tun daga wannan ranar ne shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai da ta kai ga Mahboob ne ke zuwa gidansu ya ɗauke ta ya kaita school idan an tada su ya je ya ɗauko ta, Hajiya Sarah tasan da komai, kuma ta ji daɗin kulawar da yake ba Zeenatu, saboda shi yasa yanzu bata zama da damuwa a ranta.
Daga bisani Zayn Ya auri Zahra bayan kammaluwar bikin su, Anan gidan sa na cikin Imam Estate suke da zama, yayin da Zaid ya ke jiran Sajeeda ta kammala karatu kamar yadda ta nemi alfarma a gurinsa na cewa ya bari ta gama karatu sai su yi aure, Shi ma Mahboob Zeenatu ya ke jira ta kammala karatu kafin su yi aure.
___________________________________💗🔥
Taj bai manta da alkawarin da yayi akan Zai raka Danejo takai ziyara gurin yan uwanta fulanin Daji, bayan da suka samu kwanciyar hankali, a rana ɗaya suka shirya da shi da Unaisah da mommyn ta, tare da Danejo da kuma rakiyar Isod Soldiers wanda Owais ne ya Umarce su da su basu kariya saboda yaji Daji ne in da zasu je, bayan sun isa Dajin danejo bata manta da inda rigarsu take ba, ita ta jagorance su can cikin dajin har inda rigar ta ke, Ba zato ba tsammani Yan uwanta suka ganta tare da mijin ta da iyalinsa, tsantsar Al'ajabi ne ya kama su, nan take suka fashe da kukan farin ciki, itama ta kama kukan murnar ganin yan uwanta, bayin Allah basu ta6a tsammanin za su sa ke haɗuwa da Danejo ba, tun bayan da suka ba Taj amanarta ya tafi da ita, damuwa da zullumin awani hali take a ciki ya cika zukatansu, basu ta6a mantawa da ita ba, a lokacin har sun fidda rai da ita, duk in su ka tuna da ita sai sun yi danasanin ɗaukar ƴar su marainiya su ka ba bare, amma zuwan da Taj ya yi da Danejo Ya faranta ran su, sunyi farin ciki mara misaltuwa, sun ƙara jin kaunarsa ganin yadda ya ruke amanar ƴar su, sun kuma yi mamakin ganin Angel, Ƴar yarinyar da suka sani tun tana da shekara sha ɗaya sai gata sun ganta ta girma ta zama budurwa, itama Unaisah tayi farin cikin ganin su, musamman Hasiya Yar uwar Danejo.
Benazir ta yi masu godiya sosai akan taimakon da Sukayi ma Yar ta Unaisah, gaba daya sunji dadin karramawar da sukayi masu, sati Ɗaya sukayi A rugar, Lokacin da zasu dawo Taj Ya roƙi alfarmar da su biyo su su dawo birni cikin mutane da zama, har ya yi masu alƙawarin zai taimaka masu da muhallin da zasu zauna, da farko sun nuna ƙin amincewar su saboda sun saba da rayuwar daji tun kaka da kakanni, amma da Danejo ta lallashe su ta kuma basu labarin rayuwar birni da kuma ababen more rayuwa sai suka amince da zasu biyo su, dama kuma suna cikin matsin talauci tun bayan da su ka rasa shanayensu da 6arayi su ka sace.
Taj da Benazir sunji dadin amincewar su saboda suna son su saka masu da halaccin da su ka yi wa Unaisah, bayan da suka baro rigar, kaitsaye suka nufi Jihar Joss, already Ya gyara gidansa na Joss da niyar duk in zasu kawo ziyara sai su sauka anan, Gaba daya Ya mallaka ma Dangin Danejo gidan, da ya ke basu da yawa ya ishe su har ya yi masu yawa, Unaisah ta basu kyautar Kaso mafi tsoka a cikin kudin da kotu ta raba masu na Elders, yayin da Benazir ta ƙara masu da kyautar Kuɗin da zasuja jarin sana'a, ga kuma kudin da Owais ya bada abasu kimanin miliyan goma.
suka dinga yin kukan farin ciki suna yi masu godiya, kafin tafiyar Taj da iyalinsa sai da suka rakasu kasuwa suka yi siyayyar dabbobin da zasu kiwata, a bayan gidan suka hada garken Dabbobin su, inda zasu cigaba da kiwon su, ga kuma sana'ar siyar da fura da nono da za su farayi, Taj ne Ya haɗa su da abokinsa Muhsin bayan daya nemi taimakonsa Akan ya dinga taimaka masu har su samu wayewa tun da shi anan joss ya ke da zama tare da family dinsa, Muhsin yaji dadin alfarmar da Taj ya nema agurinsa saboda shima yana Neman hanyar da zai saka mashi alkhairin da yayi masa.
bayan Taj da iyalinsa sun koma Abuja, Muhsin da danginsa ne suka cigaba da kula da dangin Danejo, suna taimaka masu ta fannin wayar masu da kai game da rayuwar birni da kuma mu'amala da jama'a, sun kuma taimaka masu gurin neman ilmin addini dana zamani.
