Auren Wata Uku Page 36-40 na Sameena Aleeyou

*AUREN WATA UKU..!*

*36*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy “Kina iya sanar da D’anki zunubanki idan kinso. I’ll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D’anki ku min sanadi ba .” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.



Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k’afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata “Tell me Mommy. Wacece Fannah.?”


Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D’an nata kafin ta jinina Kai “She… She was your Dad’s wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu.”


Haidar ya jinina Kai a hankali “So Daddy yanada wata matar a baya.?”


Mommy ta jinina Kai a hankali.


“What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?”


Mommy ta girgiza Kai a hankali “I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba.”


“Meyasa kika nemeta.?” Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.


Ta d’ago tana dubansa “Dan na nemi yafiyarta.”


Ya kuma jinjina Kai “So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?”


Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai “Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak’ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D’ah na.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido. 


Waiwaye…


Years back..!

Borno State, Maiduguri.



Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokacin da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik’e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d’aya b’angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo “Kwaise an d’aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah..” Yanda yake maganar zaka fahimci kaman Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k’arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad’i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k’araso ta sameta. Asshe k’anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik’on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani girme mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa. 


Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya “Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d’iyar leburan dake aiki k’arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka. Asshe Aliyu na ya aure ‘yar wann mutumin..!” Ta kuma rushewa da kuka.


Asshe ta dubeta cikeda tausayawa “Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Miki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k’addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k’ark’ashin ma’aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata dan ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud’i ga k’uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k’addarar hakan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki.”


Mommy ta dago tana share hawaye “Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar ‘yar lebura.”


Asshe ta furzar da huci “Toh ya kike so ai yanzu.?”


Mommy bata iya bata amsa ba sai mik’ewa da tai ta shige k’uryar daki wani sabon kuka na taso mata. 

Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek’ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa ci ranan. 


Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek’en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k’asa. A haka suka shigo har parlorn gidan. 


Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k’araso jikinsa duk a mace “Kwaise. My love..” Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu. 


A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta “Wann shine k’addarar mu Kwaise. Allah ya k’addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k’ark’ashina.


Mommy na hawaye take girgiza Kai “Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k’ara aure Aliyu. Addini ya halatta maka auren mata d’ai d’ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok’a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu.”


Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata “I love you Kwaise.. So much..! Ban tab’a son wata mace sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu’a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I’m not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki baida match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise.” 


Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k’ak’aro murmushi ta riko hannayensa “You can do this in sha Allah mijina. I’m here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira.” 


Kaman rak’umi da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba. 


Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba.  Asshe taita mamakin canzawan ‘Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk’asa k’aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye. 


Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita asibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d’aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai  Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal ‘yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d’ebesu gaba daya suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta. 


Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d’aukesa kusan wata guda. 


Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d’an girgiza Kai tace “Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na mata da ake fad’a.”


Murmusawa Mommy tai “Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me.”


Asshe ta girgiza Kai “Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?”


“Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k’afa akansa da Kansa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak’anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba.”


Asshe ta girgiza Kai “Amma ta ya zakiyi hakan.?”



Mommy ta kuma gyara zama “Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila’ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake  aiki k’ark’ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta.”


Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya “Toh ya abin zai kasance.?”


Mommy ta kuma murmusawa “Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K’anwata.”


Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta “Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan.”


Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d’akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne.” Ta k’arashe tana sakin murmushi. 


Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba. 


Fannah da fitowarta kenan daga band’aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d’auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had’ida toshe bakinta da k’arfin gaske. Fannah tana kuka tana k’ok’arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta. 


 Daddy ya dawo cikeda d’oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b’angaren ta d’aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k’ato rungume da matarsa dake d’aure da towel  ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa. 


Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad’in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata. 


Daddy ya shak’osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b’acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d’aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad’in “Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba.”


Daddy ya dubeta da mamaki “Dama ya Saba zuwa.?!”


Mommy ta jinjina Kai kaman gaske “Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa.” 


Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace “A’ah.. Wann mutumin ai mak’ocin su k’awata Baana ce. Kuma ta…” Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana.


Mommy tace “Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?”


“Ta sanar dani shi d’in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!” 


Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k’arfin ta “Haka ne.? Wann D’an iskan saurayinki ne.?!” Ya tambaya yana dubanta.


Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa “Ki amsa min..! Haka ne..!”


Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad’in “Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk’ar so. Kuma mahaifinta ya min alk’awarin bani ita.. Amma ‘yanuwanta Sun karya wann alk’awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu’amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!” Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b’arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka. 


Daddy ya ci gaba da huci “Ga b’arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la’akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk’a sa ma shayibu yana fad’in bari yaje ya duba section d’insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d’insa na cikin gidan an kwashe kud’ad’en ciki. 


Koda aka mik’a Auwalu ma ‘yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud’ad’en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud’ad’en dan su gudu su bar gari. 


Daddy bai saurara daga b’angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar. 


Sosai take kuka duk’e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari.” Yana ida fad’in haka ya mik’e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari. ‘Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad’in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k’ila da an fara k’irga ma abinda ta haifa watanni. 


Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k’ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu. 


Sam bata San Daddy ya shigo ba take b’arin zance.


Daddy ya dubeta da mamaki “Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!”


Sai Mommy ta mik’e tana girgiza Kai “A’a Engr dan Allah ka saurareni.”


“Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud’e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma  mata..? Kece kika shirya komai..?!”


Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai “Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi  ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba..”


Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa. 


Mik’ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d’inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d’aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab’akar da tai sabida halin k’unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu’amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k’unci hopping idan ta haihu zuwan D’an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa “See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d’an da zakai alfahari dashi.”


Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin.


Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik’e cikin hannunta baiba balle ya karb’e sa. Sai ma mik’ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D’anta sai hidiman bunk’asa Kasuwancinsa da yake. K’unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d’awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D’anta da Daddy yai take. Ta duk’ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d’an matsayin D’a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta’allak’a ga bunk’asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad’ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab’a ganin k’ok’arin Haidar ba har kawo girman sa.


Wann kenan.


(Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan ‘ya’ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da ‘ya’yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa).


*

Ci gaban labari..



Haidar ya share hawayen da suka zubo masa “So that’s the reason why he hates me.!” Ya fad’i haka Kansa a kife.


Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata “No Haidar.. Your Dad doesn’t hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That’s just.. his way of punishing me.!”


“Well I don’t care.!” Ya fad’i haka yana mai buga teburin gabansa da k’arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad’in “I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.!” Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake. 


Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai “I’m sorry my Son.. I’m sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!”


Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d’agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa.


Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta “Serving jail sentences won’t be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won’t rest until I see you locked up in jail..  Koda zaki k’arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don’t want to see your face ever again.!” Ya k’arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik’e ya nufi k’ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k’ofa ya fice cikin tsananin huci..



SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*




*37*







*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*





A tsorace ta d’ago tana dubansa. 


 “Can you walk.?” Ya tambaya yana dubanta itama shi take duba. Ganin bata ce masa komai ba sai ma rawa da jikinta keyi alamun dai batada strength har lokacin yasa bai kuma yin wata wata ba ya fiddota daga cikin motar. 


Ganin haka yasa ta soma girgiza masa kai tana fad’i cikin rawar murya “A’a dan Allah.. Ina ne nan… Ina ka kawo ni..?!” Cikin muryarta da bai fita sosai take maganar.


“Shut up. Just shut up.!” Ya fad’i still tana cikin hannunsa. A haka ya tura k’ofan parlorn suka shige. Ko ina an rufe da farin kyalle alamun dai babu mai zama cikin gidan. Wani d’aki ya bud’e ya ajeta saman gado. 


Ta d’ago a tsorace tana dubansa had’ida girgiza Kai ganin na k’ok’arin ficewa. Da tangadi ta nufo k’ofa tana fad’in “Dan Allah.. Kar ka barni a nan.. Ka Kaini wajen Mommy dan Allah ina buk’atan ganinta.”


Haidar ya d’auki lokaci yana dubanta kafin ya tako zuwa gabanta “Look, I don’t intend to keep you here for good. If you cooperate with me.. Bazaki jima a nan ba zaki tafi.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofan ya rufe kirif.


Ummul ta duka a wajen tana dukan k’ofan da d’an sauran strength dinta tana fad’in dan Allah ya bud’e ta ya barta ta fita. 


Shiru babu agaji ba taimako, Haidar bai bud’e ta ba sai sautin tashin motarsa da taji. Ta rarrafa da kyar ta isa jikin window nan ta hangi hancin motarsa na barin wajen. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Jin zazzabi mai zafi na sauko mata.


**


Anisa ta dubi Dr “Dr wann ai kidnapping ne. We need to see your security footage.”


Dr ya murmusa “How is that a kidnap.? Haidar shi ya d’auke matarsa.. He’s her legal Husband.. So wann ba kidnapping bane.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.


Anisa ta furzar da huci “But still you are her Dr. And it’s your duty to call him and tell him exactly the consequences of what he’s done.. I mean, she’s still recovering.. She needs to stay here at the hospital.” 


Dr ya dubeta still murmushi saman fuskarsa “If you excuse me Miss. I have some patients to attend to.” Ya k’arashe yana mai shigewa.



Anisa taci gaba da huci “Ahhhg! Imbecile.!” Ta fad’i tana sakin huci. Wayarta ne ya soma ringing. Ta duba taga Leenah ce. Gajeren tsaki tai had’ida kin d’agawa. Leenah ta kira har kusan sau uku Anisa bata daga ba sai ta turo mata SMS. 


_Remember you only have 2 days_



Tsaki Anisa tai tana sakin huci. Yanzu ya zatai ga wann D’an zafin Kan ya d’auke Ummul wacce take tunanin itace last alternative d’inta. Kodai Hilal ne zata kira.? Ta d’anyi gajeren tsaki kafin ta soma Neman layin Hilal.


Bugu biyu Hilal ya d’aga “How’s my fish brain sister doing.?” 


“Zanci k’aniyarka Hilal.” Anisa tace a hasale Jin ya kirata da sunar tsokanar da ya saba kiranta tin yarinta fish brain. 


Hilal ya dara “Hey easy. Nayi kewar tsokanarki ne. How have you been.. Bazaki zo bane sai na tafi.?”


Ta dan rausayar da ido had’ida furzar da huci “Yaushe zaka koma school din.?”


“Nayi postponing akwai abinda nake a nan.” Ya bata amsa Kai tsaye.


Anisa ta dan zaro ido “Kuma Abba na sane da haka.?”


Hilal ya dara kad’an “He doesn’t need to know.. Wani Abu kawai zan k’arasa sai na tafi.”


Anisa ta jinjina Kai “Hey Hilal, brother… Alfarma nake nema.”


Hilal ya kuma d’an darawa tinda yaji ta fara kashe murya tana kiransa brother yasan abu take nema wajensa “Fad’a kawai meye kike nema wajena.?”


Anisa ta furzar da huci “Money Hilal. Kudi nake nema wajenka.” 


Hilal ya kuma darawa teasingly yake fad’in “Kuda kuke Abuja gaki ga shugaban k’asa ina zan samo kudi a state na baki.”


“Hilal I’m being serious here. Da gaske kudi nake nema. And it’s urgent.” 


“Ok fine. Nawa kike nema.?”


“1M..!” Ta fad’i kaman mai tsoro.


Dariyar rainin hankali Hilal yai “What.! Are you kidding me Neesa.. 1 million a wajen D’an makaranta irina..? You’ve got to be kidding me. Why not ask Abba. shine D’an kasuwan bani ba. And hey I’m not his manager.” 


Anisa tace “Haba Hilal. Nasan kanada hanya Shiyasa na kiraka.. Wllhi ina tsananin buk’atar kudin nan. Look zan biyaka da zaran na samu.” 


Hilal ya d’anyi Jim Jin tayi sounding serious. Shima sai ya daina wasa “Wait Anisa. Be honest with me.. What have you got yourself into..? Gambling kika fara..? Dan nasan dai ba business din da kike. Kodai kinje kin hadu da wasu scammers ne.?” 


Anisa ta rausayar da ido “Hilal dan Allah ka taimaken mana nasan Abba naji dakai wllhi na rantse maka da Allah matsala nake ciki. Haba Hilal meye amfanin ‘yanuwa ma junansu idan bazasu rufa asirin juna ba. Nasan Mommy zata bani idan tasan ina nema amma bana so ta sani. Kasan masu kudin nan the moment suka gane abun hannunsu ya rufe maka ido akwai matsala.”


Hilal ya d’anyi jim “Anisa ni fah kudin dake account dina pocket money na ne. Kuma idan har na baki su yanzu za’azo a shiga tsakiyan semester ne ina nema. And kinsan Abba komai da lissafi yake bazan zo masa da labarin rashin kudi ba tinda yasan ya sallameni. Cewa zai wasa nake da kudi sai naje nai ko aikin k’arfi ne a can na ci da Kaina.” 


Anisa tace “But you are his favourite.”


“Even so Neesa. Kinsan yanda mahaifinmu yake idan aka zo maganar kudi.” 


Zata kuma magiya Hilal yace “Fine… Zan tura miki.. Amma ko da wasa kar ki bari ko Ammi tasan na baki banso na hadasu fad’a da Abba.”


Anisa tai alaman zipping bakinta da yatsa kaman Hilala na kallon ta “An gama my dear Brother. That’s why I so much love you.” 


Da haka Anisa taita gwada Hilal tana fad’in irin son da take ma tilon dan uwan nata. 


Gama wayar da zatai ta waigo gabanta yai wani irin fad’uwa samakon ganin mutum da tai tsaye bayanta. Taci gaba da yatsina fuska tana dubansa “Malam lafiya.? Wanene kai.?”



Huci kurum Hisham yake yana dubanta kaman zai shak’ota. Yaci gaba da jinjina Kai yana fad’in “Nasan kece.! Kece kika tassama kashe Ummul.!”



Anisa ta zaro ido waje ganin stranger da ko saninsa batai ba yana fad’in laifin da ita da Laila suka binne. Ta soma girgiza kai tana fad’in “No.. I don’t know what you are talking about Malam. Meyasa zanyi yunk’urin kashe Ummu. What could be my motive.? Wait why am I even explaining myself. I don’t even know you. Excuse me.” Tasa kai zata shige. 


“You are the only person with the motive to kill her.. Because you love Haidar.. Haka ne.?” Ya k’arashe yana tsareta da ido.


Anisa taja Birki tana dubansa shaye da mamaki. Sai ta soma girgiza kai kad’an ganin dai guy d’in nan da gaske ya sansu “Mai kake nufi..? Wanene Kai.?” 


“Na tuna miki ne. Kwanakin baya lokacin da motar ki tabi bayan motar Haidar. Cikin k’ok’arin bin bayansa da kike dan ki gano yanda yake zuwa. Someone hit your car and stopped you from following him.. That someone.. Was me.. Ni ne na bigi bayan motar ki na hanaki bin bayan Haidar.” 


Anisa ta soma tuno kwanakin baya Mommy tasa ta bi bayan motar Haidar dan gano yanda yake zuwa amma sai tai accident a hanyar ta wata mota da bata tantance ba ta bugi bayan motar ta Wanda hakan Ya hanata bin bayan Haidar.. Kenan wann mutumin ne Ya bigi bayan motarta. Ta d’ago a d’an firgice tana dubansa “Wait.. Kaman nasan fuskarka.. Wait… Aren’t you friends with Haidar.?” Ta dan murmusa tana girgiza kai “Oh now I understand.. Are you his watchdog.? Trying to play best friend of the year.? Wow you try..” Ta d’anyi shiru tana dubansa “Don’t you think… you are over reacting.. I mean, matar abokinka kake karewa irin haka.”


Hisham Ya fahimci Anisa shashasha ce kuma zata zamto makami mai k’arfi da zai amfani da ita wajen k’watan Ummul daga wajen mortal enemy d’insa Haidar. 


Anisa ta murmusa tana dubansa “Or maybe it’s the other way around.. Mai kake tunanin Haidar zai yi.?  if he finds out that his coworker or should I put it this way… His friend is in love with his wife… Kodai ku masoya ne dama tintinin.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido.  


“Think whatever you want to think.!” Ya k’arashe yana matsowa kusanta kaman zai shak’ota tana k’ok’arin matsawa baya. 


Anisa taci gaba da Zare ido “Malam idan baka k’yaleni ba zan maka ihun b’arawo.!”


Yaci gaba da jinjina Kai “Go ahead and shout! Let see waye yakeda abun fad’i ma ‘yansanda.”


Sai kuma tai shiru tana ci gaba da Zare ido. Hisham yaci gaba “If you dare think of hurting Ummul.. Believe me I’ll deal with  you myself.!”


