*AUREN WATA UKU..!*
*42*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Anisa ta d’ago fuskarta da Ya jik’e sharkaf da hawaye “Ina nufin ko ban kashe Ummul ba Boka ya mata alk’awarin mutuwa.!” Ta k’arashe tana kecewa da wani irin dariya mai sauti.
Hisham Ya daka mata tsawa da fad’in “Cut the crap.! Wai meye yake faruwa ne.? Wani boka kike magana.?!”
Sosai Anisa ke dubansa kafin ta mik’e suna fuskantar juna “Your beloved Ummulkhair.. Hajiya Kwaise Maitama my Aunt ta kawota cikin rayuwar D’anta Haidar ne domin ta karya asirin dake jikinsa da ita.. Meaning, Auren Haidar da Ummul an ginasa ne bisa k’arya, yaudara da kuma cin amana… Aure ne mai k’ayyadadden wa’adi..! AUREN WATA UKU.! Sann daga k’arshe mutuwar Ummulkhairy shine cikan AUREN WATA UKU.!”
Hisham dake dubanta babu k’ifta ido Ya kuma girgiza kai “Ki min bayani dalla dalla.. Ban fahimci komai ba..!” Ya k’arashe kaman zai shak’o wuyarta ga wani irin huci da yake.
Sosai Anisa ta razana da yanayinsa sai ta mik’e tana girgiza Kai “I think it was a wrong move to come here.!”
Hisham ya daka mata tsawa da fad’in “Kina tunanin zan barki ki tafi ne ba tareda kin fayyace min komai ba.. Mai kike nufi da AUREN WATA UKU.?!”
Anisa ta kuma daidaita tsayuwarta tana duban Hisham cikin ido. Taryan taryan ta karanto masa sirrin Mommy da mahaifiyarta da taji Wanda ta jima tana zargin akwai wani b’oyayyen al’amari mai tattareda sark’ak’iya gameda auren.
Shiru Hisham yai yana kallonta bayan ta gama karanto masa kafin taci gaba “Amma idan har Haidar yayi wani aure ba tareda sanin ahalinsa ba.. Auren da Mommy ta kawo Ummul cikin rayuwarsa dan ta warware shi toh wacece matar da Haidar Maitama da ya aura a sirrance.? Meyasa babu Wanda ya Santa.?”
“Except me.!” Cewar Hisham daga nan yanda yake zaune.
Anisa ta waigo da mamaki tana dubansa “You.? Ta yaya..?”
“Because I’m his only friend.. Na san wani b’angare na rayuwarsa da ahalinsa basu sani ba. Dareen..!”
Anisa ta dubesa da mamaki tana girgiza Kai “Dareen.? Wacece Dareen.?”
“Ita ce matar da ta aure Haidar da asiri kuma inada tabbacin ita ce Hajiya Kwaise Maitama taima Haidar Auren karya asiri da Ummul d’ita dan ta rabasu..!” Yaci gaba da huci “Why Ummul..? Meyasa ita..?” Cikin zuciyarsa yake furta ‘No.. Banyi asiri ma Haidar dan macen da nake so ta zamto makarin asirin ba. Wai meke faruwa ne.? Could this be my Karma.? Na yi asiri ma Haidar dan ya kasance da wata mace sai gashi the only mace da nake so ta zamto makarin wann asirin.. But asirin Ya riga Ya karye.. Amma what if Ummul ta mutu sakamakon Auren Haidar kaman yanda Boka yace.?’ Sai Ya soma girgiza kai a fili yana furta “No I can’t lose her.. I need to protect her from this marriage at all cost.!’
Anisa ta girgiza had’ida katse masa tunanin nasa “Wai mai kake fad’a ne..? Wacece wann Dareen d’in.. Where is she..?”
“She’s nowhere to be found.. Haidar ya rabu da ita a ranan da zaiyi accident d’in.. Amma idan har muna son cimma burinmu na raba Haidar da Ummul.. Dole mu dawo Dareen cikin rayuwar Haidar.!” Ya k’arashe yana duban Anisa.
“You must be crazy..! Bayan ya rabu da rak’ai so kake ta dawo..? So kake idan Ummul bata Mutu ba ni na mutu.?!” Ta k’arashe tana firfito da ido waje.
