Auren Wata Uku page 8 by Sameena Aleeyou - Abokiyar Hira Novels


AUREN WATA UKU..!*

*08*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Yaran Umma suna kuka suna rok’onta ta sauk’o daga saman rijiya Mama na kuma ingizata “Suwaiba ko ki fad’a ko kar ki fad’a da alama dai bak’in cikin wann ‘yar naki shi zai ajalinki.. Wayyo ni Tani zanyi kewarki Suwaiba. Ashe tafiya zakiyi ki barni.. Na yafeki duniya da lahira Suwaiba.” Ta shiga rangad’a ma Badi’a da bata jima da zuwa gidan ba kira tana fad’in ta fito tayi bankwana da Suwaiba tafiya zatayi ta barsu. 


Suwaiba ta dena kururwar da take tana duban Mama da mamaki “Yaya bazaki hanani fad’awa ba.. Rijiya fah zan fad’a..”


Mama ta kamo bakin zani tana goge hawayen da babu su “Yo ko na hanaki ko ban hanaki ba wancan ‘yar taki mai bak’in k’addara zatayi ajalinki Suwaiba. Ta shiga doka kiran Badi’a wacce bata jima da zuwa gidan ba.


“Badiatu.. Badiatu! Badiatu..!! fito kiyi sallama da Suwaiba.. Suwaiba dai lokaci yayi..!”


Badi’a ta d’age labule fuska a yatsine tana kuma turo kallabi gaban goshi “Toh Mama ki barta ta fad’a mana.. Idan bata fad’a ba ai bata tabbata shashasha ba.!”


Khulsum ta harzuk’a “Uwa bata fi uwa ba Anty Badi’a kar ki sake gangancin zagar min mahaifiya..”


Badi’a ta malamalo ashar had’ida zame d’aurin kanta tai d’amara dashi  tayo kan Khulsum tana fad’in kafin uwarta Suwaiba ta fad’a rijiya sai ta fara jefata ciki taga uban da ya tsaya mata. 



Ai sai Umma tai tsalle ta duro daga saman rijiya ta shiga janye Khulsum wacce Baid’ia Ke k’ok’arin janyota Mama na tayata. Abu sai ya koma kaman dambe Mama ta shige ma ‘yarta Umma ma ta shige ma nata ‘yar wacce taga haik’an rijiya za’a jefata. 


Ummul kaw fashewa tai da wani irin kuka sosai ganin wann tashin hankalin dik sabida ita ake. 


Tana tsaka da kuka tana rok’onsu suyi hak’uri su daina ta hangi Abba na rarrafowa daga d’akinsa hannunsa guda dafe da b’angaren k’irjinsa. Ta kirawo sunansa cikin kid’ima tana mai nufansa. 


Hakan yaja hankulansu. Nan take suma sukai Kan Abba suna ambato sunansa. Tuni idanunsa sun kafe suna kallon sama baka iya ganin bak’in k’wayan idon. 



Sai kuma suka koma kururuwa suna neman agaji. 


Kaf mutanen gidan aka rasa mai kawo masu d’auki dan dik a nasu zaton wasan kwaiwayo ne da suka saba. 


Sukai masa caa akai kowa yana ambato Sunansa suna rok’onsa ya tashi. Umma sai masa fifita take da bakin zani yayinda Mama ta kawo ruwa cikin kofi tana mik’awa Umman. Fad’i take “Suwaiba duba mana kiga yana numfashi.”


Umma na kuka take fad’in “Haba Yaya kar kiyi tunani haka. Abban Ummul na numfashi..” Taci gaba da rera kuka tana rok’onsa ya tashi kar ya tafi ya barsu.