Cikeda tsoro had’ida mamaki Anisa ke dubansa. Sai kuma ta girgiza Kai tace “And… who are you to Ummul.? Dan ban yarda kana son kareta ne kawai dan kana abokin Haidar ba.”


Kallon shashasha yaci gaba da yima Anisa dan da tasan lokacin da ya bugi bayan motarta Ya hanata bin bayan Haidar ba don Ya kare Haidar yai ba sai dan ya hanata gano Matar Haidar da Ahalin Haidar d’in basu san da ita ba wato Dareen da wann doluwar bata tsaya tana bata bakinta ba. 


“Idan kika sake yunk’urin cutar da ita .. Sann ne zaki san ko ni waye.”



Anisa ta murmusa tana dubansa “Ta Ya zan cutar da ita balle Har ka bata kariya bayan an riga an d’auketa.”


Hisham Ya dubeta ya kuma girgiza kai da mamaki “Kina so kice mun Ummul bata asibitin nan.?! Is she kidnapped or something.? Waye ya saceta.?”


Anisa ta kuma murmusawa “One question at a time. Wanda ya fimu kusanci da ita daga ni har kai shi ya saceta.. Ina nufin mijinta..!” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. Zuciyarta na tabbatar mata abokin Haidar son Ummul yake ba tareda sanin Haidar d’in ba. Amma ita idan har haka Ya tabbata ribanta ne dan zasu had’a team mai k’arfi wajen ruguza tsakanin Ummul da Haidar. 


“Ina Haidar Ya kaita.?” Ya tambaya yana duban Anisa.


Anisa ta murmusa “Why not ask him.. After all, abokin ka ne… Kasan me.? Although Haidar never introduce his friends to his family na rasa gane ya akai nasan fuskarka matsayin abokinsa… Koda yake wann Dan uwan nawa bamuyi zaton ma nada abokai ba.. Maybe kaima d’in dan wajen aikinku d’aya ne Shiyasa.. Im sure na tab’a ganinka ka kawo masa wasu takardu da Ya danganci aikin company gida.”


“Shut up.” Hisham ya katseta jin tana sunbatun da babu Wanda Ya tambayeta. Yaci gaba da dubanta “Kina jina.. Yes ina son Ummul. With every fibre of my being. Hasalima ni na fara sonta kafin ta zama matar Haidar.. You and I are going to help each other out. Ina so ki tabbatar min cewa my secret is safe with you kaman yanda naki ya zama safe dani. That is idan kina so mu raba su biyun.. Ki mallaki Haidar na mallaki Ummul.. Zan iya tabbatar Miki with my help.. Haidar will be yours forever..”


Anisa ta zaro ido waje “Da gaske kake.. Let’s team up then.. Zanyi komai.. In fact kokari kullum nake dan burina Ya cika.”

 

“Your wish has been granted..” Ya fad’i yana jinina kai. 


Take sukai exchanging phone number cikin k’ok’arin yanda zasu fara zartar da plan dinsu na k’ok’arin raba Haidar da Ummul. 


Tsaye Hisham yai a dakinsa na sirri Wanda hotunan Daddy Mommy harma da Haidar sune kawai a cikin d’akin an mammannasu jikin wall. Had’ida  dangin magazines masu d’auke da labarun Maitama Builders. Da duk wani article da ya k’unshi scandals wanda sukai  popping a labarun kasuwanci wad’anda suka danganci Kampanin Maitama da ahalinsa. kaf shi yake fitar da scandals d’in. Yai tsaye gaban hotunansu yana kallo lokaci guda yake furta “Why Ummul.? Why her..? Menene dalilinku na kawo Ummul cikin wann messed  family din naku.!” Yakai dubansa kan hoton Mommy, lokaci guda yaci gaba “Kwaise Maitama ya kikaji zaman kurkuku.? you are the one who instigated everything.! You should suffer the consequences.. All the hardships nida mahaifyata had to experienced. Kece kika jawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “It is your fault that  I had to search for people who would accept me all my life..?!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa. Yaci gaba da jinjina kai “You are now in Jail… Ke d’in yanzu kina tsare a kurkuku.. Abin takaicin kuma D’anki ne Ya kaiki. Did you know that… I was born in a prison..? Did you know that I grow up thinking ni ba kowa bane but a son of a criminal..?! Yai maganar cikin tsananin sakin huci kafin yaci gaba “This is the perfect time for me to ruin your life completely kaman yanda kika lalata nawa. Yanzu ne lokacin da ta kamata na fitar da labari akanki. Kinyi yunkurin kashe matar D’anki. Ya kika ji labarin Kwaise.? Abun zai matuk’ar k’ayatarwa musamman a shafukan labarun kasuwanci. Dan na tabbata Aliyu Maitama ba korar wulakanci kawai zai Miki ba muddin kika bata masa suna irin haka a duniyar kasuwanci. Zai tabbata dake da D’anki da kika koreni sabida shi naku rayuwar ya daidaice fiyeda yanda nawa rayuwar da na mahaifiyata ya daidaice. Saidai kashh.! Ummul ta shiga cikin wann ahalin naku. She shouldn’t get involved..! She shouldn’t.!” Yaci gaba da jinjina Kai yana sakin huci “Kaman yanda nai alk’awarin tarwatsaku haka nai alk’awarin fitar da Ummul daga wann ahalin naku. Sai na rabaka da Ummul Haidar domin kuwa ita d’in tawa ce.!” Ya k’arashe yana duban hoton Haidar da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja.


**



Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k’asa zazzabi Ya gama lullub’e ta. A hankali Haidar Ya tura k’ofan d’akin hannunsa rik’eda manyan ledodi. Hangota da yai kwance saman rug ya sanyashi saurin sakin ledojin Ya k’arasa  gareta. Ya kai hannu ya tab’a goshinta ganin sai rawan d’ari take. Nan yaji jikin nata zafi k’au. A hankali ya furta “Oh no she’s burning up. What do I do..?!” Ya furta yana dubanta gashi ya mance magungunanta a pharmacy din da ya saya. Wani tunani ne yazo masa yai saurin d’agota daga k’asa Ya daurata saman gado ya shiga janyo bargo yana rufa mata ganin sosai take rawan sanyi.. Ya soma rurrufe windows trying to keep her warm. dan dik shi a tunaninsa haka ne zai sauk’ar mata da zazzabin ta daina jin sanyi. Amma sai yaji kaman zafin jikin ya karu ga rawan sanyin da take ya karu. 


Yai tsaye yana kallonta yana tunanin abunyi.. Ko room heater zai fita Ya nemo Yai warming dakin dashi..? Ya nufo waje sauri sauri yana tunanin nemo room heater. Cak kuma yaja Ya tsaya kaman Wanda aka dakatar dashi. 


“Dr Faruk.” Ya furta a hankali kafin ya soma jinjina kai “Yes I need to call him..” Ya k’arashe yana mai Ciro wayarsa daga aljihun jeans d’insa. Nan ya soma dialing layin Dr. 


Dr yana dauka Haidar Ya soma sanar dashi cewa jikin Ummul yayi zafi sann Ya mance bai taho da maganin ba. Meye first aid da ya kamata ya soma bata. 


Dr Faruk ya murmusa daga d’aya b’angaren. Soyayyar Haidar ga matarsa na kashesa “A cool shower will help.. And she should wear lighter and more breathable clothing.”


Haidar ya jinjina kai yana nanatawa “A….. cool shower.. Ok, cool shower..” 


Dr ya kuma amsawa yana mai fatan samun sauk’i ga matar Haidar d’in. Haidar yai masa godiya kafin yai hanging up. 


Dawowa d’akin yai Ya ganta nan yanda ya barta saman gado tana rawar sanyi. Yai saurin k’arasawa Ya yaye bargon da ya rufa mata. Ya soma k’ok’arin rage mata tufafin jikinta amma sai ta takure jikinta waje guda tana fad’in Ya kyaleta dukda rawan sanyi da take. 


Cikeda takaici Haidar yai jifa da hulan da ya zame daga saman kanta “Fine then, take the shower like this.” Ya k’arashe yana mai dagota daga saman gadon Yayinda Ummul ke k’ok’arin tattaro sauran strength da ya rage mata tana janyewa daga jikinsa tana fad’in ina zai kaita ya kyaleta.


Bai tsaya amsata ba Ya nufi bathroom da ita cikin hannunsa. Taci gaba da k’ok’arin turasa Haidar na rik’eda da ita yana fadin “Stay here and take a shower. You are burning up.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin tsaida ita kan k’afafunta amma sai ta soma k’ok’arin zubewa a k’asa sakamakon rashin karfi. Bai bari takai kasa ba yai saurin k’arasowa ya rungumeta cikin jikinsa a daidai lokacin hannunsa ya tab’a switch na shower din ai kaw nan ruwan ya soma zubowa kawunansu su duka biyun. Sauk’an  ruwan da taji saman jikinta a bazata ya sa ta sakin ajiyan zuciya Wanda yasa Haidar yai mata cover da arms d’insa kaman mai tsoron kar ruwan Ya cutar da ita. Ya shigar da ita sosai cikin k’irjinsa ruwan naci gaba da zubowa kansu. Yana jin yanda ruwan ke ratsa dumin jikinta zuwa nasa jikin. A hankali Haidar ke lumshe idanunsa yana jin harbawan da zukutansu keyi kaman a tare. 


Sun d’auke minutes a haka kafin yaji temperature dinta na sauka a hankali. A haka Ya fito da ita daga bathroom din su duka biyu jikkunansu a jik’e. Cikin kayan da ya shigo dasu Ya Ciro towel sabo Ya rufa mata. Ya d’auki hand towel din yana tsane sumarsa. Lokaci guda yake furta “Change those clothes before you catch cold.” Yana ida fad’in haka yasa zai fice yayinda Ummul ta mak’ale sosai cikin towel din da ya rufa mata. Tabbas zazzabin da takeji ya dan sauka. Sanda taga haikan zai kuma ficewa ya kulleta a wann dakin tai saurin bud’e murya tace “Dan Allah ka dakata.”


Haidar Ya tsaya Cak sanda yaji muryarta.


Ganin Ya tsaya yasa Ummul ci gaba “Meyasa ka kawoni nan ka kulleni..? Dan.. Dan Allah.. Ka fitar Dani daga kurkukun nan.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya. 


Juyowa yai yana dubanta sai ya dawo da baya. Yai tsaye kanta hannayensa hard’e yayinda Ummul ta soma k’ok’arin jada baya. Sai taji ya soma fad’in “Who are you.? Meyasa kika yarda da auren mutumin da baki taba sani ba. Is that even possible.?”


Shiru tai ba tareda ta iya amsa masa tambayarsa ba sai bugun zuciyarta dake karuwa. 


“Did Mommy buy you with money.? Nawa ta biya ta sayeki dan kawai kizo cikin rayuwana.?!” Ya k’arashe cikin d’aga murya.


Ta soma girgiza kai tana hawaye. Abinda baison gani a rayuwarsa. Yai gajeren tsaki yana kauda fuska gefe jin bata amsa shi ba sai hawayen dake gangaro mata.


“Fine.. Since you don’t want to talk. Enjoy your stay here. Dan bakida ranan fita a nan.!” Ya k’arashe yana mai jifa da hand towel din da ya gama tsane sumarsa dashi zuwa gefenta Wanda saida ya dan firgitata.


Da taga haik’an da gaske zai kuma ficewa ya sanyata saurin fad’in “Nayi ne sabida Iyayena.!” Tai maganar  cikin rawar murya irinta mai kuka. 


Haidar Ya kaikaito yana dubanta. Ya tako zuwa gabanta “Kin amince da auren mutumin da baki tab’a sani ba sabida iyayenki .? Are you that desperate.?!” 


Ta girgiza  masa kai tana hawaye “Kud’in aure na.. Shi…. Shine kudin jinyar Abba na… Sann mahaifiyata…” Ta kasa ci gaba da magana sakamakon rawa da muryarta keyi.


Haidar ya kafeta sosai da ido. Ya dan d’ibi dak’ik’ai a haka kafin yace “So I was right. Mommy sayenki tayi da kudi.. Nawa ta sayeki dashi.?!” Ya k’arashe maganar zuciyarsa na masa zafi.


Ta rintse idanunta sosai hawaye na zubo mata. Ba yanda ta iya dole ta fad’a ma Haidar mak’asudin aurensa koda zai kawo karshen zamansu. Ita dai burinta taje ta fidda Mommy daga kurkukun da ake k’ok’arin kaita. Zatai komai dan ta kub’utar da Mommy matar da tun shigowarta gidan bata nuna mata komai ba face zallan k’auna. 


Muryar Haidar ta kuma ji cikin tsananin huci yana fad’in “You sold yourself to her.. You don’t deserve to go free.!” Yana maganar yana jinjina Kansa. Lokaci guda yasa kai ya fice rai bace. Kallo d’aya zaka masa ka fahimci abun ya masa zafi sosai. 


Ummul ta kuma runtse idonta wasu hawayen na gangaro mata. 


Can dare ta kuma jin shigowarsa dan har tayi zaton bazai kuma dawowa ba. Wann karon bai ko kalli yanda take tak’ure ba ya aje mata wasu ledodi. D’aya na abinci d’aya na magani.


Baice da ita komai ba ya nufi k’ofa. Yana k’ok’arin fita ta rarrafo garesa tana rok’onsa “Dan Allah ka fitar Dani daga gidan nan.. Wllhi tsoro nakeji.. Dan Allah kar ka barni a nan..!” Ta k’arashe tana had’e hannu alamun rok’o.



Wani kallo ya watsa mata kafin yasa kai ya fice yana mai rufe d’akin.


Ummul tai lamo a wajen tana mai lumshe idonta Wanda kuka ya zame masu jiki. Ga dare ga jeji. Bata jin komai sai kukan tsuntsaye. Addu’a kawai take tana kai kukanta ga Rabbil Izza da Ya jibinci lamuranta. 


**


Washe gari Haidar bashi yazo gidan ba sai wajajen azahar. Ta Ida sallah kenan taji tsayuwar motarsa. Ga yunwa da ya azalzaleta. Tin bayan abincin da ya kawo mata bata kuma saka komai cikinta ba. 


Tai saurin mik’ewa ta Lek’a window dan tabbatar ma idonta ko shi d’in ne. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sakamakon tuno abinda ya faru jiya. Tai saurin komawa da baya tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa.


Sanda Haidar ya turo k’ofan kanta a k’asa. Ya dan d’auki lokaci tsaye daga k’ofan yana dubanta. 


Janye idonsa yai daga barin dubanta yana k’ok’arin shigowa d’akin dan shima a b’angarensa yana shigowa Ya soma tuna kasancewar da sukai tare k’asan shower a jiya. Yai gajeren tsaki yana mai shigowa dakin. 


 “Have you taken your meds.?” Ya fad’i kaman baya so. Daga nan yanda yake tsaye. 


Jin bata amsashi ba yasa shi yin gajeren tsaki ya isa ya janyo ledan maganin yana d’aga ko wani maganan Wanda a rubuta dose jikin ko wanne. Nan yaga dai tasha duka. 

Cikin ko inkula Ya aje mata ledan abinci kafin ya tako zuwa gabanta “Ke.!” Ya fad’i yana dubanta.


“Sunana Ummulkhairi.” Ta basa amsa daga nan yanda kanta ke kife. 


Bai ambaci sunan nata a fili ba dukda zuciyarsa ya maimaita the moment she closed her lips. 


Takarda ya mik’a mata “Sign these papers.” Ya fad’i cikeda umarni.



Ta dubeshi ta dubi takardun da yake mik’a mata. Sai ta girgiza kai kad’an “Na menene..?”


“You want be free. Then sign these..!” Ya kuma fad’i yana mik’a mata.


A hankali tasa hannu ta karbi takardun tana dubawa. Dukda ba wai ta fahimci bayanan da suke kan takardun sosai bane. Ta gane takardu ne daga Kotu Wanda idan ta saka hannu tamkar tayi k’arar Mommy ne kai tsaye. Bata San meyasa Haidar ke fad’a da mahaifyarsa irin haka ba. Mahaifiyarsa fah yake yunk’urin kaiwa prison. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Anya yasan k’ima da darajan mahaifiya.? Waye yake fad’a da iyayensa sai tab’ebb’e.


Ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Bazan iya ba.. Bazan iya kai Mommy gidan Yari ba.!” 


Ya duk’o da fuskarsa kusan nata “Why.? Are you even related to her.?!” Yanda yake maganar tamkar fuskokinsu zasu hade waje guda. Ummul na iya jin huci da tururin numfashinsa saman fuskarta mai cikeda tsoro. 


Ya damk’o hannunta da iyaka k’arfinsa yana fad’in she should sign the papers. 


