AUREN WATA UKU.!*
*05*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
K’ara Badia ta saki sakamakon hango mahaifinsu da tai yana k’ok’arin kaiwa k’asa. Nan kuma hankula suka koma kansa. Mama ta k’araso da sauri ta tallafesa tana fad’in “Malam dan Allah ka rufa mana asiri kar bak’in cikin Ummulkhairy yai ajalinka.. Wayyo ni Tani.. Sannu Abban Salima..” A haka ta k’arasa dashi madaidacin parlonsa tai masa masauk’i saman d’aya daga cikin lamusassun kujerun dake a cikin parlorn. Sai jero masa sannu take tana bangaje Umma daga kusansa. Badia ta kawo mafifici Mama ta amshe tana masa fifita tana fad’in maza ta kawo ruwa.
Bayan shud’ewan wasu mintoci Abba ya soma dawowa hayyacinsa.
Gaba d’aya ya had’e matan nasa guda biyu. Ya d’an kishingid’a yana dubansu. Lokaci guda yake furta “Tani, Suwaiba..”
Kowaccesu ta amsa jiki a sanyaye.
Abba yaci gaba “Bazai yuwu ku maida min gida kaman gidan kallon kwallo ba.. Ke Tani kin gayyato yaranki Sunzo kuna murnan abinda ya samu ‘yaruwarsu.. Ke kuma Suwaiba kin saka ma ranki damuwan abinda Allah bai saka Miki ba.. Ita rayuwar nan wai duka kwana nawa ne za’ayi.. Kun raba mun kan ahali kun maida min gida kaman gidan maguzawan farko.. Idan kaji hayaniya na tashi a gidan nan toh wann k’ofan ne.. Akan wani dalili..?” Ya d’anyi fasali yana dubansu kafin yaci gaba “Toh ku kula.. Ku kuma tuna cewa duk abinda Kai a wann rayuwar shi zakaje ka cimma a cen.. Bazan gushe ba ina maku nasihan kubi duniya a sannu rayuwar duka ba yawa ne da ita ba.. Bazan bari ku saka mun ciwon da bani da shi ba..”
Murya a sanyaye Umma tace “Kai hak’uri Abban Ummul in sha Allah zamu gyara.. Ko Yaya..?” Tai maganar tana duban Mama.
Mama ta saci idanun mijin nasu kafin ta aikama Umma harara sama da k’asa sai kuma ta juyo da duban nata ga Abba. Tai murmushi Wanda yafi Kama da yak’e “Eh in sha Allah zamu gyara mun tuba Kaji Malam..Allah ya baka lafiya.”
Jinjina Kai yai yace “Alhamdulillah.. Allah ya ganar damu baki d’aya ya kuma had’e mana kan ahalinmu ya shirya mana zuri’armu.”
Gaba d’aya suka amsa da Ameen. Abba yai masu izinin tafiya sai kuma ya dakatar da Umma yace ita ta tsaya.
Wani birki Mama taja kaman zata dungura ta juyo tana duban Abba da yace Umma ta tsaya bayan yau girkinta ne.
“Malam ban gane Suwaiba ta tsaya ba.. Ni ce da alhakin abincika yau fah ko ka mance ne..?” Tai maganar tana tururi kai kace ba itace yanzu ta gama ce ta tuba ba.
Abba ya murmusa yana ayyanawa cikin zuciyarsa Mata sai a barsu wajen kishi. So tari yakan yi ma Mama uzuri dan kishi Tabbas akwai ciwo. Wani abun yasan zafin kishi ne kawai yake sanyata yi amma Tani d’insa tanada halin k’warai.
“Magan zamuyi Tani ba wani abu ba..” Abba yace cikin sigan lallama.
Mama ta kad’a Kai “Aiho.. Kardai garin dad’in zance a zarce a shiga hakki ehe..!”
Murmusawa kurum Abba yai ba tareda yace komai ba.
Saida Mama ta fice ya dawo da dubansa ga Umma.
