PG 1️⃣1️⃣-1️⃣5️⃣
https://chat.whatsapp.com/IaTRoVuc46O5i4oIVwPzvv
❤️DR SADEEQ 🤍
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
HAPPY BIRTHDAY TO THE SPECIAL MAN I KNOW SIR
H
Shuraihu Usman
CEO OF HAUSA EBOOK'S WEBSITE.
MAY ALLAH BLESS UR NEW AGE.....
SPECIAL THANKS TO
NOVEL ELITE WEBSITE
HAUSA NOVEL GROUP WEBSITE
ABOKIYAR HORA WEBSITE
CREATIVE NOVELS WEBSITE
TK NOVELS WEBSITE
HAUSA EBOOK'S
TASKAR HAUSA NOVEL
E..T...C
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
A GURGUJE
BOOK 3 – DR SADEEQ
Bayan Indo ta gabatar da kanta, Dr Siddiq ya dube Aliya da ido mai hankali“Next?” ya ce.
Aliya ta tashi, tana ɗan gyara hijab ɗinta Ta ɗan murmushi, tana kallon Dr Siddiq:
“Good morning, Sir Siddiq. My name is Aliya Muhammad. I’m also from Abuja, and I love fashion and community service.”
Dr Siddiq ya ɗan karkasa kansa, yana kallon ta da kyau“Nice. Seems like Abuja brought us some confident ladies today.”
Indo ta ɗan yi murmushi a gefen, tana tunanin “Aliya ma fa, za mu yi kyau a group ɗin nan.”
Aliya ta koma ta zauna, tana jin excitement, amma a lokaci guda ta lura da yadda Indo da Dr Siddiq suke kallon juna—hahaha, sai ta yi dariya a zuciya.
Dr Siddiq ya juya zuwa gaba ɗin class, yana fara lecture:
“Alright, class… now that we know each other a bit, let’s dive into Fundamentals of Patient Care. And yes, expect some practical tasks later—you’ll see how serious I am!”
Indo da Aliya sun yi exchanging glance, suna jin cewa wannan semester zai cike da comedy, drama, da small romantic tension—amma kuma dama ce su nuna kwarewarsu.
AFTER ONE MONTH
Dr SADEEQ bai kara kirar ta ba… haka itama.
Yau Sunday ce, babu lectures. Indo tana kwance a daki, tana bachii, inda Aliya ta fita don yi musu assignment.
Sai ga wata mace mai kula da ɗaliban rooms ta fito ta buga ƙofar Room 7. Indo da ƙyar ta tashi, idonta dai a rufe saboda bacci.
“U are A’ishatu Sadiq, right?” matar ta tambaya.
“Yes… I’m,” Indo ta amsa, tana ɗan gyara kafa.
Matar ta ɗan yi murmushi, sannan ta faɗi “Someone outside the building is waiting for you.”
A zuciyarta, Indo ta ji haushi. An katse mata bacci mai daɗi, kuma a bangaren daya, tana tunanin, waye yazo yanzu?
Indo ta ɗan tsaki, ta ɗan gyara rigarta, ta ɗauki phone a hannu, sannan ta tashi daga room ɗinta, tana tafiya cikin hankali amma a ɗan sauri, tana shirin fuskantar wanda ke jiran ta.
Indo ta tsaya a bakin gate, idonta na kallon mutumin da ke gabanta. Sai ta ɗan yi girgiza kai lokacin da ya yi murmushi “A’ishatu,” ya faɗi a hankali.
Indo ta ɗan yi shiru, zuciyarta na bugu da sauri. Sai ta gane murya… zuciyarta ta tsalle “Dr… Dr SADEEQ?” Ta faɗi a hankali, kamar ba zata iya magana baShi kuwa ya yi murmushi, ya kusanto, ya ɗauki hannunta a hankali“Yes, it’s me. Na zo ne domin in ga ki, kuma na ƙara baki haƙuri ".