Batajin tana da k’arfin da zatayi kokawa dashi amma abu guda da ta sani shine har abada bazata kai Mommy prison ba. Wani dabara Ya fad’o mata kawai sai ta fashe da kuka tana k’ok’arin rik’e b’angaren da akai mata aiki alamun na mata ciwo. Haidar yai saurin sakinta yana kallon yanda take kuka tana kama wajen. A d’an daburce Ya soma fad’in “I.. I didn’t mean to hurt you… This is your fault you know. Da ace kinyi abinda nace it wouldn’t have to be this way. Wait let me see..” Ya soma k’ok’arin janye rigarta ai sai ta zaro ido da gaske ganin zai dage mata riga. Ta soma turasa cikin tsananin k’idimewa tana fad’in “Ai Ya.. Ya ya daina.. k’alau nake yanzu ka gani..!” Ta mik’e tsaye kan k’afafunta kaman wacce aka razaneta cikin k’ok’arin nuna masa lafiya take ba ciwon dake damunta. 


Ya tsareta sosai da ido. Wato kukan da take acting ne kawai ba ciwon da take ji. Da taga da gaske zai d’age rigarta ta daina acting d’in. Women are so good in acting kaman dai mahaifiyarsa. 


Sai shima ya mik’e tsaye yana binta da kallo daga sama Har k’asa. Ya kula har lokacin kaman rawa jikinta yake. Ai kuwa idan Har haka ne Ya gano lagonta. Zaisa tai signing papers din cikin sauk’i. Ya soma takowa gareta tana k’ok’arin jada baya. 


“Kodai ki saka hannu a takardun nan a dad’in rai… Ko kuma…” Yana maganar yana k’ok’arin balle botiran rigarsa. Bai kuma fasa nufota ba. 


Ta soma girgiza kai hawayen gaske na zubo mata “A’a dan Allah..!” Cikin rawar murya take maganar har saida Haidar Ya cimmata.


Zuciyarta bai daina tsinkewa ba ganin ya mata rumfa “Zaki saka ne ko na sakaki kisa da k’arfi..!” Ya fad’i fuskarsa dab nata.


Dukda zuciyarta dake tsananin bugu bata fasa girgiza masa kai tana fad’in “K’ima da darajan mahaifiya Ya wuce ai fad’a da ita balle a kaita kurkuku duk girman laifinta.!”


Bakinta dake fitar da kalaman yaketa kalla zuciyarsa na kuma masa zafi da kiran Mommy mahaifiya da take dan shi a idonsa Mommy bata canci a kirata mahaifiya ba. 


Jinjina kai yake yana huci  “You think I’m playing here right.?!” Batai aune ba taji ya rufe bakinsa da nata. 


Hankalin Ummul yakai k’ololuwa wajen tashi. Al’amarin da ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta ciki ba sai gashi na k’ok’arin faruwa da ita. 


Numfashinta ne Ya soma fita sama sama… Take taja wani irin numfashi ta zube masa a wajen. 


Ya duk’a yana jijjigata yana fad’in ta tashi ta daina wann wasan kwaikwayon. 


Shiru bata tashi ba har dai Haidar Ya soma tunanin ko sumar gaske ne tai. 


Ya tashi ya fice cikin k’ok’arin kawo ruwa ya yayyafa mata aiko yana ficewa Ummul ta mik’e a guje dikda rawa da jikinta keyi ta isa ta rufe k’ofan dan dama ya bar key d’in jiki.


Da mamaki ya juyo yana duban k’ofan. Ta dai k’ara shashantar dashi a karo na biyu. Ya girgiza Kansa k’adan yana mamakin yanda Ya fad’a tarkon yarinyar Har sau biyu dikda matsalan saurin yarda da yake dashi gashi har sau biyu ya yarda da acting da Ummul tayi.  Lallai da alama wann yarinyar zata basa matuk’ar wahala kafin ya samu ya cimma burinsa na tura Mommy prison. Sai kuma yaji gaba d’aya jikinsa ya sake kaman baida sauran kuazari. Ya isa saman kujera ya zauna gijif had’ida kishingid’a. Ya lumshe idanunsa bugun zuciyarsa na k’ok’arin daidaita. 


**

Police headquarters.



Barr ya dubi Daddy da Mommy ya dan girgiza Kai “Zamu iya making abun Ya zama kaman illegal detention tinda Haidar ya b’oye matarsa babu Wanda yasan yanda take.”


Daddy yace “So does that mean they would let her off the hook.?”


Kafin Barr yakai ga bada amsa Mommy ta katsesu “No.. I don’t want money or power to speak for me.. Iyakacin abinda nake so shine D’a na ya dawo gareni.. I’ll plead guilty, if that’s what it takes… Zan amsa laifin gaban Alk’alai zan tafi prison for Haidar to forgive me.”


Daddy ya dubi Barr yace ya dan basu waje. 


Bayan Barr ya fice ya tsare Mommy sosai da ido kafin ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You don’t know what you are talking about Kwaise. Do you really want to get convicted.? That ungrateful Son of yours doesn’t even care about you..!”



Mommy na hawaye take jinjina kai “Yes.. Zanyi idan hakan zai kawo maslaha cikin rayuwar Haidar. Na rasa shi a farko.. I can’t lose him again.”


Daddy yaci gaba da girgiza kai “You know you can’t appear in court da aurena akanki, bearing my name… Mai kike tunanin sunana zai zama a duniyar Kasuwanci.?!”


Mommy na kallon Daddy take girgiza kai “Then end it Engr.!”


Da tsananin mamaki Daddy ke kallonta. Duk juran zaman da tai a gidansa dukda rikon ko inkula da yake masu daga ita Har Dan nata bata tab’a zab’an rabuwa dashi ba daidai da rana guda sai gashi yau tana fad’in haka kai tsaye. 


“It has always been… an empty marriage that’s hanging by threads… Watak’ila sabida Haidar  ka barni na zauna. Saidai a bangarena na zama lost between zama Mata ko Uwa.. Watak’ila  na zab’i na zauna ne Thinking one day komai zai wuce ahalin Ya daidaita… Na Had’iye komai sabida D’ah na da mijina. I even named him after you… I turned myself into a monster a k’wayar idonsa ba tareda nayi la’akari ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k’aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake… Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k’ok’arin ganin burina na had’e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab’a cika ba… Dik abinda naso ma nawa D’an na hana ma D’an wata ya samu.. Na rabaka da D’anka da matarka… Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad’i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish.” Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk’ar yin sanyi. 


Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba “Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D’anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k’alubali.” Taci gaba da jinjina Kai “I give up Engr.. I’m tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D’ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab’i D’ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata. 


Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k’ok’arin maida hawayen dake yunk’urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yai ta fice cikin sauri. 


Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta  fad’a uku. Dama ita bata tab’a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D’anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok’on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk’a Haidar d’inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak’inin D’anta bazai tab’e ba cikin ikon Allah matuk’a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa. 




SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*




*38*






*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*





Bayan shud’ewan awanni ta mik’e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d’uriyarsa. Window ta lek’a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k’asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d’akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d’ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad’in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab’a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had’ida jingina jikin gini. 


Ta d’auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud’e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k’ok’arin saita kanta. Bata San ya za’ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje  ta ceci Mommy. Har abada bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba. 


Sauri sauri ta isa k’ofa ta murda makullin ta soma k’ok’arin fitowa a hankali cikin sand’a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k’ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik’e hannunta. K’iris Ya rage bata saki k’ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d’ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta. 


A matuk’ar tsare yace “Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?”


Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad’in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k’arfin gaske Ya tura k’ofan d’akin Ya jefata ciki. 


Cikin rawar jiki Ummul ra soma k’ok’arin rarrafowa tana fad’in “Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk’awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!”



“Shiiii..!” Ya mata alama da yatsarsa saman labb’ansa. Ya duk’a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k’ok’arin matsawa baya ganin Ya duk’o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. 


Haidar ya dan d’auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k’ok’arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D’ankwalinta da ya fad’i gefe ya d’auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k’ok’arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D’ankwalin da yai. Ya kuma duk’awa gabanta suna fuskantar juna.


Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba.


A hankali ya soma fad’in “Look, you can call me a monster, but I don’t hate you… And..that doesn’t mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I’ll let you go..”


Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa.


Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a’a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta “Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab’a masa ba. An shar’anta wa mace neman al’jannah a k’ark’ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k’ark’ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da  kake k’ok’arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.?” Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba “Shin akwai D’an Adam din da zai wasa da aljannarsa.?” Cikin k’arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa. 


Katseta Haidar yai da fad’in “Shut up.!” Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba “Who do you think you are.?” Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad’i “You don’t have the right to speak to me that way.?”


Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad’in ‘Ni matarka ce.!’ 


Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had’ida furta  “Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don’t want to live with a monster as a husband.!” Ya k’arashe yana tsareta da ido. 


Girgiza masa kai tai “Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik’i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma..”


Katseta yai da fad’in “Enough.! Ya isheki haka.. You don’t know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!”


Sosai Ummul ta razana da yanayinsa. 


Haidar yaci gaba cikin tsananin huci “Yes you might be right.! Watak’ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k’unci da ta bani.! Yes. Watak’ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time!” Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad’a sukai jazir “She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.!” Yaci gaba “Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant… I had a hard time living in myself..!” Yaci gaba da huci yana jinjina akai “And for years… It took me years to overcome the fear and the trauma..!” Ya matso da fuskarsa kusan nata “Did you know na girma ina shakku da kokonto if she’s really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!”


Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had’ida sassauta murya “So don’t act like you know everything.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk’urin rufeta ba.


Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek’awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b’ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu’an kasancewa cikin aminci. 


Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had’ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al’amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k’asan zuciyarta bata jin shid’in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d’in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak’arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k’addara mai kamanceceniya musamman a b’angaren abinda ya shafi alak’arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad’o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata. 


Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba. 


**


Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k’are cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k’are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak’ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b’oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b’oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab’a sanar da kowa ga yanda ya b’oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k’arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d’in Anisa. Watak’ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Shi Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d’insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik’e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab’a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai. Ya isa ya janyo wani drawer. K’asan drawer d’in ya daga tile guda sai ga wani bak’in tulu an rufe samansa da jan kyalle. Dama shi yake ajiye da wann tulun Wanda hakan yasa ya rik’e Dareen a tafin hannunsa. Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i dukda da ita da sunanta da sumarta da na Haidar aka had’a akai asirin amma batada say dan bata san ina Hisham ya b’oye tulun ba. Shiyasa a kullum take bin Hisham a sannu dan Dodon tsafi ya sanar dasu duk randa wann tulun ta fashe asirin zai karye sann Haidar zai rabu da ita zai nuna bai ma tab’a saninta ba. Koda Hisham yaji haka sai yai wuf ya d’auke tulun ya b’oye dan ya samu ya rik’e Dareen cikin hannunsa ta dinga yin duk abinda ya Umarceta. Wann dalili yasa Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i sabida Tulun na wajensa ya masa b’oyo mai nisa kaman yanda Dodo ya sanar da ita. Hakan yasa Dareen ke bin Hisham a sannu gudun kar ya fasa wann tulun ya karya asirinta na kasancewa matar Haidar. 


Sauri sauri ya fito daga gidan nasa tulun rungume cikin hannunsa.



Dareen na tsaye haraban gidan tana faman safa da marwa ta hangi Hisham na zuwa. Tai tsaye Cak tana dubansa k’irjinta na bugawa. 


Bata Ida razana ba saida ta hangi hannun Hisham rungume da bakin tulun da Dodo ya k’ulla aurensu da sumarta da sumar Haidar ya rufe cikin wann tulun ya kuma tabbatar mata matuk’a wann tulun na nan yanda yake aurensu da Haidar babu abinda zai samesa sai mutuwa ce zata raba. 


Ta nufo Hisham cikin rawar jiki tana fad’in “Finally ka zab’i ka dank’a min ajiyan makullin aurena da Haidar.!” Tai maganar murmushi saman fuskarta.


Dakatar da ita Hisham yai da fad’in “Stay right there.!”


Dareen taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Cikin rawar murya take furta “Hi….Hisham.. What’s going on..?”


Murmushi Hisham yake da gefen baki “You are no longer useful to me.. Kuma kinsan abinda nake da mutanen da basuda sauran amfani wajena.. I dispose them.. Just like this..” Ya k’arashe yana k’ok’arin sakin tulun.


Dareen ta zaburo tana k’ok’arin yowa Kansa “No Hisham don’t do this.. Please kar ka aikata min haka.. Kar ka tsinka igiyan aurena da Haidar.. Wllhi I truly love him..!”


Dariyar rainin hankali Hisham yai “Love.? Did you just say love.. How is that relevant.? Ta ya zakiyi soyayya da mutumin da bashi a hayyacinsa. bai san dake ba ko ince baisan da Aurenki ba.? Ko kuma nace idan ma ya sani auren na fluctuating cikin kansa.” 


Dareen ta girgiza Kai tana hawaye “Watak’ila baisan ya akai Aurenmu ba amma nayi alk’awarin kare wann auren till my last breath. You can’t break our marriage Hisham.” 


Ya kuma murmusawa har lokacin bak’in kwaskon na cikin hannunsa “Na tuna miki yanda akai kuka hadu ne.?”


Ta kasa cewa komai sai hawaye dake gangaro mata.



Hisham yaci gaba “Wani rana ne a airport. Zamu tafi wani construction work Lagos muka hadu dake a jirgi. Tinda naga yanda kike kallon Haidar na tabbata kin kamu da sonsa. Kinyi ta k’ok’arin shige masa amma sai kika lura bazaki samu chance dashi ba. Har dai kaman kinyi giving up. Ni na sameki nai Miki proposing idan kina son Abokina da gaske. Kika kuma tabbatar min zaki iya komai dan kawai ki mallakesa. Na baki zab’i cewa zaki mallakesa amma zaki min aiki a jikinsa. Zaki zame min tamkar spy wacce zata dinga nado min komai na duk abinda yake ciki a rayuwarsa domin Nima na cimma burina Kansa. Dani dake muka had’a k’arfi da k’arfe. Ni na nemo Miki sumar Haidar muka  had’a da naki sumar muka  Kai gaban dodon tsafinku aka k’ulla aurenku da Haidar kaman yanda Dodon ya buk’ata. Ya kuma tabbatar mana duk yanda Haidar yake zai bayyana matsayin mijinki.. Zaki bayyana masa matsayin matarsa.. Haka ne.?”


Taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Hisham yaci gaba da murmusawa “Kiyi gaggawan b’acewa daga cikin rayuwar Haidar. Dan idan kika jira na fasa kwaskwon nan Haidar sai ya kusa kashe ki da hannayensa kafin ya mik’a ki ga hukuma.”


Dareen na huci take dubansa “Na ranste da Allah baka isa ba Hisham. Baka isa ka rabani da abin kaunata Haidar ba.!” Ta k’arashe tana kokawan k’wace bakin kwaskon daga hannun Hisham. 


A daidai lokacin Haidar ya k’araso. Hisham na hangosa yaci gaba da kokawan k’wace kwaskon daga hannun Dareen yana fadin “Allah ne ya toni asirinki mushirika. Ni dama na jima da fahimtar ba tsakani da Allah kike zaune da abokina ba. Kuma  yau sharrinki zai koma kanki dan sai na fasa wann kwaskon da na ganki dashi. Yau Haidar zai fahimci gaskiyar abinda naita nusar dashi akanki.!” 


Aikaw garin kokawan k’wace kwasko ya fad’i k’asa ji kake tasss ya fashe. Sai ga bak’in hayak’i na tashi. Dareen ta saki k’ara tana soshe soshe yayinda Haidar ya Kama Kansa da yai wani irin sara masa. Ya duk’a nan wajen yana rik’e Kansa had’ida sakin k’ara da bai san yana yi ba. Nan ya kwanta wajen tamkar sumamme. Hisham yayo Kansa a guje yana jijjigasa yayinda Dareen ta k’araso tana haki ta dubi Hisham dake jijjiga Haidar Wanda da alama ya sume. Ta nuna Hisham da yatsa “This is far from over Hisham. Ko ince shadow ka tsammaci dawowa ta dan nice zan dawo maka a matsayin Shadow.!” 


Murmushi Hisham yai mata da gefen baki “Kafin ki dawo na Miki alk’awarin na d’auke abinda nake son d’aukewa daga wajen Haidar. Bazaki sameni cikin rayuwarsa ba.!” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda.


Da baya da baya ta dinga tafiya har ta shiga gidan a guje ta soma tattara ya nata ya nata. 


Hisham ya d’auki Haidar ya shigar dashi cikin gidan ya kwantar sa saman kujera. Bayan ficewar Dareen.


Bayan shud’ewar wasu mintoci Haidar ya soma bud’e idonsa da sukai masa nauyi yana jin kaman abin da a kullum yake ji ya masa nauyi a k’irjinsa anyi lifting masa. Wani cunkushewa da yake ji zuciyarsa da kwanyarsa suna masa sai yaji kaman an d’aga masa Abu mai nauyi da aka ajiye cikin k’irjinsa. 


