ba tunda ba kyauta ta bamu ba, amma muka ta6a mata kudinta bayan yarjejeniyace muka ƙulla da ita akan duk in aka samu riba zamu raba kaso uku, matsalar da aka samu kuɗin data bar mana a hannun mu taƙi kar6arsu har saida tsautsayi yasa muka ta6a su...." fashewa tayi da kuka Aneelerh ta natsu tana dubanta.


  "Nayi ƙoƙarin Na saida motata don na samu na biyata kuɗinta sai dai bansamu wanda zai siya ba, Jiya ina kwance saman gado na gama shan kuka na sai ga kiran fatima awaya, na ɗaga muka gaisa da ita, tace min mominta tana son Yin magana dani inzo in same ta agida, hankalina ya dan tashi don tunda muƙe nuƙu nuƙu akan yadda zamu biyata kudin bata ta6a yin maganar dani ba, tsakaninta ne da fatiman, nace mata zuwa gobe zanzo gidan nasu, jiya ko bacci banyi ba, da sassafe na shirya babu wanda ya san na fita daga gidan nan naja mota naje gidansu fatima babu kowa afalon gidan saida mai aikin gidan ta fito daga kitchen muka gaisa take ce min ai hajiya ta faɗa mata game da zuwana in shiga ɗaki tana jirana, da sauri na juya na nufi ɗakinta gabana na faɗuwa abakin kofar ɗakin nayi mata sallama, muryarta ƙasa ƙasa tace min wanene? nace mata zahra ce ƙawar fatima mai dimple, tace in shigo ciki....." dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana faman ƙyafƙyafta ƙwayar idanuwanta.


 Cikin ƙagara da sonjin ƙarashen zancen Aneelerh tace"naji kinyi shiru? Me tace maki ne"! Yawu zahra ta hadiya muryarta na ɗan rawa ta ɗaura da cewa"Ina shiga ɗakin na same ta kwance saman gado daga ita sai ɗan undy shara shara ajikinta, arude na juya zan fuce da sauri ta kira sunana zahra zonan, cak na tsaya ba tare dana juya na dube ta ba, ta sauko daga saman gadon ta nufo inda nake a tsaye ta tsaya daga bayana ta soma yi min magana .


  Ya maganar kuɗina da zaku bani? Nayi magana da fatima tace min atare kuka kashe kudin meyasa zahra? Ban ta6a tunanin za ku yi mini haka ba, Na yadda daku na damƙa maku amana amma kuna nema kuyi mini wasa da dukiyata, ko dan ba ku san zafin nema bane"?  faɗa sosai tayi mini bansan lokacin dana fashe mata da kuka ba ina roƙonta akan tayi hakuri nayi mata alƙawarin zan biyata kuɗin ta cikin satin nan, Aunty Aneelerh ba zato ba tsammani naji ta sanya hannu ta ruƙo hannuna, ta juyo dani ta rungumeni a ƙirjinta, ban ɗauka da wata manufa ba sai da naji tana matse ni a kirjinta gabana yaci gaba da faɗuwa, cikin dabara ta miƙa hannu ta bayana ta datse ƙofar ɗakinta da jamlock, ba tare da sanina ba...." ganin yadda Aneelerh ta zaro ido waje yasa zahra ta dakata da yin maganar la66anta na kerma.


 Aneelerh tace"zahra ke nake sauraro uban me tayi maki" a kausashe Aneeleeh ta furta mata hakan, cikin ruɗu zahra tace"nayi ƙokarin raba jikina da nata amma saita ƙara tighting dina, ta zame mayafin dake akaina, ta sanya hannu tana shafa sumar kaina cikin raɗa take furta min"meyasa nake yi mata kuka? Ko dan saboda tayi mini faɗa akan kuɗinta ne, muryata na kerma nace mata ta yi haƙuri zan biyata kudinta, tace min in kwantar da hankalina ai ba dole saida kuɗi zan Iya biyanta ba, A jikina ma ina da abun da suka fi kuɗi daraja, idan na amince na bata haɗin kai zata yafe mana bashin harma ta yi mana order na kayan decoration din da muke so, cikin rashin fahimtar maganarta nace mata ni ban gane me kike nufi ba? Menene yafi kuɗi daraja a jikina? Kuma wani irin hadin kai kikeso in baki"? Har lokacin bata raba ni da jikinta ba, saima nishi da naji tana saki, tace min tana buƙatata jikina kawai takeso, zatayi amfani dani.