FLASH BACK💗💔
bari mu koma baya muji shin wanene Mahaifin Prisoner Chinonso wanda muka fi sani da Majnoon, Unaisah ce ta gano wanda ya sadaukar da shi saboda ta ƙwallafa rai akan son sanin wani mugunne ya sadaukar da ƙaramin yaro mai ta6in hankali har yayi silar mutuwar shi? saboda bata manta da shi ba, yana aranta, har Yau har gobe bata daina yi masu addu'a ba shi da Unaizah, da sauran yan uwansu prisoners wadanda suka rigamu gidan gaskiya, tun kafin ayi shari'ar Elders, ta ta6a jin labarin kundin rijistar fursinoni a gurin Owais shi ne ya fada mata yadda suka samu kundin ya kuma fayyace mata abun daya ƙunsa, ko da taji haka nan ta roƙe shi daya taimaka Ya dubo mata wanene ya sadaukar da Majnoon dinsu a cikin littafin rijistar fursinoni, bai tambayeta dalili ba, bayan daya kawo mata littafin, a gaban ta Ya buɗe shafin prisoners din da aka sadaukar Na sashen su a kurkukun, suna tsaka da dubawa nan take suka gano sunan Chinonso, da wanda Ya sadaukar dashi, bakowa bane face aminin baba Obie, Jan kunne, Chinonso yana daya daga cikin ya'yan sa daya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, gaba daya ma ya'yan da yake sadaukarwa bata hanyar aure yake samun su ba, Majority dinsu tsohuwa zafreen ce ta ke haifa mashi su, a tare suke sadaukar da jinin su gidan kurkukun, Unaisah batayi mamakin jin sunan wadanda suka sadaukar da shi ba saboda tasan Tsohuwa Zafreen takuma san kafurar zuciyarta, daga bisani tayima Chief Owais godiya daya taimaka mata gurin gano abun da ta ke nema 💔
__________💖TURAI_____,
Shin wacece Harriet (khadija) Mahifiyar Dr Jazz ? Menene asalin su? Me kuma yasa ta baro ƙasarta England da danta tazo Nigeria? Tayaya kuma akai ta samu aikatau a obie estate?
Harriet Baturiya ce ta usili, Yar asalin London ce babban birnin kasar England , ta taso a hannun Mariƙinta, kawunta kanin mahaifin ta, wanda tun bayan rasuwar iyayenta ya ɗauke ta ya dawo da ita gidan shi, Yana da mata daya tare da ɗansa Abraham wanda ya haifa tare da mariganya matar shi ta farko, kawunta ne ya rike ta tun daga ƙuriciya har ta girma ta zama budurwa, bayan data mallaki hankalinta, ta kammala karatunta, ya haɗa ta aure da ɗan su, wanda sun daɗe suna son Juna tun da kuruciya, bayan data samu cikin shi wata tara cuf ta haifi danta mai suna Eric wanda muka fi sani da Jazz, daddynsa Yana mutuwar son shi kamar ranshi, arayuwar Turai bata da matsalar daya wuce Matar Uncle dinta wato step mother din mijin ta Beatrice, Beatrice bata da mutunci ko kaɗan, ta ɗaura mata karan tsana tun lokacin da Mijinta Ya kawota gidan, bata son ta, bata kula da ita, kullum cikin ƙyarar ta ta ke yi, idan ya kasance su biyu ne a gida har wankin bango take sanyata, ta dinga yi mata barazana akan zata kashe ta.
haka lokacin da Uncle dinta ya hadata aure da dan uwanta, Beatrice ta nuna ƙin amincewarta, saboda bata son idan Abraham Ya mutu ta gaji dukiyar shi, shiyasa tun farko taso ta hada shi aure da diyar kanwarta, amma ya bijire akan baison ta turai yake so, bada son ranta ba Abraham Ya auri harriet sai don saboda Ubansa Ya matsa akan saiya hada Yar dan uwansa da dansa aure saboda baya son bare Ya aureta, kuma ya fahimci son juna su ke yi, bayan auransu Ta ƙara tsanar turai babban bakin cikinta, Arziƙin Abraham da yake yana da dukiyar daya gada agurin mommynsa, tasan muddin Ya mutu turai ce zata gaje shi tare da danta, ita kuma batason hakan ya faru, gani take kamar ma Turai badan Allah ta aure shi ba, sai don saboda dukiyar shi, gaba daya ta hana rayuwarta sukuni, gashi ta kasa faɗama kowa game da ƙuntatawar da ta ke yi mata da ya ke a gida daya suke rayuwa kowa da part din sa, ta hana ta sukuni agidan Mijinta, karshe ma ta fara shiga tsakaninta da mijinta, ta dinga kulla mata makirci duk don ta rabasu amma Allah bai nufa ba, saboda daddyn Jazz yana yi mata son da baya ganin laifinta akan komai, a wata rana Allah yayiwa Uncle dinta rasuwa sunji mutuwarshi, musamman ita daya zama gatanta, hankalinta Ya tashi saboda tasan Beatrice ba zata raga mata ba tun da mai goya mata baya baya araye yanzu zata samu damar rabata da mijinta, ko ta kashe ta kamar yadda ta saba fadin itace zatayi ajalin ta.
Kamar kuwa ta sani, bayan rasuwar Uncle dinta, ta canza salon cuzguna mata, har maza take dauka haya ta biya su kuɗi don su farmaketa saboda kawai ta shiga tsakaninta da mijin ta, amma Allah bai nufa ba, kullum batayin nasara akanta, kuma takasa tankwara zuciyar Abraham akan ya rabu da turai saboda a lokacin ya kara sonta fiye da da saboda kafin mutuwar daddynsa lokacin dayake jinya agadon asibiti saida ya roke shi akan ya kula da rayuwar yar uwarsa, ya bar mashi amana, Yasan step mom din sa bata sonta, zata iyayin komai donta rabashi da ita, don haka ya kula da rayuwarta, duk runtsi duk wuya karya rabu da ita, wannan wasiyar da babansa yabar masa ce tasa baya sauraron maganar Beatrice, akan Turai sun sha samun sa6ani da ita, saboda ya bijire mata akan Umarninta.
a lokacin da Jazz yakai shekaru Biyar, daddynsa ya rasa ranshi a wata tafiya da ya yi tare da abokan kasuwancin shi, daga London zuwa turkey, Jirgin su yayi Crashing, yana ɗaya daga cikin wadanda suka rasa ran su.
