Dr. Sadiq Page 66 Complete by Nana Kanwar Soja

 

Dr. Sadiq Page 66 Complete

6️⃣6️⃣

BUSSINES GROUP    

    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    


    DR SADEEQ GROUP UPDATE 

    👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM

    

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO

    BY

    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama 

"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

  💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 



THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM U ARE ALWAYS IN MY MINE



   MORNING UPDATE 

ENJOY YOUR DAY


    

    

    COMMENTS SECTION 

   👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1


    

      

 NOVEL ELITE 


    CHANNEL FOR MORE NOVEL'S 


    👇👇👇👇👇👇

  https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35  


    

Dr Sadeeq ya zauna kusa da Ita zuciya a cike Kaka da Nazifa sun koma gida, suka bar shi shi kaɗai a dakin asibitin ya yi shiru  sai karar AC da na na’urar da ke lissafin numfashinta beep… beep…

Ya jingina da kujera, hannayensa biyu haɗe, yana kallo ta gefe ya kasa rufe ido — duk tunaninsa ita ce.


“Me ya faru da ke Indo? Waye ya taɓa ki? Me yasa kika boye min? Me yasa ban gane jikin ki yana ta raunana ba?”


Zuciyarsa na masa zafi fiye da ciwon kai har aka kira azahar, ya miƙe bisa dole ya fita ya je masallaci Nazifa ta dawo da towon akushi, ta ajiye a gefen gadon, ta ce:


“Doctor… idan ta farka ka bata kaɗan. Ko ruwa ma sai a hankali.”Ta sallame shi, ta koma gida asibitin ya sake yin shiru…


Indo ta farka amma zuciyarta ta yi tsami a hankali, Indo ta buɗe ido maganar farko da ta ji a kunne shi ce:


“Indo… sannu.”


Muryarsa — mai laushi, mai nutsuwar da ta saba mata — amma yau tana mata ciwo.


Ta ji numfashinta ya ɗaure.

Ta san yana kallonta, amma ta ƙi ta dube shi sai ta kawar da kai gefe, ta kafe bango kamar ba shi zai taɓa zuciyarta ba ya matsa kaɗan kusa da ita, ya durƙusa da girmamawa.


“Indo… kina jin sauƙi ne?" shiru,  ta motsa hannunta kadan, ta daure jikinta, ta takura murya mai rauni “Na’am…”


Amma bata dube shi ba.

Bata so ya gani cewa hawaye ya makale mata, ko yadda zuciyarta ke bugawa saboda shi.


Dr Sadeeq ya ji zafin da bai taɓa ji ba, ya lumshe ido, zuciyarsa ta kaɗa wannan ba Indo ba ce da ya sani.

Wannan fushin… raunin… tsoron… daga ina?


“Indo… me yasa baki kalloni?”

Ya tambaya cikin muryar da ya kasa ɓoye damuwarta.


Ta yi shiru na ƴan daƙiƙu sannan ta ce cikin murya mai cike da ciwo “Don bana son gani…

Na gama…”Yayi saurin matsawa kusa da gadon“Gama me? Indo ki karɓeni yanzu… ki fada min me ke damunki.”

Ta yi murmushi mara alheri, mara ƙarfi, mara jin daɗi.“Ko baka ga halin da nake ciki ba?

kayi kamar baka san ina cikin matsala ba.

jayi kamar baka lura ba tun jiya…”


Muryarta ta sake raguwa:“Ka manta dani.”


Wani abu ya soki kirjinsaYa manta? shi?

ya yi ƙasa da murya kamar mai roƙo:

“Indo… wallahi ban manta da ke ba… ban taba…”


Ta katse shi, idonta na cike da hawaye da ta ƙi saukewa:


“Please… ka bar ni.

Inason zaman lafiya.

Kuma idan dole ne — zan daina kulawa da kai…

Duk abinda ya faru dani… saboda kai ne.”


Zuciyarsa ta yi ƙaraf!

Ya saki numfashi mai nauyi tamkar ɗan dutse.


Ya tsaya yana kallonta — ita kuma ta ƙi ta ɗaga kai ko millimeter ɗaya.

Dr Sadeeq bai jure ba

Da sauri ya kama hannun Indo ɗaya cikin taushin da yake boye tashin hankalin da yake ciki “Indo… please… ki kalleni ki kalle ni ki faɗa min me nayi—kin dame zuciyata.”

Ta janye hannunta da ƙarfi fiye da ƙarfin jikinta “Ka barni kawai!” Muryarta ta karye.

“Koba ka gane ba… bana son magana kuma idan baka lura ba… bakada wani mataki domin ka wuce yanzu—just leave.”


Kafin ya sake magana, cikin sa’a ko rashin sa’a Likitan da ke kula da ita ya shigo.

Ya kalli Sadeeq, ya yi clearing throat:

“Dr Sadeeq, please… zan duba patient ɗin.