  Saboda yarda da nayi da matar saina dauka wasa take yi mini, Cikin sanyin murya nace mata mommy amma dai zolayata kikeyi ko"? Na fada ina kokarin raba jikina daga nata saidai taƙi bari inyi hakan, kamar zata maidani cikinta.


  Babu alamun wasa a kalamanta tace min" Zahra na ta6a yi miki wasa irin wannan? Nace mata a'a, tace min toh dagaske take, dama ta jima tana kwaɗayin son kasancewa tare dani bata samu damar yin hakan ba don ta lura kamun kaine dani kuma ni ba ƴar harka bace, shiyasa ta yi dabarar amincewa da buƙatarmu ta buɗe mata company kuma taƙi kar6ar kuɗin ribarta dake a hannun mu, Ashe maƙarƙashiya ta shirya mini saboda tasan zamu iya ta6a kuɗin, Ni ban ta6a tunanin matar zatayi mini haka ba.


     Aunty Aneelerh data faɗamin hakan tsigar jikina ta tashi, na rasa uwar ubana, na soma kiciniyar ƙwace kaina daga ruƙon da tayi min ina fadin ni ki sake ni in tafi gida, wlh kin ban mamaki  na dauke ki tamkar mahaifiyata saboda ƙaunar dake a tsakanina da fatima ashe nayi babban kuskure, Ni bazan ta6a baki haɗin kai don mu aikata sa6on Allah ba, kema inayi maki fatan Allah ya shiryeki,' sai da nasha wahalar bangajeta, da gudu na damƙi ƙofa zan buɗe naji ta a garƙame kafin in zare jamlock din Naji ta damƙeni ta wurgar dani saman gado tana fadin"baki isa ki kubcemun ba zahra, dama nasan zakiyi min taurin kai shiyasa na biyo maki ta wannan hanyar, wlh idan har kika bijirema buƙatata zan saki dole ki biyani kuɗina a yau ɗin nan idan ba haka ba zan damƙa ku hannun lawyer dina, sannan zan rufe companynku,"


 Ina kuka nace mata naji ta bani lokacin da take son kuɗinta In sha Allah zan biyata amma ni kada ta kuskura tace zata ta6a jikina, ta jira taga idan ban biyata ba sai ta yi mini duk abun da ta ga dama, tana faman sakin shu'umin murmushi tace min bataso inyi danasani, don tasan banda arziƙin da zan Iya biyanta, tasan wanene mahaifina karen ƴan siyasane sai yayi masu wahala suke watsa mashi hatsin da zai samu ya tsastsaga harma ya ɗan mana, raina ya 6acin sosai jin irin wulaƙancin da take yi mini nasan nina ja ma kaina, dama ance kwaɗayi mabuɗin wahala, sannan idan har kace zaka dogara da wani kana tare da wahala, sai dai ba yadda zanyi ne tun farko da nasan wacece ita wlh daban amince ta buɗe mana company ba, daƙyar na samu ta ƙyale ni abisa sharadin gobe da safe ƙarfe 7 tana jiran alert na kuɗinta, wlh idan daddy yaji maganar nan sai ya kusa kasheni, ni bansan ya zanyi ba"


 Zuciyar Aneelerh tayi matuƙar karaya, tayi mamakin Hajiyarsu zahra me halin bunsuranci.


  "har nawa ne kudin"?

  Zahra na matsar ƙwalla tace"kusan fa miliyan shidda muka raba ni da fatima" 


  Zaro ido waje Aneelerh tayi tana mai jinjina kai tace"tabɗijancan, ashe da rabon zahra ki kwana a cell, don kuwa babu abunda zai hanaki zuwa gidan Yari, Ni har na hangoki cikin uniform dinsu" fashewa zahra tayi da kuka jin abunda aneeelerh take faɗi.