Tilon abokinsa Hisham ya gani zaune gefensa yana danna masa towel saman goshinsa.


Hisham na ganin Haidar ya bud’e ido ya sakar masa murmushi yana hamdala “Alhamdulillah Haidar ka tashi.!”


Sosai Haidar ya mik’e yana k’are ma Hisham kallo “Meke faruwa Hisham. What just happened.?” 


Hisham bai Kai ga basa amsa ba ya hangi hotonsa da na Dareen mak’ale a parlorn ta mak’alk’ale cikin jikinsa. Ya juyo yana duban Hisham zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Sai ya mik’e ya isa jikin hoton yana kallo sosai. A hankali komai yake dawo masa. Tin daga had’uwarsu a airport da irin shige masa da taso yi bata samu k’ofa ba. Dan har wajen aikinsu a Lagos ta bisu. Da tsanar da yai mata. Ya kuma tuna Tabbas yayi zaman aure da ita auren da bazai ce ga yanda aka k’ulla ba. Auren da wani lokaci Ya tuna da ita wani lokaci Ya mance da ita. 


Idonsa naga hoton yake furta “Ya akai na k’are da auren yarinyar nan Hisham.?”


Hisham ya mik’e yana mai furzar da huci. Ya dan tako kusan Haidar d’in su duka biyu suna kallon hoton kafin Hisham yai gyaran murya “Tambayar da na jima ina maka Haidar. Ka mance.?” Hisham yaci gaba “Tun a fari ban San ya akai haka ta kasance ba Haidar. Sanin irin k’iyayyar da Kai ma yarinyar a haduwarku ta farko a airport. Ka tuna.? Ganinka kawai da ita nai matsayin matarka bansan ya akai k’iyayyar da Kai mata ya rikid’a ya koma soyayya ba. Soyayyar da har ta kaiku ga aure. Auren da bayan ni ko iyayenka baka sanar masu ba kuma nima ka haneni na sanar masu.”


Haidar yai shiru kaman mai nazari dan yasan duk anyi haka.


Idonsa ya kada sosai yake duban hotonsu da Dareen yana tuna irin rayuwar da sukai Wanda sai gashi yana son tuno Abu ko tambayarta wani Abu sai ya kasa ko ya mance “How is this possible Hisham.?”


Hisham ya girgiza Kai kad’an  “Baka a hayyacinka ne Haidar.. Kaga wann..” Ya k’arashe yana nuna masa bakin tukunyar da ya fasa.


Haidar ya tako yana duban abun da mamaki. Abun da shi bai tab’a believing ma anayi ma mutane ba balle yayi tasiri akansa. 


Hisham yaci gaba “Kwanaki uku kenan bamu hadu da Kai ba. Naje asibiti wajen d’aya matarka dake kwance asibiti a tunanina zan sameka can ban sameka can ba. Hasalima Likita ya sanar Dani ka d’auki matarka kun tafi babu Wanda yasan ina kuke. So sai nayi tunanin nan gidanka ka kawota maybe ka had’ata da matarka Dareen. So da nazo sai na tadda Dareen rik’eda wann kwasko da kake gani tanata wasu sunbatu more like rituals, kaman ma yare  take dan ban fahimci mai take cewa ba. So sai jikina ya bani wani Abu ba daidai bane. Musamman yanda taketa ambaton sunanka ga yare tanayi ga kuma wann tukunyar cikin hannunta. Koda ta ganni ta razana sosai nan na fahimci my hunch was right. Shine kaga ina kokawan fasawa har Allah ya taimakeni nai nasaran fasa wann kwaskon Wanda ko shakka babu na tsafin ta ne.”


Hisham ya numfasa dan har lokacin Haidar bai iya cewa komai “ Ka gode ma Allah Haidar da ya maida mata sharrinta kanta.” Yai maganar yana mai dafa Haidar d’in. 



Haidar baice komai ba sai komawa parlor da yai ya zauna saman kujera ya k’ura ma waje guda ido. Har lokacin bai dawo daidai ba da alama.


Hisham ya dafasa kad’an “Is not easy.. Abinda kake going through ba abu bane mai sauk’i Haidar. Ace ka zauna da mace ak’alla tsawon watanni shida ba tareda sanin ya akai ka aureta ba akwai tashin hankali… Amma na maka alk’awari zata biya abinda ta aikata maka abokina. I’ll look for her yanda ta shiga ta fita.. we can’t let her get away with what she did to you..!” Ya mik’e yana jinjina Kai alamun tabbatarwa. Lokaci guda yasa kai ya fice da zummar neman Dareen. Kai kace da gaske Har zuciyarsa ya damu da Haidar d’in ne. 



Haidar ya bisa da kallo har ya bace masa ba tareda yace komai ba. Ya jima zaune wajen yanata kallon hotonsu shida Dareen. Bazai ce ga abinda yake ji ba. Saidai wann nauyin da a kullum k’irjinsa ke masa yaji kaman anyi lifting abu mai nauyin. Like he’s free from captivity. Amma freedom da bazaice ga makomarsa ba. Jiki babu k’wari ya mik’e ya fice daga gidan ba tareda ya jira dawowar Hisham ba. 


A b’angaren Hisham kaw ficewa yai cikin k’ok’arin cimma Dareen dan yasan ta yanda zai bullo mata kafin tai gangancin b’ata masa shirinsa. Saidai koda ya fita bai cimma Dareen ba ga wayarta bata shiga. Yaita buga tsaki yai saurin dawowa ga Haidar dan ya samu yaji ina yakai Ummul ya b’oye. Saidai yana dawowa yaga wayam babu Haidar babu dalilinsa. 


Ya buga tsaki yana naushin kujera da hannunsa “Damn you Haidar.! Damn you.!” Yayi duk abinda zaiyi ne dan ya gano yanda Haidar ya b’oye Ummul amma da alama Haidar ya fice ya tafi ba tareda ya jira dawowarsa ba. Bayan duk abinda yai ma Haidar d’in still yai zab’i yaita yin abubuwansa ba tareda ya sanar dashi ba. Haka ya dinga tsaki shi bai cimma Dareen ba bai kuma tadda Haidar ba. Ficewa yai yana dialing layin Anisa.



**


A b’angaren Haidar kaw koda ya k’araso gidan zama yai a veranda dake nan wajen gidan. Bai bi takanta ba bai nemeta ba sai zama da yai ya daura hannayensa saman k’afafunsa Kansa kife tamkar maras lafiya ko Wanda ke cikin yanayin damuwa. 


Ta window ta hangi motarsa. Tai mamaki Jin bataji shigowarsa ba yau d’in. Tai saurin mik’ewa ta yafa mayafin doguwar rigarta ta nufo waje. Nan ta gansa zaune ya kifa Kansa ga tsuntsayen da yake basu abinci Sun kewayesa amma ba abincin yake basu ba. 


Sosai taji mamakin ganinsa haka sai ta soma takowa cikin sand’a kaman mai tsoro ta k’araso Sallama saman bakinta. Amma sai taji shiru bai amsa ba. Ta d’anyi gyaran murya tace “Ka mun izinin…. Zama.?”


Nan ma shiru bai amsa ta ba. Sai dai kawai tai ta maza ta zauna daga can gefe dashi tana satan kallonsa ganin bazai amsata ba. 


Har lokacin Kansa a kife yake. Bai d’ago ba bai ce da ita komai ba. Ta dan sha jinin jikinta sai ta soma kallon yanda tsuntsayen suketa kewayesa alamun suna jira ya basu abinci. 


Ta saki murmushi a hankali tace “Kaman dai… Kai suke jira..” Yanda tai maganar zaka fahimci k’ok’ari take ta had’a kalaman saman harshenta. 


Nan ma shiru bai ce komai ba. Ta d’an k’ara satan kallonsa still yana nan yanda yake. Ta maida kallonta ga tsuntsayen “Bari ni na baku…. idan zakuci nawa.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Har lokacin yana nan yanda yake.


Mik’ewa tai tana satan kallonsa har lokacin yana nan yanda yake. Ta tafi ta dauko sauran abincin da Haidar ya kawo mata na ranan da ya gabata. Ta k’araso a d’arare tana watsa masu sai suka fara tashi sama suna guduwa. 


Ta d’anyi rau rau da ido tana kallonsu “Kaga ni basa son na basu.. dan Allah ka amsa ka basu.. Kaga guduwa suke..” Tai maganar kaman zatai kuka  tana duban Haidar Wanda sai a lokacin ya dago fuskarsa yana dubanta. 



Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i gani da tai fuskar nasa cikin wane irin yanayi da zatace bata tab’a ganinsa ciki ba. Ga idanuwansa Sun kad’a sunyi ja sosai. Duk sai jikinta yai sanyi. Ta sadda nata idon a hankali tana tuhumar kanta mai ma ya kawota yanda yake.? Wata zuciya tace ta haka ne kawai zaki iya fahimtarsa idan har kina son sanin wanene shi. 


Wata Zuciyar ta gargad’eta ‘Anya baki tafi da nisa ba Ummul.?’ Sai ta soma k’ok’arin janye jikinta da nufin barin wajen amma sai taga hannayensa saman nata. Ta d’ago a d’an razane tana dubansa. Shid’inma ita yake duba. Wann karon fuskarsa ya zama pale sosai tamkar ta marassa lafiya. 


Batasan ya akai ba sai ji tai ya rungumeta sosai cikin jikinsa had’ida  kwanto da Kansa saman kafad’arta. 


Zuciyarta yaci gaba da harbawa. Har lokacin Haidar na nan rik’eda ita idanunsa a lumshe. Yayinda jikin Ummul ya gama yin sanyi. Kaf nauyinsa ya d’aura mata saman kafad’arta. Ta kasa katab’us ta kasa koda motsawa Haidar kaw bai saketa ba. Sun jima sosai a haka kafin taji yana sassauta rik’on da yai mata. Ya soma k’ok’arin mik’ewa tsaye fuskarsa a matuk’ar tsare kaman ba shine ya gama rungumarta ba. Kauda kansa gefe yai kad’an  yayinda Ummul tai k’asa da fuskarta cikin sanyin jiki. 


Saida ya mik’e tsaye sosai ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa kafin ya dubeta “Let’s go.”


“Na’am.!” Ta fad’a a dan daburce had’ida dagowa tana dubansa.


“Pack your things we are leaving..” ya fad’i yana nufan mota.


Mamaki ya cika Ummul. Allah mai iko.. Toh kodai Addu’arta ne suka fara karbuwa.. Allah yasa haka ne. Allah yasa Zuciyar Haidar ne ta karkata ga mahaifyarsa kaman yanda take ta addu’a. Cikin sauri ta mik’e tai yanda yace.


Tana karasowa yasa hannu ya bud’e mata front Seat ta shige a d’arare. Tana addu’an Allah yasa ba wani wajen zai kaita ba.


Ita dai addu’a kawai take cikin zuciyarta tinda suka baro wann gida dake tsakiyan daji a cewarta. Ganin sun nufi gari yasa hankalinta ya soma kwanciya. Bata Ida mamaki ba saida taga sun doso wani dogon gini mai d’aukeda ‘yansanda tin daga waje.


Suna isowa yace ta fito. 



Tai yanda yace tana biye dashi suka shige cikin ginin. 


Haidar ya nuna mata wajen zama kafin ya k’arasa yai magana da wasu ‘yansanda. Dawowa yai yanda take ya zauna daga gefe. Sai faman rabe raben ido take tana duban wajen. Can ta hango Mommy tafe ta nufo yanda suke.


Cak Ummul ta mik’e k’walla na ciko idonta yayinda idon Mommy ma ke k’ok’arin zubda k’walla. 


A hankali Ummul ta furta “Mommy.!”


Tuni Ummul ta soma takowa zuwaga Mommy su duka biyun hawaye ke zubo masu. A yayinda suka cimma juna kuwa sai suka rungume juna suna masu bursting cikin kuka. 



Mommy ta tallafo fuskan Ummul tana duba murmushi saman fuskarta “I knew you’d come…” Shiru tai tana duban Ummul d’in kaman wacce ta tuna wani abu. Dan ita dai Mommy har kawo wann lokacin gani take turaren da boka ya basu ne mai guba ciki Wanda ya tassama ajalin Ummul. 


Hannayen Ummul ta kamo, tana mai kuma k’ak’aro murmushi “Are.. You here to withdraw the charges against me..? Zaki janye k’aran dake kaina..?”


Saurin girgiza Kai Ummul tai “A’a Mommy dama babu wani k’ara.. Dan Allah kar ki fad’i haka.. Ina Jin kaman laifi na ne da aka ajeki nan… Kiyi hak’uri banzo da wuri na fiddake ba Mommy..!” Ta k’arashe cikin rawar murya.


Murmushi Mommy ta kuma yi tana mai rik’e hannayen Ummul cikin nata sosai “Baki mun komai ba Ummul face alkhairi… Just like your name.. Ke d’in alKhairi ce.!”


A hankali Ummul ta sadda idanunta k’asa. Allah sarki sai ta soma tuna kalaman da Mama da yaranta harma da mutanen unguwa ke jifanta dashi wani sa’in harda nata mahaifiyar cewa sunan bai kamaceta ba babu wani alheri tattare da ita sai akasin sa. 


Mommy takai dubanta ga b’angaren Haidar Wanda ke tareda ‘yansanda ga lawyer d’in Mommy ya iso suna kula da al’amarin. 


Ko kallo Mommy bata ishesa ba. Sanda ya k’araso yanda suke Ummul kawai ya duba fuska a matuk’ar tsare “Let’s go..” Har ya juya zai soma tafiya sai ya kuma juyowa ya dubi Mommy “Your driver will be here to pick you.” Ya maida dubansa ga Ummul “Don’t waste my time.!” Yana ida fad’in haka yasa kai yai shugewarsa cikin sassarfa.


Ummul ta bisa da kallo jiki a sanyaye sai kuma ta juyo ta dubi Mommy. 


Jinjina mata Kai Mommy tai murmushin k’arfin hali saman fuskarta “Just go. Go with your husband.. Don’t worry about me I’ll be fine.. Ya k’ira driver zai zo ya d’auke ni. Tashi kije kinji. Allah ya tsareku yayi maku albarka.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. 


Jiki a sanyaye Ummul ta mik’e. Mommy ta bita da kallo zuciyarta na mata sanyi. 


Ficewar su Ummul da kad’an ta hangi Daddy na shigowa.



Sosai mamaki ya cika Mommy ganin Daddy yana shigowa. Toh mai ya kawosa.? Ta zaci zai rabu da ita kaman yanda ta basa zab’i. Ta zaci zai zab’i Kasuwancinsa da reputation d’insa sama da ita da D’anta da a kullum yake ikirarin basuda wani amfani cikin rayuwarsa. Take kuma zuciyarta ta soma raya mata toh kodai zuwa yai ya tabbata ya yanke sauran alak’arsa dake na har abada.? Kodai zuwa yai ya tabbata bazaki koma gidansa ba daga nan.? Dukda bugun zuciya da tunanin ya haifar mata hakan bai hanata kauda fuska tai kaman bataga zuwan Daddy ba. 



Ya k’araso yana mai gyaran murya. Dan ya tabbata taga zuwansa amma tai biris dashi. 


“Barrister called….. and told me you are free now.” Ya fad’i  daga nan yanda yake tsaye.


Ta kaiakito da kyar tana dubansa, bata ce komai ba sai ta kuma kauda fuska.


Daddy ya had’iyi abinda ya tsaya masa “Shall we go now.?” Ya fad’i a hankali.


Bata tashi ba sai ta girgiza kai “Haidar ya kirawo driver na zaizo ya d’auke ni..”


Da mamaki Daddy ke girgiza Kai “Kwaise did you hear yourself.? Ya inace miki ki tashi mu tafi kina ce min Haidar ya kira driver..”


Mommy ta kaikaito sosai suna fuskantar juna daga nan yanda take zaune “You shouldn’t be here in the first place.. Kai babban mutum ne dake jagorancin babban kampani.. Bai kamata a ganka a waje irin nan ba. It won’t be good for business and your reputation.” 


“Enough Kwaise. Nasan ina kalamanki suka dosa.. But this is not the right place to talk about that.. Ki tashi mu tafi gida then we talk..”


“Kai hakuri kaje kawai Engr. I don’t want to go with you..” Mommy tace cikin Shan k’amshi. 



Mamaki ya mugun cika Daddy. Shine Kwaise take turning d’insa down. Ya baro tulin ayyuka tinda Lawyer d’inta ya kirasa ya sanar dashi halin da ake ciki cewa Haidar yazo da matarsa kuma an janye k’ara Akan Mommyn.