You can wait outside.”

Dr Sadeeq ya daure fuskarsa amma ya tashi.

Yana fita, bai tsaya ko’ina ba — ya jingina da bango a corridor yana matse yatsunsa kamar zai murde ƙarfe Zuciyarsa ta yi masifa.

“Me yasa take fushi dani haka? Me nayi? Me na rasa? Hijabin duniya… tayi min nisa. Indo please…” ya shaƙi iska mai sanyi, zuciyarsa na zafi sosai Lallai ya lura:

Indo ba ƙaramin fushi take dashi ba.

Fushin da ya haɗe da ciwo, zargi, da jin an watsar da ita.


Ya dafe goshinsa, ya runtse ido.


“Wallahi na san akwai bayanin da take buƙata… kuma sai na sameta.

komai ya zama dole.”


   

BAYAN WASU KWANAKI


Duk yadda Dr Sadeeq ya gwada, ya gwada kuma ya gwada  Indo ta ƙi, taƙi magana taƙi kallonsa 


Ko da ya zo da fruits, da tea, da magani—har da kulawar da bata saba gani daga wurinsa—

Indo ta yi shiru kamar babu shi.

Kaka kuwa ta ce masa sau dubu“Ɗana… ka barta wannan ciwon zuciyar ne…

idan ka matsa, sai ka tsananta mata.”




Hakan yasa Dr ya hakura amma zuciyarsa duk ta karye  a haka har aka Sallame Su

Yau an sallame su daga asibiti, suka dawo gida kai tsaye part na Kaka.

Daga gefen gadon Kaka aka ware mata ɗaki na musamman —

har da kayan da za ta yi amfani da su.

Kaka ta sa aka kwaso mata kayanta gaba ɗaya daga gidan Mommy.

Indo kam ta tsaya cak tana mamaki lokacin aka shigo da akwatinta da kayanta.

Zuciyarta taji natsuwa kamar an wanke mata huhu Tayi murmushin ƙarfin hali a ranta:

“Da alama yanzu hankalina zai kwanta…

amma wannan ba zai sa na manta wulakancin Atika da ta min ba.

Dolenta ta gane ta tsokane A’ishatu Indo.”


Ta matse yatsun hannunta a hankali.

Idonta ya yi kauri kamar mai shirin ballagazawa bata da lafiya sosai—amma zuciyarta ta gama komawa mai kyau + mai zafi.

A lokacin da Nazifa ta shigo tana cewa: “Indo… ya jikinki?”Indo ta ɗaga kai ta yi murmushin dabara:  “Na warke sosai Nagode aunty Nazifa yanzu dai magana ta rabo daban.”




Nazifa ta zuba mata ido tana jin kamar akwai wani sabon abu da ya taso a zuciyar Indo—

irin nata Indo ɗin nan wacce idan ta yi shiru, alama ce akwai abu.

Kaka kuwa tana gefe ta yi duba ɗaya:

 “Indo, tun daga yau…

babu wanda zai sa ki kuka a gidan nan.

Idan wani ya kuskure… ki fada min.”

Indo ta sunkuyar da kai ta murmusa —

amma murmushin da ya yi tsami, ba kamar na jiya ba Sabuwar Indo ta dawo


    

l@@@@@@@@@@@@


    


Duk yadda Dr. SADEEQ yake ƙoƙarin ganin Indo ta saurare shi, ya kasa. Ko da ya zo ya zauna a gefen gadonta, tana juya kai gefe kamar bata sanshi ba. Kaka ce ta ce masa:

 “Ka barta ta huta, ranka zai baci sai ta warke.”


Hakan yasa ya bar su da rai a cunkushe, zuciyar sa cike da takaici da rashin fahimtar me ya tsokano wannan fushin nata.



Shi kuma tun lokacin sallamar bai ji daɗi ba. Yau kwana biyu yanzu da yake ƙoƙarin yin magana da Indo amma ta ƙi buɗe masa ko ƙofar hira.


Ya zo yanzun nan ya tsaya a bakin ƙofar parlourn, yayi sallama. Kaka ce kaɗai ta amsa. Ya tsaya yana sauraron ko zai ji muryar Indo amma shiruZuciyar sa ta buga, ya furta a hankali  “Tana nan?”

Kaka ta ɗaga kai ba tare da ta kalle shi sosai ba “Tana ciki… amma idan ba dole ba, ka bari ta huta, Dr.”

Ya yi shiru. Ya so ya ce yanzu zan shiga, amma da ya tuna yanda Indo ta kauce masa a asibiti, hankalinsa ya sake rikicewa.


Yayi ja da baya yana cewa cikin zuciya:

 “Me nayi mata? Me yasa take fushi dani haka? Ko Atika ta sake wani abu?”




Yayi tsaki a hankali, ya fita daga gidan zuciyar sa cike da radadi

    TO BE CONTINUED...

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post