  Cikin shessheƙar kuka tace"Aunty aneelerh kidaina banso, bakisan halin da nake aciki bane shiyasa kike zolayata, wlh saboda tashin hankalin da nake aciki tun safe ko ruwa ban sha ba"


  Tsananin tausayinta ne Ya kama

 Aneelerh, idanuwanta sunyi jawur dasu kamar an watsa mata barkono, muryarta na rawa tace"Aunty aneelerh ko zaki taimaka mini mu je mu nemo wanda zai sayi motata da wayata kafin lokacin Ya cika" Jikinta na kerma tayi magana.


"Lokacin da ku ka yi yarjejeniyar buɗe companyn kinyi shawara da wani? Ina nufin Uncle ko Ummi akwai wanda kika faɗa mawa"?!


  Girgiza kai zahra tayi"Ni ban faɗa ma kowa ba, babu wanda ya sani, kawai dai na faɗa masu na samu aiki a company, sun tayani murna kuma sun yi min fatan akhairi, ummi ma ta ta6a tambayana ya akai companyn yaci sunana? Kamar nawa, sai nace mata banawa bane, Yarinyar me companyn ce takwarata shiyasa aka sanya mashi Sunan Zahra world of beauty"

  

Jinjina kai Aneelerh tayi"Kinyi babban kuskure Zahra, Matar nan Tayi maki wayau, Nafi ganin laifin ki, ke fa da kanki kikace kinsan halinta masifaffiyace amma ahaka kika biyewa fatima ku ka kashe kuɗi har miliyan shidda bayan kinsan ba gadon ɗan iya bane, Idan ita yarinyar bata da wayau ai ke da hankalin ki, kuma ita dukiyar mahaifiyarta ce, ke kuma fa? Baki haɗa komai da ita ba,Yanzu ai gashinan taja maki bala'e, ko dai ki biyata kuɗinta ko ta maka ki kotu, Ni dai shawarar da zan baki shine kije ki yi mata abun da take so!" hankali akwance aneeelerh tayi mata magana, tayi tsammanin zata taimaka mata ne donsu nemi mafita amma sai taji tana fadin hakan, zuciyarta ta karaya sosai, har batasan sa'adda ta fashe da kuka ba, ta sauko daga saman kujerar ta zube saman gwiwowinta Cikin shessheƙar kuka take fadin"Na shiga uku aunty aneelerh, amma dai wasa kikeyi mini ko? Ni nasan bazaki ta6a bani shawarar in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, wallahi ina tsoron Allah, Ina tsoron ranar da zan koma gare shi"


 Ɗaure mata fuska Aneelerh tayi"Idan har baki amince mata ba zahra tayaya kike tunanin zaki Iya biyanta? Kinsan halin mahaifinki bazai ta6a biya maki kudin nan ba, Ummi kuma bata da kuɗi, zahra ƙwara ki bata haɗin kai, nayi maki alƙawarin babu wanda zai ji abunda ya faru, daga ni sai ke, kinga tace zata ƙara maku wasu kudin harma tasa ayi maku order na kayan da zaku yi amfani da su daga dubai, wallahi zahra ki amince mata idan ma don baki saba bane zaki saba a Hankali, Allah kuma gafurirrahim ne, zaki iya tuba ko daga baya ne in ta gama amfani dake" 


 Zazzare ido waje zahra tayi yayin da take kallon Aneelerh, cikin matsanancin tashin hankali da ruɗani, Muryarta na rawa ta furta"Aunty Aneelerh dagaske kike? In bata hadin kai"? Murmushi Aneelerh ta sakar mata hadi da ɗaga mata gira alamar eh, girgiza kai zahra tayi idanuwanta cike tab da ƙwalla tace"wallahi aunty Aneelerh bazan Iyaba, koda kuwa duniya zata mallaka mini don in biya mata buƙatarta bazan ta6a amincewa ba, da in sa6ama Allah na ƙwammace in rasa komai dana mallaka don In biyata kuɗin ta, ina tsoron Allah kuma ina jin tsoron ranar da zan koma gare shi, yanzu idan na mutu kafin in tuba fa"? ta faɗa yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta, kallon da take bin Aneelerh da shi, kallone na mamaki da al'ajabin shawarar da ta bata, har ta fara kokwanton Anya kuwa Aneelerh ce wannan? Ko dai Aljanu sun shige ta ne?