Makirin murmushi saman fuskar Hisham yake fad’in “For once in your life, use that tiny brain of yours..!” Ya k’arashe yana mata lamu da yatsunsa alamun yana nuni da k’ank’ancin kwakwalwarta kaman yanda yace.
Anisa ta galla masa hara tana duban yanda yake Kallonta with that infuriating half smile on his face. A kufule tace “ Toh mai babbar kwanya make me understand.
Har lokacin murmushin ne saman fuskarsa. Ya dan kauda fuska ga barin dubanta “Abun shine zamu dawo da ita ne domin ta tarwatsa yarda da aminci da Ummul tayi ma ahalin Maitama.. Zamu dawo da ita ne domin mu bud’e idon Ummul ta fahimci dalilin kawota cikin ahalin da Hajiya Kwaise Maitama tayi. Zamu dawo da ita ne matsayin matar da Haidar yai zaman daduro da ita ba k’ark’ashin kalmar aure ba..Zamu dawo da ita ne domin mu b’ata image d’in Haidar da ahalinsa a idon Ummul.. Zamu dawo da ita ne domin mu nuna ma Ummul cewa gaba d’aya ahalin Maitama Sun yaudara ta ne. Su d’in macuta ne mayaudara kuma azzalumai Wanda zasuyi komai sabida cikar burinsu..!” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Dareen ta sani a halin yanzu bazata sake mallakan Haidar ba.. Dan haka zatai komai domin ta tarwatsa masa farin cikin dake k’ok’arin shigowa cikin rayuwarsa Wanda ya rasa hakan tsawon rayuwarsa.. Kinga idan har Ummul ta fice daga rayuwarsa you can have Haidar all to yourself .. Isn’t that genius..?!” Ya k’arashe da murmushin saman fuskarsa.
Anisa sai ta soma murmushi tana jinjina Kai “Wow.. tunani mai kyau.. I must admit kwanyarka na ja… Toh amma yanzu.. A ina zaka samo Dareen or whatever.?”
Murmushi kawai Hisham yake yana duban Anisa tareda jaddada shashancinta. Dan Hisham dai bai sanar da ita cewa tareda Dareen suka k’ulla komai ma Haidar ba. Komai d’aurawa yai kan Dareen. Bazai ba ma Anisa reason ko wani k’ofa da zata samu abun threatening d’insa dashi ba. Bazai tab’a bud’e ma Anisa cikinsa tasan ko wanene shi da asalin manufarsa Akan Haidar da ahalinsa ba.
“Kar ki damu zan kula da wann.. Kedai kije kici gaba da monitoring komai acan.. Ki saka mana ido kan Haidar da Ummul kiga ina relationship d’insa ya nufa.. Sann ki saka mana ido Akan Kwaise Maitama.”
Anisa ta jinjina Kai “Kar ka damu da wann.. Zan kula da wann b’angaren.”
Ya jinjina Kai suna Sallama da Anisa.
Bayan Anisa ta fice shid’in ma gidansa ya nufa ya isa jikin hotunan Haidar da Ahalinsa Wanda yai crossing da red pen gaba d’aya. A fili yake furta “Ban jure duk wani wahala a banza ba..! Banyi duk wani fad’i tashi na ganin na zama cikakken architect a banza ba.. Nayi haka ne to easily invade your lives.. Nayi haka ne domin na fanshe duk wani k’uncin da kuka jefamu ciki nida mahaifiyata..!” Ya kuma gyara tsayuwarsa yana huci “I’m resourceful today because you rejected me Aliyu Maitama.!” Yai maganar yana duban hoton Daddy Wanda shima yayi crossing. Yaci gaba “I’m who I’m today sabida na girma cikin wahala, k’unci da takaicin zama D’anka..! Ka yarda dani wann D’an da ka sheganta da bakinka tun yana ciki baizo duniya ba shi zaiyi ajalinka da duk wani farin cikin da kake tunanin ka samu a wann duniyar.!” Ya maida dubansa kan hoton Mommy Wanda shima anyi crossing da red pen. You’re the one who instigated all this chaos.. Kece kika tada duk wani k’ura.. Daga k’arshe kin kawo Ummul d’ina ciki.. Saidai d’iyar ‘yaruwarki Anisa ta mutu amma ba Ummul dina ba.. Sai na raba wann D’an naki da Ummul d’ita duk wuya duk rintsi.. Ummulkhair is mine.. Wllhi na ranste sai na d’auketa daga wajenka Haidar.!!” Ya k’arashe yana huci yana duban hoton Haidar dake daga tsakiyan na iyayensa Wanda shima anyi crossing anja layi da jan alk’alami.
