AUREN WATA UKU..!*
*07*
©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba “Sai kinyi ajalina da bak’in ciki kiji dad’i. A sau nawa zan miki iyaka da wann gidan amma kin rantse sai kin tona min asiri Ummul. Me kike nema ki zama ne wai.!” Ta karashe tana fashewa da kuka.
Hajja Fannah wacce tun shigowar Umma ta sallami sauran ‘yan ajinta dakatar da Umma tai fad’in “Haba Umman Ummul ya kike kausasa harahenki akan ‘yarki. Shin baki san fushinki mai tasiri ne akanta koda baki nuna ba. Ke fah uwa ce kuma za’a tsai dake a tambayeki gameda kiwon da aka baki. Kaman yanda kikeda hakki akan yaranki haka suma sukeda hakki akanki.. Addini bai barmu kara zube ba face saida ya tsara mana yanda zamu tafiyar da rayuwarmu.. Yanzu islamiya har na matan aure sun yawaita.. Duk wanda kikaga ya zauna da duhun kai shi yaso.”
“Malama dalla ki min shiru ba wa’azi nazo kimin ba… Yo idan ma zan d’auki wa’azi sai na d’auka daga bakin ballagazar mace irinki mai zaman kanta wacce ta kasa zaman aure. Sann da kike maganar a koma makaranta yanzu kai waye kije garinmu kaf ki tambaya waye mahaifina.. D’iyar malamai nike jikan sha rubutu. Ubana Malami ne mai tak’ama da Zauren karatu, na girma ina kwankwad’an ruwan alk’alami da tawada.. Ni har an isa amin gorin ilimi nida na gajeta. Sauk’a uku nayi da k’ananan shekaru kafin a rufani akaini d’akin miji..!” Taci gaba da jijjiga tana nuna Hajja Fannah “Kuma bari kiji na fad’a miki idan ma kece kike ziga Ummul kike burin ki hanata aure kaman yanda ke kika kasa zaman aure toh Allah bazai baki nasara ba. Ummul tun tana ciki aka nema mata tsari da shed’anu irinku. Ko ana ha maza ko ana ha mata Ummul d’ina zatayi aure kaman yanda ko wacce mace mai mutunci keyi ehe..! Ke kuma shige muje kafin na kwashe miki albarka..!” Ta k’arashe tana tasa k’eyar Ummulkhairi wacce da alama ta gama saduda da sha’anin Umma.
Mamaki bai saki Hajja Fannah har suka fice. Gaba d’aya ta gaza katab’us. Ita a halin yanzu ta fara tantama idan Mahaifiyar Ummul na cikin hayyacinta. Girgiza kai tai cikeda tausayin Ummul tana mai ayyanawa lallai tana cikin jarabawa.
**
Khulsum da dawowarta kenan daga makaranta taji k’urin miya na k’una kan wuta duk ya cika gidan. Ga hayak’i na fitowa daga kitchen. Da sauri sauri ta shigo a tunaninta babu kowa ne amma sai ta hangi Mama zaune tsakar gidan tana gyaran k’umbarta.
Bata ce komai tasa kai zata shige muryar Mama ya dakatar da ita “Toh shafaffiya maras kunya. Kin shigo kina kallo na dan rashin mutunci ko sannun fatar baki ta gagareki. Toh ai sai ki shige ki aje jakarki kije ki gaida tukunyar miyan dake k’auri kan wuta idan ba haka ba tuwon dare ya haramceku. Ahtoh dan a banza azumin da ba lada zai hau kanku daga ku har uwarku dan nikam raina guda inada gidajen ‘ya’ya ‘yan albarka da suke kame gidan mazajensu da zasu bani tuwo. Saima gidan da na zab’a naci. Banda asara har yaushe za’a ce manyan budare da suka rik’a suka rik’e a gida ana saka masu kwanon tuwo gidan mahaifinsu. Yo sadaka kuke ci sa’anninku masu mutunci dai suna d’aunansu suna aikin lada suna girka ma mazajensu tuwo.” Ta mik’e tana buge zaninta “Idan Kinga dama kar ki duba miyan girkin uwarki Suwaiba ne dan nikam na gama girka ma k’artai irinku tuwo a gidan nan. Dan dai cikina d’aya da Malam bazai gagara ba. Amma bazai yuwu da girmana a ganni ina zama bakin murhu ina girka ma gandama gandaman ‘yanmata irinku tuwo ba. Daga me yawo da sunan karatu sai mai yawo da sunan koyon san’a..” Tasa kai ta nufi d’aki “Tani ta daina girka ma k’artai tuwo wacce duk tai zuciya cikinku ta tafi nata d’akin mijin ta girka.” Ta k’arashe tana rangad’a gud’a da shewa.
