https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
PG 1️⃣ 2️⃣1️⃣ 🌟 1️⃣2️⃣5️⃣
❤️DR SADEEQ 🤍
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
SECOND TO THE LAST PAGE
THIS PAGE IS FOR U NAMCY KHADIJAH SUFYAN ENJOY...
SPECIAL THANKS TO
NOVEL ELITE WEBSITE
HAUSA NOVEL GROUP WEBSITE
ABOKIYAR HORA WEBSITE
CREATIVE NOVELS WEBSITE
TK NOVELS WEBSITE
HAUSA EBOOK'S
TASKAR HAUSA NOVEL
E..T...C
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
A GURGUJE
BOOK 3 – DR SADEEQ
Indo ta nufi part na Dr SADEEQ da zuciya na cike da rashin tabbas. Ta shiga, taga ba kowa a cikin ɗaki—Atika ko alamarta babu a ranta ta yi tunanin, “Ko motar sa ta tafi ne? wataƙila bai dawo daga hospital ba.”
Da sauri ta ɗauki waya ta kira Dr Kamal “kuna hospital ne?” “Yes,” inji Kamal.
“Okay,” ta amsa, ta sauke waya da saurin numfashi.
Nan ta sami bolt na tsaye zuwa asibiti inda Dr SADEEQ ke aiki, office nasa duk da yanayin da ta shiga, ta sani sosai inda za ta nufa.
Tana zuwa ta tura ƙofar kai tsaye A office, ta ga Dr SADEEQ yana zaune, sanye da soft white shirt da glass, yana latsa computer ɗinsa cikin natsuwa. Nan ya juyo, ya turɓusar da kai “Who is that? bazakuyi knocking ba?”
Indo ta tsaya cak a kofar office, zuciyarta na buga da sauri. Cikin ranta, ta yi murmushi mai ɗan raɗaɗi, ta tuna dukkan tunani da soyayya da fargaba da suka ratsa tun lokacin da suka fara samun matsala wanda hakan yana da nasaba da kishi ne...
Dr SADEEQ ya kalli Indo da mamaki mai zurfi, idanunsa na fuskantar rashin gaskiya:
“Me kikeye a Abuja at this time? me ya kawo ki?” sai ya ɗan matsa kusa da ita, yana ƙoƙarin fahimtar dalilin zuwanta “Shin kina lafiya? Baki kira ba…”
Nan sai ya fara tambayoyi a jere, kamar goma zuwa goma sha biyu, kowanne na ƙara masa ruɗi “Ko lafiya ne? Me yasa baki sanar da ni? Me kike yi yanzu? Wane dalili ya sa kika fito haka?”
Indo ta tsaya a ƙofar, numfashinta na bugu da sauri, zuciyarta cike da tsoro da farin ciki a lokaci guda. Ta rasa inda za ta fara magana, amma idanunta sun faɗi gaskiya da mamaki: “At least, I'm his property"
Indo ba ta iya jimawa ba, zuciyarta ta tashi da sauri. Ta rufe idonta, ta rungume Dr SADEEQ sosai, tana matse shi kamar ba za a sake raba su ba “Are you fine?” Dr SADEEQ ya tambaya, hannayensa na rungume ta da kulawa.
Indo ta ƙara gangami a jikinsa, ƙirjinta na bugawa da kuka mai tsanani, ta fara shishiga:
“Ubanwa… ya taɓa min… ya taɓa min ke”
Dr SADEEQ ya saki ajiyar zuciya mai nauyi, ya yi murmushi mai tausayi “I’m sorry… tell me what happened. Ba zan bari wani ya taɓaki ke ba.”
Indo ta ci gaba da rike shi, zuciyarta cike da haɗuwa da tsoro da jin daɗin kasancewa a ƙarfinsa.
Indo ta tsinci kanta a cikin jikin sa da sauri, zuciyarta na bugawa da sauri, kaman zata fashe. Hannayensa sun zagaye bayanta, ya ja ta kusa da shi sosai “Are you fine?” Dr SADEEQ ya ɗaga kanta, idanunsa na kallon nata cike da kulawa da ƙauna.