**
Su biyu ne cikin d’akin yana kwance daga saman gadon yayinda Ummul ke tsaye gefe tana fito da shirts daga cikin suitcase d’in da suka shigo dashi itada Anisa. Mommy ce ta d’aureta nan wajen tace Lallai ta nema ma Haidar rigar da zai canza dan tasan halinsa tinda Ya farfado bazai taba yarda ya zauna da kayan asibiti ba.
Sai fito da t-shirts din take amma da alama Wanda take fito da Kayan dan ya gani yai selecting baida niyyan yin hakan. Dan ko kallo bata ishesa ba balle kayan da take cirowa.
Ta lumshe idonta a hankali tana tunani cikin zuciyarta ‘Mai zanyi yanzu ni Ummul. Bai kallon b’angaren da nake.’
D’ago idon da zatai sukai ido hudu. Sai ta daburce gaba d’aya.. Ta suri t-shirt d’aya ta d’ago sama tana nuna masa “Wann yayi.?” Yanda tai maganar fuskarta d’aukeda murmushin da yafi kama da yak’e sosai zai baka dariya. Kai da gani kasan maganar zuwa mata kawai yai ba tareda ta shirya yinsa ba.
Bai bata amsa ba Har lokacin dubanta yake da rikitattun idanunsa.
Ganin bai daina kallonta ba bai kuma ce komai ba Ya sanyata aje rigar ta kuma d’auko wani ba tareda ta kalla mai ta d’auko ba ta shiga nuna masa “How about this one..? Duba kaga.”
Wann karon sosai ya dad’a tsarewa yana duban abinda take nuna masa Wanda da alama ita kanta bata San mai take nuna masa ba.
Ta kasa daina murmushin yak’en da take sai juya abin dake hannunta take idanunta naga Haidar Wanda yai k’ok’arin mik’ewa alamun zai nufo yanda take. Bugun Zuciyar Ummul Ya k’aru ta yunk’ura zata nufosa tana fad’in “A’a ka dakata.. Zan taimaka maka.” Bata rufe baki ba abinda ke cikin hannunta tana nuna ma haidar wanda a tunaninta riga ce ta fad’o k’asa.. Dubawan da zatai nan taga shorts ne ashe take ta faman nuna masa. Bama tasan da gajeren wandon cikin jakar ba. Anisa ce ta saka a sace dan kawai ta had’a Ummul d’in da Haidar fad’a tinda tasan Haidar mutum ne da baya so ana kutsa masa kai cikin rayuwa without an invitation.
Ummul ta runtse idonta sanda ta d’auko gajeren wandon cikin hannunta.. Tai saurin b’oyesa a bayanta tana tuhumar kanta ‘Daga ina wann yazo. Mai kika aikata Ummul.?’
Bata Ankara ba sai jin hannayen Haidar tai ya kewayeta. Bakinsa kusan kunnenta yake furta “Who gave you the right to touch my things.?”
Ta kasa cewa komai sai zuciyarta dake ci gaba da bugu. Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa Haidar ci gaba sanda yake Zare shorts d’in daka cikin hannunta har lokacin tana rungume cikin jikinsa “I hate it when others invade my private space.!” k’arashe yana zare wandon cikin hannunta.
Daidai lokacin Anisa ta turo k’ofa ta shigo Mommy na biye da ita. A tunanin Mommy Anisa ta nemi izinin shiga an bata Shiyasa ta kutsa kai.
Anisa tai saurin cin birki had’ida cewa “Kuyi hakuri na shigo kaina tsaye. I’m sorry.!”
Mommy tai saurin janyota suka nufi k’ofa tana fad’in “Ke ai bansan Randa zaki bar wann shashancin naki ba.”
Haidar ya dan matsa baya kad’an yana dafe garu had’ida ciza labbansa kad’an sabida raunin da suke jikinsa Har lokacin. A hankali ya furta “It’s fine Mommy.. You can come in.” Ya k’arshe maganar sanda yake kishingid’a saman gadonsa ta majinyata.
Ummul ta rintse idanunta tana jin kaman k’asa ya tsage ta shige. Ko d’agowa ta dubi Mommy ta kasa. Yayinda Anisa ke ta faman aika mata harara cikeda k’iyayya k’asa k’asa.