Gyaɗa kai Zahra tayi cikin rauni na murya ta furta "Aunty Aneelerh ki daina wannan maganar kina rikita mini tunanina, idan har ba zaki taimaka mini mu nemi mafita ba bai kamata kina tunzurani akan in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, har kin sa nafara kokwanto akanki duk da nasan wacece Auntyna"


 Ta6e baki aneelerh tayi haɗi da watsa hannayenta tace" Zahra, we don't have any other solution besides this, ina ƙara jaddada maki, ki hanzarta zuwa ki biya mata buƙatarta, idan ba haka ba zata kai ƙarar ki kotune sannan ta rufe maku companyn ku, amma idan kika bata hadin kai, kinga zaki ci riba biyu da farko zata yafe maki bashin da take bin ki, na biyu kuma zata yi maku order na kayan amfani daga dubai, wannan fa babbar dama ce agare ki!!!" da sauti mai ƙarfi ta ƙarasa maganar, fuskarta babu annuri, ta yunƙura ta miƙe tsaye, Zahra ta saki baki tana kallon ta da rinannun idanuwanta.

  "Ni kinga tafiyata, Idan kin canza ra'ayin ki kina iya zuwa ɗaki ki same Ni, zan taimaka maki da mayukan da zaki gyara mata jikin ki" ta hankaɗe kafaɗa ta juya ta nufi kofar fucewa daga ɗakin.


 Kamar sakarya haka zahra tabi bayan Aneelerh da kallo har ta 6ace ma ganinta, hannu biyu ta ɗaura saman kanta, tana faman ambaton kalmar Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un" 


Tsantsar tashin hankaline akan fuskarta, wani irin azababben zazza6ine ya lullu6eta, saman floor ta kwanta, idanuwanta na fuskarta ceilling, yau Aunty aneelerh ta bata mamaki, ta karya mata zuciya, duk da har yanzu ta kasa yarda da abunda zuciyarta ke faɗa mata dangane da ita, batasan ya zatayi ba? Don ita har ga Allah bata jin zata amince da shawarar Aneelerh ta ƙwammace ta tattara duk wani abu data mallaka taje ta biyata kuɗinta zaifi mata kwanciyar hankali akan ta sa6a ma Allah, tazo tana danasani mara amfani, babban abunda take jima takaici asarar da zatayi na zuwa gidan Obinna, On friday na satin da suke ciki Za'ayi shagalin birthday na babansu, already sun fidda masu anko, decoration ne da kitso suke buƙatar ayi masu jibi, tasan tarasa wannan damar, Hajiya falmata baza ta bari ta cigaba da yin aiki a companynsu ba muddin bata amince da buƙatarta ba, gashi ita bata da komai, dole ta haƙura tama riga da ta fidda rai, shawarwari ta shiga yankewa da zuciyarta, a karshe ta yanke shawarar Zata yi magana da mahboob watakil ko cikin abokanan sa  asamu wanda zai sayi motarta da wayarta, da wannan tunanin baccin wahala ya ɗauke ta, babu ci babu sha tun safe baiwar Allah.


DAULAR OBIE ESTATE


Zayn ne kwance saman shimfiɗeɗen gadonsu, daga shi sai short a jikinshi, tun da suka dawo daga office yake ta sharar baccin shi kamar matacce, toilet door din ɗakin aka buɗe Zaid ne Ya fito waist dinshi ɗaure da towel, jikin shi da alamun danshin ruwan wankan da yayo, tun kafin ya ƙarasa gaban gadon ya soma ambaton sunan zayn.


  "Bro, get up, I want to have an important talk with you, please," ya faɗa ayayin da yake ƙokarin zama gefen gadon, hannu yakai yana bubbuga ƙafarshi"pls ka tashi zayn, baccin ya isa haka sai kace mai sleeping sickness, tun da muka dawo daga office kake ta sharar bacci ko dai ka sha ƙwaya ne"? Ya faɗa yana cunkulin kafar zayn da mugunta, dogon tsoki Zayn yaja, yana faman yamutsa fuska ya furta" 


"Zain, I don't want to be stressed, please, let me rest, I'm tired,"


Rai a6ace yai maganar ba tare daya buɗe idanuwanshi ba.

