Auren Wata Uku page 11 Complete Na Sameena Aleeyou


AUREN WATA UKU.!*


*11*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Mommy da Asshe suka dubin juna cikin k’ullewan kai.


“Malam sharud’a kuma.. Wasu irin sharud’a kenan..? Sann Kaman ya AUREN WATA UKU.?” Asshe ta tambaya tana dubansa.

Ya kuma d’auko wasu layu da guru ya jera saman layin da ya shata akan farantin. Ya k’irga carbin dake hannunsa yace Mommy ta kama ta zab’i guda d’aya. 

Mommy ta d’an juyo tana duban Asshe a d’an tsorace. Asshe ta jinjina mata kai alamun tai yanda yace. Hannu na rawa Mommy tasa ta kama guda d’aya. Ya kamo daidai yanda Mommy ta rik’e bayan ta sake. Ya jinjina kai yace “Kin canki irin macen da zata warware sihirin dake k’ulle da d’anki da kanki.”

Mommy da Asshe suka kuma duban juna.


“Tooooh Malam wace irin Mace ce haka..?”


“Itace Budurwar  da maza ke so kuma suna gudunta..” 


Suka kuma duban juna cikin k’ullewan kai “Budurwar da maza ke so Kuma suna gudunta a lokaci guda..?” Mommy tace cikin rashin fahimta.


Jinjina kai Bokan yayi “K’warai itace Budurwar da makarin sihirin da akayi ma D’anki ke jikinta..”


“Malam ita wann Budurwar ya za’ayi mu tantanceta.. Ayi mana bayani..” Cewar Asshe.


Ya kuma gyara zamansa “Itace Budurwar da maneman aurenta ke guduwa. Ita ce Budurwar  da sai gashi kaman zatayi aure har an kawo gab’an sai kuma wani abu ya gifta.. Ita wann irin Budurwar tanada farin jini a idon maza dan duk guje ma aurenta da mazan suke basu fasa neman Aurenta. Ita wann Budurwar itace makarin sihirin. Kaman yanda maza ke guje mata haka d’anki zai guje ma wancan shed’aniyar da ta jefesa da guban asiri koda dafin asirin yana sakashi yaji yana son kasancewa da ita. Yanda maza masu neman wann Budurwar suke guje mata haka d’anki zai guje wancan shed’aniyar matar, za kuma ta fita daga rayuwarsa fita ta har abada kaman dai yanda mazan suke fita daga rayuwar ita makarin asirin toh haka d’anki zai fice daga rayuwar wancan hatsabibiyar da ta jefesa da dafin asiri matuka ya mu’amulance wann budurwar da aka aura masa cikin watanni Uku na Aurensu.”


Ganin sun zuba masa idanu kaman basu wani fahimci mai yake nufi ba yasashi kuma gyara zamansa “Kunsan ance Aure halitta ne mai rai.. Aura masa irin wann Budurwa da na gabatar maku shine zai kashe aurensa da wancan matar da aka k’ulla ta hanyar sihiri. Amma saidai…” Sai kuma yai shiru yana dubansu.


Mommy tace “Saidai mene Malam..?”


Ya zana wani dogon layi tsakiyan guru da laya sai yai crossing “Rayuwa ne a tsakanin mutuwa..”


Mommy ta zaro ido waje “Malam rayuwa tsakanin mutuwa. Inji ba d’a na ne zai mutu ba..?!”


Ya girgiza kansa kad’an “Duk wacce kuka nemo.. Ina nufin duk Budurwar  da kuka karya wann asirin dake jikin d’anki da ita zata mutu kaman yanda wancan Auren nasa zai mutu.. Shiyasa na fad’a maku Aure ne amma na watanni uku kacal.. Ita d’in ta riga ta zama MAKARIN ASIRI.. Zata mutu tareda wancan Auren. Shiyasa duk wacce zaku nemo ku sani K’addararta na tsakanin AUREN WATA UKU ne.!” 