Khulsum ta girgiza kai kurum kafin ta aje jakar makarantarta nan tsakar gidan ta cire hijab ta nufi kitchen d’in. Shigarta keda wuya ta soma jiyo muryar Umma ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.
“Ko labari na sakeji kinje gidan matar can da sunan koyon San’a Ummul saidai ki nemi wata mahaifiyar amma bani Suwaiba ba. Banda salo da fitina ke da ake gab da saka miki rana yo wacce sana’a zaki koya ya wuce zaman aure dake gabanki.”
Da mugun mamaki Khulsum ke duban mahaifiyarsu “Umma.. Yanzu d’an koyon sana’ar ma hanata kikayi. Umma itafa sana’a dogaro da kai ne…”
“Ki rufe mun baki Khulsum, aure shine babban sana’ar dake gaba gareta.. Shine daraja da cikan mutuncin ‘ya mace.”
Khulsum ta saki baki da mamaki “ Umma a wann zamanin da akasarin wasu mazan basu sauk’e nauyin d’awainiyar matansu da Allah ya hukunta masu wann san’ar ba ita zata rufa masu asiri ba. Umma ko za’a baka Shi fah abu naka dad’i ne dashi.”
“Idan bakiyi shiru ba Khulsum zanzo wajen naci miki mutunci.. Hanshak’iya ana fad’a kina fad’a.”
Muryar Mama da fitowarta daga d’aki waya manne kunnenta ya katse Umma. Cikin d’aga murya Mama Ke ci gaba da fad’in “Hellaww ina jinki Badidi na Badi’atu ‘yar albarka.. Wai shi Tasi’un ya kawo miki Kaji kika soye mun.. Kaji D’an albark. lallai Tasi’u ya cika Surki na k’warai.. Allah dai ya maku albarka ya k’ara zaunar daku lafiya a gidajenku ya rabamu da sharrin mahassada masu san ganinmu a rana.”
Kuka ya kuma zuwa ma Umma bata iya sauraron wayar da Mama keyi ba ta shige d’aki.
Ita kuwa Mama tana ganin Umma da yaranta sun shige d’aki ta sauk’e nannauyan ajiyan Zuciya tana datse wayan Badi’a wacce ita kanta Badi’an ta rasa gane wasu surkulle mahaifiyarta Ke mata cikin waya. Ita da take sana’ar da ita irin uk’ubar da Tasi’u Ke bata a ‘yan kwanakin wanda ta gaza jurewa tana ce mata ita ta gaji da auren gida zata dawo sai taji tana mata wasu sunbatu wai Tasi’u ya kawo Kaji a gyare mata.
Mama ta koma d’aki ta kuma danna kiran Badi’a. Kaman jira Badi’a take ta d’aga kiran “Mama wani irin abu ne inace miki Tasi’u ya dawo da hallayansa na baya yau bugun tsiya ya min saida mak’ota suka k’waceni kina kira mun wasu kaji.”
Mama ta yarfe gumi “Ke Badi’a saurareni. Idan Tasi’u tsire naman jikinki yake haka zakiyi hak’uri ki zauna.. Zanzo gidan na sameki nasan yanda zamu b’ullo masa amma koda wasa kar kiyi tunanin dawowa gida.” Daga haka bata kuma tsayawa sauraron Badi’a da tuni ta fashe mata da kuka tana fad’in ita dai ta gaji.