Indo ta ji kamar zuciyarta zata fashe da farin ciki. Idonta ya cika da haske, daɗin zuwa ganin sa ya mamaye ta. Ta yi murmushi mai ƙarfi, zuciyarta na cewa: At least, ashe ya damu dani…
Nan take ta tsayar da kankanin nitsuwa da jin daɗi. Ta ɗan sunkuyar da kai, tana jin ranta kamar ta rungume shi daga murna.
Dr SADEEQ kuwa ya ɗan yi mamaki da wannan reaction ɗin nata—ba zato ba tsammani, ganin yadda ta ji daɗi ya sa ya kara kusanci “You look… amazing, Indo.”
Ta ɗan ja numfashi, sannan ta yi murmushi:
“Thank you… I’ve missed you,” a zuciyarta tana cewa, I can’t believe you’re really here.
Haka suka tsaya a bakin waje, har ma gashi hawaye na farin ciki sun ɗan bayyana a idonta, amma daɗi ya fi ƙarfi.
Sai Aliya ta dawo ɗauke da file, tana tsayawa cak da ganin su tsaye tare. Ta ɗan zuba ido daga sama zuwa ƙasa, sai murmushi ya ɓullo mata “Wow… perfect match,” ta faɗa cikin zolaya ta juya ta kalli Indo ta matsi kusa da kunnen ta “Ashe shiyasa kike gudun Sir Siddiq da ya nuna miki kulawa tunda kina da wannan haɗaɗɗen guy ɗin,” ta ƙara da dariya.
Indo ta ji kunya ta sunkuyar da kai, zuciyarta na bugawa a hankali, tana kallon sa Allah yasa baijiba don tasanshi ya iya jin magana komai ƙanƙantarsa Dr SADEEQ kuwa ya tsaya da murmushi mai natsuwa, bai musanta ba, bai tabbatar ba—kawai shiru.
Aliya ta matsa kusa da Indo “Introduce me mana.Indo ta ɗaga kai a hankali: “Aliya, this is… Dr SADEEQ.”
Aliya ta juya gareshi cikin ladabi, ta miƙa hannu “Nice meeting you, sir.” “Nice meeting you too,” ya amsa cikin nutsuwa.
Aliya ta yi musu murmushi mai ma’ana, ta ce:
“Okay, I’ll leave you guys,”
ta wuce ta barsu, tana har yanzu murmushi kamar ta gano sirri.
Nan Dr SADEEQ ya sauke numfashi, ya kalli Indo da idon da ke cike da kulawa. Ya saka hannu a aljihunsa, ya fitar da ATM card.
“This is TAJ Bank,” ya faɗa cikin sanyin muryaYa miƙa mata katin:
“Ga pin ɗin. If you ever need money, just use it. Zan na tura kuɗi a ciki anytime.”
Indo ta kalle katin, ta kalle shi. Zuciyarta ta yi rauni kaɗan—ba don kuɗin ba, amma don yadda yake nuna mata kulawa ba tare da hayaniya ba “Dr… this is too much,” ta faɗa a hankali“No,” ya katse ta da murmushi.
“It’s not too much. It’s responsibility.”
Ta karɓi katin cikin sanyin jiki, hannuwanta na ɗan rawa kaɗan “Nagode,” ta faɗa ƙasa-ƙasa " akwai uban fashion yau sai plaza mafi uban kuɗin nan "...
“Take care of yourself, Indo,” ya ƙara da cewa.
“Focus on your studies. That’s all I want.”
Sai ya yi mata sallama, ya juya a hankali ya fara tafiya. Indo ta tsaya tana kallon bayansa, zuciyarta cike da tambayoyi da motsin da bata iya fassara ba.
A ranta tace:
“Ko da yana nesa, har yanzu yana nan a zuciyata…”
AFTER DR SADEEQ LEFT
Indo ta tsaya a ƙofar hostel na seconds kaɗan, tana kallon hanyar da motarsa ta bi har ta ɓace ta ja numfashi a hankali ta rufe ƙofar, ta koma cikiDakin shiru.
Iskar fan na juyawa a hankali.
Ta zauna a kan gado, ta miƙa ƙafafunta, sannan idonta ya sauka kan ATM card da ke hannunta. Ta jujjuya katin tsakanin yatsunta.