Turai tayi bakin cikin mutuwar shi har saida ta yi rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da ta samu lafiya, ta fara tunanin menene mafita? Saboda tasan a yanzu bata da gata daya wuce Allah, Wadanda suke kare ta daga sharrin Beatrice sun mutu, ta kuma san bazata kyale ta ba,
tunda yanzu ta samu damar da zata iya salwantar da ita, aikuwa awata rana kwatsam tajiyo firar da su ke yi tare da aminiyarta adaki akan yadda zasu kasheta su gaje dukiyar Abraham, har tana fadin ita babban bakin cikinta, gaba daya sunan Turai ne akan kadarorin sa, ga lauyansa dake kokarin tsaya ma turai da danta don su kar6i hakkinsu, sai kawar tace"abun daya kamata suyi kafin araba gadon dukiyar tashi, su bi ta bayan fage su kashe Turai, sai su bar danta su ruke shi a hannun su ta yadda ba za'a zarge su ba"
Koda jin wannan firar tasu hankalin turai ya tashi matuƙa, tayi mamakin jin furucin matar Uncle din ta, ta rasa gane meyasa ta tsaneta har haka? Bata san cewa ita bata damu da dukiyar shi ba, burinta ta zauna lafiya da ita, amma da taga da gaske kasheta zasuyi sai tayi dabarar kiran lauyan mijinta ta fada mashi abun dake faruwa, ya nuna damuwarsa yace in ba damuwa su dawo gidansa da zama zai basu tsaro, sannan zai kai ƙarar Beatrice akan furucin kisa da ta furta mata, turai ta nuna kin amincewarta akan shawarar shi, tace ita kawai bata jin zata iya cigaba da zama a kasar, ta rasa gatanta, ta tsani zaman london tafi son tayi nesa da su ta tafi can wata kasa inda zata raini danta, kawai ya taimaka mata su siyar da kadarorin mijinta da komai nashi batare da sanin Beatrice ba, Lauyan baiso shawarar data yanke ba, amma da dayaji irin barazanar da Beatrice keyi mata sai ya go yi bayan ta bar ƙasar, kuma hada karin kalaman data furta na cewa ta tsani zaman kasar kuma shi mai biyayyane ga umarninta saboda amanar dake a tsakaninsa da Abraham.
ta bayan fage suka siyar da kadarorin Mijinta, dama Black card dinsa Yana a hannunta, tun bayan rasuwarshi ta ke boyen shi, Beatrice tasha tayi mata barazana akan ta bata komai nashi, a lokacin harta ƙwace mata key din motar, nema take ta kore ta daga gidan, amma saboda gadon Abraham data ƙwallafa rai akai Yasa ta dakata tana jiran ta kwace komai kafin ta koreta.
Batare da sanin Beatrice ba, Lauyan ya taimaka mata suka siyar da kadarorin Abraham gaba daya kudin ya zuba mata a account din sirri daya bude mata, shine ya bata shawarar ta dawo abuja ta zauna ta bar nahiyar su, saboda shi dan asalin nigeria ne mazaunin abuja anan family dinsa suke, karatune yakai shi england harya zama lauya acan.
A takaice da taimakonsa Turai ta gudu daga england tare da danta jazz suka zo Nigeria, agidan daya kama masu haya suka zauna, komai da ta ke bukata da kudin gadon su ta ke yi masu, Lauyan nan shike kula da su, duk da ba anan yake da zamaba amma baya gajiya da kiranta awaya don yaji ya lafiyar su..
Turai bata yi aikatau saboda rashin kudi ba, ra'ayin kanta ne, aranar da data tsinci Domestic Staff Application daga Obie estate a social media yana yawo
hakanan taji tana son ta jaraba neman aiki, ko ta samu family din da zata jingina da su, musamman da taji labarin Family din Obie, nan take ta cike form din da bayanan ta, cikin Ikon Allah bayan kwana uku sai ga sakon Interview invitation ya shigo ta email din ta.
taji dadin da ba zai misaltuba, ko da ta tashi zuwa yin interview din sai ta sanya sutura mara tsada, ta tafi tare da Jazz, a lokacin ba hajjaty bace head maid ba, bata ma kaiga zuwa Nigeria ba a lokacin, bayan da taje head maid din lokacin ta yi masu interview ta tantance waɗanda suka kware gurin aikatau, Turai tana daya daga cikin su, taji dadi sosai musamman da suka ware mata dakin ta, gaba daya ta dawo da zama tare da Jazz dinta ta baro gidan da ta ke haya.
a lokacin tana jin dadin zaman gidan saboda baba Obie yana mutunta ta, yana kuma son danta jazz, Kowa ya tambayeta ina daddynsa sai tace masu bazata iya tunawa da rayuwarta ta baya ba, ta dinga nuna kamar tayi loosing memory saboda kawai batason kwata kwata labarin inda take ya komama Beatrice, tasan ba kyaleta zatayi ba, ta dade tana boye ma kowa identity dinta, ga dukiya tana da ita amma bata nunawa, ko jazz baisan tana da arziƙi ba, sai bayan Shari'ar Elders Ta damka mashi gadon shi, bayan ta labarta mashi komai game da danginta da irin rayuwar da tayi agidan Uncle dinta, ta kuma bashi hakuri na kin fada mashi da batayi ba da kuma dalilinta nayin hakan.
Turai ta musulunta ne saboda kyautatawar da musulmai yan uwanta masu aiki sukeyi mata, tana jin daɗin yadda suke yin mu'amalarsu wannan ne yaja hankalinta har ta musulunta, ta sauya sunan ta daga Harriet zuwa Khadija, shi kuma Jazz daga Eric zuwa Abubakar, sunan Jazz nickname ne da baba Obie ya ke kiran shi da shi saboda yadda ya ke son Music.
Tsanar da hajiya saratu tayi mata ta samo asaline saboda auran ta da sir mubarak yayi bayan rasuwar matar shi ta farko, a lokacin Saratu ta tsani talaka bare mara asali, kuma tana zargin danta shege ne shiyasa batason asan labarin ta, wannan yasa ta ɗaura mata karan tsana a lokacin, taso ta shiga tsakaninta da sir mubarak lokacin da taji suna soyayya amma Allah bai nufa zataci galaba ba har saida Ya aureta Ya dauke ta daga gidan baban tare da danta ya mayar da su gidan shi karkashin kulawar shi 💔
*(Wannan shine taƙaitaccen labarin Turai da Jazz)*
*BAYAN WASU SHEKARU DA RASUWAR ELDERS🔥*
Katafariyar Jami'a ce da ke a cikin birnin Abuja, tana ɗaya daga cikin makarantun da suka shahara a faɗin ƙasar, kuma tana daya daga cikin makarantun da suka wadatu da ababen more rayuwa.