Yai mugun tsarewa “Haka kika ce.? Fine, ki sani duk direban da yazo ya d’aukeki a bakin aikin shi.” 


Ta dubesa da mamaki “Zaka koreshi aiki dan yazo d’aukata.?”


“Of course I’ll have him fired.” Ya bata amsa Kai tsaye.


Mik’ewa tai “Shikenan ni zanje na shiga motan haya..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa.



Yai saurin dakatar da ita “Umarni nake baki a matsayina na mijinki.. Idan har zaki bawa matar D’anki umarni da tabi mijinta Ashe ke ya kamata ki fara bin umarnin naki mijin.”


Yanzu kuma ta nan ya b’ullo.? Kenan ya jima da zuwa station din Akan idonsa tace ma Ummul tabi Haidar. Ba don taso ba sai dan babu yanda ta iya haka tabi bayansa kaman rak’umi da alkala. 


Har suka iso gida daga ita har Daddy fuskokinsu babu walwala babu mai cewa da kowa komai. Abun sai mamaki yake ba ma Daddy wai Kwaise ke banza dashi irin haka. Matar da tsawon zamanta a gidan tin bayan abinda ya faru batada buri face taga itada D’anta sun samu attention d’insa. 




Koda suka isa gida basu tadda motan Haidar can ba. Addu’an mommy d’aya Allah yasa ba wani wajen Haidar ya kuma kai Ummul ba. 


Suna isa Mommy ta bud’e k’ofa ta fice. Daddy yai saurin fitowa had’ida dakatar da ita.


“Kwaise what’s with the attitude.? This is not like you..? Ya kike Abu kaman wata yarinya. Abinda bakiyi ba a k’uruciya.. Akan Haidar kike duka wad’ann abubuwan.? Ina Haidar d’in.. Ina yake a nan..? I can’t believe you are risking everything… And even our relationship for him.. D’an da bai damu dake ba.”


Juyowa tai tana dubansa, sai tai murmushi wann karon “Did you say our relationship.?” Ta dan kuma girgiza Kai “I thought all you care about is your business.”


Cikeda mamaki ya girgiza Kai “Kwaise, amma kinji yanda kike mun magana.?”


A hankali ta sadda kanta k’asa “Tuba nake. Allah ya huci zuciyarka Engr…. Idan akwai abinda kake buk’ata kafin ka koma company.. I’ll have it prepared for you..” Dakatar da ita yai da fad’in “No, bani buk’atar komai.!” Yanda yai maganar zaka fahimci ya gama tunzura amma sai Mommy ta murmusa ta dubesa. 


“Thank you… for driving me home..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana mai shigewa.


Daddy ya bi bayanta da kallo. Maiyasa ya d’auki shawarin Alhaji Gimba da yace yaje ya dawo da Kwaise gida.. Dan lokacin da Lawyer d’insa ya sanar dashi halin da ake ciki gameda batun case din Mommy suna tare a company da Alhaji Gimba kuma shi ya basa shawarin da  yaje ya d’auki iyalinsa ya maidata gida, ya tafi da Kansa shi kad’ansa ko driver bai bashi shawarin d’auka ba. Gashi nan ya baro abinda yake dik irin mahimmanci da yake ba ma aikinsa yazo kwaise tana masa abinda batayi da ba. Ko shiga gidan baiba yai komawarsa company. 



Anisa duniya sabuwa, tana zaune parlorn Mommy ta mimmik’e k’afafu tana bawa ma’aikatan gida umarni da order Kai kace itace Madam din gidan Mommy tai Sallama. K’iris ya rage Anisa bata saki glass cup d’in dake rik’e ciki hannunta ba. 






SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*




*39*






*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*





Sosai Mommy ke kuka sanda suka iso asibitin Anisa na biye da ita itama matsan k’wallan take. Hankali tashe Mommy ta nufo hospital staff d’in tana tambayar yanda su Haidar suke.


A daidai nan su Daddy da Alhaji Gimba suka fito daga wani k’ofa. Dan dama sanda accident d’in ya faru company aka k’ira aka sanar dasu. 


Daddy yai tsaye yana dubanta yanda take kuka sosai Anisa nata kokarin kwantar mata da hankali bayan hospital staff d’in sun sanar dasu Haidar da matarsa suna cikin ER Likitoci na kula dasu.


Wayar  Daddy ne ta soma ruri. Daga Kampani ake kiransa. Dafe goshinsa yai yana mai lumshe ido sanda yake amsa kiran. Ga dukkan alamun ba labari mai dad’i yai receiving cikin wayar ba. 


Alhaji Gimba Ya dubesa had’ida girgiza kai kad’an “Akwai wani abu ne.?”


D’an furzar da huci Daddy yai “There’s been an emergency at the company..”


Alhaji Gimba Ya girgiza Kai kad’an “Emergency..? Mai ya faru.?”


Furzar da huci Daddy ya kuma yi “Ban sani ba Gimba.” 


Shiru Alhaji Gimba yai yana dubansa. Tunanin sa d’aya Engr zai iya tafiya ya bar asibitin musamman da yake Haidar ne a asibitin sanin irin alak’ar dake tsakanin Engr d’in da ahalinsa. And especially da yake matsala ne ya kunno a Kampaninsa. Ya sani da za’a ba ma Engr zab’i tsakanin Kampaninsa da D’ansa he’d always choose his company. A halin yanzu ahalinsa suna buk’atar sa fiyeda ko yaushe. Adduarsa Allah yasa kar Engr Ya tafi ya bar ahalinsa cikin yanayin da suka tsinci kansu na jarabawa. 


Yana tsaka da tunanin kaman daga sama ya sinkayo muryar Daddy “You go… and take care of things there.”


Alhaji Gimba Ya dubesa da mamaki cikin gaza b’oye farin cikinsa na decision d’in da Engr ya dauka na tsayuwa a asibiti wajen ahalinsa. Hakan na nufin Engr ya zab’i D’ansa sama da kampaninsa da Kasuwancinsa for the first time. Cikin sauri ya soma jinjina Kai “Kar ka samu damuwa abokina.. zan je na kula da komai a can.. You stay here.. Your family needs you.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin k’arfafa ma Daddy gwiwa Wanda Sam k’arfin halinsa ya hana ya nuna tsananin damuwarsa. 


Kai dubansa ga yanda su Mommy ke zaune yai bayan Alhaji Gimba ya shige. Anisa sai k’ok’arin calming d’inta take da kalamai masu kwantar da hankali cewa Haidar harma da Ummul zasu samu lafiya. Mik’ewa Anisa tai tana duban Mommy wacce har lokacin bata cewa komai sai hawaye dake gangaro mata “I’ll.. bring you some water Mommy.” Ta k’arashe tana mai shigewa. 


Bayan Anisa ta shige k’uri Daddy yaima Mommy k’uri daga nan yanda yake tsaye. Yana kallon yanda take cazgan kuka mai tsuma zuciya. Tin bayan abinda ya faru tsakaninsa da Kwaise zai iya cewa bai sake Jin ya damu da wani damuwa da ya danganceta cikin zuciyarsa ba musamman idan abun ya shafeta ita da D’anta ne. Amma yau d’in  sai yaji har k’asan zuciyarsa na jin zafin kukan da Kwaise take. Har cikin zuciyarsa yana so ya k’arasa gareta ya rungumeta cikin jikinsa amma sai yana jin bazai iya hakan ba. Lumshe idanunsa yai yana mai barin wajen cikin sauri dan Sam bai son sauraren kukan da take. It hurts him a lot. 



A can waje kuwa koda Anisa ta fita sun samu sun keb’e da Hisham. Ta kuma dubansa a hasale “You know your IQ doesn’t work at all. Waima how many gb akan nan naka..?”


Katseta yai kaman zai mak’ureta “Don’t you dare insult me. It was your idea from the very start.. Kece kika kawo shawarin a shirya masa hatsari.. If there’s someone to be blamed here that should be you.”


Anisa na huci take nuna sa “Kai addu’a kar wani abu ya samu Haidar.. Dan wllhi idan wani abu ya samu Haidar sai na tona maka asiri.!”


Murmushi Hisham yake da gefen baki “If that’s a threat, I suggest ki ajiye sa zuwa anjima har muji wani yanayi Ummul ke ciki. Dan na miki alk’awari idan har wani abu ya sameta.. Zakiyi d’andanasanin sanina..!” Ya k’arashe jijiyoyin fuskarsa suna mimmik’ewa. 


Anisa ta zaro ido tana duban Hisham cikeda mamakin irin son da yake ma Ummul. furzar da huci  tai hadida rausayar da ido dan bazata basa daman ganin gazawarra ba “Let’s not waste time pointing fingers at each other.. Bazai taimakemu ba.. I thought da ka shirya hatsarin zaka d’auki Ummul ka gudu da ita.. I thought you said you wanted to be with her so badly. Maiyasa kai wasa da damarka. Maiyasa baka saceta ba kowa Ya huta.?!” Ta k’arashe tana huci.


Murmushi yake da gefen baki yana dubanta “You think I’m stupid.?” Ya kuma murmusawa yana duban Anisa “To tell you the truth, I was the anonymous person  da ya k’ira company ya sanar da hatsarin nasu.” Ya jinjina Kai yana ci gaba da murmushi “Ina gefe ina kallon komai har yan kwanakwana suka kawo masu dauki.. Daidai da dak’ik’a guda ban bar wajen ba. I had to make sure sun samu taimako na gaggawa right away.!”


Ya kuma murmusawa yana kallon Anisa da ta zama confused tana duban makirci da ya dama nata. Hisham yaci gaba “Alak’a mai kyau mai tsafta mai cikeda yarda nake son k’ullawa da Ummul Wanda Babu algus cikinsa. And believe me na shirya hakan. Bazan tab’a bari ta zargi soyayyar da nake mata ba.. She will come to me willingly.. And she will accept me ba tareda wani ya tilasta mata ba.. Kin fahimta.?!”


Anisa ta tsaresa da ido sai kuma ta girgiza kai “I hope it happens very soon.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai ta shige tana huci.


A yanda ta bar Mommy nan ta sameta har lokacin matsan hawaye take cikin yanayi mai nunida tsananin tashin hankali. 


Anisa tai saurin sauya fuska had’ida daura damuwa saman fuskarta. Ta isa ga Mommy jiki a sanyaye ta zauna gefenta tana mai b’alle bottle water d’in da ta shigo dashi. Ta mik’a ma Mommy a hankali tana fad’in  “Mommy have some water.”


Girgiza mata Kai Mommy tai cikin zuban hawaye “I can’t Anisa. Bazan iya ba.. Bazan iya saka komai a bakina ba tareda sanin halinda Haidar da Ummul ke ciki ba.!”


Anisa ta maidoda hannunta baya cikin sanyin jiki. Ta d’aura hannunta guda saman na Mommy tana k’ak’alo hawaye “Mommy I know you are strong.. In fact, you are the strongest woman I know.. And you are my inspiration.. But sometimes even the strong ones feel vulnerable.. Because we are human beings…” Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sai ka rantse har cikin zuciyarta Abinda take fad’i haka ne. Taci gaba “Tada hankali da damuwa dole ne.. But what they need the most now it’s our prayers.. Addu’o’in mu suke buk’ata fiyeda komai Mommy.. Especially you.. Sabida ke uwa ce.. Mommy kiyi ma Haidar Addu’a.. In sha Allah zasu samu lafiya daga shi har Ummul kinji Mommy.”


Hawaye na gangaro ma Mommy sai ta rungume Anisa kuka na kuma zuwa mata. Anisa ta saki murmushin cin nasara da gefen baki. A fili kuwa fad’i take “I’m here for you Mommy.. I’m here..!”


A haka Anisa taci gaba da k’arfafa ma Mommy gwiwa Har kawo zuwa fitowan wani Dr daga hanyar da zai sadaka da ER. Yana tafe yana zame safar hannunsa. 


Cikin sauri Mommy ta mik’e Anisa na biyeda ita suka nufi Likitan. 


Daddy Wanda shima yaga fitowan Likitan zai nufesa kenan yaga Mommy ta rigasa. Sai yaja Ya dakata Ya tsaya daga bayansu. 


“Dr how’s my son and his wife..? How are they doing..? Can I see them now.. Can I see my son now.. Please tell me..” Ta k’arashe cikin tsananin kid’imewa. 


Dr ya dan girgiza Kai yana duban yanda ta rikice sosai. Ga mutum mai shekaru da Ya d’an soma ja is not good for their health. 


Karaf Likitan ya had’a ido da Daddy dake daga gefe. A hankali Daddy ya girgiza masa kai had’ida masa alama da ido alamun kar Ya fad’i wani abinda zai k’ara mata tashin hankali. 


Dr ya dan murmusa yace “Kar ki samu damuwa Hajiya.. D’anki harma da matarsa na Miki alk’awari suna samu kyakkyawan kulawa. And fortunately matarsa ta riga ta farka tana d’akin hutu. Shima munada yak’inin in a couple of hours zamu turasa d’akin hutu cikin yardar Ubangiji. There’s nothing to be worried about.” 


Relief ya nuna saman fuskarsa Mommy. Ta soma jinjina kai “Da gaske Dr. Yarana are out of danger..  Zasu  samu lafiya.. Ta dubi Anisa dake sakar mata murmushin nuna jin dadi “Zasu samu lafiya in sha Allah.”


Ta juyo ta dubi Likitan dake nan tsaye gabansu  “Zamu iya ganin Ummul.”


Dr ya jinjina mata kai a hankali “Of course you can.. This way please.” Ya k’arashe yana nuna mata hanya.


Mommy ta jinjina kai tana mai shigewa Anisa na biyeda ita. 


Bayan Sun shige Dr da Daddy suka keb’e a ofishin Likitan. 


Dr ya dubi Daddy yace “To be honest, I couldn’t tell your wife the real condition of your son.”


Daddy ya zuba masa ido. Sai Ya girgiza kai kad’an “Tell me his condition, Dr.” 


Dr ya jinjina Kai kad’an “He’s lost a lot of blood.. But.. Zamu iya cewa he’s responding well. That’s why we moved him to the ICU… Amma..” Sai ya d’anyi shiru yana duban Daddy kafin ya girgiza Kai kad’an yaci gaba “Komai zai iya faruwa.. Because the first 24hrs is critical.. Let’s just pray he wakes up before then. Otherwise, we don’t know what might happen.” Ya k’arashe yana duban Daddy hadida girgiza Kai alamun hope d’in kad’an ne. 


Daddy yai shiru cikin tsananin sanyin jiki tamkar Wanda yai nisa cikin duniyar tunani. Muryar Dr ya sinkayo yana fad’in “Muna buk’akan  jini da za’a k’ara masa cikin gaggawa.”


Daddy ya dubi Likitan jiki a mace sai Ya jinjina kai “Go ahead Dr.. Just do your job..”


Likita ya girgiza Kai kad’an “Unfortunately bamuda irin jininsa a nan. Mun samu shortage na jinin due its high demand. Ba don muna buk’ata cikin gaggawa ba da zamu iya jira tinda jini da baida wahalan samu. A halinda ake ciki any delay zai iya janyo matsala.” 


Daddy ya furzar da huci kad’an. Dan shi dai Haidar D’ansa ne amma bai tab’a sanin lafiyarsa rashin lafiyarsa balle wani blood type d’insa. Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Dr.. What’s his blood type then.?”


Dr ya sanar da Daddy blood group din Haidar. 


Shiru Daddy yai kaman mai tunani. Dr zai kuma magana Daddy ya dubesa had’ida katsesa cikin sauri “I have same blood type with him.. I hope zaku iya d’iban nawa.” 


Dr ya jinjina Kai yana mai sanar da Daddy su k’arasa lab dan suyi aune aune. 



A can d’akin da Ummul take kaw. Shigowar Mommy yai daidai da bud’e idonta. 


Ta soma k’ok’arin Ware idanunta da suka mata nauyi. Tsaf ta sauk’esu akan Mommy dake karasowa gaban gadon nata.


“Mommy..!” Ummul ta furta cikin murya irinta marassa lafiya.



Mommy ta sakar mata murmushi ta k’araso tana dafa kanta daga nan yanda Ummul d’in ke kwance “‘Yata.. Alhamdulillah kin farka. Ya karfin jikin naki..? Mai kike ji yanzu.?”