“At least ashe ya damu dani…”
ta faɗa a ranta, ba da murya ba.
Sai kuma wata murya ta biyo “But too late.”
Ta ajiye katin a drawer, ta rufe shi da sauri kamar tana ɓoye zuciyarta.
Ta miƙe ta je bakin window waje shiru ƴan students na wucewa suna dariya.
Rayuwa na tafiya.Indo ta jingina da bango.
“Na zo nan domin kaina,”
“Not for anyone.”
Aliya ta shigo dakin da leda hannunta: — “Beb, I’m back.”Ta kalli fuskar Indo: — “You’re quiet.”
Indo ta yi murmushi ƙanƙani: — “Just tired.”
Aliya ta zauna: — “He looked serious though.”
Indo ta ɗaga kafaɗa: — “People change.”
Aliya ta yi shiru, ta gane akwai abin da Indo ba ta shirya faɗa ba.
NIGHT
Haske ya mutu fan kaɗai ke motsi.
Indo kwance, ta juya gefe zuwa gefeBarci ya ƙi zuwa.
Hoton Dr SADEEQ ya zo mata a zuciya—
yadda ya tsaya, yadda ya ce “I messed up.”Ta rufe ido. “Nasan kana nadama,”
“But I’m trying to heal.”Ta ɗauki phone, ta buɗe messages.Sunansa a can…
amma babu sabon saƙo Ta rubuta:
“Hope you got home safe.”Ta kalli screen na seconds da dama sai ta goge Ta kashe wayar. Ta juya ta rungume pillow.
Hawayen da ta ƙi zubarwa tun safe, suka taru a idanuwanta amma ba su zubo ba.
“Not today,”
ta faɗa a ranta.
Indo ta rufe ido, a ƙoƙarin samun barci,
zuciyarta tsakanin tuna shi da mantawa da shi.
MORNING
Haske na safe ya shigo ta window a hankali.
Indo ta buɗe ido, jikinta ɗan gajiya saboda ƙarancin barci ta zauna kan gado, ta miƙe, ta nufi bathroom.
Ruwan brush na gudu, mirror na kallonta—
fuska ba make-up, amma idanu suna ɗauke da tunani. Ta tsaya na seconds kaɗan. “Ya kamata na yi?”Ta gama brush, ta wanke fuska, ta fito ta ɗauki phone ɗinta daga bedside table Sunansa har yanzu nan hannunta na ɗan rawa.Ta rubuta a hankali, kamar tana jin nauyin kalmomin “Hope u get home safe.”
Ta duba message sau biyu Sai ta danna send.
Ta sauke numfashi mai nauyi, kamar ta gama wani aiki mai wahala “That’s it.”
Ta ajiye phone face down.
Ta sa hijab ɗinta, ta fara shirya kayan class, tana ƙoƙarin mayar da hankalinta kan rayuwarta.Amma zuciyarta…
ta riga ta tafi wani wuri dabam.
SAME MORNING – DR SADEEQ
Phone ɗinsa ya vibrate a kan table ya ɗaga idonsa sunanta Indo drama
ya buɗe message hope u get home safe.
ya tsaya na seconds sai murmushi ya zubo masa ba tare da ya sani ba Ya jingina da kujera, ya rufe ido na ɗan lokaci “So she cares…”
Ya ɗauki phone, ya rubuta amsa ya tsaya.
Ya sake rubutawa. ya sake tsayawa. “Ka nitsu,” ya faɗa wa kansa A ƙarshe ya rubuta: “I did. Thank you for checking.”ya danna send ya ajiye phone.
MORNING (CONTINUED)
Indo na zaune kan gado tana ɗaura hijab ɗinta.Phone ɗinta ya yi vibrate ta tsaya
Ta ɗaga shi a hankali message received.
“I did. Thank you for checking.”Ta karanta.Sau ɗaya sau biyu.
Sai murmushi ya tsinke mata ba tare da ta sani ba murmushin da bai kai leɓe kaɗai ba, har ya kai zuciya Ta sauke ajiyar zuciya a ranta “At least ashe har yanzu yana damuwa da ni…”
Ta danna screen ta kashe, ta ajiye phone Amma murmushin ya ƙi gushewa.
