6️⃣2️⃣
DR SADEEQ GROUP UPDATE
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
💔❤️🔥DR SADEEQ❤️🔥💔
BOOK TWO
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 15Novel love, comedy drama
"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE
MORNING UPDATE
ENJOY YOUR DAY
COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
NOVEL ELITE
CHANNEL FOR MORE NOVEL'S
👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35
Dr SADEEQ ya tsaya cak lokacin da Kaka ta buga masa sanda a gwiwa cikin wasa.
Daga alama, ita ce kawai mace a duniya da take iya buga Sadeeq ba tare da ya motsa ba.
Kaka ta zaro ido tana tsokanar sa
“Na ce maka ai fuskarta kamar kumbure ne!
Na tambaye ta tace haka Allah ya yi.
Ashe ƙarya ce yarinyar nan ta iya bahaushen karya!”ta tabe baki tana girgiza kanta.
“yaran zamani ku dai kun wuce birni.
Kai SADEEQ, maza zo nan, ko maraba bazaka yi min ba?
Ko dai sirrin ku ne kuka ɓoye min?”
Sadeeq ya yi saurin matsawa kusa da ita.
Sai ya durƙusa da girmamawa ya rungume kakar tasa sosai kamar ƙaramin yaro.
“Sorry kaka… wallahi na yi kewarki.
Ban san kina zuwa yau ba sai yanzu.
Na ga idon Indo kawai kamar ya kumbura ne… shi yasa zuciya ta ta tashi.
Ba komai… nice nayi kuskure katse miki magana.”Kaka ta buga shi da sandar sake cikin shagwaɓa.
“To ai dole ka yi kuskure! tunda kaga kyakkyawar budurwa ɗanye sharraf munafiki
tun kafin a fara azumin nakeso nazo kana shirin guduwa kamar wanda ya ga hukunci!
Gashi har ka manta da ni — shi yasa sai nayi biko da kaina.
Amma kar ka fara gayyamin jirgi-jirgi… wallahi babu wanda zai ɗauke ni sama da gajeren sanda na nan!” Dr Sadeeq yayi dariya sosai.
“Kaka ke dai baki canza ba…
Amma wallahi sai na kai ki airport kishiga jirgi. zaki zo daga Kano har Abuja da mota
Ke fa star ce.”Kaka ta yi harara.
“Na gaya maka ka daina wannan wasan banza!Ni ba zan hau taron mangwaro a sama ba, idan dai ba Madina zan kuma ba
ƙasa da ƙasa kawai!”
Indo kuwa, tun da suka fara magana, ta yi saurin ladabawa ta miƙe cikin kunya da ciwo.
gashi tacike tana jin zazzabi, amma ta danne murmushi ta fada
“Kaka, bari in je nayi sallah.”
Ta wuce a hankali kamar mai jin jiki, tana ƙoƙarin ɓoye zafin da take ji daga duka da Atika ta mata.
Dr Sadeeq ya bi bayanta da idanu — ya lura tana takawa kamar mai ɓoye ciwo, da akwai wani abu bata faɗa ba.
Kaka kuwa ta ce
“Ka bari ta tafi, anjima idan ta huta zata maka bayanin komai, na kira yarinyar tasan darajar mutane ba kamar iyayyen ka da ƴan uwan ka ba ,
Amma kai SADEEQ ka gaya min gaskiya…
wacece wannnan yarinyar?
Ko dai akwai magana tsakaninku?”
ta daga gira biyu cikin rigima da sunjin gulma...
Dr. Sadeeq ya yi murmushi irin na wanda aka cafke shi a faɗa.
Ya tattaro nutsuwarsa, ya motsa kusa da kaka ya zauna saman carpet yana kallon ta da lallashi
Kaka… don Allah ki daina gulma irin ta tsofaffin mata
ya yi shiru, sai dai idonsa ya koma hanyar da Indo ta bi muna dai jituwa ne kawai… she’s"
Kaka ta dungura masa sanda a kai.
“Wallahi idan ka ƙara cewa jituwa zan mare ka da wannan sanda!
Kai yaro, idan na tambaya, ka faɗa min gaskiya… baka hango yanda take ganinka ba?
Bakaramin wata alama na gani a idon yarinyar nan ba…”
Ta ɗan kiftar da idanu tana shaƙar iska irin ta manya“…alamar wacce ake so… da wacce ita ma tana jin wani.”
Sadeeq ya ja dogon numfashi — zuciyarsa ta yi wani irin lugude yayi murmushi cikin ladabi, yana ƙasa da murya, kamar wanda ake zana gaskiya daga ransa
Dr. Sadeeq ya ja dogon numfashi ya ce cikin murmushin da bai iya ɓoyuwa ba:
“Kaka kenan… wallahi kin fi likitoci gano cuta da ganewar baya.
Amma bari mu tashi, na kai ki part ɗinki… kafin ki sake bugun kaina da wannan sandar da mugun zafi.”
Kaka ta ɗaga kafaɗa tana dariya.
“Ni wallahi ka cancanci a bugaka! Na same ka da abun magana tun da na shigo, kai kuma ka min shiru kamar wanda aka kama da laifi.”
Ya miƙe, yana kama sandarta a hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya tallafe ta kamar ƙaramar yarinya.
“Zo mu tafi kafin ki sake cin mutuncina a gaban yarinya.”