Mommy ta karance yanayin da Ummul ke ciki sai ta bata aike wajen nurses d’in dake reception dan tana son magana da Haidar alone. Ta dubi Anisa ma ta aiketa can waje wajen driver d’inta.
D’akin ya rage saura ita da Haidar.
Mommy ta tsaresa sosai da ido. Duba irinta ta tuhuma. Ya d’an dubi mahaifiyar tashi sai ya d’an sadda idonsa kad’an ba tareda yace komai ba.
Sosai Mommy taji dad’in hakan da Haidar yai alamun dai gradually yana sauyawa tinda tasan girmamawa ce yasa shi sadda idanunsa.
Ta janyo kujera ta zauna kusan gadonsa gefen kansa.
“Haidar.!”
Ya d’ago ya dubeta jin ta kirasa in a serious tune.
Mommy taci gaba “Kar kaga laifin Ummul dan an had’o kaya an kawo maka.. Ni ce na sakata yin hakan.”
Ya d’anyi shiru sai kuma yace “But Mommy ba sai anje cikin kayana ana bincike ba.. You could’ve sent your driver ya saya ko a boutique.. Since I won’t be staying here for too long..”
Mommy ta murmusa jin yanda yake ta kwanakwana yana maganar. Wai Haidar ne bai fad’a mata magana kai tsaye ba yaketa faman kwana.. Hakan na nuna mata Ya fara gudun b’acin ranta.
Ta d’aura hannunta guda saman nasa tana murmushi “I know Haidar.. Zan iya yin hakan amma na zab’i matarka taje ta bincika cikin kayanka ta d’auko maka kaya.. Kasan dalili.? Sabida ita d’in matarka ce.. Bata da wani shamak’i da duk wani sirri naka.”
Sai ya dan lumshe ido kad’an ba tareda yace komai ba.
Mommy ta kuma gyara zamanta “Aliyu, my son.”
Haidar Ya d’ago Ya dubeta.
Mommy taci gaba “Kaman yanda Ubangiji Ya bamu daman kasancewar D’a da mahaifiya a karo na biyu.. Ina so ka nuna godiyarka ta hanyar kasancewa miji ga Ummulkhair.. Bani so na kuma tilasta maka wani abu musamman abinda ya danganci yanke hukunci ga rayuwarka.. Amma na maka alk’awari wann shine zai zamo abu na k’arshe da Ya danganci yanke hukunci cikin rayuwarka Wanda zan buk’ata daga gareka, in sha Allah.. Please do this for me Haidar.. For the last time.. Ka bama kanka dama da Ummulkhair.. Just this once.. Na maka alk’awari.. Daga k’arshe idan bai working ba I won’t force it..” Ta dan murmusa tana dafa hannunsa “Inada yak’inin ma Khair in sha Allah.” Ta k’arashe tana duban D’an nata.
Haidar ya dan dubeta cikin yanayin da bazaka iya fasalta abinda ke cikin zuciyarsa kai tsaye ba.
Mommy ta kuma murmusawa kafin ta mik’e “Ni zan wuce gida na duba Aunt d’inka Asshe da gajiyan hanya.”
Haidar baice komai ba sai jinjina mata kai da yai. Yai mata fatan kasancewa lafiya. Da haka Mommy ta fice zuciyarta fari sol. Cikin buwayar Ubangiji D’anta Ya soma dawowa kan turba.
Bayan tafiyar Mommy daga bisani Ummul ta shigo. Aiko tana shigowa saiga Anisa ta take mata baya. Tai Sallama ma Haidar kafin ta juyo ta dubi Ummul “Ummul kema ya kamata mu tafi koh.. You know they don’t accept visitors here.”
Kaman wanda aka zaburesa haka ya juyo yana duban Anisa jin tana fad’in Ummul ta tashi su tafi.
Anisa tai murmushin da yafi kama da yak’e ganin irin duban da Haidar ke aika mata “Hos..Hospital rules.!” Ta fad’i cikin sauri da k’ok’arin kare statement d’inta.
Har lokacin wani irin duba Haidar ke aika mata “She’s not a visitor.. You can leave.” Ya fad’i a tak’aice.