“Suwaiba..” Ya kirawo sunanta
“Na’am Abban Ummul.”
“D’azu a kasuwa mak’ocin shago na ke jajanta mun al’amarin auren Ummulkhairy.”
Umma ta jinjina Kai alamun tana sauraro.
Abba yaci gaba “Bansan ko kin gane shi ba mai babban kanti na kayan masarufi da yake jikin nawa kantin.. Wasu lokutan har rancen kaya yake bani idan na saida na mayar masa uwar kud’i hardai jarin nawa ya d’an ja baya. Mutumin kirki ne Alhaji Kamilu..”
Umma ta jinjina Kai tace “Allah sarki..”
Abba yaci gaba “Toh nan dai nake labarta masa al’amarin ita wann yarinya nawa Ummulkhairy.. Toh kwatsam sai ya sanar Dani yana so na bashi auren ita Ummulkhairin idan babu wani matsala.. Toooh wato gaskiya banyi garajen amsa masa ba duba da irin abubuwan dake faruwa. Ak’alla aure nawa ake sakawa na Ummulkhairy abu baya yuwa.. Sann ko sati ba’ayi ba da abinda ya kuma faruwa na amshe lefen shi yaron nan Zubairu. Amma dukda haka bazaka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji ba. Ba wann dalilin ne yasa nace ya dakata ba.. Babban dalilina shine sai naji daga bakin ‘yata idan tana sonsa.. Idan har bata sonsa JINKIRIN aurenta bazai sa na aura mata mutumin da bata so ba.. Sabida shi Alhaji Kamilun lallai lallai ya nuna mun yana son na basa dama kuma Kinga akwai ‘yar kunya a tsakaninmu… Tooooh dai gaba d’aya kaman ya d’aure ni ne.. Dan a gaskiya..” Sai ya d’anyi Shiru kuma kaman mai nazari “Bana so Ummul taga kaman na tak’ura mata da batun aure ne tinda dudu ba’a jima da fasa..”
Bai kai aya ba Umma ta katsesa “Haba Abban Ummul.. Ta ya ma zakace haka.. Yo har wani lokaci zaa d’ibar mata.. Shifa lokaci baya jira. Ka duba sa’anninta duk suna d’aki daga masu yara uku hudu kai har masu shida akwai sa’anninta… Yo ai ko ta gansa ko bata gansa ba tinda har zai rufa mana asiri ya aureta ai shikenan..”
Katseta yai da fad’in “A’a Suwaiba, JINKIRIN Ummulkhairy ba zaisa na tilasta mata kasancewa da Wanda bata so ba.. Kece mahaifiyarta, ki kirata a d’aki a natse ki sanar da ita. Idan tayi na’am falillahil hamdu yau da dare sai na d’aga waya na kirasa gobe idan Allah ya kaimu sai yazo su fahimci juna.. Alhaji Kamilu mutumin kirki ne kuma yanada matan aure biyu da yara da d’an dama.. Ki kira ita Ummulkhairy ki sanar da ita a natse. Idan Sun daidaita kansu shikenan sai ai maganan aure tinda babban mutum ne ba wani Jan lokaci za’ayi ba. Hasalima Jan lokacin baida wani alfanu..”
Umma tai karaf tace “Ai ko gobe ma sai a d’aura kawai nidai ta tafi d’akinta..” Ta d’aga hannu sama tana fad’in “Oh Allah na gode maka ni Suwaiba.. Allah maji kukan bawansa mai maida asara da alkhairi..”
Girgiza kai kurum Abba yai yana dubanta. Zaman Ummu a gabansa bai d’aga masa hankali ba kaman fitinar mahaifiyarta matarsa Suwaiba . Fatansa Allah ya had’a Ummul d’insa da miji na gari wanda zai kular masa da ita ya kaunaceta tsakani da Allah dama sauran yaransa gaba d’aya.
Cikeda farin ciki tamkar wacce aka yaye mata kaf damuwarta na gidan duniya haka Umma ta fito tana k’wlla kiran Ummulkhairy.
