Dr. Sadeeq Book 3 Page 1 to 10

 

Dr. Sadeeq Book 3

PG

     1-10


    

❤️DR SADEEQ 🤍


    BY


    NARNAH ƘANWAR SOJA 

My 15novel comedy love and drama 


    

    https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


  

THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*



    

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 



    BUSSINES GROUP    


    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    

HAPPY BIRTHDAY TO THE SPECIAL MAN I KNOW SIR 


    H

Shuraihu Usman 


    CEO OF HAUSA EBOOK'S WEBSITE.


    MAY ALLAH BLESS UR NEW AGE.....


    


    

SPECIAL THANKS TO


     NOVEL ELITE WEBSITE 

HAUSA NOVEL GROUP WEBSITE 

  ABOKIYAR HORA WEBSITE 

 CREATIVE NOVELS WEBSITE 

  TK  NOVELS   WEBSITE 

HAUSA EBOOK'S 

TASKAR HAUSA NOVEL

    E..T...C

        

TITLE 

    Love is a flame that burns bright, even in the darkest night



      A GURGUJE

    BOOK 3 – DR SADEEQ


    Dr Kamal ya shigo da sallama ganin kofar gidan a bude abun ya bashi Mammaki yana rigi da bag in Nazifa tana bayan sa da karamin cikin ta da take fama dashi ganin Dr sadeeq tsaya a bakin kofar Indo abun ya ɗaure masa kai bill haqqi ya tsaya " Lafiya Honey" cewar Nazifa itama ta tsaya ganin abinda Dr Kamal ke kallo Dr Sadeeq a kofar yana zaune " Dudde what are u doing here Indo ce ta rufe ma ƙofar " hararra kawai Dr yayi don ganin Nazifa baison girman sa ya faɗi ya fita ko hi bai musu ba nan suka bishi da kallo Nazifa ta taɓe baki" wallahi Bansan yaushe Dr Sadeeq zai sauke wanan girman kai ya gayawa Indo yana sonta ba " ta zauna tana nishi Kamal yayi dariya " No kinsan miskillancci yana damunsa sai yayi asarar ta ga wani zai gani bashi da wayyo tunda yanzu haka yana shirin turata University shine babban ganggancin da zaiye akan Indo".


    


    WASHEGARI 


    Da sauri Dr SADEEQ ya shirya yasan Indo na kitchen a wanan time in wanan shine babban damar dazai ganta Atika ce ta biyo sa tana masa magiya" Please kifita daga idona sai da nagayamiki kar kishaga harkar yarinyar nan ,domin ne kika taɓa ,itta rayuwata ce kawai Inason ta dawo hankalin tane nayi hakan batare da sanin hakan zai jawo min Matsala da ita ba " ya fita ya barta zama taye akan kujerar sai ga hawaye a idon ta " Son masu wani ƙoshin wahala Amman Nima ba laifi nabane ƙaddara tace a hakan kasani inason ka har ga Allah ko wa wani nace zan aure ka ,kuma nayi nassara Amman na kasa samun nasarar shiga zuciyar ka ,har zaka iya ganin ido na kace wata ce rayuwar ka , lallai hausawa sunyi gaskiya da suke cewa So mai sonka , soyayya gaskiya ce , ƙiyayya ma gaskiya ce ba mai sa wani a zuciyar sa ta dole sai Allah ya tsara hakan .


    


    


    

A gefe guda kuma,

Dr SADEEQ ya tsaya a bakin kitchen, yana jin karar cokali da tukunya ƙamshin shayi ya buge shi amma zuciyarsa tafi tafasa ya ɗaga hannu zai yi sallama sai ya tsaya.


 

Indo tana tsaye a kitchen,

sanye cikin Pakistan wando da riga, launin milk da ɗan green

rigar ta laushi, wandon ya zauna mata dai-dai,

ta yi tsaf kamar ba ita ce jiya cikin hargitsi ba.


Gashinta a ɗaure, fuskar nan babu kwalliya mai yawa,amma kyau na halitta ya fito fili.


Ta na juya cokali cikin tukunya a hankali—

cikin ta bai gama wucewa da zafi ba,

amma zuciyarta tafi jin zafi , tana rera sabuwar waƙar Naziru Sarkin wa'ka da Fati Niger me sunan Balaraba


A dai-dai lokacin nan,

Dr SADEEQ ya tsaya a bakin ƙofar kitchen.