Shin meke faruwa ne a cikin wannan Hamshakiyar makarantar, naga interior designers daga kamfanin Zahra World Of beauty sun dage damtse sunata ƙawata katafaren event hall din makarantar, da wajen Pool da kayan ado masu matuƙar ɗaukar ido da jan Hankali..
Ashe Yau babbar rana ce mai muhimmanci ga malaman makarantar, kasantuwar yau ce rana ta farko da za su fara yaye ɗaliban jami'ar da suka kammala karatu.
Gaba ɗaya Glass windows din Makarantar, da saman gate din makarantar wani hadadden rubutune ke displaying ɗauke da sunan Jami'ar.
Da abaka labari ƙwara ka gani da idonka, don haka ni ma bazan bari abarni abaya ba, dani za'ayi shagalin yaye daliban nan, saboda in bawa idanuna abinci...
Around Ƙarfe 12 na safe daidai agogon Nigeria ta buga, a wannan lokacinne School buses suka fara shigowa ta main gate din makarantar, ɗauke da Students a cikin su, daga jikin buses din hada Tambarin makarantar da suke mai ɗauke da sunan Imam Educational Institute (IEI)
Kaitsaye buses din suka nufi Parking space na jami'ar.
Na ƙura idanuna ina jira inga su wanene ɗaliban dake a cikin Buses din.
Lokacin da Bus divers din suka yi parking, kofofin motocin suka soma buɗewa
Tabarakallahu
Gaba ɗaya na ruɗe ganin Ex-prisoners na kurkukun ƙaddara suna fitowa daga cikin buses, sanye cikin uniform din su kyawawan gaske sun sauya daga ka gansu kaga ya'yan hutu wadanda suka gaji arziƙi.
Yan Secondry School ɗin suna a sanye da kyawawan Uniform ɗin su, ƴan matan sun yi rolling head scarf, ya yin da mazan kowan nan su ka kalli kanshi haɗaɗɗen haircut ne na wayayyu.
Admins din makarantar ne su ka yi inviting ɗaliban Makarantar Imam da iyayensu donsu taya yan uwan su murnar kammala karatu, dress code din da suka basu shine uniform din su shiyasa kowannan su ya sanya uniform din shi banda Yan jami'a su nasu kayan gidane as usual suna asanye da Casual dress na kece raini.
Rayuwa kenan, waya taba tunanin bayin Allahn nan zasu samu yan'ci da canjin rayuwa? Shiyasa kada ka taba fidda rai da rahamar ubangiji, babu wani yanayi na dundundun a duniyar nan, in ma bakaji dadi anan ba in kayi kyawawan ayyuka zakaji daɗi aranar gobe ƙiyama, fada ce ta Allah buwayi, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma Allah yana tare da masu hakuri, ga misali nan mun gani arayuwar fursinonin kurkukun ƙaddara, rayuwarsu su ke yi cikin jin dadi da walwala babu takura, babu tashin hankali, babu fargaba, ba wahala sai zallar gatanci da jin dadin rayuwa.
ko wanda ya taso cikin gatantawar iyayensa bai kai su jin dadi ba ayanzu saboda kulawar da suke samu, babu abunda suka nema suka rasa sabanin da, da kullum cikin uniform daya suke, kulle adaki daya, cikin kurkukun karkashin ƙasa, abinci sau daya arana, ba shige ba fuce, rayuwar ƙunci da takaici, rayuwa mai cike da fargaba, rayuwa mara yan'ci amma yanzu komai ya zama labari 🤩
Fuskokin su ɗauke da murmushi cikin raha suke fira a tsakanin su Yayin da su ke tafiya atsanake suka nufi event hall din da za'a gudanar da taron.
Katafaren event hall din Ya Cika makil da mutane babu masaka tsinke, ya kawatu da colorful balloons and streamers, ga wata katuwar banner mai ɗauke da rubutun
*Congratulations Graduates!*
Daga gaban Hall din dogon table ne mai ɗauke da Katon Cake tare da refreshments, and a microphone for the speeches, gaba ɗaya admins din makarantar suna a zaune kan kujerun gaban table ɗin.
da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilmin kasar duk sun hallara, kowan nan su ya kure kur'adakansa shiga ta mutunci ta alfarma.
gaba ɗaya manyan bakin da aka gayyata tare da iyayen yaran suna a zaune kan kujeru na alfarma da aka kawata musamman saboda su.
Daga tsakiyar Hall din ƙawatattun kujeru ne aka jera wanda asaman su Students suka zauna.
Daga gefe ɗaya na Hall din wasu hadaddun Chairs din ne musamman saboda Graduates din aka tanade su.
Graduates din suna asanye da graduation gown da suka ɗaura asaman outfit dinsu, launin navy blue with golden trim, sun sanya
Mortarboards On their head.
Yan Jarida da photographers sun hallara domin gudanar da aikin su.
Iskar Hall din ta gauraya da fragrance din mutanan dake a cikin shi.
Hayani ce ta cika ko'ina sai fira ake cikin raha da annushuwa...
Wasu gungun students na hango sun ke6e gefe daya suna tattaunawa atsakanin su ƙasa ƙasa kamar basu son aji me suke cewa.
"Unaisah bata picking call, bansan meyasa ba, tun kafin inzo hall din nan nake ta kiranta..." Sajeed ne ya faɗa yana duba agogon hannunsa, shima yana daya daga cikin graduates
Haris Yace"nima inata kiranta bata ɗagawa, Na kira Batool itama batayi picking ba, ban san me ya tsayar da su ba"! ya fada fuskarsa a yamutse.
"May be basu kammala shiryawa bane..." sajeeda ce ta faɗa matashiya mai jini ajika, itama Graduate ce.
Zeenatu da ke a tare da su bata tanka ba, Saboda hankalin ta baya atare da su, yana akan wayar ta da take dannawa ga dukkan alamu da saurayin ta take chatting duba da yadda take sakin Murmushi, tayi kyau a cikin graduation gown din ta.