HOSTEL CORRIDOR
ANOTHER MONTHS PASS
Aliya na shigowa, hannunta cike da files ta tsaya cak da zarar ta hango Indo.
“Hmmmm…”
Indo ta ɗago ido: “Me kuma?” Aliya ta matso kusa, ta tsaya tana kallon fuskar Indo sosai, kamar mai bincike.
“This smile… ba na ganin shi sai idan akwai something.”Indo ta juya: “Aliya ki wuce, kar ki fara.”Aliya ta yi dariya ta zauna: “No no no, I’m serious.”
“Tun jiya kika dawo kamar ba ke ba.”Indo ta ɗauki handbag ɗinta: “Ni fa lafiya.”Aliya ta ɗaga gira: “Lafiya har kina murmushi kina kallon phone?”
“Indo… is he back?”Indo ta tsaya na ɗan lokaci.
Sai ta ce cikin sanyi “Ya zo jiya.”
Aliya ta buɗe baki “who ?”
“Dr SADEEQ?”
Indo ta jinjina kai kaɗan: — “Mm.”
Aliya ta tashi tsaye da sauri: — “Kinsan shi yasa nake cewa—” — “That man is not done with you.”
Indo ta ɗaure fuska: — “Aliya don Allah.”
Aliya ta riƙe hannunta: “Listen to me.” “Namiji idan ya bari wata na wata ɗaya ba tare da kira ba, sai ya zo da kansa…” — “That means ya kasa mantawa.”Indo ta ɗan yi shiru.
Aliya ta ƙara: “Kuma ga Sir Siddiq nan…” “Two men, one heart.”
Indo ta ja hijab ɗinta, ta ce a hankali: — “Please, ban shirya wannan ba.”
Aliya ta yi murmushi: “But your heart is already inside Dr SADEEQ it.”
( Gudu Gudu sauri sauri hhhhhhh wallahi nima nagaji da typing Dr SADEEQ na ƙusa na fara muku AFNAN )..
END OF SECOND SEMESTER – CAMPUS GROUND
Aliya na tsaye a gefen Indo, hannunta na rawa kaɗan duk da ƙoƙarin ta na murmushi “Indo… yau fa za a kafe result,"ta faɗa tana riƙe file a ƙirji “We are ready amma zuciyata na bugu sosai.”
Indo ta juya ta rungume ta, ta matse ta a jikinta: “Me too, Aliya.” “But In Sha Allah we will pass.”
Aliya ta ɗaga kai, idonta na sheƙi: — “Tare za mu yi celebrating.”
“Zamu je Abuja hutu ko?”Da wannan kalmar Abuja
zuciyar Indo ta yi tsalle Hoton gida ya faɗo mata a rai Gidan da Atika take ko gidan su Mommy , muryoyi Faɗa.
Kuka ta girgiza kai da sauri: “Ohh no…” Aliya ta kalleta: “Why?”
Indo ta sauke ajiyar zuciya, ta ce cikin sanyi amma cike da ƙarfi: — “I think… for the first time…” —
“Zan je Adamawa State, Modirre.”
Aliya ta buɗe ido: — “Seriously?”
Indo ta jinjina kai: — “After many years.” — “Ina buƙatar wuri da zuciyata zata huta.”
Aliya ta kama hannunta: “That’s good.” “Wani sabon chapter ne.”
Indo ta kalli nesa, ta yi murmushi mara ƙarfi: “Eh… sabon chapter.”
“Ba Abuja “Ba rikici.”
Sai dai a cikin zuciyarta, wata murya na faɗa mata a hankali: “Amma Dr SADEEQ fa?”
Ta lumshe ido, ta ce a ranta: — “Zan bar wannan tambayar har sai lokaci ya yi.”A can nesa, ana fara manne papers ɗin RESULT a board Dalibai na taruwa Numfashi na ƙaruwa.
Rayuwa na shirin juyawa.