Kaf ‘yanuwansa maza dake zama cikin gidan aka rasa mai zuwa ya dubasa balle a kaisa asibiti. Dama gidan Sun gaji gaba na ‘yanubanci tin daga iyaye da kakanni. Yan wann d’akin babu ruwansu da yan wancan d’akin. Shi Abba kusan shine babba cikin mazan dake rayuwa a gidan sauran yeyyen nasu duk mata ne suna gidajensu. Shi a d’akin mahaifiyarsa shi kad’ai ne namiji. Hasalima su biyu mahaifiyar tasa ta haifesu. Daga shi sai kaw ‘yaruwarsa k’anwarsa mai suna Inna Dije. Inna Dije da mijinta basu jima da komawa garin Dutse na jihar Jigawa ba yanda mijinta ke aiki. Hasalima mijin nata d’an asalin jihar Jigawa ne amma yayi zaman Kano yanda yaga Inna  Dije k’anwa ga Abba ya aureta. Sun zauna tsawon lokaci a Kano kafin iftila’in rashin tilon d’ansu ya samesu. Tin bayan rasuwar D’ansu basu kuma zaman Kano ba hakan kuma yai daidai da canjin wajen aiki da mijin Inna  Dije ya samu. Sann tin bayan wann lokacin Inna Dije bata kuma saka k’afarta a garin Kano ba.


Wasu dattawan unguwar masu ganin mutincin Abba su suka Kaisa wani k’aramin asibitin gwabnati  mafi kusa. Mama da Umma sukai masu godiya.


 Jigum jigum sukai gaba d’aya suna jiran ba’asi daga wajen likitoci.


Daga yanda  suke zaune Mama ta kafe Umma da yaranta dake zaune daga d’aya b’angaren suna hawaye. Sai cika take tana huci dan wann dik dalilin Suwaiba da ‘yarta ke faruwa. Ta sauk’e idanunta kan Ummul wacce ta kasa daina kuka maras sauti. Kaman wacce aka sinkara ta soma furta “Wann duk laifinki ne Ummul.. Idan Abbanku ya rasa ransa ki sani alhakin mutuwarsa zai ratayu ne a wuyanki.. Kece nan kikai silan mutuwar mahaifinku..!”


Umma ta d’ago tana duban Mama shaye da mamaki “Yaya ya zaki ce haka.? Ta ina Ummul ta zama Sila..?”


“K’warai kuwa ita ce Sila dan bak’in cikinta da abunda ke faruwa da ita su suka taru  suka haddasawa mijin mu ciwo ehe.!”


Badia dake koke Koke tana ambato sunan mahaifinta ta k’arasa a guje ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in shegiya mai bak’in k’addara kafin ki kashe  mana uba sai and  fara kasheki kowa ya huta. Daidai lokacin su Azeema da Salima sauran yaran Mama dake gidajen aurensu suka iso ai nan suma suka aukawa su Khulsum. Fad’a dai yaci gaba a asibiti. Har saida ma’aikatan asibitin suka tasamma koransu. 


Da kyar dai aka raba bangarorin guda biyu fada. Kowa suka koma gefe suna aika ma juna mugun kallo.


Can da jimawa wani Likita ya fito. Suka mik’e gaba d’aya suka nufesa.

Sukai ma likitan caaa da tambayoyi kowa naso a soma amsa nasa. Mama da yaranta su Salima na yi Umma da Khulsum na yi. Ita dai Ummul ita kad’ai ce baka Jin bakinta. 


Likita ya zuba ma sarautar Allah idanu yana duban wann ahali Wanda majinyacin da suka kawo baya buk’atan irin wann hayaniya da tashin hankali nasu. Ya d’an girgiza kai yana k’ok’arin kwantar masu da hankali amma sai yaga kaman basa gane wann yaren. Tsawa ya daka masu yace duk suyi shiru ko su fice su bar masu asibiti.


Bayan Likitan ya kebe da Mama da Umma Ya dubesu yace “Ku sani yanzu ba lokacin tashin hankali bane. Lokaci ne da mijinku ke tsananin buk’atar kwanciyar hankali. Ko kunsan mijinku na d’aukeda matsanancin ciwon zuciya mai haifar da Kumburin zuciya.!”


Ai sai suka rikice Umma kuka Mama kaw mik’ewa tai dafe da k’irji “Likita kumburin zuciya fah kace.?!”


Likita ya jinjina mata Kai “K’warai Hajiya.. Kuma ciwonsa ya wuce matakin farko.. Hasalima zamuyi k’ok’ari ne mu turasa can babban asibitin koyarwa dan a can ne zaifi samun kula sunada k’wararrun likitoci da ya shafi ciwon zuciya..”