"Hmm Ko kuma suna can suna bacci ba" acewar Javed..
Sajeed yace "Bana so afara basu gama hallara ba, musamman Unaisah nasan dole a neme ta idan za'a bada award"
Kafin wani daga cikin su ya kuma yin magana, Sautin taken makarantar da aka kunna Ya katse hanzarin su, Kowa ya nutsu yana sauraron University Anthem din su..
Bayan da taken Ya ƙare, Kowa Ya koma gurin zamansa, School Dean ya soma yin magana babban mutunne yana magana gently hankalin kowa ya koma kansa.
"Distinguished guests, esteemed faculty, proud parents, and most importantly, our graduating students, welcome to the graduation ceremony of the Freedom's Gate University"!
"Today marks a significant milestone in the lives of our graduates, It is a day to celebrate their hard work, dedication, and perseverance I am honored to lead this institution, and I am proud of each and every one of our graduates.."
Gaba ɗaya jama'ar dake a hall din suka soma yin clapping!
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya karasa Speech dinsa mai ma'ana..
Vice Dean of Academic Affairs ta ɗaura da cewa
"Today is a big day for us, a day we will never forget, a day of remembrance. It marks the first day our first student graduated from this university. Coincidentally, today is also the anniversary of the day we opened this school."
"Over the years, our school has gained fame and received awards from around the world, thanks to our talented students who have become symbols of our glory."
ɗan dakatawa ta yi da yin bayanin idanunta akan mutanen dake sauraranta suna ta tafa hannayen su.
Numfasawa tayi cikin nutsuwa ta ɗaura da cewa"Before I finish my speech, Ina farin cikin gabatar da wadannan lambobin yabon ga haziƙan daliban da suka kammala karatun su, haƙiƙa sun cancanci ayaba masu saboda ƙwazon su da jajircewar su dan ganin sun cimma wannan matakin"!
da jin wannan maganar ta vice Dean nan fa hankalinsu su Sajeed Ya tashi jin shiru sauran ba su ƙaraso ba.
"ko bamu faɗa ba, kun san su wanene waɗannan fitattun da zamu kira sunayen su.."
Tunkan Ta karashe maganar students suka din ga ambaton sunan Unaisah da twins da Zeenatu saboda kowa yasan su da kaifin basira.
"ina fata suna a kusa kuma suna sauraron mu.."
Ta faɗa tana bin graduates din da kallo kafin ta soma kiran sunan ukun farko kamar haka Sajeed Ubaid wadata, da Sajeeda Ubaid wadata, da kuma Zeenatu Ubaid wadata.
miƙewa su ka yi daga kan kujerarsu, gaba daya idanu suka dawo kan su, suka ruke hannayensu cikin na juna, walking gently suka nufi kan stage fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki..
Department Chair of cybersecurity ce ta damƙa ma Sajeed kyautarsa wani hadadden wrapped box ne mai faɗi tare da certificates na shaidar kammala degree dinsa na farko.
hannayensa na kerma cike da zumuɗi ya kar6a cikin girmamawa yayi godiya.
Director Of the Human Rights Program Ya bawa Sajeeda da Zeeenatu awards da gifts din su, cike da tsantsar farin ciki kowan nansu ya sanya hannu cikin girmamawa suka kar6a.
cikin harshen turanci su ka yi godiya tare da nuna irin farin cikin da su kayi, su ka kuma ba sauran yan uwansu dalibai shawarwari akan su dage da karatu su maida hankali ta yadda zasu zama wasu agobe.
Jama'ar da ke a hall din sai tafa masu su ke yi, musamman yan uwansu ɗalibai tsabar zumuɗin su tayasu murna, suna ta daga masu hannu tare da ƙwala masu kira..
Komai da ke faruwa akan idanun Hajiya sarah da su Alhaji ubaid da sauran Yan uwan su da su ka hallara, sam sun kasa rufe bakunan su saboda farin ciki kamar waɗanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.
suna saukowa daga kan Stage cike da zumuɗi su Haris suka nufe su da fara su ka soma rungume su suna taya su murna, daga bisani suka nufi gurin iyayen su da ke tunkaro su, rungume su su ka yi sunata taya su murna.
Taken makarantar da aka kunna ne yasa Kowa yayi shiru tare da komawa mazaunin su..
Bayan da taken Ya dauke, Dean of the School ya soma magana
"And now, it is my pleasure to present the 'Excellence in Computer Practice' award to an outstanding graduate from the Computer Science (CS) Department."
gaba ɗaya hankalin masu sauraro ya koma kan shi cike da zakuwa suke jira suji karashen zancen shi.
"The recipient of this award is *UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN"!*
gaba ɗaya students suka soma tafi suna shewa saboda farin cikin jin Unaisah ce kamar yadda suka zata.
"I WILL REPEAT, UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN, PLEASE COME FORWARD AND RECEIVE YOUR GIFT"
shiru Babu alamun mai sunan zata amsa.
Yan uwanta ɗalibai sai neman ta su ke yi a cikin hall din, kowa ya baza idanu yana jira yaga ta ina zata 6ullo sun san mawuyacin abune ta yi fashin zuwa school.
Rashin baiyanarta ya haifar masu da rashin jin daɗi, daga malaman nasu har daliban da bakin da suka hallara gaba daya sun ƙagu da su ganta kamar kamar me.
"UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN! TANA INA NE? KO BATA ZO BA NE"?
Duk wani mai numbar wayarta saida ya jaraba kiranta amma kwata kwata bata picking daga ita har iyayenta ba wanda ba'a tuntuba ba.
Gunagunin da mutane suke yi ne ya cika hall din.
"Meya hanata zuwa"!
"Bata da lafiya ne"?
"In bata da lafiya meyasa ba'a faɗa mana ba"?
Kowa da abun da ya ke faɗa.
"Sir, Unaisah bata zo ba, bamu san dalili ba, saboda bata kira ta fada mana ba, kuma mun jaraba kiran layinta bata ɗagawa",
Sajeed ne ya daga murya yana magana, Hankulan Kowa ya dawo kan shi.
