Auren Wata Uku page 5 by Sameena Aleeyou - Abokiyar Hira Novels


AUREN WATA UKU..!*

*06*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*


K’ofan gidan Hajja Fannah Mama ke nuna masa “Yauwa Alhaji. Nasan Kai mutumin kirki ne. Ance matanka ma ko fita unguwa basayi tsaban yanda kake kaffa kaffa da iyalanka. Toh kaga can yanda kaga mata da maza suna safa da marwa.”


Alhaji Kamilu ya kuma duba k’ofan gidan wanda shaguna suka saka a tsakiya ga samari sai kai komo suke tsakanin shagunan can gefe harda shagon aski ga ‘yanmata masu sana’an koyon d’inki suna Kutsawa suna shiga gidan Hajja Fannah.


Mama taci gaba “Toh wann gida dai dake gani Ummul tana ciki da ita ake wann kai komo tsakanin wad’ancan samari marassa tarbiya masu aski irin na shed’an.” Idanun Alhaji Kamilu ya sauk’a samarin da Mama Ke nuni dasu wanda suka fito shagon Aski gana ganinsu kaga samari marassa tarbiya ga wani aski da aka musu an kwashe gefe d’aya an bar d’aya. D’aya saurayin ma harda sark’a a wuyansa. 


Alhaji Kamilu yai Shiru kaman mai nazari. Sai kuma yace “Da zaran na aureta ta dena fita ko k’ofa dan mata na ko taron biki da suna basa zuwa babu yanda suke zuwa sai asibiti da ya zama dole.”


Mama tai ‘yar bazaurar murmushi “Toh ai Alhaji ba a nan gizo Ke sak’an ba.” Ta kuma gyara tsayuwarta “Kaga wann gida da Ummul Ke zuwa da sunan koyon Sana’a. Matar gidan ba kowa bace face gasunk’umar kawaliya. Wllhi nake fad’a maka Alhaji ta addabi kowa ta fitini kowa a unguwar nan. Mata take tarawa cikin gidanta maza kuma suna daga waje a shago. Maza take had’awa waje mata kuma cikin gidan ayita aikata masha’a ana aikata alfasha. Kuma ba zallan ‘yanmata harda matan aure a wann bad’ala da take had’awa. Na tabbata bazaka so ka auri yarinyar da ta gama watsewa wajen wann hatsabibiyar Matar  wacce ko aure bata dashi zaman kanta take zaman daduro.. Wann shago da koyar da sana’a da take cikin gidanta ba komai bane face rufa rufa gudun idon mutane. Amma mu da mukaga jiya mukaga yau a unguwar kowa ya kwana da sanin Kawaliya ce. Amma idan baka aminta da abinda nake fad’a maka ba zaka iya tare mutanen unguwar nan ka tambaya Kaji idan ba zaman kanta take ba. Ko aure bata dashi babbar Magajiyar karuwaice. Kaf ‘yanmata da matan aure dake zuwa wajenta da sunan koyon sana’a, karuwanci suke fitowa su fake da san’a. Meyasa Ummul tak’i aure..? Kai bakai ma kanka wann tambayar ba. Mace har mace kyakkyawa irin Ummulkhairy ta gaza samun mijin da zai aureta.. Ai kaima kasan da walakin wai goro a miya.”


Ganin Alhaji Kamilu ya kifa kansa had’ida maida hannayensa baya irin yanda manya suke idan suna tunani yasa Mama ci gaba “Ni wllhi ganin mutuncinka ne kuma ganin Malam zai yaudareka ya lik’a maka ‘yarsa da ta gama yawon ta zubar a kororo yasa nai wann shahadar nace bari dai na sanar dakai gaskiya ka gane dalilin da Ke sa ko wani namiji mai kamala da mutunci Ke guje ma aurenta. Malam bai dubi amanar dake tsakaninku ba. Ba kalan suturan da baka masa ba amma ya zab’i ya maka lumbu lumbu dan dai kawai shima ya rabu da alk’ak’ai.. Yo shima ya gaji da ita.” 


Birki tai da kalamanta ganin Hajja Fannah ta fito biyeda ita Ummulkhairi ce rik’e da kayan d’inki suka shige shagon d’inki ga wani matashi ya fito daga cikin shagon ya gifta ta gefen Ummulkhairi. 


Mama tai kabbara tana hamdala “Ka gani ko.. Ka tabbata ba sharri nake ba. Wai ance gani ya kori ji.. Kana nan kanata rawar k’afa zaka angwance toh aikin banza kake wai rufin d’aki da b’arawo dan k’artai bila adadi sun rigaka..” Ta numfasa had’ida gyaran murya “Toh Alhaji ni na gama nawa, Allah ya gani na fita na sanar dakai. Kuma ka gani ma idanunka. Ya rage maka ka amince ka sai ma kanka da iyalanka tikitin mutuwa dan k’anjamau ne zai maku sallama. Ka  taimaki kanka kaman yanda saura suka taimaki kawunansu. Ni na Barka lafiya Alhaji..” 


Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige zuciyarta fari tas. 


Alhaji Kamilu kuwa sai kallon k’ofan shagon yake yana jira yaga ko Ummulkhairi zata fito amma shiru. Zuciyarsa sai tafarfasa take haka yaja k’afafunsa yana sab’a babbar rigarsa da take  ‘yar duk’unaso ya nufi motarsa. 

**


Mama tana shigowa gidan ta cire mayafi ta soma zuba ruwan bala’i 


“Iyi.. Kan wani dalili za’a tare ni a hanya ana mun cin mutunci kan laifin da banji ba ban gani ba.. Babu wanda ya huta a gidan nan duk akan rai guda.. Baga yarana dake gidan mazajensu ba yanzu abun har ya tsallako kaina… Toh wllhi bazan d’auki cin mutunci daga kowa ba kan ‘yar da ban haifa ba..!”


Umma ta fito daga kitchen afujajan tana goge idanunta da hayak’i ya sanya mata su hawaye “Yaya lafiya.. Meke faruwa..? Wani abu ne aka miki..?”


Mama taci gaba da tururi “Yo uban meye ma ba’a mun ba.. Gashi can Alhaji Kamilu yake ko ya tareni a hanya ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba saikace alhakin tarbiyan Ummul a hannuna yake.!” 


Cikin Umma ya bada wani irin sauti k’uuuu “Wani abu ne Ummul d’in tayi Yaya.?”


“Meye kuwa batayi ba bayan ganinta a gidan Matar nan da yayi wacce kowa ya kwana da sanin Gasunk’umar magajiyar karuwai ce.. Ai bansan shashashancinki ya kai har haka ba Suwaiba.. Ni na zata da kika samu wanda zai rufa ma Ummul asiri ya aureta kinyi mata iyaka da gidan wann Kawaliyar mai zaman kanta ashe saketa kikai kamar tinkiya tana ci gaba da zuwa.. Yo a haka ne kike buri da fata ta samu mijin aure bayan kowa ya kwana da sanin ga hark’ar da Matar take d’aura ‘yanmata. Ai gashi can Alhaji Kamilu dik yanda akai yaji daga bakin mutane.  ya tareni yana sanar dani dama munsan ‘yar mu yawon ta zubar take waye ya mutu waye tashi..” Ta kafe Umma da tuni duniya ya shiga juya mata kafin taci gaba “ Bari kiji Suwaiba nidai ban haifi Karuwa ba Allah ya gani ehe..!” Ta k’arashe tana mai shigewa fuuu. 


Umma ta soma girgiza kai tana dafe kai ta shiga bin bayan mama tana “Na shiga uku ni Suwaiba..! Yaya kar kiga laifina.. Wllhi laifin Malam ne na mata iyaka da wann koyon san’a amma shi ya k’yaleta yace dole ya koyi san’a tinda ba karatun take ba.. Amma anyi na farko anyi na k’arshe bazan bari Ummul ta kuma jaza mun ba..!” Ta k’arashe tana zaran mayafinta. Ta nufi waje a fujajan. 


Mama ta bud’e murya tana fad’in “Miyar tuwonki fah.. zai k’one..”


“Yaya ki rik’e min ni nayi nan..!” Ta fad’i takalma a hannu ta nufi waje kaman zata tashi sama.


Tana ficewa Mama ta kece da wata irin muguwar dariya. Har ga Allah shashancin Suwaiba na saka ta nishad’i. Wai Malam ya rasa da wa zai had’ata su goga a kishi saida wann shashasha ballagaza lamba d’aya wacce sam wayau da hankali basu isheta ba. Indai kishiya irin Suwaiba ne a kawo mata gomansu ma. Ta kuma kecewa da dariya tana kwaikwayon gudun Umma takalma a hannu. Ta bud’e murya tana fad’in “Kiyi a hankali dai kar ki fad’i ayi haihuwar guzuma uwa kwance ‘ya kwance.” 



**



Abuja.




Hisham ya kuma girgiza kansa a karo na biyu yana duban Haidar dake zaune calmly kaman babu abinda Ke faruwa saima d’an tapping table din dake gaba garesu da yake da yatsarsa guda fuskarsa na duban wani b’angaren. 


“Haidar kamata yai muyi suing news outlet da sukai publishing labarin nan for defamation of name..” 


Kaikaitowa yai yana duban Hisham, ya d’anyi still kafin ya girgiza kai “Seriously Hisham..Are we going to waste our time going against the media..?” Ya d’an girgiza kai “Don’t you  think we should focus on finding the traitor that leaked the video..?”


Hisham ya d’anyi Shiru kaman mai nazari. Sai kuma ya jinina kai “Yeah you are right.. Gaskiyanka ne fad’a da media ba riba.. Wann b’eran na cikin company zamu kama sai ya sanar damu wanene uban gidansa. And I’m pretty sure shine wanda ya fitar mana da bayanan sirri na company.” Rufe bakin Hisham keda wuya wayarsa ta soma ruri. Daga Company ake kiransa.


