Auren Wata Uku page 10 by Sameena Aleeyou - Abokiyar Hira Novels


AUREN WATA UKU..!*

10

©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Sautin kukan Ummul dake fita a hankali ne ya d’auki hankalinsa. Ya d’an kaikaito yana dubanta. Kanta a kife saman gwiwoyinta.

Ya maida dubansa ga mahaifiyarsa “Hajja wacece wann..?”

“Kaga Hisham jeka aje jakanka. Zuwa kai akan gab’a daidai lokacin da nakeda buk’atan hakan dikda zuwan ba zata ka min.”

Zai kuma magana ta shiga turasa tana fad’in “Kaje kawai ba lokacin bayani bane yanzu.. Allah yasa da motarka kazo.”

Ya jinjina mata kai yana mai nufan hanyar d’akinsa. Yana tafe yana waigowa yana duban Ummulkhairi da har lokacin kanta a kife yake. 

Fitowan Hisham yai daidai da mik’ewarsu tsaye. Yai mutuwan tsaye yana kallon budurwar. Fuskarta fayau alamun kuka da damuwa. Bai tab’a ganinta tareda mahaifiyarsa ba balle yayi tunin ko ‘yaruwarsu ce. Danginsu ma gaba d’aya ai suna Maiduguri so baya tunanin ‘yaruwar mahaifiyarsa ce. 

Yai tsaye daga gefe yana sauraron mahaifiyarsa dake kuma kwantar ma budurwar hankali. 


Agogon hannunsa ya duba yaji ana kiraye kirayen sallar la’asar. Ya d’anyi gyaran murya wanda yasa Hajja juyowa tana dubansa. Sai ta maida dubanta ga Ummul tace “Yanayin kinnan anya ma kuwa kin saka wani abu cikinki Ummul.”


Girgiza mata kai tai. A hankali cikin Sanyin muryarta ta furta “Kiyi hak’uri Hajja na k’oshi bana jin yunwa. Bazan iya cin komai ba.”


Hajjah Fannah ta fahimceta dan wani tashin hankalin ya wuce gaban komai. Dafata ta d’anyi “Maza shiga d’akina kiyi sallah. Zan shigo na sameki.”


Ta jinjina mata kai tana mai shigewa jiki a sanyaye.


Hisham ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta har ta shige. Ya rage daga shi sai mahaifiyarsa. Ya d’an bud’e hannayensa yana d’aga gira kafin tai masa tayin abinci “I’m still full.. Don’t worry about me.” Ya shiga nuna k’ofan d’akin yana tambaya a hankali “Hajja who is she..?”


Kunnensa guda ta kamo ta shiga janyosa tana fad’in “Ban gama da kai  ba zaka sanar dani dalilin da ya hanaka sanar dani kana tafe.”


Ya d’an saki k’ara yana k’ok’arin dafe kunnensa “Yi hak’uri Hajjata.. Idan na sanar dake kuma ai bai zama bazata ba.”


Ta murmusa tana dubansa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk’i “Watau dai bazaka daina min bazata ba. Kaidak bazaka girma ba.” 


Ya murmusa “Na jima wann karon banzo na ganki ba shiyasa.” Suka soma sabon gaisuwa Hisham na kuma tambayarta wacece wann budurwar. 


Ta d’an dubesa “Naga alama ka k’agu kaji ko wacece ita. Yanzu dai kaje kayi sallah police station zaka kaimu..”


Ya d’an dakata da nad’e hannun rigarsa da yake “Hajja police station kuma.. Meke faruwa ne wai.?” 


Ta d’an lumshe idanunta had’ida furzar da huci “Je kayi sallah Hisham.”


Ya jinjina mata kai kafin yasa kai ya fice yana tunanin mai zaikai mahaifiyarsa ofishin ‘yansanda. 



A natse take sanar da Hisham abindake faruwa game da kama ‘yaruwar Ummulkhiairi da akayi. Mahaifinta dake kwance gadon asibiti ga kuma mahaifiyarta da suke tsammanin b’acewa tai. Saidai bata sanar dashi sanadin faruwar komai ba. Tinda ba huruminsa bane. Wann ma dole ne ta sanar dashi.


Hajja ta mik’e “Jiramu a waje muna fitowa. Barin duba Ummul d’in.” Ta fad’i tana nufan k’ofan d’akin da Ummul ke ciki.