"amma idan ka bani izni zanje gida na dubo ta..."
Vice Dean tace "mun baka izni sajeed ka yi sauri..." (sunyi mashi alfarma ne saboda muhimmanci Unaisah a gare su)
amsa wa yayi da toh bayan daya mikawa Haris gifts dinsa ya ruke masa, ya juya cikin sauri Ya nufi kofar fita daga Hall din.
Bai kaiga ƙarasawa ba, Unexpected ta shigo ta kofar hall din da gudunta gaba ɗa ya hankali ya dawo kanta..
Wow Tabarakallahu Ahsanul khalikin! Kamar ranar suka fara ganin ta, kowa ya ƙura idanun sa akanta.
Tana gudu graduation gown dinta na tashi sama saboda iskar da ta yayo, hakan ya bayyana Outfit din ciki data sanya, fitted gown ce baƙa, tayi tighting din jikinta ba Dan laifi, kamar a jikinta aka dinkata, daga wuyan rigan ta matse ma sha Allah in ka ganta bazaka taba cewa ƙwailar nan bace ta kurkuku komai ya fito raɗau, gudun da ta ke yi ne yasa jikinta ya dinga girgiza, musamman wide curvy hips dinta sun cika 6ul6ul da su.
Fatarta tayi haske sosai sai sheƙi ta ke yi tana walwali daga gani taji gyara da tsadaddun mayukan gyaran fata, ga wani shu'umin ƙamshin turaren dake fita daga sako da lungu na jikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin kogon turare.
Hutu da kwanciyar hankali sun zauna mata, saboda saurin da takeyi ne yasa ta manta bata saka Mortarboard dinta ba, hakan ya bayyana kyakkyawar sumar kanta da ta sha gyara, tayi dark brown sai Shining ta ke yi
kamar ba Unaisar da muka sani ba siririya yanzu ta zama cikakkiyar budurwa mai jini a jika.
Kowa Kallonta ya ke yi, manyan baki sun saki baki da hanci, sunata kallonta, surar jikinta tayi matukar jan hankalin su, kamar su kai mata hari sai faman hadiyar yawu su ke yi kamar wasu mayu..
Sautin highheels din kafarta Ya cika kunnuwansu kwas! kwas! kwas!! Saboda hall din yayi tsit ko tari ba kaji kowa ya nabba'a yana kallon Unaisah yayin da take tunkarar Stage still da ɗan gudun ta.
"Sis, Kin manta da hularki! ..."
Muryar Batool ce ta katse mata hanzarin ta, a rude taci burki, sumar kanta tayarfo ta gaban forehead dinta, sai haki takeyi tana zazzare gray eyes dinta dara dara..
Kunya ta hana ta dubi mutanan da ke kallonta, duk ta kame kanta kamar marar gaskiya..
Ƙarasa shigowa ciki Batool tayi jikinta sanye da black abaya, ta saka niqab akan fuskarta, cikin sauri ta nufi Unaisah ta daura mata mortarboard din asaman kanta.
"Thank you sis.." ta faɗa a wahalce kafin ta dubi admins din su adabarbarce tace..
"Ina bada haƙurin makara da nayi.." murmushi kowan nan su yayi su kansu suna alfahari da ita komai nata na burgewa ne.
Dean yace"kinyi laifi Unaisah, bakizo da wuri ba, kin bar mu munata kwala kiran sunanki, makoshinmu duk ya bushe, don haka dole mu hukunta ki"
arude tace"am sorry sir na gane kuskure na bazan ƙara ba ." ta faɗa tana kama kunnanta..
Photographers din dake a gurin har sun fara daukarta hotuna da videos, sautin cameras din su ya cika hall din ƙyat! ƙyat!! hasken camera duk ya kashe mata idanun ta, tunkan abasu iznin su ɗauka, ga dukkan alamu ta tafi da imanin su..
Da hannu vice dean ta nuna mata inda zata tsaya murya na rawa ta furta"thank you ma'am"
ta hau kan stage din daga gaban mic ta tsaya, all eyes on her.
Dean da kanshi Ya mika mata ƙyautarta tare da certificate din ta, cikin girmamawa tayi masa godiya.
Students sunata kiran sunanta, waving ta dinga yi masu tana yin tsadadden murmushin nan nata.
Calmly ta soma yin speech cikin nutsastsiyar muryarta
"Alhamdulillah, thanks be to Allah for showing me this day I've been waiting for I'm incredibly happy I'd like to thank those who supported me, including my parents, my mentor, and my teachers, thank you very much, May God reward you with the best of his blessings"
kowa dake a gurin ya nutsu yana sauraran speech dinta, yanayin yadda take magana cikin harshen turanci ba karamin tafiya tayi da su ba, muryarta kamar ana busa sarewa don dadinta, wasu har lumshe idanunsu su ke yi saboda yadda take ratsa kunnuwansu, gashi tana magana dimples dinta na lotsawa, in ta yi murmushi ko ta yi dariya ba ƙaramin Jan hankalin su ta ke yi ba.
Bayan data kammala jawabin ta.
Commissioner of Education ta nemi ganawa da iyayen ta saboda ta jinjina masu bisa ga kokarinsu na tarbiyantar da yar su.
"Iyayena basu halarta ba.." ta fada tare da sunnar da kanta kasa, kowa ya shiga damuwa da jin abun da ta faɗa, azaton su wani abunne ya faru daya hana su zuwa.
"Meyasa? Ko wani uzirin ne Ya ruƙe su? Amma ya kamata ace sun zo ta ya ki murna" vice ce ta fada.
"hidima ce ta hanasu zuwa.."
bata ƙare maganar ba, Batool ta yi su6ul da baka gurin furta
"hidimar auranta... "
dafe kai tayi da tafin hannunta, tana aikawa Batool harara a fakaice, wato ta kwafsa mata, gaba daya hall din suka sanya shewa da tafi kamar zasu fasa bangon hall din..
Muryoyin students suka cuka kunnuwanta.