Umma ta share hawayen da suka zubo mata tana tuna ranan da mijin nasu yai masu wasiya da hak’uri da zaman lafiya “Likita yanzu mai zai faru da mijinmu..?” Tai maganar cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni.


Sauk’e ajiyan zuciya yai yace “Kwararrun Likitocin da suka shafi b’angaren ciwon zuciya ne kad’ai zasu iya sanar daku abinda zai faru.. A halin yanzu bazan iya ce da ku komai ba.. Zuwa gobe da yardar Allah zaa tafi dashi can asibitin koyawar sai Likitocin zuciya su dubasa. Amma ku kwantar da hankulanku ba wani abin tashin hankali ana warkewa cikin k’udarar Ubangiji. Kuyi hak’uri na fad’a maku gatsau sabida Kun Kai hak’urina bango ne shiyasa. Ku kwantar da hankulanku ku had’e kan ahalinku ko dan samun lafiyan mijinku.. Please do this for your husband.” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyu.


Mama tace “Sunan maganin ka fad’a Likita.?”


Ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza Kai “Cewa nai kuyi hakan domin mijinku.”


Suka jinjina Kai a tare Likitan ya k’arada “Kar ku damu babu abinda zaku biya mutanen da suka kawo sa nan sun biya komai. Saidai idan an kaisa can babban asibitin koyarwa dole zaa bukaci kud’i ko nace kudade masu yawa.”


Daga haka Sallama likitan yai masu suka fito jikkunansu duk a sanyaye.


**



Abuja.



Hisham ya dubi Haidar wanda ya bada hankalinsa sosai ga laptop d’in dake gabansa wanda da gani ko ba’ace kasan aiki tuk’uri yake domin achieving goals dinsa. Ya d’an Sauke ajiyan zuciya “I hope he approves the new proposal.”


Shiru Haidar yai idanunsa kan computer din har lokacin. Yeci gaba da juya pen d’in dake mak’ale cikin yatsunsa guda biyu  “I know my Dad, he’s so meticulous… So everything should be done carefully..”


Hisham ya jinina kai yana mai mik’ewa “Alright, with your permission Sir, zan koma bakin aiki na.”


“Dama ban rik’eka ba.” Haidar yace yana d’an juyi cikin kujeran da yake. 


Kafin Hisham yakaiga ficewa wayarsa tai ruri. Mahaifiyarsa ce mai kira. Ya fad’ad’a murmushinsa yana mai d’aga kiran. 


Sosai yake hira da ita cikeda so da k’auna da alamun kewan juna daga duka b’angarorin nasu. Haidar na iya sinkayo muryar mahaifiyar Hisham yanda take ta binsa da addu’o’i nagartattu yana amsa mata da ameen. Baya kasa kunne ya saurari abinda bai shafesa ba amma sai ya tsinta kansa da sauraron wayan Hisham da mahaifiyarsa.  Har dai Hisham d’in suka ida waya da mahaifiyarsa Hisham na sanar da ita bazai jesa Kano anytime soon ba she shouldn’t expect him bayan bai jima da sanar da Haidar yana son daukan hutu yaje ya duba gida cikin kwanakin. 


Haidar ya d’an dubesa. Sai Hisham ya murmursa “Ban sanar da ita ina tafe soon ba. I want it to be a surprise.” 


Gajeren murmushi Haidar yai “Idan bazatan zai sanayata farin ciki.”


Hisham ya jinjina kai “I hope so.. Nayi kewar Hajjata.. She’s my everything Haidar.. Ina mata son da bayada iyaka.. Na girma matsayin maraya amma bansan maraici ba sabida ita.. She’s my two in one.. Zatayi komai domin farin cikina..”