A daidai bakin farandar d’akin Abba ta riski Mama rik’eda farantin abincin Abban. Umma tana ganinta ta tsuke Baki tana zancen zuci Wanda sam bata san ya fito fili ba tsaban farin cikin da ta tsunduma ciki “A sirrace nema a bayyana samu.”
Rangaji Mama take tana dubanta daga sama zuwa k’asa. Kafin tai murmushi mai sauti tace “Ayi dai mai mu gani wai gurguwa da auren nesa.” Ta k’arashe kaman zata bangaje Umman ta nufi parlorn Abba.
Umma ta tab’e Baki ta nufi d’akinta cikeda farin cikin abin alkhairin da ya sameta dan yau d’in Ji take burinta na gidan duniya ya gama cika.
**
Abuja.
Cikin bacci yake Jin vibrating d’in wayarsa na kuma k’aruwa alamun wayar ta gaza yin Shiru. Yai k’ok’arin mik’ewa had’ida janye Dareen dake kwance saman k’irjinsa. Hannu yasa ya d’auki wayar dake aje gefen bedside yana ganin lokaci quart after six na safiya. Lokaci guda ya d’anyi relaxing jikin pillow yana k’ara wayar a kunnensa yana rage girman idanunsa masu cikeda bacci wanda hasken hantsi da ya soma bayyana ya tilasta masa yin hakan.
“What Hisham.” Ya Fad’i yana gyara zaman wayar a kunnensa.
Daga d’aya b’angaren Hisham Yace “Haidar, Kana Ina ne.. me kakeyi..?”
Da mamaki Haidar yace “What kind of question is that..? What could I been possibly doing at this time..? Bacci nake obviously kafin ka tadani.”
Hisham ya katsesa “Have you seen the news..?”
“What news..?” Haidar yace cikin muryarsa mai cikeda bacci.
Hisham ya furzar da huci “Lallai na yarda kana bacci.. Check your phone ka karanta labarun kasuwanci kaga abinda muka tashi dashi.” Daga haka katse kiran yai yayinda Haidar ya shiga shafa wayarsa. Tin daga saman fuskar wayan yake karo da notifications.
Notification guda d’aya ne ya d’auki hankalinsa. THE BUSINESS PRESS. Yanda aka rubuta *Top Business Scandal.* Saurin clicking yai ya shiga kan labarin. Abinda ya soma karo dashi a labarin shine hotonsa da mahaifinsa lokacin da ya cakumosa a cikin Kampaninsu yana jijjigasa yana fad’in yayi disappointing d’insa, daidai wajen akai cutting a video d’in Wanda aka fitar da hoton sosai yanda ya rik’e kwalan Haidar d’in ga jini gefen bakin Haidar. K’asan hoton kad’an an rubuta kamar haka *Owner of Maitama Builders Engr Aliyu Maitama gets into a physical fight with Son over augment.*
“Damn it..! This is not happening.” Ya furta a hankali. Sauri sauri ya mik’e ya shige bathroom dan shiryawa.
Dareen dake baccinta peacefully ta soma bud’e idanunta masu cikeda bacci wanda ko shakka babu shirin da Haidar d’in keyi ne ya katse mata baccin.
Ta zuba masa idanu tana duban yanda yake komai a gaggauce. Ta saki murmushi zallan k’aunarsa cikin zuciyarta. A hankali ta sakalo k’afafunta ta sauk’o daga saman gadon.
Yana tsaye gaban full length mirror yana k’arisa shiri yaji ta rungumosa ta baya had’ida matsesa sosai cikin jikinta.
“Good morning..” Ta furta tana mai d’aura hannayenta saman nasa ta amshe agogon da yake k’ok’arin d’aurawa taci gaba da d’aura masa
“Are you leaving this early..?” Tace sanda take kaikaitowa ta dawo ta gabansa.