Indo ta ƙara matse shi, tana jin dumin jikinsa da ƙamshin sa na kusa da ita. Ta shishige cikin kunnensa “I… I missed you… sosai…”
Dr SADEEQ ya murmusa, ya saki hannayensa ya taɓa fuskar ta a hankali “Ni ma na damu da ke sosai… Ina so ki sani, babu wanda zai iya cutar da ke… I’ll always protect you.”
Indo ta miƙe idonta cikin zafi da farin ciki, ta ji kamar zuciyarta zata fashe saboda soyayya. Ta yi ƙoƙarin rungume shi da ƙarfi, tana jin duniya na tsaya cak a wurin, kawai su biyun suna kallon juna da zuciya ɗaya.
“I love u Dr Balarabe” ta ƙara magana da murya mai rauni, amma cike da gaske.
Dr SADEEQ ya ja ta da ƙarfi, yana murmushi:
“And I love you… fiye da yadda zaki iya tunani. Kullum, Indo, kullum…”
“I love you… please don’t leave me alone, Dr Balarabe…”
Muryarta na rawa, hannayenta sun manne da rigarsa kamar idan ta sake, duniya zata rushe. Dr SADEEQ ya rufe idanuwansa na ƴan daƙiƙu, annushwa da nauyin soyayya suka mamaye shi gaba ɗaya.
“You are my husband… and I didn’t even know,” Indo ta ƙara, hawaye na gangarowa.
“I love you… kar ka ƙara barina nayi nisa da kai. Please… I love you.”
Ya buɗe idanuwansa, ya ɗaga fuskar ta a hankali, ya share hawayenta da yatsunsa. Murmushinsa ya cika da tausayi da ƙauna “Indo… I’m here,” ya faɗa da murya mai sanyi.
“Ba zan bar ki ba. Not today, not ever.”
Ya ja ta kusa, ya matse ta cikin ƙirjinsa, ya jingina goshi da nata. A cikin shiru mai daɗi, ya sumbace ta a saman goshin ta ta natsu. Ta ji kamar ta dawo inda ya dace—a gefensa.
“Stay with me,” ta raɗa “Always,” ya amsa, yana rungume ta sosai.
Duniya ta yi shiru. Abin da ya rage alkawari ne tsakanin zuciya biyu ya ja ta kusa da jikinsa, zuciyarsa na bugawa da sauri.
A hankali, ya lumshe ido ya haɗe bakin su for some second s " I missed your soft....." cike da ƙauna da annushwa.
Indo ta tsinci kanta a cikin shiru mai daɗi, hannayenta a wuyansa, zuciyarta ta narke. Duk duniya ta tsaya a wannan minti, komai ya tsaya sai su biyu.
Ya sake kallon idanuwanta, murmushi ya bayyana a fuskar sa, ya ji dadin ganin ta natsu a gefensa. Wannan ɗan sumbaci ya zama alkawari na soyayya, na tsayawa tare da juna.
Indo ta shafa fuskarsa da hannunta, tana numfashi cikin annashuwa:
“Don Allah… kar ka sake barina.” “Zan tsaya… koyaushe,” ya amsa a hankali, yana rungume ta sosai.
Shiru ya mamaye su, amma zuciyoyin su biyu sun haɗu, sun fahimci cewa soyayya ba ta da iyaka idan akwai gaskiya da juriya.
Indo ta jingina da jikin Dr SADEEQ, tana jin bugun zuciyarta da sauri. Hannayensa sun rungume ta a hankali, yana jin dumin jikinta da ƙamshin ta “Indo… I’ve missed you so much,” muryarsa ta yi mata rauni ....
Ta dagan kansa, idanuwanta cike da hawaye da annushwa “Dr… I love you… I can’t be without you anymore.”
Sai ya taɓa fuskarta da hannayensa biyu, yana kallon idanunta “You are mine… forever,” yace da muryar soyayya.
Indo ta rungume shi sosai, tana jin cewa finally ta samu wurin tsaro da soyayya—ba wani abu zai raba su ba.
Dr SADEEQ kuma ya ƙara matsa, yana jin cewa komai da ya faru a baya yanzu ya zama forgotten, yanzu akwai su kawai da junansu.
Indo ta jingina da jikin Dr SADEEQ, tana jin bugun zuciyarta da sauri. Hannayensa sun rungume ta a hankali, yana jin dumin jikinta da ƙamshin ta “Indo… I’ve missed you so much,” muryarsa ta yi laushi, amma cike da ƙarfi.
