Dr. Sadeeq page 65 by Nana Ƙanwata Soja

 

Dr. Sadeeq page 65

6️⃣5️⃣

BUSSINES GROUP   

    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    

    DR SADEEQ GROUP UPDATE 

    👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO

    BY

    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama 

"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

  💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 

THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE

   MORNING UPDATE 

ENJOY YOUR DAY

    COMMENTS SECTION 

   👇👇👇👇👇👇https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1

     

 NOVEL ELITE  CHANNEL FOR MORE NOVEL'S 

    👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35 

    Kaka ta ja numfashi mai ƙarfi, ta kalli Mommy da tsananin ido:

“Dole… dole Zainabu Sai ki bawa Indo haƙuri. Ba zan yarda wani abu ya faru ba—kowa ya tsaya ya kalli abin da zai faru!”


Kowa ya tsaya da mamaki—har Atika ma ta tsaya a gefe tana kallon Indo. Mommy ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta tashi da ƙasa

“Okay… KIYI ha’kuri, Indo.”


Indo ta ja hannun ta, tana jin tsoron firgicewa, sannan ta juya ta koma dakin Kaka  amma a ranta, ta san cewa kaka ba zata bar ta ba.


Nazifa ta bi Indo zuwa dakin, tana ɗauke da sauran kayan da Indo ke bukata. Indo ta samu ɗan sauƙi ganin sister Nazifa tana kula da ita.


Kaka ta faɗa da murya mai ƙarfi:

“Daga yanzu, anan Indo zata rayu—part na Kuma duk wanda ya yi ƙoƙarin cutar da ita, to… zan tabbatar babu wanda zai tsira!”


Indo ta zauna, zuciyarta cike da haɗuwa da tsoro da kwanciyar hankali. Ta san yanzu kaka ce zata kiyaye ta, kuma babu wanda zai iya mata zalunci a wannan gidan.



Nazifa ta zauna kusa da kaka, tana kallon Indo da damuwa:

“Kaka… dole fa sai an sa mata drip. Jikin ta na ƙara zafi, har yanzu tana amai…”


Kaka ta matso kusa da Indo, ta latsa kafafunta da hannayenta, ta ce da murya mai ƙarfi:

“To… kira shi Sadeeq, nan yanzu!”


Nazifa ta ɗauki wayar Indo, ta duba kira—amma sai ga missed calls guda huɗu. Amma Dr Sadeeq bai ɗauka ba.


Indo kuwa, tana jin kuka a ranta, ta fara hawaye a hankali. Ta dinga tunanin yadda ya manta da ita, yadda kullum take jiran sa tun jiyap kulawarsa, har yanzu shiru yake. Zuciyarta cike da rashin tabbaci da jin ƙunci—amma a gefe guda, tana jin tasirin Kaka da kulawar Nazifa na ba ta ɗan kwanciyar hankali.

Kaka kuwa ta yi murmushi da ɗan faɗin murya:

“Yarinyar nan… kada ki damu. Duk wanda zai raina ki, ko ya yi shiru, zan tabbatar ba zai cutar da ke ba. Sai mu fara ganin lafiyar ki yanzu.”

Indo ta dubi kaka, tana jin ranta ya ɗan sassauta. Ko da ciwon da take ji, ta fara jin cewa yanzu akwai wanda zai kula da ita har sai ta samu lafiya.

Nazifa ta shirya cikin doguwar riga pinch ta ɗaura veil a hanzarce ta rungume jikinta saboda zafin da take yi. Driver ya buɗe musu ƙofa, suka shiga mota.


A baya:

Kaka da Indo – Indo tana jingine a kafaɗar Kaka, tana rawar sanyi, hawaye na sauka ba tare da ƙarfi ba.

A gaba:

Nazifa da driver – zuciyar Nazifa na bugawa kamar ƙaho “Karka yi yawo, ka taka hankali… jikin yarinyar nan ba lafiya,” Kaka ta faɗa da murya cike da damuwa.


Suka isa AL NOOR SPECIAL HOSPITAL, babban asibitin da ke da tsadar gaske da kulawa na musamman. Tun daga kofa aka hango tashin hankalin Nazifa da Kaka, hakan yasa nurses suka karɓe Indo kai tsaye zuwa Emergency Room.

A dakin gaggawa aka kwantar da Indo. Nurse ɗin ta duba ta, ta girgiza kai:

“Her temperature is too high… 41.9°C. She needs IV immediately!”

Dr ɗin gaggawa ya shigo, suka fara haɗa drip, oxygen, da ƙarin allurai don rage zafi.

Nazifa na tsaye a gefe tana jijjiga kanta:

“Kai… Allah ka taimake ta…”


Bayan mintuna 10, Bill ɗin farko ya fito: ₦75,000.

Nazifa ta janyo jaka, tana neman ATM card ɗinta—kafin ta saka PIN sai wayarta ta yi vibrating “Dr Sadeeq calling…” ta yi saurin ɗauka:

“Doctor… Indo ba lafiya sosai… yanzu muke emergency…”

Ba ta gama magana ba, ya katse a cikin tsantsar tashin hankali “Send me the account. Right now!” Nazifa ta tura masa.