“I have to.. I need to take care of something.. I’ll see you later..” Yace a tak’aice yana d’aukan wayarsa da mabud’in mota
Ta take masa baya ganin zai fice cikin sauri. Ta kamo hannunsa guda “What about breakfast..? Your cool tea is in the fridge.. Tun asuba na had’a maka.. The way you like it.. Should I serve you..?”
D’an dubanta yai kafin ta girgiza kai “Kar ki damu, I’ll be fine..”
Ta kuma rik’e hannunsa “Does that mean ka amince da k’orafina ka fasa aje aikinka a Kampanin Daddynka.?” Tai maganar idanunta tar akansa.
Ya d’anyi still yana dubanta “I don’t know… I’m not sure.. I.. must go now.. Take care..” Ya k’arashe yana shafan b’angaren fuskarta guda da tafin hannunsa.
Ta janyo hannunsa ta sumbaci tafin hannun kafin ta sakar masa murmushi tana masa fatan nasara har saida taga tashin motarsa. A hankali ta lumshe idanunta had’Ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ta koma cikin gidan..”
ya d’auki car keys d’insa da wayarsa ya fice a gaggauce.
Yana tafe saman kwalta wayar Hisham amininsa kuma abokinsa a wajen aiki ya kuma shigowa.
“Haidar this is bad.. Very bad.!” Abinda Hisham yace kenan koda Haidar ya d’aga kiran.
Jinjina Kai Haidar yai
“Yanzu zaka yarda da magana na.. Someone is sabotaging the company.. And trust me, I know exactly how to catch that rat.” Shiru yai alamun yana sauraro daga b’angaren Hisham.
Hisham yace “Kuma ba yanda za’ai ka kamo wann b’eran har sai kana aiki da Kampanin. Now more than ever you can’t quit your job.. You need to fix this Haidar.. You need to clear your Dad’s name.. Bazaka bari sunan Kampanin ya b’aci ba..!”
“Oh Shut up Hisham..!” Ya fad’i yana mai katse kiran lokaci guda yana mai k’ara gudun motar.
A can gidan mahaifinsa kaw ya tsare mahaifiyarsa ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ga ‘yan jarida sunyi chaa a bakin gate suna jiran fitowarsa.
Yaci gaba da nuna Mommy da yatsa “Call that pathetic son of yours and tell him to fix this mess immediately.. Bayan asaran da zamu tapka sabida shashashancinsa, I won’t allow him to ruin my company’s image.!” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana mai ci gaba da zagaye katafaren parlorn nasa.
Furzar da huci Hajiya Kwaise tai, tana mai kuma dialing layin Haidar amma shiru bai d’agawa.
Dad ya kuma dubanta “He’s not answering right..?”
D’an lumshe idanu tai had’ida mik’ewa tsaye “Engr please calm down.”
Ya kuma katseta “Seriously Kwaise..? Are you asking me to calm down.? Ko bakiga babban abun kunyan da wann shashashan d’an naki yai bane.. Kwaise, I’m a highly respected person. A well known businessman. I have a reputation to protect.. Bazan bari wann d’an naki ya ruining d’ina ba.”
Izuwa lokacin cikin ta tunzura itama “Aw laifin Haidar kake gani..? Kai bakaga laifinka ba.. Kan wani dalili zaka cakume kwalan d’anka a bainar mutane.. Cameras all over ba dole masu Neman ganin bayanmu suyi amfani da wann damar ba.. Yanzu sai ka yarda da maganan Haidar da yace maka akwai mai maka zagon k’asa cikin mutanen da ka aminta dasu..”
Katseta yai cikin b’acin rai “This is natural in a business world. We’ve business rivals and competitors. So ba abin mamaki bane idan sunada spy cikin Kampaninmu.. Amma babban abun takaicin shine yanda muka gaza handling such situations.. And this is all your Son’s fault.. He’s weak, idiot.. A pathetic loser.. Yana can ya saka mata a ransa.. What do you expect..?”
Ya kuma jinjina Kai yana sakin huci sai yarfe gumi yake kai kace ba sanyin AC ne ke circulating cikin parlorn ba.