Ya yi sallama a hankali “Assalamu alaikum…”

kafin ya ƙara wani kalma Indo ta dago kai.


Idanuwansu suka haɗu  lokaci ya tsaya ba murmushi na gaisuwa , sai kallon da ya ɗauki dukkan labarin rayuwarsu.


Idon Indo ya sauya launi, zuciyarta ta bugo,

amma ta ɗaure fuska, ta mayar da hankalinta kan tukunya,

kamar bata ganshi ba.


Dr SADEEQ ya ɗauki mataki guda ciki,

muryarsa ta ɗan karye  “Indo…”


Ta katse shi cikin sanyi mai zafi:

 “Dr, idan magana ce da Atika, ya wucce kabarni kawai”


Kalmomin sun soka shi fiye da wuƙa.


Ya haɗiye yawu, ya ce “Ni da ke nake so muyi magana.”Ta ajiye cokali a hankali.

ya juya ta kalle shi kai-tsaye, idonta babu tsoro “Babu abinda zamu tattauna.”  “Abinda kake so ka riga ka zaɓa.”


Ya matsa kusa da kitchen table,

amma bai kuskura ya taɓa ta ba  “Indo, ki saurare ni.” “Wallahi ba haka nake nufi ba.”


Ta yi dariya ƙanƙani dariya mara daɗi:

 “Kullum haka kake faɗa.”  “‘Ba haka nake nufi ba’,

amma sakamakon kullum ni nake ɗauka.”


Ta ɗauki plate ɗin , ta matsa gefe: “Don Allah ka bar kitchen. Ina aiki.”Ya tsaya cak  “Ina sonki.”


Kalmomin sun faɗo cikin kitchen kamar dutse Indo ta ɗan tsaya—amma ba ta juya ba.


Ta ce cikin murya mai ƙarfi amma sanyi:

— “Idan so naka yana sa ni kuka, tsoro, da wulakanci to wannan ba so bane.”


Ta ɗaga plate, ta wuce kusa da shi ba tare da ta kalleshi ba.

Kamshin turarenta ya bishi,

amma zuciyarta tuni ta rufe ƙofa.


Dr SADEEQ ya tsaya shi kaɗai a kitchen,

yana kallon bayan Indo tana fita—

ya san a wannan safiyar

ya ƙara rasa wani abu mai muhimmanci .....


    


Dr SADEEQ na tsaye, kamar an ɗaure shi.

Maganganun Indo na yawo a kunnensa—“wannan ba so bane.”


Sai ya ji ƙafar mutum a bayansa  “Bro… what’s going on?”

Dr Kamal ne, ya shigo a hankali, ya lura da yanayin fuskar sa.


Dr SADEEQ ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi “Kamal… I messed up.”

Kamal ya jingina da counter, ya kalle shi sosai: “That girl is hurt. Not angry—hurt.”


Dr SADEEQ ya shafa fuska da tafin hannunsa “Na san haka.”  “Kuma na san anjima zata tafi Kano.”


Kamal ya ɗan miƙe, muryarsa ta zama mai tsanani amma cike da shawara “Exactly. That’s why you must act now.”


Kamal ya ɗan matsa kusa, ya rage murya kamar wanda baya so wani ya ji:

“Sadeeq, listen to me carefully.”

 “Idan kaji mace ta ce ‘kada ka biyo ni’, ba yana nufin bata son ka bane.”  “Yana nufin ta gaji da ciwo.”


Dr SADEEQ ya kalli ƙasa, idonsa ya yi ja  “So what do I do, Kamal?”“Na riga na yi komai da ya kamata in guje masa.”


Kamal ya girgiza kai a hankali.

 “No. Har yanzu akwai abu guda ɗaya da zaka iya yi.”  “Respect her Nature ,her feeling”


Ya tsaya da kyau, yana fuskantar shi kai tsaye:

“Ka bari ta tafi Kano lafiya.”  “Ka daina matsa mata.” “Ka nuna mata cewa ka canza—ba da magana ba, da aiki.”


Dr SADEEQ ya ɗaga kai  “Amma Atika fa?”