 Ummul ta dubi Mommy tana k’ok’arin tuno abinda Ya faru. Take ta tuna sansa Haidar yace birkin motarsa bata aiki. Ta tuna yayita k’ok’arin ya tsaida motar bai iya ba. Ta tuna sanda motar ta bar saman kwalta Haidar Ya mata rumfa da jikinsa cikin k’ok’arin ganin yayi saving dinta wani abu bai faru da ita ba.. Ta tuna jini da ta hango Ya wanke fuskar Haidar da ya bar saman seat d’insa yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ga idanunsa a lumshe tamkar baya numfashi. Tinda taga Haidar a wann yanayin bata kuma sanin ina kanta yake ba sai farfadowa da ta ta ganta a gadon asibiti. Ta soma girgiza kai hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar.. Ina Haidar yake..? Dan Allah ku fad’a mun ya samu sauki.!” Ta soma k’ok’arin mik’ewa tana fad’in “Dan Allah ku kaini wajen shi.. Dan Allah ina so naga Haidar.. Please Mommy..!” 


Saurin rik’eta Mommy tai itama din hawaye take. Bata bari Ummul d’in ta bar saman gadon ba take fad’in “Haidar yana can likitoci na kula dashi Ummul. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Kema ba k’oshin lafiya ne dake ba. Look duba kiga ga bandage a goshinki da hannunki.”


Cikin zuban hawaye ta katse Mommy da fad’in “A’a Mommy banjin ciwon komai.. Ni Haidar kawai nake son gani dan Allah..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.


Anisa dake gefe juya ido rai cikeda takaicin Ummul. Cikin zuciyarta take fad’in ji wani iyayin banza. Sai wani neman ganin Haidar take bata ta kanta. Yaushe ma suka San juna ita Haidar d’in. Makirar banza. Ta kuma juya ido ganin Mommy ta rungume Ummul  dake kuka sosai cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali dudka Mommyn ma hawaye ke zubo mata.



A can b’angaren Daddy kaw bayan an ida d’iban jininsa an k’ara ma Haidar duban Dr Daddy yai “Doc, I want this to stay between us.. Bana so Matata ta San ni na bama Haidar jini… Ko shi Haidar d’in idan ya farka.”


Dr ya jinjina cikin tabbatar ma Daddy baida matsala da hakan.


Daddy ya jinjina kai had’ida masa godiya kafin Ya k’ara da “Can I please, see him now..?”


Dr ya jinjina kai “Sure.. But it should be quick.” 


Daddy ya jinjina kai yayinda Dr Yai masa jagora zuwa cikin ICU bayan an basa wani rigar kariya da hula harma da nurse mask kafin ya nufo yanda Haidar ke kwance na’ura ta ko ina. 


Tin daga nesa jikin Daddy yai matuk’ar sanyin yanda ya hango Haidar kwance cikin buwayar Ubangiji. Yana takowa yana tuna Haidar d’in tin haihuwarsa. Gwagwarmayar rayuwa da Ya fuskanta musamman dasu iyayensa. Ya tuna a lokutan baya sanda yake rige rigen kawo masa sakamakonsa na makaranta da kyauttukan da aka basa amma daidai da rana guda bai tab’a kalla ba balle Ya yabesa. Ya tuna banda hantara tsana da kyara babu abinda ke tsakaninsa da D’an nasa. Ya tuna irin k’ok’ari da yake a company kan duk wani aiki da aka d’aurasa ba dan komai ba sai dan ya tabbata baiyi failing mahaifinsa ba. Still nothing was enough. Ya tuna auren da Kwaise Tai masa Wanda bai saka hannunsa ba balle Ya halarta matsayinsa na tilon D’ansa dukda sanin aure wani gab’a ne mai mahimmanci a rayuwar D’an adam. Haka yaita tuna rayuwarsu na baya Har kawo tattaunawarsu da Alhaji Gimba da yanda Alhaji Gimba yace dashi yai tunani Ya gyara alak’arsa da iyalensa tun kafin Lokaci ya k’ure masa dan Lokaci baya jira. Saiga hawaye na kwararowa daga k’uncin Daddy. Yakai hannunsa dake tsananin rawa yana k’ok’arin Shafa kan Haidar. 


Sosai muryarsa ke rawa sanda ya soma fad’i a fili “Aliyu..!” Ya furta a hankali yana shafa kan Haidar d’in. For the very first time da ya tab’a ambaton Haidar da sunan from his heart tin bayan da aka rad’a masa sunan. Daddy yaci gaba “My Son.!” Nan ma karo na farko da Ya ambacesa da D’ansa kai tsaye. Yaci gaba “Shin kasan a ranan da aka haifeka a lokacin da mahaifiyarka ta nuna mun kai a wann rann na samu k’arfin komawa bakin aiki.?” Ya murmusa hawaye na kuma gangaro masa “People might think kasuwanci na da Kampanina sune abinda sukai keeping dina moving.. But the truth is that you were the one that kept  me going.. You brought me back my strength koda ban nuna hakan ba.” Ya shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin yaci gaba “Meyasa na hukunta ka cikin laifin da ba naka ba Wanda baka da masaniy akai.?” Ya dan numfasa yana kuma shafa kan Haidar d’in “I was so angry at your Mom… That I didn't even realize I wasn't only a husband who’s been hurt and betrayed… I was also a father.. Na mance ni mahaifi ne da Allah Ya dank’a mun amana da kiwo Wanda zai tsaidani Ya tambayeni kan wann kiwon.. Nayi abubuwa cikin fushi..  Na d’auki tsangwama da kyara na d’aura akan ka just because you’re Kwaise’s Son.. Fushi yasa na mance you are also a part me.. My soul… my flesh and blood..” Ya lumshe idonsa hawaye suka kuma gangaro masa “Bai kamata na barka ka shiga cikin matsalolinmu ba. Why are You the one who's suffering the consequences... It shouldn't be this way.. If there is one thing I regret the most shine sake da damata da nai cikin shekarun da Allah Ya albarka ce ni da kai matsayin D’ah…. Forgive me son… Ka yafe mun D’ah na..!” Ya k’arashe kuka na neman cin k’arfinsa. Saida Yai masa addu’o’in samun sauk’i kafin ya baro d’akin duk jikinsa a mace. 


A hanyar ficewa suka had’u da Mommy. Daddy ya bita da kallo saidai batace da shi komai ba tasa kai ta shige. Jiki babu k’wari yaja k’afarsa Ya bar wajen.


A yanda Mommy taga Haidar sosai hankalinta Ya tashi. Haka ta kwantar da kanta gefensa tana kuka tana fad’in irin k’aunar da take masa tana fad’in kar Ya tafi ya barta. Hannun Ummul taji saman k’afadarta wacce itama ta kasa hakuri har saida likitoci suka hakura suka barta ta shigo dan taga mijinta.


Ummul na k’ok’arin bama Mommy baki amma sai ta kasa sai k’unshe bakinta tai dan sosai taji kuka na zuwa mata musamman yanda taga Haidar na kwance idanunsa a lumshe ga na’ura ta hanci ta baki. 


A hankali kukan Mommy ke tsagaitawa, ta sa hannu tana shafan sumarsa. Murmushi da hawaye saman fuskarta take fad’i da Ummul “Tin lokacin da yake ciki rayuwarmu ta sauya. Na shiga matsansncin  damuwa.. And maybe that’s why he was so tiny lokacin da na haife shi… Amma dukda haka he was strong, a fighter..” Ta kuma murmusawa tana hawaye “Sann Koda ya zama cikakken mutum mai cika ido da kyaun k’ira bai huta ba.. Tin haihuwarsa  baisan wani farin ciki ba.. And that’s all my fault..” Ta k’arashe tana share hawayen da suka zubo mata. Taci gaba “Meyasa nake ji kaman laifuka na yake biya..?”


Saurin girgiza mata kai Ummul tai “Kar kice haka Mommy.. Bawa baya wuce k’addararsa a rayuwa. Duk abinda ke faruwa muk’addari ne daga Allah. Wasu abubuwan suna faruwa ne cikin rayuwarmu domin su zamto mana darasi. Ubangijinmu zai jarancemu ta ko wata fuska. Muyi ma Haidar addu’a Allah Ya tashi kafad’unsa Ya basa lafiya..”


Mommy ta jinjina mata kai tana mai rik’e hannun Ummul d’in cikin nata. Ummul ta kamo hannayen Mommy sosai tana fad’in “Muje ki huta Mommy. Zan tsaya a nan na kula da Haidar..”


Mommy ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge hawayen da suka zubo mata. Haka Ummul ta rik’o hannunta har suka fito dikda itama ga rauni jikinta. A nan k’ofa suka had’uda Anisa. Ummul ta mik’a ma Anisa hannun Mommy tana fad’in ta kula da ita tana buk’atan hutu.


Anisa ta jinina kai tana fad’in “Ummul is right.. You need to have some rest Mommy.. this isn’t good for your health.. Haidar bazai so ya farka yaga kema ba lafiya ba.. Muje Mommy..” Ta k’arashe tana rik’o Mommyn wacce da gani tafiyar kawai take. 



Suna shigewa Ummul ta koma cikin ICU d’in. Ta jima tana kallon Haidar dake kwance tana tuno yanda had’arin nasu Ya kasance. A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata. Ta janyo kujera ta zauna nan gaban gadon nasa. Kallonsa take tana tuna yanda aurensu Ya kasance Wanda ko sanin wanene shi balle kamanninsa batai ba  farko. Ta tuna lokacin da ta shak’i poison Dr ya sanar da ita yanda Haidar Ya kula da ita. Ta tuna d’auketa da yai Ya kaita wann gidan Ya kulle.. Ta tuna yanda yai fitar da Mommy da kansa daga hannun ‘yansanda Wanda a baya ya dage sai  an kulleta a prison. Ta tuna tattaunawarsu kafin Had’arin Ya faru yanda yace mata bazai saceta ba kuma bazai sake rufeta ba sann zai sawwak’a mata tai tafiyarta shima  zai tafi zai tafiya mai nisa far from everyone and everything. Ta tuna sanda hadarin ke faruwa yanda ya finciki seatbelt d’insa yai tsalle daga nasa kujeran yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Bayan mahaifinta bataji akwai wani D’an adam da Ya tab’a ba ma rayuwarta mahimmanci irin haka. Ta bud’e lumsassun idanunta masu zuban ruwa tana kallonsa. A hankali ta soma k’ok’arin kai hannunta dake rawa ta d’aura saman nasa hannun. A hankali take furta “A lokacin da Umma ta shirya aurena da kai na shiga damuwa da tashin hankali na rashin sanin wanene zata aura mun.” Ta kuma goge hawayen da suka gangaro mata “Ban tsammaci farin ciki ko wani rayuwa mai inganci cikin auren ba kama daga mutanen da shafin rayuwa zata had’ani dasu Har zuwa mijin.” Ta k’ura masa ido hawaye na kuma gangaro mata “Shin kasan kowa gudu na yake.? Ni Ummulkhairi ban tab’s tsammanin akwai wani D’anadam da zai fifita rayuwata sama da nashi ba. Koda ace akwai ban tab’a tsammani daga wajen mutum irinka ba. Wanda na tabbata ka fini a komai sau babu adadi. Sann mu biyun duniyar mu sun banbanta. Haka ne.?” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Dole ce tasa na danne nawa raunin gaban Mommy dan na bata k’warin gwiwa.. Amma kasan me..? Banida wani k’warin gwiwa.. Dan Allah ka tashi kaji.. Ka tashi..!” Ta k’arashe kuka na neman b’alle mata da gaske. Tai k’ok’arin saita kanta kafin ta kuma dubansa murmushi da hawaye saman fuskarta “A koda yaushe kana kiran kanka Monster.. Ni kuma ina fad’a maka kai ba mugu bane.. Mugu bazai tab’a zama mai kyakkyawan zuciya wanda ke saka damuwar wasu sama da nasa irinka ba. Yau d’in na kuma yarda da haka bayan abinda ka mun.. Watak’ila da baka zab’i ka bani kariya ba Watak’ila da ni ce zan kasance nan a kwance ba kai ba..!” Ta share hawayen da suka ziraro mata. Ta kuma daura yatsun hannunta saman nasa “Ina tareda kai.. Zaka samu lafiya cikin k’udurar Ubangiji.. Allah Ya baka lafiya…SweetMonster..!” Ta k’arashe tana mai kwantar da kanta gefensa kad’an. 



**



Kano…




Hilal na Ida parking Ya juyo ya dubi Umma dake zaune bayan motar. Murmushi Ya saki kad’an “Umma mun iso..”


Umma ta sauk’e ajiyan zuciya tana dubansa “Hilal.. Na haneka kak’i ji.. Mai zai faru idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata.?”


Ya d’an girgiza kai kad’an “Ammi bazata sani ba Umma. Taimako nayi niyyan yi kaman yanda kema taimakon kikayi. Ina addu’an Allah Ya had’a mu cikin lada.”


Umma ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Ameen Hilal d’an albarka. Mu k’arasa ko.”


Hilal Ya jinjina kai yana mai fitowa had’ida bud’e ma Umma k’ofa.



A daidai lokacin motan Ashshe dake biye dasu ba tareda saninsu ba ta iso wajen. Ta bama driver umarni da yai parking can gefe dasu.


Sai huci take tana ayyana gidan Uban wa Suwaiba alak’ak’ai zata kai mata D’ah.? D’aga kan da zatai taga sun nufi cikin Kotu. Asshe ta zaro ido waje tana d’ora hannaye biyu a k’irji “Na shiga uku ni Asshe mai Hilal yake a Kotu.?!”


Batasan sanda ta finciki marfin mota ba tabi bayansu a fusace. 




SameenaAleeyou📚


*AUREN WATA UKU..!




*40*






*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*






“Ke Suwaiba dakata.!” Ta furta da k’arfin gaske daga nan yanda take tsaye bayansu.


Gaban Umma ya yanke ya fad’i. Ta kasa juyowa sai furtawa da Tai cikin zuciyarta ‘Asshe.!’ 


Shi kaw Hilal da tsananin mamaki Ya juyo yana dubanta “Ammi.!” Ya furta cikeda mamaki.


Asshe taci gaba da jinjina kai tana huci “Baka tsammace ganina ba koh..? Nace baka tsammaci ganina ba koh..?”


Hilal Ya d’an lumshe ido kad’an ya k’araso yana k’ok’arin janye mahaifiyarsa “Ammi please don’t make a scene here.” A hankali yake maganar yana k’ok’arin janye ta.


Ta funcuke hannunta tana nunasa Umma da d’an yatsa “Kina jina Suwaiba kurwar zuri’ata kur..! Idan na sake ganinki kusada d’a nah.. Kinga nan.” Ta nuna mata kotu dake gaba garesu “Wllhi a nan za’a rabamu.!”


Hilal yai saurin katseta “Ammi Umma bata tilasta mun zuwa wajen nan ba.. Nazo ne da rad’in kaina..”


“Rufe mun baki kai kuma kafin na Sallamaka da gaske kabi daji.!”


Umma ta k’araso cikin sauri tana girgiza kai   “A’a Asshe dan Allah kar kice haka.. Wllhi Hilal yaron kirki ne mai biyayya.”


Da mugun mamaki take duban Umma “Kul.! Ahir d’inki kar ki sake ki sake saka mun baki ina magana da D’ahna. Suwaiba ke har zakiyi magana akan biyayya..?!” 


Umma ta sadda kai k’asa a sanyaye.


Asshe taci gaba “Kina jina idan har baki sakar mun kurwan D’ah ba wllhi sai na maidake abin kwatance a garin nan.! Ban haifo muku D’ah dan yaji da matsalolinku da gurguntaccen ahalinku ba ehe.!”


Ta dubi Hilal “Kai kuma idan ni ce na haifeka ka saka k’afarka a kotun nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige mota fuuu kaman zata tashi sama. 


Hilal Ya dubi Umma yace “Kiyi hak’uri Umma bansan Ammi na biyedamu ba..”


Umma tai saurin girgiza masa kai alamun a’a “Kar ka damu Hilal kabi umarnin mahaifiyarka. Ni zan shiga na saurari k’aran Yaya Tani. Idan bata ganni a kotun ba zatai tunanin na kuma watsar da ita ne.. Inada yak’inin Allah zai kawo yanda za’a biya mutumin nan kudinsa Tani ta dawo gida.”


Hilal Ya jinjina Kai a hankali “Umma biyan kudin bazai zama matsala ba in sha Allah.. Na Miki alk’awarin baza’a sake zaman Kotu akan wann batun ba.”


Kaman daga sama suka sinkayo murya “Zaman Kotu da Tani yanzu aka fara dan sai na karb’ar ma D’anuwana hakkinsa rabon gadonsa da Tani tai yana raye. Idan banci taran Tani ba ba sunana Dije ba.!”


Tsaf Hilal ya gane Inna Dije ita ce dai Kanwar Abbansu Khulsum dake wajensa a asibiti sann koda aka sallame su Khulsum d’in ta tabbatar masa gidan Inna Dije dake Dutse zasu wuce da Abba yanda zaici gaba da jinya.