RESULT DAY – NOTICE BOARD
Cikin cunkoso da hayaniya dalibai suka taru a gaban notice board wasu na dariya wasu na kuka.Wasu kuma zuciyarsu na bugawa kamar za ta faso ƙirji.
( THAT'S LIFE ).
Aliya ta riƙe hannun Indo sosai: — “Please Indo, ki fara duba sunan ki.”
Indo ta haɗiye yawu, idonta na bin layuka a hankali. Heart beat ɗinta ya ƙaru Suddenly a maimakon ta duba nata sai ta duba na Aliya kafin nata
“ALIYA!”
muryarta ta ɗaga ba tare da shiri ba.
Aliya ta firgita: — “What? Me?”
Indo ta nuna paper ɗin: — “PASS.”
“Not just pass… GOOD PASS.”
Aliya ta zaro ido, ta duba nata da sauri: — “Yaaaa Allahhh!” “Ni ma PASS!”
Su biyu suka rungume juna tsakiyar jama’a. Aliya na dariya, Indo idonta ya cika da hawaye.
“Mun yi nasara, Aliya.” — “Mama ta na alfahari da ni yanzu.”Aliya ta matse ta: — “This calls for celebration!”
Indo ta yi murmushi, amma a ranta ta ce: — “Wannan nasarar bata wa kaɗai bace kaɗai amman na san wahalar da na sha kafin na kai nan.”
SAME DAY – LECTURE HALL (UNEXPECTED)
Ana tsaka da shirin fita daga class, sai aka ji muryar da ta taɓa gigita zuciyar Indo tun first clash ɗinsu.
“Excuse me… everyone stay back for a minute.”Indo ta ji jikinta ya yi sanyi.
DR ABUBAKAR SIDDIQ Sir Siddiq.
Ya tsaya a gaban class, hannunsa ɗaya a aljihun rigar lecturer, idonsa na bin fuskar Indo kai tsaye “I heard results are out.”
Dalibai suka yi hayaniya: — “Yes sirrr!”
Ya ɗan murmusa: — “Congratulations to those who passed.”
Idonsa ya tsaya kan Indo, kamar yana magana da ita kaɗai: — “Especially… those who proved people wrong.”
Indo ta sunkuyar da kai Zuciyarta ta buga.
Sir Siddiq ya ce: — “Before you go—everyone should introduce themselves again.” — “Fresh semester, fresh mindset.”
Ana ta gabatarwa har aka zo kanta.
Indo ta miƙe a hankali: — “My name is A’ishatu Sadiq… popularly called Indo.” — “From Abuja ” “Nursing student.”
Ta zauna cikin nitsuwa.
Sir Siddiq ya yi shiru na seconds kaɗan, yana kallonta kamar tauraruwa. Sai ya ce cikin murmushi mai ɗaukar hankali:
“Interesting.”
“Welcome… once again.”
Aliya ta matso kusa ta raɗa: “Beb, wannan sir ɗin fa yana kallon ki like movie.”
Indo ta ɗan harare ta “Shut up.”
Sir Siddiq ya ɗora: — “I’m Dr Abubakar Siddiq.” “You can call me Sir Siddiq.” — “I’ll be taking you on Fundamentals of Nursing Ethics & Professional Conduct.”
Dalibai suka yi “woooo”. Indo kuwa— zuciyarta ta faɗi.
"wanan mayen ya fiye kallo wallahi "
Sir Siddiq ya ɗan murmusa kamar ya karanta tunaninta “Class dismissed.”
Yana fita, ya tsaya ya ce: — “A’ishatu… see me after class.”
Indo ta ɗaga kai, idonta ya haɗu da nasa.
AFTER CLASS – PRIVATE CONVERSATION
Class ya watse. Dalibai suka fita ɗaya bayan ɗaya, sai Indo kaɗai ta rage tsaye, handbag ɗinta a kafaɗa, zuciyarta na bugawa amma fuska a nitsuye.
Sir Siddiq ya jingina da desk, ya kalle ta da murmushi: — “Relax, I won’t bite.”
Indo ta ɗaga ido kaɗan: — “I’m relaxed, sir.”