Kamal ya yi murmushi mara daɗi  “Atika matar ka ce a takarda.” “Amma Indo ce a zuciyar ka.”“Kada ka haɗa biyun, zaka rasa su duka.”


A wannan lokaci, Atika ta shigo part in

Fuskarta a ɗaure, idonta na haske da hawaye da aka riƙe. 

 “Toh yanzu ta tafi?” ta tambaya cikin sanyi.

Dr SADEEQ bai kalle ta ba  “Eh.”


Atika ta yi dariya kaɗan—dariya mara daɗi.

“ka ga? na faɗa maka. Ita ba ta dace da kai ba.”


Nan Dr SADEEQ ya juya, ya kalleta karo na farko tun tashin hankalin nan.

Idonsa babu fushi—amma babu ƙauna  “Atika,” ya faɗa a hankali, “Please… kada ki sake magana akan Indo stay away from her .”


Atika ta tsaya cak.

“Me yasa?”

 “Saboda duk abin da ya faru tsakanin mu,” “Indo ba ta da laifi.”

Wannan kalma ta tsaga zuciyar Atika kamar wuka ta haɗiye kuka, ta ce  “Ni fa?” “Ni me nayi?”


Dr SADEEQ ya sauke ajiyar zuciya “Kin zama matata.”  “Amma ban zama namijin da ya dace da ke ba.”Shiru ya sauka a ɗakin Kamal ya ɗauki jacket ɗinsa:

 “I’ll give you two some space.” Ya fita.


Atika ta zauna a kujerar parlour, hawaye suka zubo ba tare da ta hana ba. “So this is how it ends?”


Dr SADEEQ ya tsaya a gefe, ba ya iya kusantarta, ba ya iya tafiya  “A’a.”  “Amma this is how it begins.”




 A HANYAR ABUJA → KANO


Indo na zaune a bayan motar private car, taganenta a buɗe kaɗan.

Iskar hanya na bugawa fuskarta, tana share mata hawaye a hankali.


Ta ɗora hannu a ƙirjinta ta ce a zuciya:

“Ba zan kalle baya ba.”

“Zan zama Indo—ba Indo ta kowa ba.”




    FIRST DAY – HOSTEL LIFE

Lamido Crescent Hostel, Nassarawa LGA


Motar ta tsaya a hankali a gaban Lamido Crescent Hostel.

Indo ta fito da kafarta ta dama farko—kamar tana shiga wata sabuwar ƙaddara.


Driver ya buɗe boot ɗin mota.

Bag ɗaya… biyu… uku… manya-manya, zallar kaya ne.

Fashion queen fa ce—Indo doesn’t joke with style Ta tsaya tana kallon hostel ɗin, zuciyarta na bugawa da sauri.

Sabuwar rayuwa… sabuwar ni.

 “Ranki ya daɗe, ga key da form ɗin ki,” cewar waccan matar office ɗin hostel.


Indo ta karɓa, ta duba:


ROOM 7


Ta yi murmushi, murmushin da bai cika zuciya ba amma yana ƙoƙari  “Lucky 7,” ta faɗa a hankali  “Allah ka sa ya zama alheri.”


Driver ya ja bag ɗin farko“Ina ɗaki ne ranki?”

 “Upstairs,” ta amsa, tana gyara mayafi.


Matakala na hawa suna ɗauke da ƙamshin sabon fenti da rayuwar ɗalibai.

Dariya, hayaniya, sautin WhatsApp calls, da kiran ‘my roommate!’ na cike ko’ina.


Sun iso Room 7 Indo ta buɗe ƙofa.


Ɗaki mai tsabta—beds biyu, table, wardrobe, window mai fuskantar titi.

Haske ya shiga ya bugi fuskarta.


Ta shigo ciki, ta tsaya tsakiyar ɗakin  “From today,” ta faɗa a zuciya, “nan ne duniyata.”


Driver ya shigar da bags ɗin, ya jera su gefen gadon da yake kusa da window.

 “Allah ya miki albarka a karatu,” ya ce.

 “Ameen,” Indo ta amsa, ta ɗan miƙa masa godiya.Da ya fita, shiru ya mamaye ɗakin.


Indo ta zauna kan gadon, ta sauke ajiyar zuciya mai tsawo.

Ta duba hannunta—har yanzu yana ɗan rawa.