  Zain na murmushi yace"Haba babyn mommy, you should wake up, you've had enough sleep. I know it's not just work tiredness that made you sleep, because your secretary told me that you're not doing anything other than gathering girls in your office. Ko nayi ƙarya?" He spoke jokingly, looking at Zayn's face, tamkar bai ji me yace ba, Ya haɗe fuska babu annuri.


  "Dole kayi shiru, tun da baka da abun cewa, adai dinga jin tsoron Allah, taƙamarka kana da kyan fasali shiyasa kake maƙure Ƴan matasan mata a office kana zare masu ido, don kasan dole suyi maka biyayya tunda suna aiki a ƙarƙashin ikon ......" bai ƙarasa maganar ba, sakamakon zaburar da zayn yai ya miƙe tare da damƙar pillow, ya buga mashi akai, Ya janyo wani pillow ya dinga bugunshi ta ko'ina, Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yake fadin"zaid ka takura ma rayuwata, kai ma ka sani wallahi nafi ƙarfin in maƙure ƴa'ƴan mutane a office, Ni bana yima mace dole in ba ita ta nuna tana buƙatana ba, kai ne dai bunsuru da baka Iya gani ka kauda idonka, Ni  da aji na matane suke kawo kansu wurina bani nake kiran su ba" ya faɗa yana hararansa"shashasha kawai mai kama da daddy" Ya ƙare maganar Yana haki kamar wanda yasha gudu, idanuwanshi sun kaɗa jawur saboda baccin da bai ishe shi ba.


   "Zayn? Ni ne bunsuru? Kuma mai kama da daddy? Kana nufin shima daddyn mu bunsurun ne"? Fuskarshi a ɗaure yayi maganar.


  Ɗaga mashi gira zayn yai"ƙarya nayi ne? Babyn daddy, Nifa ba ina nufin bunzuru na dabba ba, No, just ina kwantanta Namiji mai bin mata ne da sunan bunsuru, kasan shima bunsurun haka ɗabi'unsa suke, duk inda yaga mace sai ya bita, shiko namijin da mata suke kawo kansu gare shi bazai yiwu ba a kirashi da bunsuru, sannan Ni bance hada daddy ba, kai kaɗai na ce" a fusace zaid yace"kada ka manta, dani dakai bamu da banbanci ko a murya, idan ina kama da daddy then you look like him too, and you're a he-goat as well.


gwalo zayn yai mashi"Oho dai, ai kwanan nan zanje ayi mini surgery amaida mun kamannin fuskata irin na mommyna, donni bana son abunda zai haɗa ni da ku" da zolaya yake yi mashi magana, amma shi zaid sai yake ganin kamar baison shi ne, ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa zayn saurin cewa" wasa fa nake yi maka, kaima ka sani ni da kai abu ɗayane, na fadi  hakanne don in 6ata maka rai kamar yarda ka tada ni daga bacci"

  Yamutsa fuska Zaid Yai"naji, yanzu dai mu ajiye wannan gefe, Ya maganar zuwanmu america"? Yai tambayar yana duban fuskar Zayn

  "Bamu da isassun kuɗi a account, Ni dai na hakura, ƙwara kaima ka haƙura kawai muyi zaman mu a ƙasar mu ta gado,"

  Girgiza kai Zaid yai"bazai yiwuwa ba, zayn bakasan yadda naci burin haɗuwa da Ummi ba, Jiya har mafarkin ta nayi, na kasa gogeta acikin zuciyata"


  Ta6e baki zayn yai"faɗamin acikin mafarkin me kuka aikata"

  "Bamu aikata komai ba, kawai dai mun hadu a jabi lake mall, har nake tambayarta yaushe ta shigo ƙasar? Kafin ta bani amsa ka katse mini bacci ka tada ni kana fadin lokacin sallar asuba yayi"


  Murmushi Zayn ya sakar mashi"kace nayi maka buƙulu, wata'kil da har kiss ta manna maka da hug"

  Harara zaid ya jefa mashi atakure yace"ya zamuyi ni dai? Ko dai mu kar6i Atm din daddy daya ce zai bamu"? da sauri zayn ya girgiza kai Yana fadin"No, ba zamu kar6a ba" zaid yace"why? Ni bansan meyasa baka son mu kar6i Atm dinsa ba, maƙudan kuɗi ne fa zayn zasu ishe mu muje duk inda muke so, wai kai kafi son muyita wahalar jiran salary"?