Mama kaw ta mik’e tana tunanin yanda zasu b’ullowa al’amarin Tasu’u mijin Badi’a.
**
Abuja.
Maitama Builders (MB).
Zauren tattaunawar ta cika da ‘yan jarida abinda ya shafi b’angaren kasuwanci. Kowa shirye yake da tambayoyin da zai Engr AA. Maitama yake. Hisham ya shafi goshinsa dan interview d’in zai kasance live ne sakamakon yanda kowa ya k’agu yaji gaskiyar al’amarin bayan video da yai trending a manyan shafuka musamman shafukan watsa labarai na kasuwanci.
Hisham sai kai komo yake yana duba lokaci yana add’uan Allah sa kar Haidar ya badasu. Wann shine kad’ai damarsu ta k’arshe da zata d’aga darajan Kampanin ta kuma wanketa daga daud’an da aka shafa masu.
Masu gabatar da interview sun cire rai da zuwan Haidar. Sun mik’e da zummar tafiya Hisham yai saurin dakatar dasu yana sanar dasu Lallai Haidar zai zo shi.
A can gidan Daddy kuwa suna zaune shida Alhaji Gimba a parlor suna duban live event d’in yanda Daddy Ke girgiza kai. Ko janye idanunsa daga screen bayayi “I told you he’s not capable of anything good..”
Alhaji Gimba ya girgiza kai “Inada yak’ini akanshi, Zai bayyana, kuma zai abinda ya dace.. Na tabbata bazai bamu kunya ba.”
Daddy ya soma k’ok’arin mik’ewa da zummar haurawa sama yana furta “This is a complete waste of time Gimba. Ni zan shige ciki..”
Alhaji Gimba yai saurin dakatar dashi “A’a Abokina.. D’an Dakata, kalli nan..!” Yai masa nuni da screen yanda aka hasko Haidar yana k’arasowa cikin hall d’in. Yayi kyau cikin shiga irinta cikakkun ‘yan kasuwa masu huld’a ciki da wajen k’asa. K’warjininsa ya cika wajen.
Bakin Alhaji Gimba ya gaza rufuwa sabida farin ciki.
Daddy ya jinjina Kai “I hope it doesn’t turn out to be another scandal.” Ya fad’i idanunsa akan Haidar da ake haskowa.
A can Company Hisham ya murmusa yana duban abokin nasa harda d’aga masa yatsa guda alamun jinjina. Wani duba Haidar ya aika masa kafin ya wuce yanda aka tanadar masa domin zama.
Yana k’arasawa mai gabatarwan ya mik’e had’ida mik’a masa hannu sukai misabiha kafin Haidar ya gyara zaman suit d’insa ya Zauna attentively.
Nan da nan aka soma gudanar da interview d’in. Yana jefo ma Haidar tambaya yana amsa sa daki daki cikeda k’warewa da sanin aikinsa nan ya jefa floor ma audiences wani ya d’aga hannu ya soma jefo ma Haidar nasa tambayar “Yallab’ai, munga wani hoto na yawo a kafafen sadarwa har wani gidan jarida ya wallafa wani labari cewa fad’a ya kaure tsakaninka da mahaifinka sabida gazawarka da kuma banbancin ra’ayi da kuke dashi. Shin menene gaskiyan al’amarin..?”.
Haidar ya kafesa da idanu kafin yai clearing throat d’insa.
“A ko wace ma’aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra’ayi tsakanin shugaba da ma’aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet..”
Babu wanda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination.
Mutumin ya jinjina kai “So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?”
Haidar yai masa k’uri dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d’an had’e waje guda “I’m not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn’t make me different from others. If I don’t receive any VIP treatment it’s because that’s the company’s policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges.”
Ya kuma jinjina kai. “One more question Engr. “Is it true that your company is going bankrupt.. And the economy is at the state of crisis.?”
Haidar ya d’an rage girman idanunsa kad’an yana duban mutumin, lokeci guda ya d’an gyara zaman suit d’insa “Let’s call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assure you, MB (Maitama Builders) does not… and will never fear challenges..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik’e yana mai mik’awa Haidar d’in hannu alamun musabiha “Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade.