Kafin minti biyu, alert ya shigo ₦100,000 RECEIVED – DR. SADEEQ

Nazifa ta saki ajiyar zuciya tana kallon kaka:

“Kaka… ya biya. Yana nan zuwa.”


Kaka ta ja tsaki ta ɓoye murmushi:

“Da alama zuciyarsa bata da nisa da yarinyar nan… ai sai ya iso ya ga irin abinda aka yi mata .”

Indo kuwa tana kwance, idanu a rufe, hawaye na zuba a gefen kumatunta, zuciyarta ta yi nauyi, jikinta ya sake yin sanyi, ta lumshe ido cikin raunin daci

Cikin Emergency Room…

Indo tana kwance a gado mai jikin ta na rawa sanyi da zafi lokaci guda. Idanunta a rufe, amma hawayen da ke zuba ba su tsaya ba. A duk lokacin da nurse ta taɓa ta, sai ta ɗan murɗa jikinta saboda raɗaɗi.


Nazifa ta tsaya kusa da ita, tana rike da hannunta a hankali kamar yarinya karama.

Kaka kuwa ta tsaya a ƙofar Emergency Room cike da faɗa da takaici.


Kafin minti 20 bayan alert ɗinsa, an ji gadon asibiti ya ɗauki hayaniya.


Dr Sadeeq ya shigo da gudu cikin farin labcoat, har yana mantawa da rufe button ɗinsa. Idanunsa sun cika da tashin hankali da nutsuwar likita mai damu da marasa lafiya—amma a yau ba kawai marar lafiya ba… Indo ce.


Da ya isa bakin gado, ya tsaya cak yana kallonta kamar zuciyarsa ta taɓarɓare ya karanta chart ɗinta da sauri, ya tattaro gani da damuwa a lokaci guda:


Sadeeq (a hankali, muryarsa na rawa):

“41.9°C… dehydration… bruises…? Bruises??”


Ya ɗaga kai, idonsa ya haɗu da na Nazifa.

Nazifa ta haɗiye yawu, ta ɗan durƙusa ta ce da rauni “Doctor… jikin ta ɓoro-ɓoro ne… kamar an mata duka kuma tana amai tun safe.”


Wani irin haske da zafin fushi ya kunna a idon Dr Sadeeq.

Ya runtse ido kaɗan tamkar wanda yake ƙoƙarin shawo kan zuciyarsa kada ta hargitse shi.


Ya ce da nurse mai aiki kusa “Prepare cold compress, IV No.2, monitor heart rate every 5 minutes And get me her full vitals now.”Nurse ta yi hanzari Kaka ta kutso kai

Kaka ta tsaya a bakin gadon, ta kalle shi da idon da ba likita yake gani ba – idanun tsohuwa da ciwon jinin jikarta " a haka kana cewa amana ce ita ashe harda dukan ta ake ana azabtar da yarinya ƙarama da tsanguma tana jurewa ".

Ya ɗago kansa da sauri, ya kama hannun kaka da girmamawa “Kaka… ki yafe. Ni ba zan bari wani ya sake ta ba. Indo ba zata kara shan wahala ba wannan ranan na miki alkawari.”cikin zuciyarsa kuwa, magana ta daban ke ƙona shi:“waye ya taɓa ki Indo? me suka yi miki? me yasa kika boye min?”

sai zuciyarsa ta ƙara tsinkewa da jin zafin ganin ta da rauni.


A hankali ta buɗe ido. Idon ya yi nauyi kamar dutse. Da ta ga Dr Sadeeq ne wajen gadonta sai zuciyarta ta buga sau biyu ta maida idonta ƙasa tana murmurin ciwo.

Ba ta iya magana ba sai da ƙyar“Doctor… ka manta dani…” Sadeeq ya tsaya cak.

zuciyarsa ta yi wani irin murɗawa mai raɗaɗi.

ya matsa kusa da ita sosai, ya sa hannunsa a goshinta yana duba yanayin zafin jikin na ta.

“Indo… I will never forget you ki daina irin wannan tunanin.”

Hawayen Indo suka zubo ba tare da ita da ta san suna zuba ba, ta juya fuskarta gefe, tana jin tsoro da kunya a lokaci guda.


Nazifa ta tsaya a ganin su  ta ja baya,ta san akwai wani abu mai ƙarfi tsakanin su biyu—duk da Indo bata yarda ta faɗa mata ba, Kaka ma ta ware ido:“Aha! To shikenan… na kama!”

Amma ta yi shiru ta bari likita ya gama aikinsa.

“Kaka… Indo tana bukatar kwanciya a asibiti yau. Infection da dehydration sun yi yawa.

Za mu yi scanning for internal injuries saboda bruises.”Kaka ta jinjina kai, amma ta ce da murya mai kaifi:


“Yi komai da ya kamata. Amma wallahi… babu ruwan ku ɗin gidan nan da yarinyar nan daga yau yarinya Ba uwa ba uba " ya ce a hankali:“Kaka… ki yarda da ni. Zan kiyaye ta.”

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post