  "Eh, ƙwara mu jira salary, akan mu kar6i kudin da ba mu san inda aka same su ba, ka yi amfani da hankalin ka mana, ina daddy yake da arziƙin tara waɗannan millions of dollars din? Abun da baka sani ba, Dana zauna na lissafa dukiyar mommy ko rabin tashi bata kai ba, ita da ta gaji arziƙin kenan, da farko nayi tsammanin ko kuɗinta ne ta bashi ajiya amma daga bisani na zauna nayi nazari sosai na gane cewa kuɗin nan fa bana mommy bane, kuma ba albashin daddy bane suka tara mashi su, Ni tsorona kada mu je mu kar6i kudin sai mun gama sharholiyarmu asiri ya tonu agano daddynmu yana aikata wani abun, duk da ina kyautata mashi zato, amma gaskiya ni zaid ban yarda da kuɗin nan ba, bada guminsa ya tara su ba, akwai dai wani abun a ƙasa"


  Damuwace ƙarara akan fuskar zaid sam babu alamun Ya fahimci zancen twin bro dinsa.


  "Na lura zayn baka son daddy, baka ƙaunar shi, kafi son mommy, sai kace bashi bane ya haife ka, na tabbata da ace mommyne ta baka atm dinta jiki na rawa zaka kar6a ka yi amfani da kuɗin amma da yake na daddy ne shine kake neman yi mashi ƙazafi, wallahi kaji tsoron Allah zayn, mahaifin mu babu abunda yake aikatawa da guminsa Ya tara kuɗin shi, wata'kil dama can me arzikine Ya dai 6oyene don baison agani, amma nidai ina kyautata mashi zato, kuma atm daya bamu don yaga muna buƙara kuɗine Yana so ne Ya faranta mana" Zayn ya natsu yana kallon dan uwan nashi ya haƙiƙance Yana yi mashi magana, sai da yakai ƙarshen Aya tukunna zayn yace"baka amfani da ƙwaƙwalwa, ta inda muka banbanta kenan, Zaid ka faɗa min wani ubane zai ɗauki maƙudan kuɗi irin wadannan yaba ƴa'ƴanshi don suyi sharholiya? Ba tare daya tambayi me zasu yi da kuɗin ba? uba na gari bazai ta6a aikata hakan ba, Ni bani ke bansan daddy ba, shine baison mu zaid! Saboda tun da muke dashi bai ta6a zaunar damu a matsayin shi na mahaifinmu yayi mana nasiha akan rayuwar duniya ba, ko lahirarmu, komai mu ka yi dai dai ne a wurin shi, Mommy ce kaɗai take tsawatar mana idan mu ka yi ba dai dai ba......"


 Tun da Zayn ya fara magana muryarshi a kausashe, idanuwanshi sun kaɗa sun ciko da ƙwalla, zaid dake sauraron shi, Yayi shiru yana kallon shi, Jikin shi ya fara yin sanyi, dakatawa ya ɗanyi yana faman fitar da huci, kafin ya ɗaura da cewa"idan har dagaske kuɗin shi ne meyasa be yi amfani da su ya gina mana gida na kanmu ba? bayan yasan duk irin gorin da ake yi mashi, hmmm kawai baison asan Yana da kudin ne don yasan za'a tuhume shi ina ya same su, shine kawai," shiru su kayi ɗakin Yayi tsit na ɗan wani lokaci, 


  "Kaina harya fara ciwo, Inaso in kwanta In huta" Zaid ne ya ambaci hakan tare da miƙewa Ya nufi closet din Kayansu dake acan cikin ɗakin,

  Kwantawa zayn yai saman mattress yayin da idanuwanshi suke fuskantar ceilling, abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba, Yana matuƙar jin ɗacin irin rayuwar da mahaifinsu yake yi.