Alhaji Gimba ya dubi Daddy “Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I’m super optimistic about him.”
Daddy dai baice komai saima mik’ewa da yake k’ok’arinyi.
Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d’a irin Haidar Wanda yake d’aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d’aure masa kai yanaji inama nasa d’an ya kasance kaman Haidar.
**
Hisham ya kuma duban Haidar had’ida girgiza kai “Ban fahimceka ba Haidar.”
“Meye baka fahimta ba..?” Haidar yace yana duban Hisham d’in.
D’an gyara tsayuwarsa Hisham yai “Kanaso kace min gadar zare yaso k’ulla maka da ya shirya wann interview d’in..? Kanaso kace min ya shirya hakan ne just for you to fall into his trap and create more scandals.? Kana so kace min shi kake zargi da yi ma Kampani zagon k’asa.?”
“He gave me all the reasons to suspect him.”
Hisham ya kuma jinjina Kai “Amma zanji mamaki idan haka ya kasance duba da kusancin shi da mahaifinka.. So what are you planning now..?”
“Of course I’ll play his little game. Shiyasa ma na halarci interview d’in.” Ya k’arshe yana k’ok’arin mik’ewa.
Hisham ma ya mik’e suka soma takawa.
“If that’s the case, I’ll support you Haidar har gaskiya ta bayyana.”
Ba tareda ya dubi Hisham ba yace “I’d rather do it alone. This is my battle and I’ll fight it alone.. I’ll make my Dad swallow all his words a lokacin da zan kamo wuyan mutumin da ya aminta dashi matsayin babban mak’iyinsa. Each and every insult da ya jefeni dashi sai na sashi ya cinye kalamansa. And hakan zai faru ne kawai idan ya d’aurani Akan project d’in nan. So I’ll do whatever it takes to make sure ya mallaka min ragamar wann project din.”
Hisham yai still yana duban Haidar d’in “Haidar kana magana kaman fansa kake so akan mahaifinka. Haidar.. Anya lafiya kake.. Mahaifi fah ya wuce wasa.?”
“Wani mahaifin kenan.. Amma wani suna ya tara..!” Yana ida fad’in haka ya bud’e motarsa ya shige.
Har ya bace ma ganin Hisham bai daina mamaki ba. Al’amarin Haidar da mahaifinsa ya soma zarce tunaninsa.
***
Kano.
Tinda Abba ya shigo gidan hannunsa na hagu ke dafe da b’angaren k’irjinsa. Ya kuma duban Umma dake zaune gefensa ta rapka uban tagumi tana masa sannu.
Ya amsa yana mai gyara zamansa bayan yasha maganin da ta kawo masa.
Saida ya daidaita zamansa sosai kafin Ya soma magana “Suwaiba” Ya kirawo sunanta.
“Na’am Abban Ummul.” Ta amsa duk jiki a mace ganin yanayin Abban.
Abba yaci gaba “Magana nake so muyi amma ina so ki kwantar da hankalinki.”
“Toh Abban Ummul.. In sha Allah zan kwantar da hankalina.. Nidai burina ka samu lafiya..”
Abba ya d’an b’ata lokaci kad’an kafin yace “Ai na sanar dake yanda mukai da manemin auren Ummulkhairy. Wato Alhaji Kamilu mak’ocina a kasuwa.”
Umma ta jinjina kai “Eh kwarai anyi haka..”
Abba ya kuma jinjina kai “Wato Suwaiba bayan shi Alhaji Kamilu yazo yaga Ummul kwanaki uku da suka shige. Washe gari da safe kaman yanda kika sani sun taho har nan k’ofar gidana shi da wani abokinsa sun bada sadaki.. Alhaji Kamilu ya bada sadaki naira dubu d’ari a matsayin sadakin ita Ummulkhairy lakadan”
Umma kam tsaban farin ciki bata tsaya taji k’arshen zance ba ta shiga gud’a tana fad’in Ummul dinta tayi goshi ‘yan bak’in ciki saidai su Mutu.