Ta dagan kansa, idanuwanta cike da hawaye da annushwa “Dr… I love you… I can’t be without you anymore.”
Sai ya taɓa fuskarta da hannayensa biyu, yana kallon idanunta “You are mine… forever,” yace da muryar soyayya.
Indo ta rungume shi sosai, tana jin cewa finally ta samu wurin tsaro da soyayya—ba wani abu zai raba su ba.
Dr SADEEQ kuma ya ƙara matsa, yana jin cewa komai da ya faru a baya yanzu ya zama forgotten, yanzu akwai su kawai da junansu.
Indo ta zauna a kusa da shi a office, tana murmushi kamar wata yarinya mai jiran something special
Dr SADEEQ na kallonta, yana jin dumin zuciyarsa da yadda take yi masa tsokaci cikin ladabi “Na yarda zanyi wankan, amma ka tabbatar kazar babba ce,” yace da dariya, yana tsokanar ta cikin muryar soyayya.
Indo ta buga dariya mai laushi “Wai Dr Balarabe, baka manta ba?”
“How could I forget our best moments, sweetie?” ya amsa, yana rike da hannunta a hankali, kusa da jikin sa, kamar duniya ta tsaya cak.
Suka isa gida, hannu cikin hannu, suna murmushi da jin daɗin kasancewa tare. Indo tana kallon gidan kamar tana ganin sabuwar duniya—amma cikin zuciyarta, tana jin ƙauna da nutsuwa a gefen Dr SADEEQ.
A part na Kamal, Nazifa ta yi dariya mai taushi “Finally, Aunty Indo!”
Dr SADEEQ ya ɗan rikice, yana kallon Indo:
“She is… my wife,” ya ce a hankali, yana jin wani dumin zuciyarsa yana cika shi “ya zan yi da Mommy yanzu? Ya zan gayyamata?”
Nazifa ta yi dariya, tana masa shiru cikin ladabi “It’s okay, brother gobe muje tare.”
Indo ta kallon Dr SADEEQ, ta ga yadda idonsa ke cike da kulawa da so mai zurfi. Ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tana murmushi a hankali “At least, finally… I am really yours,” ta ce cikin zuciya, amma ta rufe baki da murmushi mai sanyi.
Dr SADEEQ ya riƙe hannunta sosai, yana cewa cikin muryar da cike da soyayya:
“And I’ve waited for this moment… for so long, sweetie.”
Nazifa ta tsaya kallon su, tana dariya cikin farin ciki,
Kamal ya tsokane Dr SADEEQ da dariya mai ƙyalli a idonsa “But don’t tell me Indo zata kwana anan? kaima kace zaka kwana? Better ka tafe gun amarya!”
Suka yi dariya gaba ɗaya. Indo ta juya, murmushi mai haske “Dr Kamal, kana samun Dr a tension. Good night, dear!”
Dr SADEEQ ya hararre ta, ido cike da tsoro da dariya “Kin gaji dani ne ko? anan zan kwana” Ya zaro ido, yana ƙoƙarin nuna tsoron Allah da tsoron tuna daren farko da ita.
Indo ta yi dariya, tana matse hannunsa a hankali “Kai, Dr… yau, kawai za mu kwana lafiya. Babu wani tashin hankali. Na gode da kasancewa tare da ni.”
Dr SADEEQ ya sauke ajiyar zuciya, ya kalle ta cikin dumin zuciya da soyayya, yana murmushi“Allah ya sa na iya kare ki, honey. Kullum.”
A nan suka kwana tare a part na Kamal, zuciyoyinsu cike da farin ciki da annushwa. Ko da yake kwanciyarsu yana cike da natsuwa, amma duk wani kallon ido, murmushi da ɗan motsi a jikin juna ya bayyana soyayya i ta kulawa
Indo ta rungume Dr SADEEQ, ta tsoma kai a kirjin sa, tana jin dumin jiki da tsaro. “Kai, Dr… na gode da kasancewa mijina,” ta fada cikin ƙanƙantar muryarta, zuciyarta na cika da jin dadi.
Dr SADEEQ ya ɗaga hannunsa ya shafa gashinta, yana murmushi“Honey… I promise, zan kasance tare da ke kullum. Babu wanda zai raba mu.”