Ba tsoro bane ’Yanci ne.


Ta miƙe, ta buɗe wardrobe.

Riguna masu launi, shoes, Bag's Sai ta ji ƙarar ƙofa  “Assalamu alaikum…”


Indo ta juya.


A bakin ƙofa, wata yarinya ce—fara’a, da ɗan murmushi a fuska, ɗauke da manyan Bag's ukku. “Wa alaikum salam,” Indo ta amsa.

 “U can call me Indo .”


Yarinyar ta yi murmushi mai faɗi “Nice to meet you. Ni Aaliya.”

 “Looks like… we’re roommates.”


Indo ta ɗan yi dariya  “Seems so.”

Aaliya ta kalli manyan bags ɗin “Wow… fashion alert.”


Indo ta ɗan girgiza kai, murmushi ya ɗan fito da gaske wannan karon “You have no idea.”


Outside, rana na faɗuwa a hankali.



    


    


WELCOME OF NEW STUDENTS PARTY – NIGHT 1

Lamido Crescent Hostel, Nassarawa LGA


Dare ya sauka da sauri.

Hostel ɗin ya rikide—from calm to loud.


Haske masu kala-kala sun cika compound.

Music na tashi: Afrobeats, Hausa remix, small R&B.

Dariya, ihu, snapping pictures—freshers vibe.

Aaliya ta juya daga mirror: — “Indo, hurry up! This party is once in a session.” Indo tana tsaye gaban madubi sanye take da abaya sky blue gashin ta a ɗaure, lip gloss kaɗan, perfume mai taushi Ta kalli kanta.

 “I’m coming,” ta ce a hankali.


Sun fito tare. A harabar hostel, DJ na ta ɗaga wuta.‘Yan mata na rawa, wasu na dariya, wasu na shan soft drinks.Samari suna ƙoƙarin burgewa—fresh confidence.

 “Welcome freshers!” “CCUK babes in the building!”


Aaliya ta ja hannun Indo: — “Come, let’s sit there.” Sun zauna kusa da wani table.

Wasu ‘yan mata biyu suka zo.

 “Hi, what’s your name?”  “ Me Indo my nickname”

 “Nice! Ni Zainab, wannan kuma Khadija.”

Suka fara hira—course, hostel, where you’re from.

Indo tana murmushi, amma zuciyarta ba ta cika ba. Sai waƙa ta canza Love song.

Cikin hayaniya, Indo ta ji zuciyarta ta ɗan buga.Hoton Dr SADEEQ ya wuce mata a rai—

yadda yake kallonta, yadda ya  iya faɗin “ina sonki” 

Ta tashi tsaye. — “Aaliya, I need air.” “You okay?” “Yeah… just need a minute.”

Ta matsa gefe, kusa da fence.Iskar dare ta bugi fuskarta.  “Indo…”


Ta juya.

Wani saurayi ne—dogon jiki, neat, murmushi mai sauƙi. — “I’m Hassan. Nursing too.”

 “Nice to meet you,” ta amsa, cikin ladabi “You look… different. Calm.”

Indo ta ɗan yi murmushi mara nauyi: — “That’s life.” Music na ci gaba a baya.


Indo ta kalli taurari a sama, ta faɗa a zuciya: Dr SADEEQ, ko kana tunani na?

Ni kuwa na fara sabon babi.

A gefe guda, wayarta na cikin bag—

ba message, ba call.


Party na ci gaba zuciya na ƙoƙarin warkewa.


₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦

DR SADEEQ’S HOUSE – NIGHT


Gidan ya yi shiru fiye da kima.

Too quiet Dr SADEEQ ya shiga parlour, ya kunna haske—komai nan, amma babu rai.

Kujerar da Indo ke zama… babu ita.

Kitchen ɗin—no sound, no movement.


Ya zauna a kujera, ya cire agogon hannunsa a hankali zuciyarsa na bugawa kamar ana buga ƙofa daga ciki.  “Indo…”

Sunanta ya fita daga bakinsa ba tare da ya shirya ba. Ya ɗauki wayarsa.

Ya buɗe WhatsApp. Sunanta a saman chat—online earlier.Yana rubuta “Kin isa?” Ya goge.

Ya sake rubutawa:  “How was the journey?”