Mommy da Asshe suka dubi juna. Mommy ta dubi bokan tace “Amma Malam ba yanda za’ayi a karya sihirin sai anyi Auren..? Kuma ni Malam bana so a halak’a kowa wajen ceton nawa d’an.. Dama za’ace ita wancan da tai masa sihirin itace zata mutu ba wacce ta karya sihirin ba ai da kaman sauk’i.. Malam bana son abinda zai ja min farrak’u da nawa mijin dan idan har a k’arshe yasan abunda nayi zai rabu da ni ne rabuwa ta har abada…” Ta d’an mumfasa duk zuciyarta a dame kafin taci gaba “Kuma Malam ni a gaskiya ba ko wace shara zan kawo cikin rayuwar d’a na ta rayu dashi har na tsawon watanni uku ba. Musamman da ka fad’a irin wann budurwar ai ta riga ta zama shara bola juji wanda mutane ke guje mata.”


“Duk dalilan da kika lissafo su suka sa ta zama makarin sihirin dake jikin d’anki.” Ya bata amsa kai tsaye.


Mommy ta kuma girgiza kai “Kai inaa, shi kansa Haidar na san ba lallai ya amince ya zauna da macen da zan aura masa har wata mu’amala ta gifta tsakaninsu a tsakanin watanni uku..  Yanzu haka ma gaba yake dani toh ta ya zan iya janyo ra’ayinsa har ya amince da wann Auren.?”


Girgiza mata kai yai “Ba wace hanya sai wann hanyar.. Saidai kuma idan zaki hak’ura da d’anki ki sallamasa ma wancan hatsabibiyar..”


Asshe tai saurin girgiza kai “Gafarta Malam gaskiya sharud’an sun mana tsauri da nauyi bana tsammanin zamu iya.. Kar garin neman gira aje a rasa ido. Aunty Kwaise tashi muje.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin mik’ewa. 


Bokan ya dakatar dasu da fad’in “Toh kuwa ku shirya rasa d’anku rashi na har abada..” ya tsaida idanunsa akan Mommy “Ba d’anki kawai ba harta ahalinki da dukiyar mijinki da dik wani abinda kika mallaka kike tak’amada a duniyar nan kaf zaki rasasu domin kuwa kar ki mance na sanar dake ita kanta matar da ta aure d’an naki ta hanyar sihiri ture ce a cikin rayuwarsa. Akwai babban shed’ani a sama wanda shine ummulhaba’isan komai.. Kuma bazai sarara ba sai yaga bayan ahalinki.. Dan k’asa bazata tab’a mana k’arya ba. Allah bamu alheri..!” Mushirikin Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa cikin tafiyarsa da yafi yanayi da durk’uso.


Har zai shige cikin wani k’ofa nan cikin bukkan wanda yake kaman shige a durk’ushe tsaban k’ank’ancin k’ofar Mommy tai saurin dakatar dashi “Malam dakata.. Na amince..! Na amince da sharud’anka..! Na Amince zanyi ma d’a na AUREN WATA UKU..! Na amince zan kub’utar da ahalina koda za’a rasa rai..! Na amince zan kashe ko nawa domin na tabbata ban rasa masarautar da na Jima na d’ibi shekaru ina ginawa ba.. Idan irin macen da ka fad’a itace makarin sihirin dake jikin d’a na zan nemota duk yanda ta shiga ta fita.. Idan kud’i zai sayeta zan sayeta dasu domin d’a na da ahalina su tsira..!” Ta k’arashe cikin jaddada kalamanta har wani huci da tururi take fitarwa.


Dattijon ya kaikaito yana duban Mommy. Sai ya kad’a ya dawo da baya da baya ya zauna a mazauninsa. Ya buga k’asan gabansa ya dubi Mommy “Ke da kanki kika zab’i nau’in Budurwar da makarin Asirin da aka jefi ahalinki ta jikin d’anki yake tattare da ita… Kar ki mance dole macen ta cika wann sharud’an idan aka samu sab’ani ko akasi ki sani tashin hankali ne maras misaltuwa biyeda ahalinki.”


Ya mik’e cikin tafiyarsa da yafi kama da durk’uso. Ya d’auko wani bak’in ruwa cikin wani k’ok’o mai launin ja. Suka zuba masa idanu yanda yaketa tsifface tsiffacensa cikin ruwan. 