"Unaisah wanene zaki aura? Wani me nasaran ne zai mallake ki"?
"Yaushe ne bikin naki?
Gaba daya sun cika ta da tambayoyi kamar yan jarida ta rasa wa zata fara amsamawa.
"Listen pls.." Dean ne ya faɗa nan take kowa yayi shiru.
Dubanta yayi"Unaisah meyasa baki fada mana kin kusa yin aure ba uhym? Wani mai sa'ar ne zaure ki? Meyasa mu ba'a gayyace mu ba"? ya fada da fara'arsa.
ga dukkan alamu kamar sun manta abunda su ke yi, jin maganar auren ta yasa hankali ya koma kanta.
Kunyace ta kamata, ta sanya tafukan hannayenta ta rufe fuskarta, hakan ba karamin dariya ya basu ba, cike da nishadi kowa ke kallonta kamar sun samu tashar bollywood..
"Ke muke sauraro Unaisah.."
zolayarta suka dinga yi..
Dakyar ta samu kwarin gwiwar furta sunan shi.
"Dg Owais... " cike da mamaki kowa ya zare idanu yana kallon ta, suka kama tafa mata..
Manyan Baƙin dake a gurin suka shiga jinjina kan su aransu suka ayyana shine daidai da ita, don mallakar hamshakiyar mace irinta sai babban goro magogin karfe 👑
"I invite you all to my wedding next week, after Friday prayer, at the Sheikh Imam Malik mosque here in Abuja"
("Ina gayyatar ku baki daya daurin aurena a mako mai zuwa, bayan sallar Juma'a, a masallacin Sheikh Imam Malik da ke nan Abuja)
bata kare maganar ba ya katse ta da cewa "There's no invitation card?"
Tana noƙe kai cike da jin kunya tace "Sorry Sir, I forgot to send the invitation to our school WhatsApp group"
Vice dean tace "Okay idan kin koma gida, kada ki manta ki tura mana, don ba zamu bari ayi babu mu ba, duk da bikin na manya ne amma tun da ɗalibar mu za'a aurar toh damu za'ay komai sai munga abun daya turewa buzu nadi"
cikin zolaya ta ƙarashe maganar, dariya suka sanya gaba ɗayan su.
daga bisani aka kikkira sauran graduates din da suka tantanci ya bo aka karramasu
Daga bisani photographers suka cigaba da ɗaukarsu hotuna, sunyi da malaman su, sunyi da bakinsu, sun ku ma yi da yan uwansu dalibai, kowa burinshi ya yi hoto da Unaisah musamman special guests din nan ta tsone masu ido, saukin ta ɗaya sunji wa zata aura, da ba abun da zai hana su addabeta, ita Batool da yake ta rufawa kanta asiri ta sanya abaya da niqab bata ja hankalin kowa ba, da itama sai sunyi rubibinta saboda kyawun surarta.
~________________________________🌹~
Students ne tsaitsaye agaban katafaren Pool din makarantar sun kewaye Graduates.
photographers sunata daukarsu hotuna.
Graduates Suna ta wurga hulunansu saman Iska cike da nishadi.
Kwatsam sukaga Unaisah ta wurgar da gifts dinta Cikin pool ta juya cikin sauri ta nufi parking space, gabansu ne ya fadi ganin abun da tayi kuma kwata kwata bata waiwayo ta dubi kowa ba..
Sajeed ne ya daka suka ya fada cikin ruwan ya dauko gifts din da ta jefar.
Batool da sauran yan uwansu suka bita da gudu suna ƙwala mata kira, Unaisah! Sis! Ukhty!
ko waiwayon su batayi ba, A kan ground floor ta jefar da graduation gown dinta da sauri Batool ta ɗauke mata ita.
Ta kuma jefar da hularta haris Ya dauke ta, gaba daya sun rude sun rasa gane meke damun ta kamar mai ta6in hankali..
"Unaisah ki tsaya pls! Ina zaki je ba'a kammala party ba! Meke damunki ne? Kina cikin hayyacinki kuwa? Baki ga abun da ki ka yi ba"?
Ko sauraron su batayi ba, kuma tana jin su.
"Pls Unaisah ki bi a hankali, kada ki fadi, takalmanki zasu iya kayar dake.."
Babu alamun zata tsaya, bodyguard din da ya kawo su yana atsaye bakin motorsa Yana jiran su, tun lokacin da ta fara zuwa School Chief Owais ya bashi aikin kula da su, don ya runka kai su school ko in zasu fita outing ita da Batool kwata kwata basu hawan Bus.
Yana hango ta yayi saurin buɗe mata cardoor ta shige ciki ta zauna ta kulle kofar, tare da kifa kanta saman laps dinta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya! daga gani akwai wata damuwa da ke cin zuciyarta.."
"Ma'am, what's wrong? Why are you crying?"
Bodyguard din ne ya tambaya yana lekenta ta saman gilashin tagar da ke a bude.
Batare data dago ta dube shi ba, cikin shesshekar kuka tace"am ok, ba abun da ke damuna, ka kaini gida kawai, banaso na kara minti daya a cikin school din nan.."
"Amma yan uwanki suna ta kiran sunanki"?
"Kada ka sauraresu, ka shiga kawai ka kai ni gida.." duk baiji dadin halin da take a ciki ba, lafiyalou ya kawo su baisan meya bata mata rai ba.
Shiga ciki yayi ya zauna a driver's seat, kafin su Batool su karaso tuni motar ta fuce daga gate din makarantar.
akan idanun su, kwata kwata basu ji daɗi ba, ko celebration din ba'a kammala ba ta tafi tabarsu da kayayyakin ta, mutane sai tambayarsu su ke yi Ina Unaisah? sai dai su ka yi karyar anyi mata kiran gaggawane shiyasa ta tafi, gaba daya suka kasa zama makarantar, saboda hankalinsu yaki kwanciya da halin da Unaisah ta shiga farat ɗaya..
A hankali Motar ta kunno kai cikin harabar katafaren Gidan daddynta dake a cikin Imam Estate.