Suka yi dariya tare,
A cikin wannan dare, Indo ta gane gaskiyar zuciyarta—Dr SADEEQ mijinta ne, kuma tana son sa da dukkan zuciyarta. Kuma Dr SADEEQ, duk da abubuwan da suka gabata, yanzu yana jin cikakken farin ciki da samun Indo a matsayin matar sa.
********************
Kafin Indo ta farka, Dr SADEEQ ya tashi da sanyin safe, zuciyarsa cike da kulawa da soyayya. Ya shirya mata wankan tsarki cikin ladabi, yana tabbatar da cewa komai ya kasance tsafta da natsuwa.
Indo ta tashi daga bacci, idonta na ɗan rufe, amma murmushi ya bayyana a fuskar ta. Ta ji dadin kulawar sa, zuciyarta cike da annushwa.
Bayan sun gama, ya taɓa goshi ta cikin ƙasƙantar da ido yana cewa “Nagode, Honey… da kasancewa matata, ta bin sunnah.”
Ta rungume shi da ƙarfi, tana jin farin ciki da natsuwar aure, zuciyarta ta cika da soyayya da aminci. Wannan rana, sun fara sabuwar rayuwar aure, cike da romance, farin ciki, da soyayya mai ɗorewa.
Safiya ce a part na Kamal, Indo ta zauna a kitchen table tana ɗan jin gajiya daga baccin dare. Sai Dr SADEEQ ya fito da plate mai ɗauke da indomie da ƙwai da ya soya da kansa, murmushi a fuskar sa.
“Good morning, Honey,” yace yana mika mata abincin.Indo ta kalli plate ɗin da mamaki da dariya a lokaci guda:' “Ai, baka iya girki ba, bazan ciba ba.”
Amman Dr SADEEQ ya rungume ta daga baya, yana tsokanar ta da confidence “No way… wallahi na fi ki iyawa! Zan nuna miki yadda namiji zai girka wa matarsa!”
Indo ta fashe da dariya, zuciyarta na bugawa da annushwa “Kai Dr… baka san yanda zai bata min baki ba, !”
A haka ya bata har suka gama suka shirya a gaggauci
Duk shiryarwa sun tashi, Indo a tsorace, tana jin zuciyarta na bugawa da sauri. Amma duk da haka, tana kallon Dr SADEEQ wanda ya riga ya sanar da Daddy cewa yana da magana da mutanen gidan.
Cikin kwarin guiwa da nutsuwa, Dr SADEEQ ya tsaya kusa da ita, idanunsa cike da kulawa:
“Indo… kada ki damu, komai zai kasance lafiya. Zan tsaya tare da ke.”
Indo ta ji ƙarfin guiwa nan take, amma a ranta akwai tsoron bala’e da kishin Atika. Ta kalli Atika, wacce kuma take tare da su ”
Atika kuwa tana lura da Indo, sai ta yi murmushi takaice daman yasan wanan rana zaizo ranar da Dr zai nunawa duniya cewa zai aure Indo, har Indo ta ji kamar zuciyarta ta buga bala’e—kamar wutar da ta ratsa ta. Amma sai ta ɗauki ajiyar zuciya, tana tunanin cewa Dr SADEEQ ne kawai zai iya bata kwanciyar hankali a yanzu.
Dr SADEEQ ya shafa hannun ta a hankali, ya murmusa “Na san ke tsoron bala’e, amma ni zan tabbatar babu abin da zai dame ki a nan.”
Indo ta murmushi ƙasa da sautin romance da annushwa, har zuciyarta ta fara sassauta daga tsoro, ta fara jin cewa koda kishin Atika yana nan, amma soyayyar Dr SADEEQ na gamsar da ita.
Suna isa babban parlour, kowa ya tsaya cikin mamaki da baza ido na biye musu. Dr Kamal ya tsaya gaba, ya yi murmushi mai kyau sannan ya fara bayani:
“Tun daga farkon mutuwar Mama Indo, Indo ta kasance a kulawar mu. Bayan haka, mai unguwa ya ɗaura aure, kuma aka kawo ta gidan nan.”
Kowa cikin parlour zuciyarsu na buga da mamaki, wasu suna tausayin Indo, wasu kuma suna jin dadin ganin soyayya da kulawa. Amma idanunka na ganin Dr SADEEQ, za ka hango tsoro a fuskar sa.