Ya sake gogewa.

 “Me yasa nake tsoron magana?” ya tambayi kansa a zuciya.

Ya tashi ya kuma part nasu ya zauna ya jingina still holding his phone .

Atika ta fito daga daki, ta tsaya a nesa tana kallonsa ta ga yadda yake—lost.

 “Dr… dinner fa?” ta ce cikin sanyi.


Ya ɗaga kai ya kalle ta, amma idonsa bai gan ta ba. — “Ban jin yunwa.”


Ta haɗiye maganar da take shirin faɗi.

Ta juya ta koma ɗaki—with tears unshed.


Dr SADEEQ ya tashi, ya shiga  part nasu a bedroom nata 

A gefen gado, ya ga mayafin Indo da ta manta.

ya ɗauka, ya ɗan matse shi a tafin hannunsa.

Flashback ya bugi kwakwalwarsa— murmusinta, shiru-shirunta, yadda take kallonsa idan ta ji rauni “I failed you,” ya faɗa a hankali.Wayarsa ta yi vibration.Unknown Number Ya ɗaga “Hello?”

“Sir, this is the driver. Mun sauke Indo lafiya. Hostel Lamido Crescent.”Numfashinsa ya tsaya na sakan ɗaya. — “Thank you.” ya kashe wayar. Ya zauna a gefen gado, kai a sunkuye.

 “She’s safe…”  “But I’m not.”


A wannan daren, Dr SADEEQ bai yi barci ba.

ya zauna da kuskurensa, da kalmomin da bai taɓa faɗa ba.

A can Kano, Indo na kallon rufin dakin hostel—Lucky 7.

A nan Abuja, Dr SADEEQ na kallon duhu—without her.



    


    


    


      MORNING – FIRST LECTURE


Safiya ta waye da sanyin iska na Kano.

Indo ta tashi da wuri—fresh mind, fresh beginning.


Ta yi light make-up, ba yawa ba, just to glow.

Ta saka abaya ash colour, ta yi mata kyau sosai Masha Allah.

Handbag ɗinta a hannu guda, jotter a ɗaya.

Aliya kuma a bayanta, abaya butter-powder colour, sun dace kamar an tsara su tare.

 “Lucky 7 kenan,” Aliya ta faɗa da murmushi.

Indo ta ɗan yi dariya: — “Allah ya sa luck ɗin ya bi mu har graduation.”


Suka nufi school tare. Akwai ɗan nisa amma ba mai yawa ba.

Hanyar cike take da sabbin dalibai—new faces, new hopes.


Da suka shiga class, aka ji ɗan hayaniya.

Wasu har yanzu ba su hallata ba, ana jiran su.


Sai aka ji murya mai ƙarfi amma nutsattsiya:

“Good morning students.”Nan take class ya yi shiru  “My name is Dr. Amina Yusuf,”

 “I’ll be taking you Introduction to Nursing Science.”


Indo ta daidaita zama, ta buɗe jotter.

Zuciyarta na bugawa—not fear, excitement.


Dr. Amina ta ci gaba: — “Before lectures start fully, we’ll do class orientation and introductions. Nursing is not just a course—it’s a calling.”


Indo ta kalli Aliya, suka yi eye contact. A zuciyarta ta ce: — “Mama… I’m finally here.”


Class ɗin na cikin nutsuwa.

Dr. Amina Yusuf ta fara bayani a hankali, tana duba fuskar ɗalibai ɗaya bayan ɗaya.

 “Nursing is about discipline, empathy, and knowledge,” ta faɗa.  “Now, who can tell me what nursing really means—in your own words?”


Shiru ya sauka a class.

Wasu na kallon juna, wasu na sunkuyar da kai.


Indo ta ji zuciyarta na bugawa.

This is my moment… ta faɗa a ranta. Ta ɗaga hannu a hankali.


Dr. Amina ta kalleta: — “Yes, you. Go ahead.”


Indo ta miƙe tsaye, muryarta a sanyaye amma cike da ƙarfin gwiwa: — “Nursing is not only about treating sickness,”

 “it’s about caring for the whole human beingphysically, emotionally, and psychologically.”


Class ɗin ya yi shiru sosai.


Ta ci gaba: — “A nurse is someone who becomes strength for the weak, hope for the hopeless, and calm for those in pain.”