Cikin sanyin gwiwa Anisa ke jinjina kai “Haka ne na mance..She’s your wife.. I.. am the visitor here.” Tai maganar cikin k’ok’arin danne k’uncin dake taso mata ga murmushi mai ciwo saman fuskarta.
Ummul dai ta dubi Anisa ta dubi Haidar.
Anisa taima Ummul saida safe had’ida fatan samun sauk’i ma Haidar.. Tasa kai zata fice Haidar Ya dakatar da ita “Do yourself a favour and quit coming around. As you mentioned, visitors ain’t welcome.!”
Da mamaki Anisa ke dubansa jiki a matuk’ar sanyaye yayinda Ummul ma ke binsa da kallon mamaki.
Anisa ta k’ak’aro murmushi mai ciwo tana jinjina Kai “As you wish..Dear Cousin.” Ta k’arada “Get well soon.” Ta k’arashe tana Kai dubanta ga Ummul wacce sosai damuwa ya nuna saman fuskarta.
Anisa na ficewa tai bursting cikin kuka. Gudu gudu ta fice daga asibitin.
Ummul ta maidoda dubanta ga Haidar Wanda ke k’ok’arin zame rigar dake jikinsa sai faman tamke fuska yake sabida zafin rauni da basu gama sake shi ba. Sam bama ta kula da abinda yake ba dan sosai korar da yai ma Anisa yai mata zafi.
Kaman zatai kuka. Cikin sanyinta ta soma fad’in “Haba mana.. Mai ka aikata ne ..? Meyasa zaka Kori Anisa. Laifi ne dan an nuna damuwa akanka.?” Kallan Yanda tai da fuskarta kaman mai shirin kuka Haidar yake. ‘How dare she interferes! Who does she think she is?’ Cikin zuciyarsa yake zancen saidai Ya kasa furta komai.
Bai ce da ita komai ba sai k’ok’arin sauk’owa daga gadon da ya soma. Sai sann Ummul ta kula babu riga jikinsa. Ai sai ta d’an daburce ta soma k’ok’arin kare idonta da tafin hannunta tana sadda Kai k’asa ga Haidar dake nufota. Ta soma matsawa baya tana fad’in “Wai mai kake aikatawa ne. Da.. Da cewa Kai na baka waje zaka canza..”
Bai amsata ba bai daina nufota ba har suka isa jikin gini. Hannu yasa ta bayanta Wanda ya sanyata saurin d’agowa a matuk’ar tsorace tana dubansa zuciyarta bai daina bugawa da sauri ba. Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin Haidar ya mik’a hannunsa sosai ya d’auki riga cikin suitcase d’insa dake daga gefen Ummul saman drawer.
Ganin ya d’auki rigar ya soma takawa a hankali ya sanyata lumshe ido had’ida sauk’e ajiyan zuciya a hankali.
Shi kaw Haidar na hankalce da ita yana kallonta ta wutsiyar ido. Murmushi ya saki da gefen bakinsa kafin ya dan saki k’ara yana rik’e gefen ribs d’insa Wanda yasa Ummul saurin Ware idonta. Bata san sanda ta nufosa da sauri ta mik’a hannayenta ta tallafosa tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo yake ji.
Haidar bai daina ciza labb’ansa yana tamke ido had’ida sakin k’anan k’ara alamun yana jin pain har saida suka isa saman gadon.
Ummul ta kuma dubansa a kid’ime bayan ta taimaka masa ya d’an kishingid’a “Kana jin ciwo ne.? Kana so na kiraka maka Likita.? Kaga barin kirawo su.” Ta k’arashe tana k’ok’arin dirowa daga saman gadon amma sai taji Haidar ya rik’o hannunta.
Cak ta dakata da abinda take ta juyo a sanyaye tana dubansa.
Ya d’an sha mur ganin tana duban fuskarsa kafin ya sakar mata hannun “Why would you call them.? Bayan gaki nan a nan.!” Ya k’arashe maganar yana d’aura mata rigar saman hannunta.
Ta dubesa ta dubi rigar da ya saka cikin hannunta da mamaki. Sai ta d’an girgiza Kai kad’an alamun bata gane mai yake nufi ba. Mai zatai da rigarsa.
Sai shima ya d’aga mata gira had’ida yi mata alama da ido da ta saka masa rigar.
Sai Ummul ta soma girgiza Kai “A’a bazan iya ba.. Ka saka rigarka da kanka.”