Hajiya Saratu ❤


A tsaye take gaban mirror, jikinta sanye da Jallabiya, babu mayafi akanta, hakan ya bayyana kitson zanan dake akanta, hannunta ruƙe da wayarta ta karata a kunnanta, fuskarta da fara'a, ga dukkan alamu magana take yi da wani awaya.


  "Nayi mamakin ganin kiranki, Allah dai yasa lafiya, don nasan hakanan baki nema na, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba" 


On the other hand matar da suke yin waya ta soma magana, Daga jin muyarta babbar macace mai ji da qasaita.


  "Oh, saboda kada na fara yi maki ƙorafin baki kirana shine kika rigani yin magana"?


 Hajiya saratu na dariya tace"wallahi ba haka bane Hajiyata, abubuwane suka yi min yawa, amma duk da haka ai ina ƙoƙarin tura maki saƙon barka da juma'a, ke dai ce baki nemana, amma nayi maki uziri saboda hidindimun al'umma da kuke fama da su, nasan sune suka sanyaki busy"


 "Hakane, amma kada ki damu, dama dalilin dayasa na kira ki, game da zuwanmu gidane, Naga saƙon ankon da kika tura mini nagode, so abunda nikeson kiyi mini, Inaso ki fada min me baba yafi so"? murmushi saratu tasaki, Har cikin ranta taji dadin tambayar da tayi mata.


  "Gift ne zaki shirya mashi na birthday dinshi"?


 "Eh, na tambayi yayanki akan ya faɗa min me yafi so, kinsan halin shi, cewa yai shi baisani ba, Duk abunda yayi mini in siya mashi, Ni kuma nafi son abun zai burge shi sosai"


 Dariya hajiya saratu tayi tana fadin" Gaskiya baba ni kaina bazan Iya cewa ga abunda yafi so ba, amma kwanakin baya naji yana magana da abokinshi akan yana son suturar su na al'adar inyamurai, tun lokacin dai banji sun ƙara magana ba, kuma ba akawo kayan ba, idan har kika shirya mashi su a matsayin gift dinsa, Nasan zai yi farin ciki sosai kuma zaiyi mamaki"

   

  "Okey, Send me his measurements through WhatsApp, and please don't let anyone know. I want to surprise him." ta amsa mata da toh nima agaida mun da yayan nawa, ko na kira shi sai yaga dama yake ɗagawa, Ina nan ina jiran shi zamu haɗu ne" sautin dariyar hajiyarne ya cika kunnanta da ba'a tace"Ai kin fi kowa sanin yayan naki, sai dai ki ba wani labari" Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama, Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin zama gefen gadonta, Muryar Hajjaty ta katse mata hanzarinta, tayi mamakin jin sallamarta, don koda gigin wasa bata ta6a tako ƙafarta zuwa ɗakinta ba, Jim ta ɗanyi kafin ta furta"Wacece" ta fada tamkar bata gane me magana ba"


  "Hajjaty ce" jinjina kai Hajiya saratu tayi tuni mood din fuskarta Ya canza, jim ta ɗanyi kafin tace"zaki Iya shigowa"


  A hankali ta turo ƙofa ta shigo ɗakin, tun daga ƙasa hajiya saratu ta soma binta da wani matsiyacin kallo, pakistan ne ajikinta farare, ta ca6a uban ado, sai dai babu ƙamshin turaren nan, sai ka matsa kusa tukunna zaka Iya jin shi, hannunta biyu ruƙe da wooden tray, kayan abincine shaƙe asaman shi.


    Lamarin ya ɗaurewa Hajiya saratu kai, tayi sototo tana kallon ta

  Muryarta na ɗan rawa ta furta"Ina wuni" yamutsa fuska tai"da ban wani ba kin ganni, shin wai ma me ya akawo ki room dina? Makuwa ki kayi ne"? Fuska adaure ta mata maganar.

  Duk tasha jinin jikinta, adabarbarce ta furfa"am..umm...dama abincine na kawo maki, Ni na girka shi da kaina abincin ƙasar mu ne..." daƙyar ta ƙare maganar a tsananin tsoroce.