Ta tadda ta ida sallar. Ta linke abin sallan kafin ta dubi Hajja dake tsaye tana jiranta. Hajja ta sakar mata murmushin k’arfafa gwiwa kafin ta sanar da ita bak’on da ta gani D’anta ne dake aiki can Abuja. Yazo hutun aiki ne. Yanzu haka yana waje yana jiransu zai kaisu police station ayi belin Khulsum sann ayi filing report na missing person idan har b’acewa Umma tai. 


Ummul ta jinjina kai a hankali tana ma Hajja Fannah godiya. Hajjah Fannah tace ta daina mata godiya ita ‘ya ta d’auketa. 


Koda suka fito Hisham na tsaye jikin motarsa yana waya. Sam ita bazama tace ta iya tantace shi ba dan har lokacin ba wai ta dawo cikin hayyacinta bane. Karfin hali ne Kauai. Tasha jin labarin ana cewa Hajja Fannah nada D’ah saurayi amma baya zama garin kano zuwa yake lokaci zuwa lokaci domin ya duba mahaifiyarsa. Duk zuwa gidan da take bata tab’a arba dashi ba sai wann karon. 


Back seat Hajjah Fannah ta bud’e mata ta shige yayinda ita Hajjar ta shige mazaunin mai zaman banza gefen d’anta. 


Suna tafe saman kwalta suna kowa yayi jigum jigum. Hisham bai saba zama haka shiru da mahaifiyarsa ba. Zai iya cewa they are best of friends shida mahaifiyarsa sabida tsananin shak’uwa dake tsakaninsu. Yau d’in duk sai yaji babu dad’i. Sai ya sata kallon Ummul ta cikin mirror yanda ya hangi Siraren hawaye basu daina sauk’a saman k’uncinta ba. 


Ji yai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Rabin hankalinsa naga kwalta rabi naga Ummulkhairi.  


Hajja Fannah takai dubanta ga mirror yanda Hisham ke satan kallon Ummul. Bata kuma cewa komai ba sai d’an sauk’e ajiyan zuciya da tai. Sosai yarinyar ke bata tausayi. 


**

Lexus ce bak’a wul taketa kutsawa cikin k’ungurumin daji. Kai da gani kasan ba lafiya ba kaga motan manyan mutane irin wann na ratsawa cikin daji. 


Saida sukai tafiya mai nisa daga bakin kwalta zuwa wani k’ungurumin k’auye da yake tsakiyan daji kafin Mommy ta juyo ta dubi driver dinta tace ya fita ya basu waje zasu tattauna. Driver yai yanda Mommy tace. Juyowa tai tana Duban k’anwarta Asshe dake zaune gefenta cikin motar “Asshe kin tabbata aiki yakeyi mai kyau...”


Asshe ta murmusa  "Aunty Kwaise kenan. Ni ina zama ya ganni kishoyoyi sun sakani tsakiya. dole na kutsa nasan duk wani malami mai tashe da yake aiki kaman yankan wuka. Sha yanzu magani yanzu.”


Asshe itace kanwar Mommy dake aure garin Kano. Mijinta D’an kasuwa ne da kasuwancinsa ya zaga garin Kano harma da wasu jihohin Arewa. Su uku ne wajen mijin nasu tanada uwar gida da amarya itace ta tsakiya. Itace kuma mahaifiyar Anisa sai d’an uwan Anisa mai suna Hilal.


Zaune sukai gaban gasunk’umin bokan da ya ari sunan malanta ya yafa. Sumarsa furfura ya cika kama daga kansa dake rufe cikin hulan sak’i har izuwa sajensa da ya zagaye fuskansa. 


Wani k’aton faranti ne gabanshi mai lallausan yashi a ciki. Hannunsa guda nad’e cikin doguwar carbin da takai tsawonsa koma tafi. D’an bukkan kuwa ko ta ina shirgi ne da tsummokara. 


Asshe ta gyara zama “Allah gafarta Malam itace ‘yaruwata da kwanaki na labarta maka tana so a mata aiki akan d’anta.”


Hannu guda ya d’aga ya dakatar da Asshe yaci gaba da jan doguwar carbin yana furta wasu kalmomi da basu iya tantancewa.


Lokaci guda yasa hannunsa ya shafi k’asan ya zana wasu layi kusan guda uku. 


Sai ya soma jinjina kai yana duban farantin “Naga AURE cikin rayuwar d’anki.”