(Allah kai mana tsari da b’ata ka tsare mana imaninmu. Ameen). 


Har suka baro wajen bokan jimamin abun suke. Ta ya za’a soma neman irin wann matar wacce Auren Haidar ke nufin Ajalinta.? Shin wacece zata sadaukar da rayuwarta dan rayuwar nata d’an ya inganta..? Idan ma sun samu irin wann Budurwar shin Haidar zai amince da ita..? Kai abun da kaman wuya wai gurguwa da Auren nesa.  Mommy ta dubi Asshe “Asshe ta ya za’a ce dole sai irin wann budurwar ce lak’anin ke jikinta.. Wai dama ana haka..?”


Asshe ta murmusa “Aunty Kwaise kenan.. Kin mance akan bawa mutum lak’ani na arziki ta irin matar da za’a gindaya masa ya aura.. Wata cewa za’ayi sa’arka na tareda ita shiyasa sai kiga duk yanda irin wann matar take mutum ya tafi ya nemo. Ai a duniyar nan babu abinda ba’ayi.. Fatanmu mu samu irin budurwar da Malam yace cikin gaggawa. 


Mommy ta jinjina kai a hankali Tana tsaka da tunanin taji Asshe da driver suna karaton salati. Bata ankara ba sai gani tai mutum kwance gaban motar saman kwalta sun bige wata mata. 

Tuni Mommy ta fara salallami tana fad’in Driver ya fita ya duba matar da suka bige ko tana numfashi. 


**



A b’angaren su Ummul kuwa sun zaga police station kusan guda uku a na hud’u sukayi dace.


Hannayen Ummul rik’e cikin na ‘yaruwarta Khulsum wanda k’araffan k’ofan cell ya raba tsakaninsu. Ta kuma share hawayenta tana duban Khulsum.


Khulsum ta girgiza kai kad’an tace “Adda meyasa kika tak’ura kanki wajen nema na..? Wann hukunci na nake karb’a.. Nayi addu’a wa mahaifiyarmu cikin b’acin rai. Nace Allah yasa jami’an tsaro su kamata sai gashi ba’je ko ina ba addu’a na ya dawo kaina. Take naga ishara . Sai na zamto ni ce wacce jami’a tsaro suka Kama.. Lallai na kuma yarda iyaye ba abun wasa bane. Kuma al’amarin su al’amari ne mai girma. Ban tab’a mafarkin zuwa police station ba dukda taran rikici irin nawa sai gashi kausasa harshe da nai Akan Umma yasa nazo police station kuma har gark’ame ni anyi.. Snn ‘Yaruwata da muke uba d’aya bama bare ba itace ta zamto Sila..”


Ummul ta jinjina Kai a hankali ta kuma share hawayenta “A littafin Allah mai tsarki wajaje da dama yayi umarni da a kyautata ma iyaye Khulsum. Yazo a hadisin Abdullahi bin Mas’ud yanda yake tambayan Manzo S.A.W wane aiki ne yafi soyuwa wajen Allah. Bayan sallah akan lokacinta sai biyayya ma iyaye ya biyo. Har ila yau matsayin uwa yazo a hadisin Abu Huraira wani mutum ya tambayi manzon tsira S.A.W wanene yafi cancanta yayi kyakkyawan zama dashi.? Manzo S.A.W yace mahaifiyarka. Ya sake tambaya ya sake amsa masa da mahaifiya.. Saida akayi haka sau uku yana cewa mahaifiya kafin a na hud’u yace mahaifi.. Har ila yau Manzo S.A.W ya fad’a cikin hadisin da Tirmidhi ya rawaito cewa ‘ Yardan Allah na tareda yardar iyaye haka fushin Allah  na tareda fushin iyaye.’ Kinga Hakan kawai ya ishe mutum ya fahimci girma da k’ima da iyaye ke dashi musamman mahaifiya.. Shiyasa kikaga dukda abubuwan da Umma ke fad’i akaina daidai da rana guda ban tab’a fatan na sab’a mata ba. Sabida ita d’in mahaifiyata ce.. Kuma zanci gaba da mata addu’a har Allah ya fahimtar da ita. Naji dad’i da kika fahimci haka Khulsum. Kar ki damu yanzu zamu tafi kinji.. Zaki fita daga wajen nan.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta.