Haidar ya jinjina kansa a hankali yana jin rayuwar abokin nasa total opposite da nasa rayuwar. Amma sabida k’arfin hali irin nasa sai ya kauda tunanin yana mai ci gaba da abinda yake.  Saidai da alama tunanin yak’i barinsa, Ya kasa yakicewa daga zuciyarsa. Sosai Hisham da mahaifiyarsa suka birgesa. Inama shine yakeda kusanci irin haka da nasa mahaifiyar. Ba abunda ya nema ya rasa a rayuwarsa ta duniya face soyayyar iyayensa guda biyu. Da ace dukiya shine farin cikin rayuwar duniya tabbas da ahalinsu ya cika da farin ciki. Saidai kash sab’anin haka ne cikin ahalinsu. Da ace za’a karb’e duk abinda suka mallaka na duniya a azurtasu da farin ciki kwanciyar hankali da soyayyar junarsu tabbas da sai yafi masa duk wann k’yale k’yale na duniya da suketa bautuwa akai. Ya d’an limshe idanunsa yana mai canza direction d’in tuk’insa. Can k’asan zuciyarsa yana jin akwai gibi babba cikin rayuwarsa. Har ya iso k’ofar gidan mahaifinsa yana tunanin shiga ya duba Mommy wacce sukai kwanaki basuyi koda magana ta waya ba kaman dai ba d’ah da mahaifiya ba. Ringing d’in da wayarsa tai ya dakatar dashi. 


Dareen ce mai kiransa hakan yasa ya fasa shiga gidan ya juya Kan motar. 



**


A can Kano kuwa 

Tuni an tura Abba babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Ana kan basa kula na gaggawa had’ida da masa gwaje gwaje da yake bukata.



Mama tai saurin funcuke takardan da likita ke mik’a masu tin kafin Umma ta mik’a hannu. Sai ka ranste tasan mai aka rubuta cikin takardan ne. Ta shiga juya takardan tana dubawa “Babu damuwa Likita za’a sayo maganin Allah sa babu tsada..”


Dr dai bai tsaya sauraronsu ba yasa kai ya shige. 


Mama ta kuma yatsina baki tana juya takardan “ Toh ma Wai Ina yaga kud’ad’en da zaa masa jinya ne wai.. Wllhi Suwaiba keda d’iyarki dai anyi annoba.. Ummul ta haddasa masa wann ciwo..”

Jiki a matuk’ar sanyaye Umma tace “Kar kice haka Yaya..”


Ta watsa mata harara had’ida jan tsuka kafin tai saurin tare wata nurse da tazo shigewa “Yauwa ‘yar nan dan Allah nace ba ko zaki iya duba mun mai aka rubuta takardan nan..”


Nurse d’in ta amshi takardan tana dubawa “Sunayen magani ne da allurai..”


Mama tace “Tooh inji dai basuda kud’i..?”


Nurse d’in ta d’an kuma duban Mama “ Magunguna ne da allurai masu kud’i dan allura guda a nan yakai dubu goma.. Kije pharmacy zasu Miki bayani..” Bata kuma tsyawa sauraron Mama ba tasa Kai ta wuce.


Mama ta waro idanu “Tirk’ashi toh idan jinyar Malam da tsada haka ai akwai matsala dan irin wann babban jinya kankataraf sai ya cinye d’an abinda zai bari ma yaran nasa bayan babu shi..” Ta juyo sosai tana duban Umma “Wann duk laifinki ne Suwaiba.. Ke da ‘yarki ku kuka kashe Malam a tsaye dan haka sai Kuje ku nemo kud’ad’en da zaa masa Jinya.”


Cikin rawar murya Umma ke furta “Haba Yaya ki dubi yanda muke fah.. Asibiti fah muke.. Sann meyasa zaki d’aura alhakin ciwon mijinmu kaina nida ‘Yata.. Kinsan bazamu tab’a so haka ya same shi ba..”


“Ke dalla rufe mun baki munafukar banza da wofi idan ba takaicin Ummul da hayagaganki ba me ya janyowa mijinmu ciwon zuciya.. Kinji na rantse Miki da Allah kije ki nemo kud’ad’en masa jinya.. Ina zaki samu bai dameni ba kawai abinda na sani shine alhakin ciwonsa na wuyanku keda Ummul.!”


Jin hayaniya yasa wasu nurses k’arasowa suna masu fad’an asibiti suke ba dandali ko kasuwa ba idan hayaniya zasuyi zasu koresu.