Ta buga masa kafa.
“Wacce yarinyar? Haba ai idan kana so faɗa! Ni ma na fara jin daɗin hirar da nake gani a cikin zuciyarka.”
Ya yi saurin bude ƙofar parlour ɗin ta ɓangaren dama, suka shiga hanyar da ke kaiwa part ɗin kaka.
Wani ƙofa ce madaidaiciya, an kawata shi da kyau da girma, da kayan ado
Sadeeq ya murɗa handle ɗin ya tura ƙofar cikin natsuwa.
A gabansu ɗaki ne mai fadi sosai — babu tarkace, babu hayaniya — amma duk wanda ya shiga sai ya gane ɗakin tsohuwa ce:
Akwai kwalli da dugwui-dugwui a gefe, turaren gargajiya da saka-zuma.
Amma duk cikin tsari da tsaftar Dr. Sadeeq:
AC tana aiki, gadon kuwa lafiyayye ne kamar na asibitin VIP.
Ya miƙe hannunsa ya gyara mata matashin baya sannan ya fara tattara ƙananan abubuwan da suka tashi ba daidai b
“Kaka, wallahi kin bar min wahala. Kamar wacce ta wuce nan da gudu.”
Kaka ta zauna tana zumburawa hanci.
“Ai kaima ka san ƙafata bata jure zama waje ɗaya. Kuma ka san babu wanda ya fi ka shirya min kaya. Ni dama dama nake yi maka hira ka ce baka so?”
Ya yi dariya yana gyara ɗanyen hijab ɗinta.
“Ni ban ce ban so ba. Na ce ki rage gulma ne.”
Ta harare shi.
“Ko kai ka fara tunanin Indo lokacin da nake magana?”
Ya yi shiru — shiru mai kamar amsa.
Kaka ta yi ƙarya ta ɗaga sanda kamar zata doke shi.
“Na gaya maka! Idonka ya faɗa min komai tun kafin ka yi magana!”
Sadeeq ya duƙa yana gyara ƙafar gadon, yana murmushi cikin nauyin da zuciyarsa ta fara yi tun da Indo ta wuce da zazzabinta.
Dr. SADEEQ
“Kaka na… ki min hakuri. Ki huta. Ni zan kawo miki shayi bayan na duba Indo. Da alama bata jin daɗi sosai.”
Kaka ta gyara zama ta kwantar da kai a matashin:
“To ka tafi. Ka duba yarinyar. Idan baka zo da labari ba… ka san sakamakon sanda ta nan.”
Ya tashi yana dariya:
“Ni dai na san wannan sandar tana da aljanu, wallahi.”
Ta buga ƙafarta tana dariya.
“Aljanun ka suke ji! Tafi ka duba Indo tukunna kafin zuciyarka ta buga ka.”
Sadeeq ya juya da sauri — zuciyarsa na masa raɗa kamar ana ja da igiya ko Indo na buƙatar taimako?
Zazzabi ne sosai?
Dukkan motsinta yau sun masa nauyi a rai.
Ya fita cikin nutsuwa, zuciyarsa cike da wani abu da bai faɗi ba — amma Kaka ta gane tun tuni.
Yana fitowa daga ɗakin Kaka, zuciyarsa na masa wani irin tsalle-tsalle saboda Indo…
Ya yanko zuwa corridor, yana hanzari kamar wanda ke da gaggawar ceton rai, sai ji yayi—
“Assalamu alaikum… Sadeeq?” ya tsaya cak.
Mommy ce ta dawo a gajiyi, hannunta na riƙe da jakar aiki, idonta cike da tambaya.
Ta kalle shi sama da ƙasa cikin mamaki:
“Yau kai a part ɗinmu? A wane hali haka?
me ya faru Dr?”
Sadeeq ya ji jikinsa ya yi tsalle kamar wanda aka kama da laifi sai ya ɗan goge goshinsa, ya ɗaga kafaɗa cikin rawar murya.
Dr SADEEQ:
“Uhh… Mommy… Kaka taxo. Ina… ina kai mata abu ne naa zo dubawa ko… ehm… abincin dake dining… ko akwai…”
Mommy ta ƙure shi da ido.
“Laa… kai kuma kaushe ka fara damuwa da abincin dining?”
Kafin ta ƙara magana, ya yi saurin mikewa kamar wanda aka tura shi “Mommy zan dawo just, just checking something!”
Ya yi saurin juyawa zuwa dining kamar zai samu wata gaggawa ta gaskiya.
A can dinning ɗin yana zagayawa da ido — komai yana can a tsaf, babu abin da ya ɓace babu wanda ke buƙatar taimako.
Babu Indo.
Ya zaro numfashi sosai—
“Innalillahi… wannan wanne irin haɗuwa kuma? Haba Sadeeq…”
ya ce a hankali yana jin kunyar irin yadda Mommy ta same shi.
Sai ya juya da gaggawa ya bar parlour kafin Mommy ta sake cafke shi.
Yana fitowa yana jin kamar ya yi laifin sata ne...
UZURI JIYA PLEASE BAN SAMU DAMAN NIGHT POSTING BA NASAN KUNYI TA JIRA NA INA BAKU HAƘURI AKAN HAKAN ..
THANK YOU...
BANGA KUNYI MURNAR BAYYANA KAKA BA GUY'S
.jpg)