A can gaban kanta kaw Hisham sai fafatawa yake da ‘yansandan dake duty. Sun dage bazasu bada beli ba a cewarsu ba huruminsu bane. Kai da ganinsu kasan wani Abu suke son tatsa jikinsa musamman da sukaga yanayi akwai tattare dashi.


Hisham ya murmusa dan shima ya d’ago jirginsu. D’an matso da fuskarsa yai kafin yace “Officer kenan. Tell me your bank details . Let’s settle this once and for all.” 


D’ayan ya dubi d’ayan “Mai ka maida mu.. Gurb’atattun ‘yansanda ko me..? Don’t abuse our uniform.”


Katsesa Hisham yai da fad’in “Nasan matsalar ka.. Take this..” Ya k’arashe yana janyo hannun police d’in had’ida dunk’ula masa kud’i masu d’an yawa. Gajeriyar murmushi saman fuskarsa.


Gurb’ataccen D’ansandan  ya bud’e hannunsa yana duban yawan kud’ad’en take ya shiga washe baki harda sara ma Hisham. Ya dubi d’ayan d’ansandan wanda da gani assistant d’insa ne ya daka masa tsawa.


Take ya k’ame yana amsa masa.


“Maza shige ka bud’eta..”


D’ansandan ya jinjina Kai ya wuce cikin sauri. 


Nan da nan aka fito da Khulsum. Tai tsaye tana duban mutumin da ya taimaka aka fitar da ita.


Saidai ganinsu da tai tareda Hajja Fannah yasa tai zaton ko wani nata ne. 


Khulsum ta  kariso a hankali kafin  ta risina ta gaida Hajja Fannah da mutumin da ta gansu tare had’ida masu godiya.


Murmushi saman fuskar Hajja Fannah  ta girgiza mata Kai alamun ta daina masu godiya. Ta shiga tanbayan da fatan babu dai abinda suka mata.


Ta girgiza kai tace basu mata komai ba. 


Ummul dai duban fuskar ‘Yaruwar tata tai da mamakin yanda yai luhu luhu alamun yasha tafi. Tasan duk yanda akai bazai wuce wann ‘yarsandar da sukazo suka tafi da Khulsum d’in bane ta mammareta. Batadai ce komai ba tinda Sun samu an fitar da ita. Gwara suyi gaggawan barin wajen kafin su bisu da wani sharrin. 


Asibiti suka nufa daga nan wajen Abba. Saida aka fafata da Mama kafin ta bari su Ummul suka shiga wajen Abba. Dan saida Hajja Fannah tai da gaske kafin Mama ta bari. Ya tabbata Umma bata asibiti wajen Abba. Hankulansu ya kuma tashi ga duhun dare da ya riga yayi. 


Hajja da Hisham suka kwantar masu da hankali da fad’in za’a sami mahaifiyarsu cikin yardar ubangiji. Hisham yace idan har bata zo asibitin a daren ba zuwa gobe zai filing missing person report ma ‘yansanda tinda ma ba’a sanar da cigiya a dokan yansanda sai after 24hrs. 


Bayan sunyi sallama da Hajja da nufin dik yanda ake ciki gobe idan Allah yakai rai da abun zasu tashi Ummul ta d’ago ta dubi yaron Hajja Fannah da taji ta kirasa da suna Hisham.. Cikin sanyin murya take masa godiya na taimakon da yai masu musamman da ya kasance zuwansa garin kenan ko hutu bai samu ba matslolint suka tarbesa.


Murmushi saman fuskarsa ya girgiza mata kai “It’s nothing. Ki daina min godiya.. I’m glad I helped out.. Ummul-khair.” 


Yanda ya ambaci sunan nata da wani irin siga sai yasa ta sadda idanunta kad’an.


A d’an daburce tai masa sallama had’ida komawa wajen Khulsum cikin sauri.


Shi kaw kallo ya bita dashi har saida ta b’ace ma ganinsa kafin ya nufi mota yanda Hajjarsa ke jiran karasowarsa. 

SameenaAleeyou📚


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post