Ya tsaya a gefe, hannayensa suna ɗan rike, zuciyarsa na buga kamar za ta fito daga kirji. Yana tsoron hukuncin iyayyen sa, amma a ransa ya san cewa ba zai iya rabuwa da Indo ba, cewa ita ce zuciyarsa, rayuwarsa, kuma mata wacce yake kauna da gaske.
Indo kuwa, tana kallon Dr SADEEQ daga gefe, ta fahimci tsoronsa da ƙaunarsa a lokaci guda.”
Kowa a cikin parlour ya lura da irin kulawar da Dr SADEEQ ke yiwa Indo, har wasu suka fara tambayar zuciyarsu me ke faruwa. Amma babu wanda ya iya cewa komai akan soyayyar su..
Dr SADEEQ ya tsaya a tsakiyar parlour, idonsa na kallon kowa, muryarsa mai nauyi da natsuwa “Na yi kuskure tun farko da na ɓoye muku wannan auren.”
Zuciyarsa ta cika da nadama, amma a lokaci guda, akwai ƙarfin da ke bayyana cewa yana so a fahimce shi. Ya ɗan jinjina kai, sannan ya ci gaba da cewa: “Ina neman haƙuri daga gare ku duka, musamman Mommy saboda duk abin da kuka sani, ko ba ku sani ba, ni ne na ɗauki matakin da bai dace ba.”
Kowa a parlour ya yi shiru, ido na kallon fuskar sa, cike da mamaki da jin tsoron abin da zai biyo baya. Amma cikin zuciyar Indo, ɗan nauyi ya sauka, tana jin cewa Dr SADEEQ ya fara nuna gaskiya da nadama.
Yayin da ya miƙe hannu, murmushi mai taushi ya bayyana a fuskarsa, yana ƙoƙarin bayyana cewa yana so a yafe masa kuma a sake samun haɗin kai a cikin gidan.
Indo ta ɗaga kai, idonta na cike da ƙauna da ɗan tsoro, ta ce “Mommy… please talk.”
Murmushi mai taushi ya bayyana a fuskarta. Ta miƙe hannu ta ɗan latsa na Indo a hankali, sannan cikin ƙwarewa da kulawa ta ce:
— “I know, Sadeeq… amma ya ZANYI na tsane Indo? Amma inasonka sosai. Hakan yasa na sani da kyau, na bincika sosai tare da Daddy… mun gani cewa matar kace ka ɓoye mana. Muma munyi shiru saboda muna jiran mu ga ranar da zaka bayyana mana.”
Kalmar ta na ta bugawa a zuciyar Indo kamar ruwan sanyi ya shigo. Tana jin cikakken natsuwa da farin ciki, amma har yanzu akwai ɗan tsoro a ranta—tsoron rashin fahimtar abin da zai biyo baya.
Dr SADEEQ ya miƙe kai, idonsa na kallonta, cike da ƙauna da nadama, yana jin cewa a wannan lokaci lokaci ne na gaskiya da haɗin kai tsakanin dangin sa......
Daddy ya ɗaga hannu ya kalle su duka, ido cike da tsanani amma kuma da ƙauna. Sai ya ce cikin muryar da ke ɗauke da hankali:
— “Ku saurara, dukkan ku… wannan lokaci ne na gaskiya, na fahimta da tsoron Allah. Abin da ya dace shine ku rike gaskiya da adalci, ba tare da ɓoye abu ko ɓata wa juna rai ba.”
Ya juya ya duba Atika, ido na ƙarfin nuna daraja amma cikin hankali “Ke Atika, ki fahimci cewa abin da ya dace shine ki guji hassada da fushi. Soyayya ba ta bukatar rikici, amma ta bukaci hankali da tsoron Allah.”
Sannan ya kalle Indo da Dr SADEEQ “Indo, ki rike haƙuri da daraja, kuma ki fahimci cewa soyayya gaskiya tana bukatar aminci da tsoron Allah. Sadeeq, ka sani cewa duk abin da ka aikata, Allah na ganin sa ka tabbatar ka rike su bisa yarda da adalci da kulawa, kuma kada ka ɓoye wani abu daga iyalanka.”
Kowa ya yi shiru, zuciyarsu na bugawa da nauyi da kuma fahimtar darasi..
**********