Ya ɗan yi dariya: — “You’re sharp. I like that.”
Indo ta haɗa hannaye a gaba: — “Sir, if this is about class—I'm ready.” — “But if it’s personal, I prefer we keep it professional.”
Sir Siddiq ya ɗan tsaya, ya kalle ta sosai kamar yana nazari: — “Straight to the point. Good.”
Ya matsa kaɗan: — “I just wanted to say… you surprised me.” — “Strong, focused, and different.”
Indo ta ɗan sauke ajiyar zuciya: — “Thank you, sir.” “I’d like to know you more.” — “Outside lectures.”
Nan take fuskar Indo ta sauya, muryarta ta yi laushi amma ta cika da nisa: — “Sir, I’m not interested in any relationship.” — “Especially now.”
Sir Siddiq bai yi mamaki ba. Ya yi murmushi mai natsuwa “Fair enough.” “But can I at least have your number?” “For academic reasons.”
Indo ta yi shiru na seconds. A ranta: — “Ba soyayya bane… number kaɗai.”
Ta fiddo wayarta: “Okay sir “But strictly school matters.”Ya karɓa, ya ajiye lambarta: — “Deal.”
Yana kallonta: “You’ll see… we’ll get along.”
Indo ta juya zata tafi, ta ce: — “Have a good day, sir.”
Ta fita ba tare da ta waiwaya ba. Sir Siddiq ya tsaya yana kallon kofar “Interesting girl,” ya furta a hankali.
DR SADEEQ (ABUJA)
Dr SADEEQ yana zaune a parlour, laptop a gaba amma hankalinsa ba nan ba. Tun safe Indo ke yawo a zuciyarsa “Second semester results sun fito today…”
Ya buɗe phone, ya tsaya kan sunanta. Yayi typing… ya goge. Yayi typing kuma… ya sake goge.
“Why am I scared?” ya tambayi kansa. .. nan ya mata two missed call bata ɗauka ba....
Sai ya yanke shawara ya kira Aliya. Call ta shiga , “Hello sir!” “Aliya… results fa?”
Aliya ta yi dariya “Alhamdulillah sir! “Indo passed very well.”
Zuciyar Dr SADEEQ ta sauke nauyi. Ya lumshe ido “Alhamdulillah…”
Aliya ta ƙara: “She’s doing great.” “Confident… happy… changed.”
Wannan kalmar changed ta bugi zuciyarsa “She okay?” ya tambaya a hankali “Very okay.” “Sir, she doesn’t even talk about home anymore.”
Call ya ƙare. Dr SADEEQ ya jingina da kujera.
“So… she’s moving on.”
Ya miƙe, ya fara tafiya a parlour kamar mai neman mafita a zuciyarsa “Na rasa damar da na samu.” — “Ina sonta… but na ji mata ciwo.”
Ya ɗauki key ɗin mota. — “I need to see her.”
Amma wani sashe na zuciyarsa ya ce: — “Ka bari tunda kasan Abuja kawai zata taho?”
A wannan lokaci, wayar Indo ta vibrate a hostel.
Unknown number.
Text ɗaya ya shigo “Good evening A’ishatu.
This is Sir Siddiq.
Hope you got home safe.”
Indo ta kalli screen, ta yi murmushi kaɗan
ta ajiye wayar zuciyarta “zuciyata har yanzu tana da sunan guda ɗaya.”
" DR SADEEQ "
TSOKACI
A soyayya akwai hana laifi , yau zakuyi faɗa ko ba yafiya ko bada haƙuri idan kukaye kwana biyu ba magana ko fushi a lokacin da kuka haɗu mantawa zakuyi da cewa kunyi faɗa ko kun samu rashin jituwa domin zuciyar ku wa sunan ku kawai take bugawa wannan ittace ake cewa soyayya gaskiya ƙauna da shakuwa sun samu muhalli a zuciya ku , hakan zaisa kuye mararrin juna , kamar yadda ya faru da Indo da Dr Sadeeq, ta manta cewa taye fushi dashi ......
Allah ka haɗa mu da soyayya ingantacce.