Drivern nayin Parking, ta buɗe motar, cikin sauri ta nufi main falo, tana dira kafarta ciki, kunnuwanta su ka jiyo mata muryoyin su.
"Ni wallahi tun farko banso aka sanya bikin nan sati uku ba, yayi kusa, yanzu gashi abubuwa suna nema su haɗe min"
"Dan Allah ki daina damuwa, meye a ciki toh? mu fa namu gyara amarya ne kawai, Owais ya riga daya yi mata komai"
"Hmmm ba zaku gane ba"
"Da yaushe ne za'a kawo Invitation bags din"?
"Yau ne fa, ɗazu nayi waya da daddynta ya faɗa mun sunyi magana da Owais, wai daga Companyn su zahra za'a kawo kayan"
"Allah ya kawo su lafiya"
"Bari na sake kiran Aneelerh naji Ya jikin nata! Nasan ma ba lallai yau ta samu damar zuwa ba kinsan me laulayin ciki" da zolaya ta yi maganar..
A hankali ta dan saci kallon su da idanunta wadanda suka kaɗa jawur..
Su uku ne zaune kan Sofas, Mommynta da Ummi tare da Aunty Danejo, basu daɗe da dawowa daga kasuwa yin siyayyar kayan abincin biki, a falo suka baje kan rug suna huce gajiyar su.
A hankali ta ɗan zukunna tare da zame takalmanta daga kafafunta, ta ruƙe su a hannayenta don kada suji sautin tafiyarta, Cikin sanɗa ta dinga tafiya har ta samu ta haye upstairs ta nufi bedroom dinta ta shige, jefar da takalman tayi kan floor, Idanunta cike tab da kwalla ta nufi gaban gadonta, ta zukunna tare da janyo drewer chest din jikin gadon, bakomai ne a ciki ba face kyaututtukan da ya ke bata, anan take ajiye su, ramadan boxes, Eid gift boxes, Hajj gifts, umra gifts.
Cikin shekarun nan ya bata gifts sun kai guda ɗari Uku.
Runtse idanunta tayi gam, hawaye suka dinga sintiri kan kuncin ta, ta rasa ya zatayi da zuciyarta? Meyasa bazata daina azabtar da ita akan son abun da bazata taba samu ba?
_Ka hanani bacci, ka hanani sukuni, ka hana wani ya maye gurbinka a cikin zuciyata, ka mutu ban huta ba, ka zamar mun ƙarfen ƙafa, tayaya zanyi aure da jarabar son kasancewa da matacce? Ya ilahi_
Zancen zuci ne takeyi.
Ta rasa gane ya akai hannun agogo ke nema ya koma baya! Meyasa saida auranta ya rage saura kwanaki kaɗan zuciyarta ta ke matsa mata akan son matacce wanda babu shi araye?
Why why why...!!!
da ƙarfi ta furta, tare da rufe drawer din, ta kifa kanta jikin gadon, ta gaza yarda itace zatayi aure ba tare da shi ba! Farin cikinta ragagge ne, duk nasarar data samu batare da shi ba faɗuwace a gareta.
Da tunaninsa take samun kwarin gwiwar gudanar da komai, kuma da tunaninsa take jin dadi.."
duk don ta cire shi a zuciyarta yasa ta rabu da komai na shi da take da shi amma ina kamar tana kara rura wutar sonshi a zuciyarta, bata da hotunanshi amma idanunta sun gaza mantawa da suffarshi, kwakwalwarta ta haddace memories din su, wata irin kasalace ta baibaye ta, dakyar ta lalla6a ta haye kan gadonta, ta janyo pillow tayi hugging dinsa a kirjinta sosai, ta dan lumshe idanunta, eye lashes dinta sun jiƙe sharkaf da hawaye.
_Kyakkyawan murmushin shi, Kallon shi, dariyar shi, tafiyar shi, sumar kan shi, hancin shi, la66ansa, kyawun surarsa gaba daya, komai nashi takeso ta sake gani, tayi mahaukacin kewarshi, tayaya zata iya ganinsa bayan ya mutu? Wallah ji take da ace ana iya dawo da wanda ya mutu araye da ba abun da zai hana ta ki dawowa da shi._
Numfasawa tayi tana mai kara ƙanƙame pillow din data matse a kirjinta, ji take kamar shi ne ta rungume.
Farkon haduwarsu ta fara tariyowa.
At first time datayi tozali da shi duk da tashin hankalin da take a ciki saida ta razana da ganin kyawun shi.
Nutsuwa tayi tana cigaba da tariyo komai daya faru a tsakanin su tun a gidan kurkukun ƙaddara.
Rana ta farko da jikinsu ya fara haduwa dana juna, ita kadai tasan me taji but,taji wani abu mara misaltuwa duk da ba wani hankali gareta sosai a lokacin ba Amma abun yana a ranta...
_"Kai wani irin jaki ne? ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko"?_
_"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."_
Tunawa da waɗannan maganganun da suka ta6a yi ne yasa batasan sa'adda ta ƙyalƙyace da dariya ba...
"My man, inama ace kana araye, da na nuna maka baby Angel dinka ta girma, itama tayi abun nan irin na yar gidan daddy da ka ke muradin ganin ta da su.."
ta faɗa cikin karyayyar murya kafin ta ci gaba da tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su.
_the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_
"Dame zaka biya ni idan na koya maka"?
"I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want"
"does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?"
"yeah"
Murmushi tayi tunawa da wannan firar ta su.
_"My man na soka kamar raina, na so mu rayu a matsayin ma'aurata, dana nuna maka irin masifar son da nake maka, zan zama baiwarka, in dauki dukkan ɗawainiyarka, in mallaka maka kaina kamar bana sona, meyasa ka mutu ka barni? Meyasa burin mu bai cika ba? Har yau ina danasanin tursasa maka da nayi duk da nasan wayou na ko dabarana bai isa ya sauya abun da ya ke rubutacce a cikin littafin kaddarar ka.."_
ita kaɗai take ta sambatunta, in ta fara tunanin shi saita shafe awanni tanayi kamar mara aikin yi... 💔