Gaisar da Inna Dije yai yana mai k’arasowa gareta “Ni zan biya taron Innah.. A kashe wutan maganar nan kowa ya huta.. Kar ki manta ku ahali ne kai juna Kotu ba naku bane musamman yanzu da Abba yake cikin wann yanayi.. Inna Idan Abba ya farfado daga jinyarsa yaga ahalinsa suna fad’a da juna irin haka mai kike tunanin zai kuma samunsa.?”


Shiru Babu Wanda yace komai daga Inna Dije har Umma. Hilal ya samu k’warin gwiwan ci gaba “Rashin lafiya irin na Abba baya buk’atan tashin hankali irin haka. Salama da kwanciyar hankali yafi buk’ata ta. Na tabbata idan Abba ya tashi yaga ahalinsa sun had’e. Suna k’aunar juna sun mance duk abinda Ya faru a baya. Sun kuma yafi juna wann kad’ai sai yafi maganin da Likita zai bashi.” Ya k’arashe yana duban Inna Dije. Sai kuma ya soma saka hannu a aljihu “Zan biya ko nawa ne idan hakan zai kawo maslaha da zaman lafiya cikin ahalin.”


Inna Dije na murmushi ta dakatar dashi “A’a haba.. Idan na karbi kudi hannun surki na mai na zama kuma.” Tai maganar tana fad’ad’a murmushinta. Sai ta soma mutsuke ido tana janyo bakin mayafi tana share hawayen da suka soma zubo mata bagatatan “Na jima banji kalaman da suka ratsa zucuyata irinta yau ba. Tabbas Babu komai cikin k’iyayya da gaba. Tabbas D’an uwana ya farka yaga ahalinsa sun dunk’ule waje guda shine babban maganin da yake buk’ata. Laidai kam bakai halin mahaifiyarka ba. Al basa batai halin ruwa ba. Ubangiji ya maka albarka. Lallai ka cika D’ah na gari da kowa su iyaye zasuyi buri da mafarkin samu. Da ace duniyar zata cika da mutane irinka masu k’ok’arin ganin Sun wanzartar da zaman lafiya tsakanin Al’umma da rayuwa ta canza. 


Haka Inna Dije taita sharb’an kuka tana fad’in ta tuba ta canza halinta. Taita saka ma Hilal albarka har ya bar wajen. 


Mamaki ne ya cika Umma matuk’a da al’amarin Inna Dije dare d’aya dai kokuwa rana d’aya tak Inna Dije ta sauya. Ta ya za’a ce kalaman Hilal da basu shige a k’irga ba Sun karkata Zuciyar Dije. Kai abun da mamaki matuk’a. 


Har Umma ta dawo gida mamakin wann kayan al’ajabi take.


A nan tsakargida ta yada zango ta kwab’e hijabinta ta lank’aye saman gajeren katanga dake tsakargidan. 


A haka Badia da Azeema suka shigo tsakar gidan suka taddata. Duban Umma sukai a tare suka dubi juna da mamaki ganin sunata Sallama bata amsasu ba. 


Suka k’araso a tare cikin sauri suka zube gabanta. Badia ta kamo hannun Umma cikin nata a dan firgice “Umma Mama ta Miki wani abin ko.? Umma saida muka fad’a Miki Mama tuban d’an muzuru tai.”


Azeema ta cab’e “Umma mun fad’a Miki gaskiya Mama bazata tab’a saduda ba.. Mun santa kuma munsan halinta tinda ita ta haifemu ta kuma rainemu.. Duk abinda Mama take acting kawai take dan ta samu a fiddata ta shak’i iskan ‘yanci ta fito taci gaba daga yanda ta tsaya.”


Badi’a tace “Umma fad’a mana, Mama ta miki wani abu ne..? Ki fad’a mana Umma idan ta Miki wani abu ne zamu fuskanci Mama koda ta kasance mahaifiyarmu. Dan munyi alk’awari bazamu sake bari wani ya cutar dake muna kallo ba. Koda baki haifemu ba mun Miki alk’awari zamu kasance ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe tana duban Umman cikeda kulawa hannunta cikin na Umman.


Umma ta murmusa hawayen farin ciki na gangaro mata. Ta dubi Azeema ta kuma duban Badi’a. Hannayensu su duka biyun ta kamo ta rik’e cikin nata. Ta girgiza Kai a hankali “A’a yarana, Yaya Tani bata mun komai ba.. Kuma ina nan Akan bakata in sha Allahu. Zanyi iyaka k’ok’arina wajen ganin ta dawo garemu. Wani al’amari da ya d’aure mun Kai ya faru.”


Badia da Azeema suka dubi juna da mamaki “Wani al’amari kuma Umma.? Wane irin al’amari kenan. Mai ya faru.?” Cewar Azeema tana duban Umman cikeda kulawa.


Umma ta jinjina Kai tace “Yau da na tafi sauraron k’aran Yaya na gamu da Innarku Dije.”


Suka kuma duban juna da mamaki “Inna Dije.?” Azeema ta nanata.


Umma ta jinjina Kai “K’warai Dije dai k’anwar mahaifinku.”


Badia tace “Allah yasa dai ba wani abin tai Miki ba Umma.”


Umma ta girgiza Kai “A’a ko kad’an bata mun komai ba.” Nan take ta labarta musu taryan taryan yanda sukai da Inna Dije. Ta k’arada “Har cewa tai ina iya zuwa naga mahaifinku a Dutse dik sanda nake buk’atan hakan..”


Daga Azeema har Bad’ia ido suka zuba mata. Azeema ta mik’e k’afa tana girgiza Kai cikin yanayin salon da take idan bata gamsu da abu ba “Aaaa haba Umma. Wllhi matan nan wasa kawai da hankalinki suke. Wai Mama da Inna Dije ne dare d’aya suka zama salihan bayi.. Kaji ‘yan rainin hankali. Kut wllhi k’arya suke.” 


Duban da Umma tai mata yasa ta kame bakinta kad’an “Ai afuwan Ashe munce zamu k’ok’arta mu rage wasu abun. Yo baki ya saba aita sorry damu Umma in sha Allahu munata k’ok’arin saita halayyan namu koda salihanci baya mana dad’i. Amma dai wllhi idan bindiga za’a saka mun bazan yarda mata guda biyun nan tuban k’warai sukai ba. Haba Mama ce fah da Inna Dije ake magana a nan.” 


Badi’a ma girgiza Kai tai “Gaskiya Umma Nima zuciyata bata amince da wann canzawa da Inna Dije tai tashi guda ba. Kaman yanda har yau na kasa amincewa da tuban Mama. Umma suna amfani ne kawai da Zuciyar ki mai kyau dan su cimma wani buri nasu.”


Umma tai shiru tana tunani. Ta sani Dije tanada masaniya kan abinda Tani batada masaniya akai tinda Akan idon Dije akai auren Ummul. Babban fargabanta shine kar Dije tai amfani da abinda ta sani gameda auren Ummul ta tarwatsa sabon alak’an dake tsakaninta da abokiyar zamanta Tani. Kaf fad’in danginsu Dije ce kad’ai takeda masaniya kan cewa Ummul AUREN WATA UKU tai. Mai zai faru idan tai amfani da wann damar ta tarwatsa mata ahalin da take k’ok’arin had’ewa kaman yanda tai alk’awari a baya. Fargabarta d’aya dik randa Ummul tasan da saninta tai mata AUREN WATA UKU ‘Yarta zata tsaneta sann zatayi danasanin duk wani biyayya da tai mata matsayinta na mahaifiyarta. Ta lumshe idonta tana addu’an Allah ya kawo mata mafita ya daidaita komai kafin komai ya lalace.


Azeema ta d’an tab’ata “Umma kar ki damu. Idan ma Inna Dije wasa take bugawa ki bita a haka. Kinada manyan ‘yan wasa tareda dake. Kinada goalkeeper kinda defender. mu nan zamu tayaki buga wasanta. Umma alk’awari muka Miki bazamu tab’a barinki ke kad’ai ba. Mu ‘ya’yanki zamu tare Miki duk wani fad’a.. Umma a d’an zaman nan da mukai dake kinyi hak’uri damu. Kinyi mana abubuwa da mahaifiyarmu batai mana ba.. Kin zama uwa ta gari a garemu nida ‘Yaruwata. Umma mu kuma munyi miki alk’awarin zama ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.


Umma ta dubi Azeema ta kuma dubi Badi’a. Sai taji k’walla Sun ciko idonta. Allah sarki rayuwa, tayi addu’a Allah ya bata ikon gyara kuskuren da tai kan ‘ya’yanta guda biyu Ummulkhairi da Ummukhulsum. Ya kuma bata ikon zama uwa ta gari ga ‘ya’yan mijinta guda biyu Azeema da Badi’a. Sai ga hawaye na gangaro mata.


Badi’a ta kamo hannun Umma “Umma Watak’ila tunanin ‘yanuwan mu kike Ummul da Khulsum. Haka ne.?”


Sai Umma ta lumshe idonta hawaye na kuma gangaro mata. 


Azeema ta kamo d’aya hannun Umman, murmushi saman fuskarta “Umma, nasan kina hango fuskokin Ummul da Khulsum cikin namu fuskokin.. In sha Allahu watarana ‘yanuwanmu zasu rik’e hannayenki kaman yanda nida Badi’a muka rik’e hannayenki yanzu..”


Umma ta murmusa hawaye na kuma gangaro mata. Ta shiga jinjina Kai a hankali “In sha Allahu yarana. Wataran ahalinmu zai cika da alkhairi.. Wataran zamu had’u gaba d’aya cikin alkhairi. Wataran komai zai wuce ya zama labari.”


Suka jinjina mata Kai a tare murmushi saman fuskokin su. Umma ta janyosu ta rungume tana mai lumshe idonta. Addu’anta d’aya Allah ya had’e kan ahalin mijinta ya kuma bashi lafiya. 


Suna a haka suka sinkayo Sallamar Inna Dije. 


A tare Badia da Azeema suka mik’e zaune suna duban Inna Dije dake shigowa haraban tsakar gidan cikin yanayin da zasu ce bata tab’a ganinta ciki ba. Idan ma Sun tab’a Watak’ila tun kafin ta rasa farin cikinta tilon D’anta Fa’iz. 


Mik’ewa Baida tai cikin huci “Da wanne kika zo Innah.?”


Umma tai saurin kamo Badia ta zaunar cikin k’ok’arin dakatar da ita.


Azeema tace “Ai dai gwara mu tambayeta Umma dan idan da tashin hankali tazo bamu maraba da ita. Kaf fad’in gidan nan a halin yanzu babu k’ofan da yakai k’ofan nan zaman Lumana dan haka bazamu bari a kawo mana tashin hankali ba.” Ta k’arashe tana watsa ma Inna Dije mugun kallo.


Umma ta girgiza Kai kurum ganin irin kallon da Azeema ke yi ma k’anwar mahaifin nasu. Ta sani Sun canza sosai Sun rage wasu abubuwan sosai. Amma wasu abubuwan sai a hankali su daina dan haka ga duk Wanda ya san su waye su a baya dole yai masu uzuri.


Umma ta murmusa tana mai janyo Azeema kusanta “K’warai d’iyata k’ofan mu ya zama k’ofan zaman lafiya da lumana cikin yardar Ubangiji. Hakan yasa Innarku shigowa cikin lumana.” Ta k’arashe tana duban Inna Dije wacce ta koma tamkar salihar mage “Haka ne Dije.?”


Inna Dije tai saurin d’agowa ta dubi Umma sai ta jinjina Kai a hankali “K’warai Suwaiba. Babu abinda yafi yafiya, zaman lafiya da lumana.”


Umma ta jinjina Kai kafin ta maido da dubanta ga Badia da Azeema “Ku gaisar da k’anwar mahaifinku.”


Suka dubi juna suna yatsina fuska. Umma ta tsare sosai tana dubansu alamun tana jira su aiwatar da abinda ta umarcesu. 


Murya can k’asa Badia tace “Wllhi darajan Umma kikaci.!”


Zuciyar Dije yai wani irin tsinkewa jin wai yau ita ake ce ma taci darajan Suwaiba shashashar matar D’anuwanta. Ta had’iyi abinda ya tsaya mata sanda ta sinkayo muryoyin yaran D’anuwan nata suna gaidata da k’yar. Ta amsa masu a Mutunce da sakin fuska kaman dai ba Inna Dije ba. 


Umma tace Badia ta kawo ma Inna Dije abinci sann Salima ta gyara mata d’akinsu ta kwana ciki tinda tace washe gari take komawa Dutse. 


Sosai Inna Dije ta saki jiki ta nuna musu komai ya shige. An bud’e sabon shafin rayuwa na zaman lafiya da k’aunan juna tsakani da Allah. Harda ba ma Umma zab’i tai idan tana so a dawo da Abba gida cikin ahalinsa.


Umma ta murmusa had’ida girgiza Kai kad’an “A’a Dije zamansa a can yafi. Kinga har yanzu akwai abubuwan da bai sani ba. Kaman auren Ummul da Tani dake tsare. Kuma kinga shi mutum ne majinyaci shiga damuwa ko tashin hankali ba nasa bane.” Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad’in “Yau a k’alla watan Ummul guda da aure harda ‘yan kwanaki.. Dije kinfi kowa sanin auren Ummul mai k’ayyadadden wa’adi ne.. Nafi so idan wa’adin ya cika Ummul ta dawo garemu kaman yanda Hajiya Asshe ta tabbatar mana sann a lokacin Tani ta dawo sai mu fuskanci Malam gaba d’aya matsayin ahali.!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka.


Inna Dije ta matso gareta ta dafata kad’an “Suwaiba Hak’ik’a kurakurai mun riga mun taptapka a baya. Gyaran da zamu masu kenan shine mu gyara gaba.”


Umma ta jinjina Kai a hankali tana duban Inna Dije itama Inna Dijen Umma take duba ko wanne da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa. 


**


Hilal yana isa gida kaman jira take   ta soma kiransa. Ya murmusa  kad’an yana mai lumshe ido dukda jikinsa Ya basa ba kalamai masu dad’i zaiji cikin wayar ba. 


Ya d’aga yana jiran da mai zata fara.


“Wai Kai dan Allah a sau nawa zance maka ka daina shiga al’amarin ahalina..? Shin bakada wani abin yi ne? Ko kuma dai ka zama wakilin wanzar da zaman lafiya ne.?!”


Ya murmusa kad’an yana mai relaxing cikin kujerar motar “I’d rather become a Peacemaker and a unifier da ace na zama mafad’aci..”


Kafin yakai aya yaji an finciki marfin motar an fuzge wayar. Ba kowa bace face mahaifiyarsa.


Khulsum wacce batasan meke faruwa ba daga d’aya b’angaren taci gaba “Ni Khulsum Ina maka gargadi na k’arshe da ka daina shiga hidiman ahalina dan zaman lafiyarka da naka ahalin.!”


Asshe dake huci ta katseta “ Ke mai kika ce.?!” Ta fad’a da mamaki tana duban Hilal da Ya zuba ma sarautar Allah ido. 


Khulsum kaw tinda taji muryar mahaifiyar Hilal cikin wayar sai ta katse kiran a daburce zuciyarta na tsinkewa. 



Asshe ta dubi Hilal da tuni ya fito daga cikin motar “Mai ya had’aka da yarinyar nan Hilal.? Nace mai ya had’aka da ita.?” Ta shiga salati tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Asshe Sun ranste sai Sun lasheka.! Ka amsa min Hilal!” Ta k’arashe kaman zata rufesa da duka. Daidai lokacin Motar mahaifin Hilal Ya shigo gidan.



Yanda sukaga yanayinsa daga ita Har Hilal d’in Ya d’aga masu hankali. Musamman yanda sukaga Ya nufosu a zafafe ga wane irin kallo da yake bin Hilal d’in dashi.

  

Yana k’arasowa yace su biyosa parlornsa. 


Asshe ta dubi Hilal Wanda shima ita ya duba cikin tunanin yanayin da yaga mahaifinsa ciki.


Suna shiga ya nuna ma Hilal saman carpet gabansa “Zauna nan.!” 


Ba musu ya isa ya zauna yana kokarin gaida mahaifin nasa Wanda ko amsawa bai ba. Abinda bai tab’a masa ba tun tasowarsa. 


Mamaki ya kuma cika Asshe dan tasan Hilal dan gaban goshin mahaifinsa ne Tun tasowarsa. A Cewar sauran ahalin gidan baya laifi idon mahaifinsa. Jiki a sanyaye tace 

“Alhaji lafiya.. Meke faruwa.?”


“Ki tambayi wann D’an naki.!” Ya k’arashe cikin huci yana nuni da Hilal. 


Ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Hilal. 


Asshe ta kuma duban mijinta  duk hankalinta a tashe da yanayinsa. Ta kuma duban Hilal.


“Hilal.? Meke faruwa ne wai..?” 