Isowar Haidar k’ofan gidan mahaifin nasa yai tozali da dandatson ‘yan jarida. Ai kuwa kaman jira suke suka nufosa suna jefo masa tambayoyi ta ko ina. “Yallab’ai Aliyu. Da gaske ne mahaifinka ya tareka da fad’a bayan cecekuce da ya kaure tsakaninku cikin Kampanin mahaifin naka..? Engr Maitama ka amsa mana..”
Da kyar ya samu ya kutsa cikin gidan sabida tambayoyi da kalaman da manema labaren keta jefo masa.
Yana dosowa parlorn Daddy ya nufesa a zafafe kaman zai shak’o sa Mommy tai saurin shiga tsakani cikin k’ok’arin dannar mijinta.
Sosai yake huci kaman zai kifa k’asa yana nuni da Haidar hannunsa har rawa yake.
“You.. You and your entire existence is a disappointment..! Kai kayi kad’an ka lalata mun suna da sunan Company.. You better find a way to fix this mess kafin business rivals d’inmu su samu abun yawo damu kaji na fad’a maka.. Bazan tab’a bari bak’in cikinka yayi ajalina ba.. I will make sure to cut you off kafin hakan ta kasance..” Yatsanshi na rawa yaci gaba da nuna Haidar “So Kar ka sake kayi abinda zaisa na haramta maka amfani da sunana..!” Daga haka sa Kai yai ya haura sama dan a halin yau fita ma bai ganshi ba ‘Yan jaridu ta ko ina. Dan yasan K’iris abokan adawansu na kasuwanci Ke jira. Har yayi step biyu ya kuma juyo ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sukai jazir “Kaje ka sallami mutanen can da ka tara mun kof’ar gida.!” Yasa kai yaci gaba da haurawa.
Furzar da huci Haidar yai yasa kai zai shige. Dan yasan mahaifinsa bazai tab’a sauraransa ba. Momy ta dakatar dashi
“Mom please not now.!” Ya katseta da fad’in haka.
Cikin rawar murya take furta “What’s wrong with you Haidar.. Why are you doing this to us to yourself.. Meyasa ka maida iyayenka Abokan gabanka.. Why can’t you open your eyes and see my son.. Your Dad is only trying and struggling to make a proper man out of you..”
“Oh really Mom.! Is he really trying to make me become a better person by pressuring me to meet all his expectations..?” Muryarsa ya soma rawa sanda yake furta “Na gaji.. Na gaji.. I’m fed up with everything around here..!” Bai kuma tsayawa sauraronta ba yasa kai ya fice yana haki da huci ga wayarsa da ta gaza yin Shiru. Kira ne keta shigo masa.
Saiga Mommy ta koma gefe tana hawaye. Meke faruwa da rayuwar ahalinta.. Meke damun Haidar.. Dik yanda akai something is wrong a wani wajen.. Zama bai ganta ya zama dole ta tashi tsaye. Da wann tunanin ta nufi nata b’angaren duk jikinta a mace kaman dai ba Mommy ba. Mace mai zafi da jajircewa.
Jiki a sanyaye Anisa ta k’araso rik’eda waya ta mik’a ma Mommyn tana fad’in “Ammi Ke son magana dake tana ta kiran wayarki bata samu.”
Mommy tana amsar wayar ya fashe da kuka tana fad’in “Asshe ba lafiya.. Asshe gidana a hargitse yake..”
Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa ‘yan uwan waje su tattauna. Sosai hankalinta ya tashi da ganin yanayin Mommy dan tinda take bata tab’a ganin ‘Yaruwar mahaifiyar nata cikin irin wann yanayi ba.
**
KANO
K’aton parlor ne mai d’aukeda kekunan d’inki kusan guda biyar. Yafi kama da wajen koyon d’inki.
Wata mata ce da ta d’an data a shekare tsaye cikin babban zauren tana duba kekunan.