Asshe da Mommy suka dubi juna.


Mommy ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Aure kuma Malam..?”


Mutumin ya jinjina mata kai cikin tabbatarwa.


“Malam anya kuwa..? Aure cikin rayuwarsa..? A gaba kenan dan a halin yanzu ko maganar mace baya so a masa balle aure da aje iyali.”


Wani kwanon sha ya d’auko wanda tsatsa tai mata dabaibayi ta ko ina ya nuna mata cikin kwanon mai cikeda ruwa. Take fuskar Haidar ya bayyana.


“Wann ba shine D’anki Aliyu ba..?”


Mommy tai saurin jinjina kai alamun eh “Eh.. Eh shine Malam.”


Ya kuma kad’a kai “Tabbas D’anki yayi Aure ba tareda saninku ba..”



Mommy ta dafe k’irji cikin d’imauta “Na shiga uku Ni Kwaise..!” Ta dubi Asshe jikinta har rawa yake “Asshe tsanar da Haidar ke min har yakai yai aure ba tareda sanina ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raj’iun..!”


Bokan ya katseta “Shi kansa baisan yayi auren ba.!”


Suka dubi juna itada Asshe shaye da mamaki.


Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Malam mai haka yake nufi ya za’ayi yayi Aure bai sani ba.?”


“Koda yasan da Auren baya cikin hayyacinsa akayi Auren. Aure ne da aka k’ulla akan sihiri. Aure ne da aka k’ullashi a Fadan dodon tsafi. Aure ne da aka masa k’ulli uku mai K’arfi.. Aure ne da akayi sa dan a masa farrak’u da Iyayensa.!”


Jikin Mommy ya d’auki rawa. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina “Malam.. Auren sihiri fah kenan. Na shiga uku ni Kwaise.. Haba biri yayi kama da mutum. Na fad’a Haidar baya cikin hayyacinsa. Malam wace shed’aniyar ce ta shigo rayuwar d’ah na dan ta rabamu..?”


Ya kuma zana k’asa yana fesa ruwan bakinsa saman yashin “Saninta bazai miki amfani ba dan D’anki bazai tab’a bud’e baki ya sanar dake gameda wann auren nasa ba.”


Mommy ta soma girgiza kai “Malam duk yanda za’ayi a karya wann mugun sihiri da aka masa. Ni kuma nayi alk’awarin ko nawa ne zan kashe domin na dawo da d’ah na cikin hayyacinsa.”


Girgiza kai ya soma yana aje wani igiyan guru saman tray d’in “Abinda k’asa ya hasko min shine an bisne wann asiri a wani waje yanda ita kanta wann matar da yake tareda ita matsayin matarsa bata san yanda tukunyar sihirin yake ba. Wani wanda yakeda burin ganin bayan d’anki da ma ahalinki gaba d’aya ya mallaki tukunyar ya mata ajiya mai nisa. Dan a yanda k’asa ya hasko mun ita kanta wann matar da umarnin wani take aiwatar da komai.. Har sai wann tukunyar ya fashe kurwan d’anki da aka d’aure ciki ya kub’uta.”


Zufa yaci gaba da karyowa Mommy “Na shiga uku ni Asshe waye mai burin ganin bayan ahalinmu irin haka..? Yanzu Malam ba yanda za’ayi a fasa wann tukunyar.?”



Ya kuma zana k’asa sau uku sai kuma ya d’ago ya dubi Mommy “Da sihiri ake karya sihiri.. Akwai hanya d’aya tak da za’abi a karya wann sihirin.”


Daga Asshe har Mommy rige rigen tambayar hanyar suke.


“Wani Auren shi zai karya wann Auren.. Sabida asirin ajikin d’anki akayi..!”


Mommy ta girgiza kai “Kana nufi idan yayi wani auren shikenan asirin zai karye.”


Shiru yai kaman mai nazari sai kuma ya jinjina kai “Aure ne ba kaman ko wani Aure ba. Aure ne da yake k’unshe da sharudd’a.. Aure ne da za’ayisa domin warware wani auren. Aure ne da ba ko wace irin mace za’a aura ba sai macen da ta cika k’a’idodin da zan sanar daku. Aure ne da yakeda iyaka wa’adin da zai rayu. Aure ne da zai wanzu a tsakanin watanni uku tak.. AUREN WATA UKU..!”





SameenaAleeyou📚

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post