  Murmushin yaƙe hajiya saratu ta sakar mata"dama ke ce kike kawo min abinci? Ina masu aikin gidan ne? Ko sunyi yaji ne"


  "Suna a kitchen suna aiki, kawai nayi ra'ayin in kawo maki ne da kaina, nasan zaki ji daɗin girkin tun da baki saba cin kalar shi ba" hankalin ba akwance ba take yin maganar,

  Ruƙe ha6a hajiya saratu tayi tana faman jinjina kai tace"To fa, sabon salo, tanan kika biyo? An gaya maki bani da hankali ne da zanci abincin da kika girka da hannun ki? Wato bokan ki ya haɗo ki da maganin barbaɗe kin zuba min aciki shine ki kawo mun don inci in mutu saboda kinsan abinci ne lago na ko"? 


 Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, cikin sanyin murya tace"Allah shine shaidata, tun da nake arayuwata ban ta6a takawa naje wurin boka ba, kuma ni banzo da niyar in cutar dake ba, abincine kawai na kawo maki, dan Allah ki kar6a ki ci......" Kafin ta ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dakata mata tsawar data firgitar da ita, jikinta ya kama kakarwa, nuna mata hanyar fita tayi daga ɗakin"Fuce min daga ɗaki tunkafin Inyi ƙwallo da tray din hannun ki, Ƴar rainin wayau, wallahi na fi ƙarfinki ba za ki ta6a cin galaba akaina ba, tunda can baki ta6a girka abinci kin kawo min don inci ba sai yau da kika shirya kashe Ni"?


 Tuni idanuwan Hajjaty sun cicciko tab da ƙwalla, cikin shessheƙar kuka tace"meyasa kika tsaneni? Laifin me nayi maki? Duk cikin masu aikin gidan nan ni kaɗaice ke bakiso, idan laifi nayi maki ki faɗa min sai in gyara"


 A tsawace Hajiya saratu tace"wai ke baki da hankali Ne? Kin manta wacece ni acikin gidan nan? Ko kin fara shaye shaye ne? Ni narasa gane wani tsautsayin ne ya kawo ki cikin ɗakina, I don't know where you get the nerve to talk to me face to face, ke ga ta6ararra dallah fuce ki ban wuri"


Juyawa Hajjaty tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, Kamar zatayi tuntu6e, gutun tsoki Hajiya saratu taja tare da samun wuri ta zauna gefen gado, tana mai mamakin ƙarfin hali irin na Hajjaty.


Kaɗan daga Cikin na sati mai zuwa Idan Allah yakaimu da rai da lafiya 🔥🔥🔥


A firgice Zainab ta dago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen, Cikin shiga ta baƙar jallabiya, Ta rufe fuskarta da niqab, Hannunta ɗaya ruƙe da trolley, sam babu natsuwa atattare da ita, hankalin zainab ba ƙaramin tashi yai ba, tsananin tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta"baiwar Allah wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? Ƙarfe sha biyu na dare"? Aruɗe take jefa mata tambayar,

  Shessheƙar Kukan matar ne Ya ƙara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana ƙoƙarin guduwa cikin gidan don ta faɗo ma Hajiya layla abunda ke faruwa sai dai kafin Ta juya muryar Matar Ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faɗin

  

عمتي زينب، هذه أنا بنازير، أين أبي؟ أمي، والدتي؟ أين زوجي وابنتي؟


har bada bazata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amfarkine Tajita tabbas zata shaida mamallakiyarta,

   A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali Ta daura ziraran yatsun hannun ta farare tas ta ruƙo ƙasan niƙab ɗin fuskarta ta ɗage shi sama" tsabar kiɗima da ganin fuskar da tayi kimanin shekara sha shidda batayi tozali da ita bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al'ajabi akan fuskarta, ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar matar, sam takasa yadda da abunda idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!!!


Kamar Fatalwa, Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta ko'ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.........  💋ABBAN SOJOJI💋 

💋KURKUKUN ƘADDARA💋Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440  whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za'a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature


 ✍ Mu haɗu Monday In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin
First bank
3196407426,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post