Ummulkhairy ce ta soma halarta cikin d’aliban nata. Dama ita d’in da wuri take zuwa kafin lokaci yayi dan ta taimaka da share share da gyare gyare.
Sallama saman bakinta ta shigo.
Matar ta fad’ad’a murmushinta “Wa’slaikissalam uwar alkhairi. Dan haka take kiran Ummul d’in a akasarin lokuta.
Ummulkhairy ta risina ta gaidata. Ta amsa kaman ko yaushe da sakin fuska “Uwar alkhairi kece dai kullum akan gaba kina masu wayo kina kwashe ladan. Wataran bazaki huta ba.. Jiki da jini Ummul kink’i ayi maku roster da kowa tasan ranan nata aikin.”
Ta murmusa “Hajja ai nafi son na tara ladan da albarkan ni kad’ai ne..”
Hajja Fannah ta murmusa “Ai kuwa da izinin Allah albarka na bibiye dake.. Kinci sunanki uwar alkhairi..”
Murmusawa ta d’anyi kad’an jikinta na kuma yin sanyi da kalaman Hajja sakamakon tuno tashin hankalin da ta baro a gida. Ta mik’e da sauri gudun kar Hajja ta fahimci yanayinta ta d’auko tsintsiya zata soma shara Hajja da tuni ta karanci yanayinta ta dakatar da ita.
“Zo nan Ummul, zo ki zauna magana zamuyi kafin sauran d’aliban su k’araso. Bar sharan nan.” Tai mata nuni da gefenta saman tabarma.
Jiki a sanyaye Ummulkhairi ta isa ta zauna.
Hajja ta gyara zamanta “Fad’a mun me Ya faru.?” Hajja Fannah ta jefo mata tambayar dan dama tana sane da halinda Ummul d’in ke ciki. Gidanta na bayan layin su Ummul layin da ke babban kwalta. Hajja Fannah tanada shagon d’inki da yara maza masu d’inki a shagon ta dake gaban gidan nata yayinda take koyar da ‘yanmata sana’ar d’inkin a cikin gidanta. Sunyi sabo mai tsafta da Ummul tin sanda ta soma koyon d’inki wajenta. Tana bata shawarwari had’ida kwantar mata da hankali hakan yasa Ummul ke samun sanyi wajenta, takan kai mata damuwarta su zauna su tattauna ta kuma bata shawarwari masu amfani a gareta had’ida nitsa zuciya.
Ummul ta d’an share hawayen da suka gangaro mata “Hajja wllhi na gaji.. Harga Allah na gaji.. Ita fah Umma ko wanne irin mutum so take na aura babu ruwan ta ko ina san wann mutumin ko bana so.. Ita burinta kawai nai aure da farin ciki ko babu. Ni kuma a halin yanzu wllhi batun auren nan ya fita kaina ni sana’ar nan da nake nafi samun kwamciyar hankali cikinsa fiyeda komai. Shin wai ita mace ba’a mata uzuri ne a rayuwar nan..? Hajja ba biye biyen maza nake ba.. Allah shine sbiadana ina k’ok’arin tsare mutuncina.. Sann azumin litinin da Alhamis duk basa wuceni ba wai dan na Gaza rik’e kaina ba sai dan sabida nasan shi azumi garkuwa ne Hajja.. Amma ita Umma duk fah bata ganin wann. Ita kawai damuwarta mutane da abinda suke Fad’i.. Shin Hajja menene laifin wacce Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure..?” Ta k’arashe damuwa fal fuskarta hawaye na kuma gangaro mata.