Mama tai saurin nuna Umma “Kun ganta nan ita zaku kora itace silan ciwon mijina gashi zata k’ara masa. Tinda mijina ya aureta tsiya ke bibiyarsa, Kayan kantinsa ya daina bunk’asa ta kuma haifo masa annoba wacce kowa ke gudu.”


Nurse guda tace “Malama wann ba matsalar mu bace zan kira security yai waje dake idan bazaki mana shiru ba.”


D’ayar tace “Visiting hours ya shige mutum d’aya ne zata iya zama, ki gode ma Allah mijinku ya samu d’aki mai d’aukan mutum guda godiya ga sabuwar gwabnatinmu dake k’ok’arin inganta hark’an kiwon lafiya da yanzu dole ku nemo namiji da zai zauna.. Yanzu mace d’aya cikinku zata tafi..”


Ai bata Kai aya ba Mama ta nuna Umma “Itace zata tafi dan bamu San idan ya farka ya ganta mai zai faru ba tinda ita da d’iyarta ne silan ciwon.. Na tabbata zuciyarsa bugawa zai idan ya ganta.”


Umma ta girgiza Kai tana duban Mama “Kiji tsoron Allah Yaya.”


“Da tsoronki zanji Suwaiba.!” 


Ta girgiza Kai kurum tasa Kai ta fice tamkar kazar da k’wai ya fashe ma a ciki. 


A haka  Umma ta dawo gida cikin jimami.


Aiko tin daga bakin k’ofa take sinkayo sautin yaran Mama Salima Badia da kuma Azeema Sun saka Ummul gaba sai kwashe mata albarka suke suna fad’in ta kashe auren Azeema bai isheta ba zata kashe masu mahaifi toh wllhi idan mahaifinsu ya Mutu ta dalilin bak’in cikinta sai Sun d’auki fansa akanta. Duk fad’a irin na Khulsumu da k’ok’arin karb’ar ma ‘yaruwar tata ‘yanci yau sai ta gaza tab’uka komai sakamakon tuno halin da mahaifinsu ke ciki Wanda yake tsakanin rayuwa da mutuwa. 


Umma ta k’araso da sauri ta rungume Ummul. Umma kuka Ummulkhairy kuka.


Kaman an jefo Mama haka ta shigo gidan tagajan magajan. Ashe koda Umma ta fice ta biyo bayanta. Nan ta tadda yaranta na d’iban albarka wa Ummul da mahaifiyarta.


Mama ta cab’i zancen daga sama “Shisa nace bazan bari Suwaiba ta kwana wajen mijinmu ba. Kuma sun gama rab’ansa har Allah ya tashi kafad’unsa daga ita har ‘yar tata. Zuriyan annoba.”


Azeema tace “Kinyi daidai Mama dan wllhi ko ni nan ko kan gawan mahaifina bazan bari Ummul taje ba.!”


“Ya naji ana zancen gawa.. Abban ya cika ne..?” Badia tace tana dubansu.


Mama tace “ Baidai cika ba amma yana hanya. Dan idan ba’a samu kud’ad’en da zaa masa jinya dasu  ba nan da kwanaki k’alilan toh fah mahaifinku zai zama gawa silan wad’ann..!” Ta k’arashe tana nuni dasu Umma.


Sai sann da abun ya ishe Khulsum ta mik’e idanunta na zubda hawaye take dubansu gaba d’aya “Tir da hali irin naku.. Tir da ahali irinku.. Abba na gadon asibiti kuke maganganun marassa kan gado irin haka.. Idan burinku ya Mutu ne domin ku tozarta ‘Yaruwata da mahaifiyata in sha Allahu babu d’aya daga cikin burinku da zai cika.. Allah zai tashi Abba zai basa lafiya sann rayuwar mahaifiyata harma da ta ‘Yaruwata zai inganta.”


“Ke rufe mana baki k’aramar maras kunya.!” Mama tace tana huci.


Badia da Azeema suka soma k’ok’arin kwance d’ankwali zasu yi d’amara.