Dr. Amina ta yi murmushi—irin murmushin nan na lecturer da ya gamsu. — “Excellent,” ta ce.  “What’s your name?”

 “A’ishatu Abubakar Sadeeq, ma’am.”

 “Very impressive, A’ishatu. You’ll go far in this profession.”


Wasu dalibai suka fara kallon Indo da mamaki easu da sha’awa Wasu kuma… da hassada.


Aliya ta murɗa baki a gefe: — “Kai Indo, kin kashe class ɗin nan wallahi.”


Indo ta zauna, zuciyarta cike da farin ciki.

A zuciyarta ta ce: — “Dr… ko ba ka nan, nasan zan yi abin da zai sa ka yi alfahari.”


Dr. Amina ta rufe lecture da cewa: — “This class has potential. I’m watching you all.”


Indo ta rubuta a jotter: FIRST DAY ✔

FIRST IMPRESSION ✔




Indo ta katse kirar Dr SADEEQ, ta ɗan tura wayar gefe, idonta na kallon Aliya:

“Haba beb… ba kyau wulakanta masoyi,” Aliya ta ce cikin dariya da ƙwarin gwiwa.


Indo ta kalli Aliya, ta miƙe ƙananan kafarta:

 “He is not my love… he is a cheater. Forget him. Muna da lectures da yamma. Get ready!”


Aliya ta ɗan yi murmushi, ta ɗauki bag ɗinta, tana jan Indo “Come on, let’s face the real world. Dukkaninmu muna da future fa, ba soyayya kawai ba.”


Indo ta ja numfashi mai nauyi, ta ɗauki jotter ɗinta, amma zuciyarta na tunanin Dr SADEEQ.


“Cheater ko a’a… har yanzu zuciyata tana jin muryarsa.”


Sun fita daga hostel ɗin cikin fara’a, sun shirya fuskantar lectures na yamma, amma raye Indo na cikin tunani da motsin zuciya.





Indo ta shiga classroom, tana ɗauke da handbags da jotter. Aliya na bin ta a hankali. Yana da ɗan nisa, amma kafin su kai tables ɗin su, sai suka hango wani saurayi mai tsayi, fuskar sa mai kyau, idanu masu zurfi, da murmushi mai jan hankali.


Sai ya tsaya a gabansu, yana kallon su da irin ƙwarewar da ke sa duk wanda ya kalle shi ya ɗan yi shiru.


Aliya ta ɗan yi dariya  “Beb, kaga nan… someone zai yi clash da ke yau, hmmm.”


Indo ta sunkuyar da kai, tana jin zuciyarta na ƙara bugawa da sauri. Amma kamar ta san zata iya fuskantar shi, ta ɗan gyara jakar hannu da nitsuwa.


Saurayin ya matsa kusa da su, yana kallon Indo da ido mai zurfi: suka wuce yabi bayan su 

 “Good morning. Please take your seats. Let’s start.”


Indo ta ɗan yi murmushi mai ƙarfin hali, tana jin kamar wannan lecture zai zama challenge.


Da suka zauna, sai ya fara gabatar da lecture ɗin  “Welcome to Nursing Science 101 – Fundamentals of Patient Care. My name is Dr Abubakar Siddiq, you can call me Sir Siddiq. I’ll be your lecturer for this course.”


Indo ta ɗan sunkuyar da kai, tana tunanin ” Amma ta tattara kanta da nitsuwa, tana so ta gabatar da kanta da kyau.


Sai ya ce  “Let’s do introductions. Each one of you, tell your name, your background, and one interesting fact about yourself.”


Indo ta miƙe jiki, cikin rawar kai  da nitsuwa, tana kallon Dr Siddiq a ido “My name is Indo A’ishatu Abubakar Sadeeq… I’m from Abuja, and I aspire to be a professional nurse who makes a difference.”


Dr Siddiq ya ɗan karkasa kansa, yana kallon ta kamar tauraruwa, murmushi a fuska:

“Hmm… very impressive. Welcome to the class, Indo. I hope your performance matches your confidence.”


Aliya kuwa ta ɗan yi tsaki a gefen, tana murmushi da dariya:

 “Drama , Beb… before lectures even start!”


Lecture ya ci gaba,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post