Hisham ya d’aga suna gaisa nan ya fahimci aminin mahaifin Haidar ne Alhaji Gimba mai kiran. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko suna tareda Haidar.


Saida ya dubi Haidar d’in wanda hankalinsa ya koma kan wayar salular salulansa kafin ya d’an matsa gefe ya sanar dashi eh suna tare. Magana suka d’anyi na lokaci kafin daga bisani sukai sallama. 


Hisham ya dawo wajen zamansa ya zauna yana tunanin ta yanda zai soma sanar da Haidar abinda Alhaji Gimba ya sanar dashi. 


“That was Alhaji Gimba. One of the board of directors.. Aminin Dad..”


Haidar ya murmusa da gefen bakinsa kad’an jin yanda Hisham Ke masa bayanin mutumin da ya masa farin sani “What’s with the introduction..?” Yai maganar yana tsare  Hisham da idanu. 


Hisham ya gyara zamansa cikin kujeran “He called to say ya shirya maka interview with the media tomorrow by 10am at the company.” 


Haidar ya kuma murmursawa da gefen bakinsa irin na Wanda takaici ya gama cikasa yana mai girgiza kai  “Unbelievable.!” Ya furta a hankali. Yanzu ba Daddy kawai ba even his friends suna intruding cikin rayuwarsa.


“Kan wani dalili zai shirya mun interview ba da sani ba..?” 


Ya mik’e tsaye yana nuna Hisham d’in “Look, you call that man right this instant and tell him I’m not attending.!”



Hisham ya girgiza kai had’ida furzar da huci kad’an yasan halin abokin nasa yasan kayansa hakan dama zai kasance. Shima d’in mik’ewa tsaye yai “Of course you are attending..” 


Haida ya dubesa da mamaki “Amma kaji yanda kake min magana..?” 


Hisham ya kuma furzar da huci “Haidar he’s only trying to help here.”


“Did I ask for his help..?!” Ya katse Hisham a fusace. 


“But..”


“Bana buk’atar taimakon kowa.. And Much less from him.!” Ya k’arashe yana mai buga table d’in da hannunsa. Lokaci guda yasa kai zai shige. 


Hisham yai saurin dakatar dashi “Haidar this is the only way to save…”


“The Company’s image, right.?” Haidar ya katsesa da fad’in haka.



“No.. I mean to fix this.. Ina nufin ya shafi sunan mahaifinka Haidar.. Harma da ahalinka.”


“Oh c’mon.! What family.. Wani ahali kake magana..? Kafi kowa sanin banida wani ahali.”


Hisham ya d’anyi still “Haidar kullum ina fad’a maka ba’a fad’a da iyaye a zauna lafiya..”


“Oh shut up.!” Ya fad’i yana mai nufan motarsa.


Hisham ya furzar da huci kad’an yana mai take masa baya yake ci gaba da fad’in “Haidar kai kad’ai kafi cancanta ka jagoranci project d’in nan.. You work so hard to get to where you are now.. Bazaka bari all your efforts and hardworking su tafi a banza ba.. I know you so well, you don’t surrender. You just need a minute to cool off..” 


Kaman dai badashi yake maganar ba haka yaba ma banza ajiyarsa ya isa ga motarsa cikin sassarfa. 


Daidai sanda Haidar ke tada motar  Hisham ya bud’e murya yana fad’in “10am tomorrow at the company.” Yai maganar cikin d’aga murya dan tuni Haidar yaja motarsa ya bar wajen.


Hisham ya girgiza kai kad’an dafe da kunkuminsa yabi bayan motar Haidar d’in da kallo. Yasan ba lallai Haidar ya halarci wann interview d’in sanin wanene abokin nasa. 


Yana tafe cikin mota yana kuma nazarin abun. Wai Alhaji Gimba ya shirya masa tattaunawa da ‘Yan jarida. How could he..! Ta yaya zai yanke babban hukunci haka ba tareda ya tuntub’e shi ba. Akan me za’a sakashi magana da media ba tareda amincewa da yardarsa ba. Duk ma ba wann ba since day one bai k’aunar mutumin sabida k’ok’arin shiga rayuwarsa musamman tsakaninsa da mahaifinsa da yake. Ya tsani a shiga rayuwarsa without an invitation. Idan bai gayyaceka cikin rayuwarsa ba kawai kar ka shiga. Ya furzar da huci a hankali yana so ya gano wani abun. 

**

Kano.



Banda sautin keken d’inki dake tashi cikin zauren baka iya sauraron komai. Ko wacce ta bada hankali da himma wajen ganin ta zama k’wararriya a sana’ar da suke koyo. Kaman daga sama suka soma jiyo kururuwa na nufosu. 


Gaban Ummulkhairi ya yanke ya fad’i. Cak ta dakata da abinda take tana mai furtawa a hankali “Umma..!”






SameenaAleeyou📚


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post