Badia na dukan k’irji take fad’in Mama ta k’yaleta ta gurji bakin Khulsum yayinda Umma ta mik’e da sauri ta tare yaranta guda biyu hawaye bai daina ambaliya a fuskarta take fad’in “Yaya dan Allah kuyi hak’uri.” Ta dubi su Salima kafin taci gaba “Ku tuna halinda mahaifinku ke ciki.. Yanzu ba lokaci ne na tada rikici ko nuna yatsa ba. Yanzu lokaci ne da ya kamata mu had’e matsayin ahali ko dan samun lafiyan mahaifinku.. Kunfi kowa sanin yanayin gidan nan yanda ‘yanubanci ya raba kan ahalin tin kan iyaye da kakkanni.. Idan bamu had’e kawunanmu ba kunfi kowa sanin babu mai yiwa mahaifinku kaf gidan nan. Dan Allah muyi hakuri duka mu nemawa Malam lafiya koda da abinda ya mallaka ne.”


Mama tai saurin katseta “Ban gane koda da abinda ya mallaka ba.. Yo me ma ya mallaka da zaa masa jinya dashi.?”


Umma ta jinjina kai “K’warai ya mallaki kanti. Ko Kayan ciki aka sayar da gaba d’aya kantin na tabbata zaa iya rage wani abin saura sai a nema wajen bayin Allah tinda ga yanayin ciwon nasa ciwo ne da za’a buk’aci kudade ga yanda komai ya koma a k’asar.”


“Ke malama da Allah dakata.!” Mama ta katseta kafin taci gaba “Wllhi Suwaiba kinji na ranste Miki idan ina numfashi babu mai saida shagon nan.. Toh a bar ma yaran nawa mai..? Inyi.. Shikenan su koma basuda gadon mahaifinsu miji ya samu abun goranta masu ..? Toh ahir d’inki wllhi koda wasa kar na kuma jin wann batu daga bakinki.. Idan keda yaranki Baku buk’ata mu muna buk’ata dan bazai yuwu Ana shafe shekaru bila adadi ina dawainiyar Malam a barni fankinfayo ba.. Ke bari ma kiji na fad’a Miki.. Wann ciwo dai ba warkewa zai ba dan haka bazamu zubda dan abinda zai bari Akan jinyar da ba tashi zai ba. Shi fah irin wann jinyar kaf abinda ka mallaka sai ya k’are ba’a samu biyan buk’ata..” Ta d’an dakata kafin taci gaba “Toh ma ai Suwaiba keda yaranki bakuda gadonsa dan Kune kuka kashe sa.. Ku kuka jaza masa wann ciwo.. Ko a sharia duk Wanda ya kashe wani bai cin gadonsa.. Dan haka Kun fita da fitarku.! Ko ku nemo kud’ad’en da zaa masa jinya ko ya rub’e a gadon asibiti. Ta juyo ta dubi yaranta “Kusha kuruminku babu uban da ya isa ya tab’a maku gadonku ina raye ehe.!” 


Yaranta suka rangada shewa suna kuma ingizata.


Daga Umma har Khulsum da Ummul Cak kukansu ya d’auke suka ma nemi kukan da suke suka rasa. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Wacce irin duniya muke rayuwa ciki.? Ace iyalanka daka rayu dasu ahalinka Wanda kafi kowa kusanci dasu ba damuwarsu ya zaayi ka samu lafiya ba. Ashe damuwarsu mai zaka Mutu ka bar masu ne..? Shin ina allan attajiran dake tara dukiya kota halin k’ak’a su Mutu su bar ma magadan da ko tausayinsu basa ji balle suyi masu addu’a.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Matarka da ‘ya’yanka.. Hasbunallah wa ni’imal wakil.. Muyi ma kanmu karatun ta natsu tun munada dama kafin dama ta kufce mana. Mu Gina ma kawunanmu ayyukan alkhairi. Mu d’ibi dukiyoyin mu muyi aikin alkhairi dasu tun munada dama. Mu Gina ma kawunanmu sadaka mai gudana har bayan rayuwarmu dan ba Lallai abinda ka bari su maka ba. Allah ka bamu ‘ya’ya masu albarka Wanda su kansu zasu zame mana sadaka mai gudana Ameen. 