Bata Kai aya ba ya bata amsa da “But I can’t move my arms.. It hurts.. And since you are my caretaker, Ke yafi kamata kiyi. Haka ne.!” Ya k’arashe yana tsareta sosai da ido.
Sukai shiru su duka biyun suna duban juna kafin Haidar ya k’ara da “I thought kin d’auki alk’awari ma Mommy.. Cewa zaki iya shiga cikin rayuwata..? Here.. Do it.!” Ya k’arashe cikin sigan rad’a yana mai kuma dank’a mata rigar cikin hannunta.
Ummul tai rau rau da idanu tana dubansa kaman zata sakar masa kuka tace “Amma..Toh.. Amma ya akai ka cire wancan.?”
Har lokacin muryarsa k’asa k’asa “It’s just a patient wear.! Hakan na nufin zan iya cirewa cikin sauk’i..” Ya k’arashe yana tsareta da ido.
D’an rausayar da ido kad’an tai tana mai satan kallonsa. Har lokacin idon Haidar na kanta alamun yana jiran ba’asinta. Sai Ya kashe mata ido guda alamun yana jira.
Ta d’an gyara zamanta tana duban gefe da gefe. Ta kai idonta kan hospital gown da ake sanyawa wa marassa lafiya Wanda Ya cire. Tace “Amma.. amma Na zata saka rigar asibitin ma dokace.”
Kafin tai shiru ya bata amsa da fad’in “You should understand by now that I don’t follow rules.!” Ya k’arashe yana mai tsareta da ido. Wanda hakan Ya kuma sanyata maida idonta k’asa.
D’akin Ya d’anyi shiru banda lugude Babu abinda k’irjinta keyi. Ta Ya zata soma sanya masa riga.?
Haidar ya soma k’ok’arin saka rigarsa yana hankalce da ita sai faman juya yatsun hannunta take. Sarai yasan tunani take.
A hankali yake zira hannunsa still yana kallonta.
Out of nowhere ta sinkayo muryarsa “Kenan k’arya kike da kika ce kin dau ma Mommy alk’awarin shiga rayuwata.?”
Shiru batace komai ba sai sadda kanta k’asa da tai kaman wata maras gaskiya.
Dak’ik’ai suka gifta babu mai cewa komai cikinsu.
“Zamanki a nan baida amfani.. You shud also leave please.” Ya fad’i yana k’ok’arin saka rigar da kansa.
Ta soma girgiza kai tana dubansa cikin d’an daburcewa. K’ara ya saki kad’an alamun ya fama ciwonsa.
Ba shiri Ummul ta k’araso da sauri ta rik’e hannunsa da rigar tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo ke masa. Duk ta daburce a hankali take zira masa rigar Har saida ta fitar masa da hannunsa. Idonsa kyam a kanta Har ta gama zira masa rigar ta gyara masa pillow ya kishingid’a.
Zata mik’e Ya rik’o hannunta. Ta kaikaito suna duban juna.
“You should.. also change.. You can’t sleep with…those cloths.!” Yai maganan yana nuni zuwaga kayan jikinta da idonsa.
Ta k’ak’aro murmushi “Kar ka damu.. Zan iya.”
Bai kuma cewa komai ba sai tab’e bakinsa da ya d’anyi.
Tana kallonsa daga nan yanda take zaune ya tada sallan isha har ya sallame. Can wani ma’aikacin asibitin Ya nemi izinin shigowa Ummul tai masa iso. Nan ya shigo yana turo wani keke irin Wanda ake d’aura abincin majinyaci.
Iyakacin k’ayaddajen abincin da majinyacin zaici aka shigo dashi harda dose din maganin da zai sha na wann lokacin.
Mutumin zai soma b’alle magani Haidar ya dakatar dashi “Just leave it from here. Kana iya tafiya.”
Ya jinjina masa kai kafin ya dubi Ummul Ya bata wani k’aramin card Wanda zata karbi abincinta dashi a cafeteria.
Ita dai Ummul sai juya card d’in take tana mamakin asibiti kaman a turai. Dole ma ace ba’a buk’atan d’an tayin jinya tinda duk wani kula za’a baka. Ga na’ura dake indicating musu abubuwa da dama Wanda daga yanda suke zasu fahimci hakan.
Haidar yai gyaran murya kad’an Wanda hakan Ya dawo da hankalinta gareshi. Yai mata alama da ido da ta k’araso ta zauna.