Girgiza kai kad’an Hajja Fanna tai, cikeda tausayi. Ta kuma gyara zama tana duban Ummulkhairy “Ummul, shi fah d’an Adam a koda yaushe bai rasa abin Fad’i.. Sann har abada bazaka tab’a Iyar masa ba.. Mutum sai Allah..” Ta kuma gyara zamanta “Wato muna cikin wani irin Al’umma ne da k’addararka take iya zama zunubi a gareka.. Mai nake nufi da k’addararka tana zama zunubi a gareka? Macece Allah zai jarabceta da JINKIRIN aure sai kiji mutane suna cecekucen cewa ta zauna a gida tak’i aure. Idan wacce take karatu ne sai kiji ance ta rungumi boko tak’i aure.. Idan ma Sana’a take dan ta rufa ma kanta asiri sai kiji ana cewa maza ke bata kud’i ta Kama Sana’a ne dan ya zame mata garkuwa kar a zargeta.. Ita dai mace wai bazata rayu ba saida tallafin namiji. Mace ce Allah zai jarabceta da mutuwar aure sai kiji ana cewa ta kashe aurenta ta dawo gida bazaki tab’a Jin ance miji ya kashe mata aure ba sai k’alilan a’a itace dai Sarkin laifi. Kuma babban abin takaicin mutanen da tafi kusanci dasu Sune mutanen da take soma fuskantar k’alubale daga wajensu. Kowa sai ya tsangwameta a cikin gidan baga iyayenta ba baga ‘yanuwanta ba a wasu lokutan. Kinga a nan k’addararta ya zama kuskurenta.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Ummul ba ina fad’a Miki haka bane dan kiga laifin iyayenki ko wani abu mai Kama da haka. A’a ko d’aya, burin ko wasu iyaye shine da zaran ‘yarsu ta isa aure su ganta a d’akin mijinta. Kuma babu iyayen da zasu so suga auren ‘yarsu ya Mutu. Toh amma idan jarabawan Ubangiji ya shigo ciki sai ayi hak’uri a fawwala masa lamuran. Ka tsara rayuwarka yanda kake burin Ubangiji ya tafiyar maka da ita tareda fatan mafarkan ka su cika ba laifi bane hasalima Wanda baya planning rayuwarsa baisan ina ya dosa a rayuwar ba. Toh amma wasu lokutan yanda muka tsara ba haka rayuwar take zuwa mana ba. Dalili kuwa shine ba muke da hakkin tsara rayuwar ba iyakacin namu mafarkai da burika had’ida fata na gari. Ubangijin duka shike tsara mana rayuwar yanda yaso. Kuma tsarinsa a koda Yaushe shine daidai. Idan ya amsa mana addu’anmu ya tabbatar mana da burinmu da fatanmu sai muyi farin ciki mu kuma gode masa. Sann idan ya jarabcemu ya janye wann fata daga garemu bamu samu abinda muke mafarki da buri ba shima sai mu masa godiya sabida shi yasan abinda yasa ya hana mu kodai abin mai cutarwa ne a garemu. Ko kuma ya mana tanadin Wanda yafi wann.” Ta kamo hannun Ummulkhairy cikin nata “In every delay, I believe there’s khayr.. Just like your name Uwar alkhairi. In sha Allahu JINKIRINki zai zamto cikeda d’imbin alkhairi.. Babban abinda zan Miki wasiya dashi shine biyayya ma iyaye. Kar ki kuskura koda wasa ki fasa musu biyayya matuk’a bazasu ce ki sab’i mahaliccinki ba.. Idan kika rik’e biyayyan iyaye alkawarin Allah ne rayuwarki zai cika da d’imbin alkhairi kinji ko..”
Ummulkhairy ta jinjina mata Kai a hankali kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta. Hak’ik’a tana samun relief da kalaman Hajja Fannah. Inama Ummanta zata kasance mai fahimta kamar haka. Sallaman wasu daga cikin d’aliban yasata k’ok’arin saita kanta Hajjah Fannah na fad’in ta kwantar da hankalinta komai zai shige ya zama tarihi da izinin Allah. Ta mik’e tana amsa gaisuwan ‘Yanmatan da suka shigo tana fad’in yau dai Ummul d’inta zata huta Sune zasuyi shara su gyara waje.
Daga can bakin Layi Alhaji Kamilu Ya aje motarsa Mama na biye dashi tana fad’in “Kai dai muje ka bama idonka abinci Alhaji.”
SameenaAleeyou📚