Abba ya lumshe idanunsa kad’an yana jin zafin k’irjinsa na k’aruwa. Daurewa yai ya d’an bud’e murya yai mata tsawa kad’an data saurare shi.
Umma ta kuma wahse baki tana gyara zama “Yi hakuri Abban Ummul.. Farin ciki na ne ya gaza b’uya. Ummul d’ina lokaci yayi. Ai ni dama tin a nan wajen ka kirawo yan uwanka a nan cikin gida suka zama shaidu aka d’aura.”
“Suwaiba ki dubi girman Allah ki saurareni.” Ya kuma fad’i cikin tsarewa.
Ta saka hannayenta biyu ta kame bakinta “Na tuba.. Nayi shiru Abban Ummul.. Ina sauraronka yaushe suka nema a saka lokacin biki..? Ni wllhi na ma basu wuk’a da nama su saka ko gobe ne.”
Abba ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana girgiza kai kafin yaci gaba “Toh kinsan kwanakin baya kasuwa ta d’an ja mun baya har na amso bashin hatsi a nan cikin kasuwa..”
Jikin Umma ya soma sanyi amma sai tace “Kasan mutane yanzu idan Sun bika bashi sunyita korortoto kenan kai kace duniya ka amsa wajensu.. Su kwantar da hankulansu lokacin biyansu yayi in sha Allah..”
“Ki saurare ni Suwaiba.”
“Toh Ina sauraronka Abban Ummul..” Tace tana gyara zamanta.
Abba yaci gaba “Toh shekaran jiyan da suka kawo sadakin sai shi Wanda yake bina bashin hatsi Ya taho mun da buk’atan kudinsa. Lallai Lallai shima yana neman kudinsa zai amfani dasu. Kuma nima nasan yanda Kasuwa ta koma a halin yanzu. Wasu lokutan Har ka fita ka dawo ba’a zuwa saye. Godiyan Ubangiji ne kawai amma al’amarin k’asar sai addu’a. Hakan yasa na d’auka cikin sadakin Ummulkhairy na biya tinda gadarana sadakin ‘yatace. Banida hanyan biya sai wann sadakin. Na cira ciki na biya.. Yau kwatsam da naje Kasuwa Alhaji Kamilu ya tareni da batu mai tada hankali.”
Ai bai kai aya ba Umma ta soma girgiza kai tana fad’in “Dan Allah. Dan tsarkin mulkinsa da buwayarsa Abban Ummul ka rufa mun asiri ka mun sutura.. Kar kace min shima ya amshe sadakinsa.. Wayyo ni Suwaiba na shiga uku na Mutu na lalace..”
Abba ya kifa kansa yana girgizawa yana jin yanda Umma ke fad’in ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Takaici da ya cika shi ganin tak’i sauraronsa sai kuka take tana jefa kanta a uku. Abba yace “Aima baki gama jefa kanki a uku ba Suwaiba sai kinji irin wulak’anci da kwance zanin da bawan Allahn nan ya mun a cikin kasuwa.!”
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa hannayenta duka biyu dafe da k’irji yayinda Abba yaci gaba da fad’in “Tinda nake a rayuwata ba’a tab’a min irin tozarci da wulak’ancin da bawan Allahn nan ya min ba. Suwaiba, Alhaji Kamilu dai ya amshe sadakinsa ba yanda banyi ba ya bini bashin sauran kud’ad’ensa amma sai cewa yai bazai iya jira ba dan haka yasa yaran shagonsa suka kwaso kaya a nawa shagon darajan kud’ad’ensa makotanmu a kasuwa masu burin su ganmu a rana duk suna kallo. Wann wulak’anci da mai yai kama Suwaiba..”
Kukan Umma ya k’aru mik’ewa tai ta fice tana rera kuka tana fad’in Ummul zatayi ajalinta.
Daga Ummulkhairy har Khulsum a tsorace suka nufo waje jin Umma na ambaton zata fad’a rijiya.
SameenaAleeyou📚