Kafin Hilal yakaiga bude bakinsa  mahaifinsa ya katsesa “Meye dalilin da yasa ka bar karatunka.? Meye dalilin da yasa ka bar makaranta wann karon.?!”


Salati Asshe ta soma cikin tashin hankali tana girgiza kai “Hilal.! Makarantar ka kuma bari wann karon ma..? Na shiga Uku ni Asshe.. Hilal asirina kake so ka tona.. Meke damun rayuwarka ne.. Abubuwan da bakai a k’uruciya ba kake so kayi yanzu.?”


“Gwara ki tambayesa idan ma shaye shaye Ya fara. Dan wann karon idan ya watsar da karatunsa sisin kobona bazai sake ciwo akansa da sunan karatu ba. Makaranta na nawa aka canza masa.? Sa’anninsa daga masu aure sai masu ‘ya’ya shi Har yanzu baima san ina nasa rayuwar ta dosa ba. Shi ba kasuwa ba shi ba wani sana’an hannu ba shi ba karatun ba. Sanin kanki ne sauran yarana sai Sunyi zaman yaran shago kafin na barsu suyi wani karatu amma shi da yake gata Ya masa yawa gashi nan bai san mai yake ciki ba.!” 


Cikin tashin hankali Asshe take duban Hilal “Kace mun hutu kake Har yanzu.!” 


“Makarantar su sun jima da soma karatun wann zangon. Daga gidan Alhaji Halilu nake akwai nasa yaran a makarantar nasu. Muna labari yara sunata hutu yake sanar Dani ai Sun tsufa can Cyprus. Gashi nan ki tambayeshi.!” Ya k’arashe yana nuni da Hilal d’in cikin b’acin rai. 


Asshe ta fashe da kuka ta mik’e tana nuna Hilal da yatsa tana fad’in bayanta yake son gani.


Sai sann Hilal ya katseta “Ammi I didn’t dropout.. Ok.. Ni bar makaranta ba..”


“Idan ba bari kai ba mai ya hanaka komawa.?!” Ta tambaya tana kuka.


Ya dubi mahaifinsa cikin kwantar da kai “Abba ba makarantar na bari ba.. I Only take.. half a semester off..”


Mahaifinsa ya katsesa “Akan mai zaka jingine karatunka na wani lokaci.. Akan mai..? Mai kake yi a nan d’in.?!”



Zuciyar Asshe ya kuma tsinkewa kar dai sabida matsalolin zuriyan Suwaiba Hilal ya shashantar da karatunsa. 


“Tambayarka nake.?!” Mahaifinsa Ya kuma katsesa.


“Abba.. Aure nake so a nema min kafin na koma.”



Daga Asshe Har Mahaifin nasa da mamaki suke dubansa.


Asshe baki sake tace “Aure.? Aure Hilal.? ‘Yar wa kake nema.?”



Muryar Mahaifin Hilal d’in ne ya katsesu “ ‘Yar waye yake nema ba shi bane matsalar. Matsalar shine bazan masa aure bai koyi komai a rayuwarsa ba. Kodai ya koyi san’a na basa jari yayi aurensa ko kuma yayi karatu. Amma bazan nema masa auren ‘yar kowa baida sana’a ko aiki ba. Son da nake masa bai kai na sangartasa Har haka ba. Nima nawa iyayen ba haka suka mun ba. Dan haka bazanyi ma nawa d’an kisan gwani ba. He must learn to take responsibilities. Kuyi shawari da D’anki. Kodai ya kama Sana’a ya hakura da karatun yayi auren ko kuma ya ci gaba da karatu kafin yayi auren.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zai fice. Sai kuma ya juyo ya dubi Hilal “Kana jina, ka dawo da duka kud’ad’en da na baka da sunan makaranta. K’wandala ban yarda ka bari wajenka ba. Kar ka bari na sake maimaita maka ka dawo mun da kud’ad’ena.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice. 


Asshe taji duniyar na juya mata. Ta k’araso gaban Hilal dake duk’e wajen “Ina jinka.. Wace yarinyar ce ta d’auke maka hankali haka..? ‘Yar waye.. Waye mahaifinta a garin nan.?!”


Ya d’ago yana murmushi mai ciwo yana duban mahaifyarsa “Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..!” Yana ida fad’in haka ta mik’e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa  fal damuwan yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud’ad’ensa kafin wa’adin da ya basa Ya cika. 


Yana ficewa Asshe ta mik’e tana tunanin abun yi. Wacece ta d’auke mata hankalin D’a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya parlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad’ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad’o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak’i Suwaiba da ita. 


Saurin ficewa tai ta nufi nata sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata. 


Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi.


Asshe ta shafe goshinta tace “How’s my sister doing Anisa..? Yaya ‘yaruwata take.?”


Anisa takai dubanta ga Mommy wacce Daddy ke rik’e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk’awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa. 


Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar “Your sister needs you Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik’a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d’in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud’e idonta ta gane cewa ita d’in annoba ce kuma had’ari ce ga rayuwar Haidar.. Ammi only you.. Ke kad’ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud’i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab’a yarda ba.!”


Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b’ullo mata ya wuce gaban tasa k’afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d’an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab’a bari Hilal dinta Ya fad’a cikin wann bala’i ba. Nan take ta sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki. 


Anisa tace da mamaki “Ammi yanzu ita Ummul d’in Har tanada ‘yaruwa da Hilal ya k’yalla ido kanta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud’ad’ensa.?”


Asshe tace “Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D’anuwanki kobon mahaifinku bazai ciwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.”


Anisa ta katseta “Ammi you are wrong.!”


Asshe tace da mamaki “Mai kike nufi.?”


Anisa taci gaba “Ammi.. Bana jin Hilal yanada  kud’ad’en maida ma Abba yanzu.” Tai maganar kanta staye. 


Da mamaki Asshe tace “Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?”


“Ammi Hilal ya tura mun kud’ad’en dake account d’insa.!”


Da mamaki Asshe tace “Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?”


Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb’an kud’ad’e wajenta ita kuma tana tambayar Hilal.


Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai “Kin kashe ni Anisa..!” Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida  masa kud’ad’en ba dole k’arshe zai fad’i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana zai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai  San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha’inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b’angare na auren da ‘yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn ‘yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana cewa ita ce  sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata  bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba. 


Gaba d’aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine laifi ga d’aya b’angaren. 


Anisa na kuka take fad’in “Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had’arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!”


Cak hawayen Asshe suka k’afe “Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b’ata komai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!”


Anisa na kuka take fad’in “Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d’iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I couldn’t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!” 


Ta share hawayenta tana huci “But there’s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen Mommy. Ba ni kad’ai Mommy zata yak’a ba Ammi.. ‘Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne.. ‘Yaruwar da ta rik’eki har kawo Aurenki.. ‘Yaruwar da ta d’aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsaya a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.!” Tana ida fad’in haka ta kashe kiran.



Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d’aurin goro. Ta d’aura hannu biyu akai tana fad’in ‘ya’yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar Bata tab’a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba. 


Mik’ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije.


Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab’a.



Saida ta Lek’a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d’aga kiran. Babu b’ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran.


Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe..



Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama “Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?”


Dije ta murmusa “K’walliya munsan abinda muka sani dai.”


Asshe ta furzar da huci “And we have common enemy here.”


“A’a a’a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.?” Ta k’arashe tana fiddo idonta waje.



“Ina nufin munada mak’iyiya guda d’aya.. Ita ce Suwaiba.!”


Inna Dije ta murmusa “Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon ‘yaruwa Suwaiba take min ba mak’iyiya ba.”


Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutuwan tilon D’anki.?”



Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d’in da aka tarbeta dashi “Waye yace miki Dije tana yafiya..?”

Ta kuma gyara zama “Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D’aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son gani ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!”


Asshe ta jinjina kai “Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k’asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k’asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.!” Ta k’arashe idonta tar cikin na Inna Dije.


Murmushi Inna Dije take tana dubanta “Maiyasa kika kirani.?”


“Kiranki nai mu taru mu had’a k’arfi da k’arfe mukai Suwaiba k’asa. Dan bazan tab’a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri’arta ba. Bazan bari Alakan D’ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D’ahna ba. Bazan tab’a bari D’ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab’a bari na had’a zuri’a da Suwaiba ba.!” Ta k’arashe tana huci. 


Inna Dije ta murmusa “Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.”


Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D’anta Hilal da kudin da ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata asiri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud’ad’ensa Har kawo auren da Hilal d’in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so ba face ‘yar Suwaiba.


Inna Dije ta sauk’e ajiyan zuciya “Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri’arki zab’i d’aya kike dashi a nan.”



Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wane zab’i kenan.?”



“Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!”



Asshe ta d’ago da mamaki tana duban Inna Dije “Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar da Suwaiba ke fad’i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!”



Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad’an daga cikin kujeran “Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak’i iskan ‘yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi irinta gogaggun mata saman fuskarta. 


Asshe tai shiru kaman mai nazari.  Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d’aya. Zataja layi ma D’anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zaiso mahaifinsa yasan cewa ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa kud’ad’en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk’awari baya tab’a sab’awa musamman tsakaninsa da ‘yaruwarsa. Yana k’aunar ‘yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fitar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d’aure Hilal. 


Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k’asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai.



“K’warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na nufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.”


Inna Dije ta jinjina kai “Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma yarda da sakin jiki Dani. A sauk’ak’e zamu kaita k’asa.”


Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai  da yanda zasu gudanar da komai. 


**


Bayan kwanaki uku da faruwan wann al’amari Tani ta shak’i iskan ‘yanci. Duk a tunanin Umma Inna Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud’ad’ensa harda tara. 


Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk’awarin zama da kowa lafiya. 


A b’angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak’a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad’in “Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud’ad’en yayi amfani dasu wajen d’aukar ma surkar Haidar Lawyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d’in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d’aga koda k’adarata..”



Katseta yai da fad’in “Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud’ad’en.”


Ya dubi Hilal “Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud’ad’en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d’aukesu matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk’uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud’ad’ena.” Yana ida fad’in haka Ya mik’e ya fice yana sab’a babbar riga. 


Hilal ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud’esu ya dubi Amminsa cikin mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa. 


Kafin yai wani magana ta dakatar dashi “K’warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud’ad’en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab’a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba ‘yar Suwaiba.! Ka nemi ‘yar gidan ko waye ka aura amma ba ‘yar Suwaiba ba.!”



Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa “Kinyi haka ne dan ki d’aureni Ammi..? Sabida haka kika zab’i taimaka masu.?”


“Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark’an Suwaiba da zuri’arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud’i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi ‘yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda ‘yar Suwaiba ehe.!”


Ya girgiza Kansa “Kiyi hak’uri Ammi.. You don’t have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma  ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice. 


K’arshe dai Asshe ciwon k’arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar. 

**


Abuja..




Yau kwanan Haidar ak’alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk’ufa addu’a gareshi da rok’ar masa sauk’i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa. 


Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na’urar nasara Sun masa k’awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido. 


Mommy taci gaba “A lokuta da dama mukan mance wasu ni’imomin  da Allah yai mana na d’an lokaci ne ba mai tabbata ba… Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman ‘ya’ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a’a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk’e nauyin da aka d’aura maka na hakkoki..?” Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni “Ina rok’on Allah yasa da sauran rayuwar  da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok’on Allah Ya tashi kafad’unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib’icin Al’amaransa..” Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata “Ina rok’on Allah Ya nuna mun zuri’ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He’s all I have.. I can’t lose him..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.


Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k’ok’arin k’arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar zai tashi cikin yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D’ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.!”


Ta d’ago tana duban Ummul wacce itama d’in Mommyn take duba hawaye fal idonta.


Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata  “Na fad’a zan k’ara fad’a, kin amsa sunanki Uwar alkhairi.. Kinzo da d’imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.!” Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d’ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba “I entrust my son to you.. Please take care of him.. Be patient with him.. Don’t let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri’a ta gari.”


Sai Ummul ta sadda idonta k’asa cikin jin nauyin Mommy. 


Mommy ta murmusa kad’an tana dubanta kafin tace “Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak’on sa yana jirana a reception.” 


Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik’e ta nufi bathroom. 


Koda Mommy ta mik’e sai ta nufi jikin gadon Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta “My handsome Boy. Allah ya baka lafiya.” karanto masa addu’o’i samun sauk’i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k’auna kafin ta fice.


Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Haidar. 


A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud’esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had’arin da sukai. 


Ya tuna sanda motar ta sauk’a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na’urar dake hancinsa lokaci guda ya furta “KHAIRY.!” 


A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom. 


Haidar na jin an tab’a k’ofa ya kuma lumshe idonsa kif.


Ummul takai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen.


Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan yini akai  tana dubansa dake nan jikin gadon. A ‘yan kwanakin da sukai asibitin.. 


Tagumi tai da hannayenta biyu had’ida tsura masa ido daga nan yanda yake kwance. Ta shiga tuno kalaman Mommy a gareta wanda tamkar amanar Haidar d’in ta damk’a hannunta. Sai ta tsinci kanta da shakku da kokonto musamman da ta tuna kafin had’arin ya faru ya furta mata cewa he’d set her free.. Zai sawak’a mata. A b’angaren guda ga Mommy tace don’t let go of his hand..! Mai zai faru idan k’addara bai bata daman sauk’e alk’awarin da ta d’aukar ma Mommy ba.? A wani b’angare na zuciyarta tana tunanin aurenta ya k’are a daidai wann gab’ar bayan ta d’aukar wa mahaifiyarta alk’awarin bazata waiwayi gida ba har sai ta cika watanni uku da aure. Wani k’alubale zata fuskanta bayan ta koma gida.? Shin ta Ya zata fuskanci Umma da sauran ahalin gidansu idan har aurenta Ya Mutu. Auren da ga yanda Ya kasance Tun farko.. Tabbas batasan yanda zata fuskanci Umma ba muddin aurenta Ya k’are kafin aje ko ina.. Ita duk ba wann ba. Ko kiran waya Umma ta haramta mata mai zai faru idan ta koma da sunan auren ta Mutu.? Ta lumshe idonta a hankali tana furtawa cikin zuciyarta ‘Allah duk yanda kayi daidai ne.! Ka shiga al’amari na ka zamto majib’icin lamrana.!’ 


Ta bud’e lumsassun idonta ta zuba su tsaf akan Haidar dake kwance. 


Sosai k’irjinta ke bugu sanda Takai hannunta dake tsananin rawa mai d’aukeda damshin ruwan alwala tana shafa goshinsa zuwa sumarsa a hankali. Abunda tasan ko bindiga za’a saka mata idan idonsa biyu ne bazata tab’a iya yin hakan ba. 


Tamkar electric shock haka Haidar yaji sauk’ar hannun nata saman goshinsa. Har lokacin bai nuna alamun farkawa ba. 


A hankali taji tana samun natsuwa, bugun zuciyarta na daidaita bata daina abinda take ba. 


Ta tsinci kanta tana mai sakin Murmushi a yayinda  take dubansa. Har lokacin bata daina shafa goshinsa zuwa sumarsa ba “Kasan mai..!” Ta furta a hankali had’ida gyara zamanta. Ta d’aura hannunta saman yatsunsa a hankali “Kanada sa’a. Kai d’an gata ne.. Ina nufin kanada mahaifya da take matuk’ar k’aunarka..!” Ta k’arashe maganar cikin sanyin jiki tunowa da nata mahaifiyar da tai da kuma irin rabuwar da sukai bayan tayi aure. Ta jinjina kai a hankali tana share hawayen da suka gangaro mata. Sai ta d’an tsura masa ido kad’an “Kanaga zan iya sauk’e nauyin alk’awarin da na d’aukar ma Mommy.?”


Sai ta d’an girgiza kai “Na tabbata da idonka biyu zaka ce.. Ke! Get out of my face.! You don’t want to have a monster for a husband.!” Tai maganar cikin tsarewa ita a dole tana kwaikwayonsa. 


Sai kuma ta bama kanta dariya. Ta murmusa kad’an tana mai tsura masa ido tsananin tausayinsa kwance cikin k’irjinta. Tai raurau da ido Kaman mai shirin kuka tace “Watak’ila You are a bit of a Monster, but you are also sweet.. So sweet…. Sweet Monster.!” Taci gaba da sakin sassanyar murmushi tana dubansa “Na gode da ka ceci rayuwata.! Na gode da rayuwata ta kasance mai mahimmanci a wajenka. Allah ya baka lafiya.!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa. K’ok’arin zame hannunta daga nashi take amma mai .? Sai ji tai gam Haidar ya tamke hannunta cikin nasa.


K’irjinta yai wani irin bugawa. Ta zaro ido waje tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Ta kasa juyowa ta dubesa sai rawa da jikinta yake.




SameenAleeyou📚


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post