Wann rana da jimami Umma da yaranta suka yini. 


Ummul ta dubi Umma su duka biyun idanunsu a kod’e “Umma yanzu ya zamuyi. Haka zamu bari Mama da yaranta suyi yanda suke so..?”


Khulsum dake gefe ta k’ura ma waje guda idanu tace “Mai kuke tunanin a gidan da cikin Umma ma gaba suke da juna balle ‘yanuba..?”


Umma ta kuma goge hawayenta dan ta d’ago ina maganar Khulsum ya dosa. 


Ummul ma tai saurin d’agowa ta dubi Khulsum sai kuma ta dubi Umman “Umma ko Inna Dije zamu kira mu sanar da ita halin da Abba ke ciki..?”


Shiru Umma tai kaman mai nazari kafin ta girgiza Kai tace “Har yau babu Wanda yasan abinda ya haddasa gaba da k’iyayya tsakanin mahaifinki da tilon ‘yaruwarsa da suka fito ciki guda.. Mahaifinku ya b’oye mana bai sanar damu abinda ya rabasa da Dije ba.. Amma ya datse alak’a da ita kuma itama ta datse alaqa damu.”


Khulsum tai saurin d’agowa ta dubi Ummul wacce keta k’ok’arin danne marayan kukan dake taso mata jikinta har rawa yake tamkar wacce ta tuna wani abu. 


Lokaci guda Khulsum ke ci gaba “Tin sanda Ya Fa’iz tilon d’an Inna Dije ya rasu Abba da Inna Dije basu kuma zama ‘yan uwa ba.”


Take Ummul tai boasting cikin kuka mai tsanani ta mik’e ta nufi uwar d’aki.


Umma ta dubi Khulsum “Maiyasa Khulsum.. Maiyasa zaki ambato mata Fa’iz… Meyasa zaki d’ago mata wann mik’i..” Sai kuma muryarta ya soma rawa. Cikin rawar murya take furta “Tinda Fa’iz ya koma ga mahaliccinsa ahalinmu bai kuma daidaito ba.. Tabbas da Fa’iz nada rai duk abubuwan da suke faruwa watak’ila da basu faru ba.. Tabbas da Fa’iz na nan a raye da yanzu Ummul d’ina ta jima a d’akinta.. Allah sarki Fa’iz ka tafi ka barmu da tarin k’alubale da iftila’i.. Tabbas rashinka babban gurbi ne a garemu.. Ka tafi da kurwar ahalinmu Fa’iz…!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka.


Khulsumu ta k’araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta “A’a Umma duk abinda ke faruwa tuntuni rubutacce ne.. Allah ya nufa hakan dole sai ya kasance.. Wann itace k’addaran ahalinmu.. Auren Adda Ummul kuma ko ya Faiz na raye ko baya raye bazai tab’a faruwa ba sai lokacin da Allah yaso. Umma kiyi k’ok’ari kiyi tawakkali da sannu Allah zai kawo mana mafita kinji Umma ta… In sha Allah Abba zai samu lafiya kuma farin ciki zai dawo cikin ahalinmu da izinin Allah.!” 


Umma ta rungume ‘yar tata kuka na kuma kufce mata.


Tamkar wacce aka sinkara haka Umma ta janye jiki daga na khulsum. Ta shiga girgiza Kai tana duban Khulsum d’in “Yaya tayi gaskiya Khulsumu, Anya ba wani mugun k’addara bane yake bibiyan ‘yar uwarki..? Meyasa Fa’iz ya Mutu kafin yakai ga aurenta.? Meyasa tin bayan da Fa’iz ya bar duniya duk wani maneminta basa kaiga aure maganar ke watsewa.. Shin Anya ba alak’ar Ummulkhairy da Fa’iz bane yai Ajalin Fa’iz..? .. Anya ba wann dalilin bane ya raba tsakanin ‘yan uwa biyu..? Ina nufin mutuwar Fa’iz shine ya raba tsakanin Mahaifinku da ‘yaruwarsa.. Anya ba Ummul ce tayi sanadin Fa’iz ba.?!”




SameenaAleeyou📚


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post