Ba musu ta k’araso saidai idonta a k’asa dan ita dai tinda ta sanya masa riga ta kuma kasa had’a ido dashi.
“Can I take my drugs…now.?” Yai maganar yana mai kai dubansa ga agogon bango dake manne d’akin. Alamun yana nuna mata lokacin shan maganin zai shige.
Sai ta dubi magungunan ta girgiza kai “Ban.. Ban san ya zanyi ba.”
Ya tsareta da ido sai yace “Come close.. I’ll show you.”
Da dan dubesa sai ta d’an matso kusansa kad’an. Shi kaw har lokacin ya tsareta sosai da ido “Closer.!” Ya furta a hankali. Ta kuma dubansa sai ta d’an kuma matsowa.. Saida ya tabbata ta matso kusansa sosai kafin yace ta d’auko parantin maganin ya nuna mata. Ita dai jinsa kawai take amma da ganinta zaka fahimci a tsorace take.
Ta d’auki glass cup da bottle water da mutumin ya shigo dashi ta soma tsiyayawa hannunta sai rawa yake alamun nervousness. A haka take yunk’urin kai ruwan da maganin bakinsa Har lokacin hannunta bai daina rawa ba. Shi kaw Haidar sosai ya tsareta da ido. Charaf yai grabbing hannunta. Wanda hakan Ya sanyata d’ago ido tana dubansa a d’an tsorace.
Shid’inma ita yake kallo “Just.. relax..!” Ya fad’i yana mai kai hannun nata saitin bakinsa har lokacin idonsa akanta.
A haka dai ta ko k’arta ta basa maganin. Akazo maganar abinci zata tashi nan ma yace bazai iya moving arms dinsa ba she should feed him. Haka dole ba yanda ta iya ita ta basa abinci. Ko wani motsi nata kan idon Haidar. Ranar dai ta zamto tamkar personal nurse d’insa. Dan duk wani abu da suke na kula da majinyaci baya bari suyi ita takeyi saidai Wanda yafi k’arfinta ko layin ma’aikatan lafiya ne kawai. Dik yanda taso ta zille ma Haidar Ya kasa barinta.
Can dare tana kishingid’e saman sofa shi kaw sai kallonta yake daga nan saman gadonsa ta majinyata. Nan yaga ta tak’ure waje guda ta k’udindune cikin hijab dinta.
A hankali Ya mik’e daga saman gadonsa da kyar. Ya tako zuwa yanda take. Zama yai gefenta yana k’are ma fuskarta kallo. Kallo irin Wanda bai tab’a tsayawa yai mata ba. Hannu yasa yana zare Hijab d’in hakan yai daidai da juyin da zatai. Take yaji wani abu ya tsargar masa kaman electric shock. Nan yake binta da kallo head to toe. Ya jima sosai yana k’are mata kallo kafin ya karkatar da ita kad’an Ya kwanta nan gefenta kasancewar kujerar mai fad’i ne sosai. Ya matso da ita cikin jikinsa Ya janyo abin rufuwar Ya rufa musu.
**
A can gida kuwa yanda Anisa taga rana haka taga dare. Sai kai komo take a d’aki ita kad’ai tana safa da marwa. Ta lallaba ta tafi d’akin da aka sauki Amminta.
Ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata dake sharan bacci tana tunanin hirarsu da Mommy da ta sinkaya a asibiti gamed auren Haidar da Ummul.
Kodai ta tashi Ammi ne ta sanar da ita taji komai. Tasan komai a halin yanzu.? Toh Amma Hisham yace ta bar masa komai.. Ya mata alkawarin zai cire Ummul daga rayuwar Haidar ko ta halin k’ak’a.. Idan ta sanar da Ammi wani abu yanzu shirinsu da Hisham ka iya b’aci. Bazata bari hakan ta kasance ba. Sauri sauri ta koma nata d’akin. Ta kagu gari ya waye ta bullo da wata hanyar da zata samu taje ta duba Haidar da Ummul tinda Haidar dai ya mata iyaka da asibitin.
**
Asubahin fari ta farka tana mamakin yanda bacci mai nauyi ya dauketa itada take yawan farkawa cikin dare. Nan tajita cikin jikin mutum kuma. Zuciyarta ta tsinke. Ita tsoro ma abin ya bata dan Sam bata kawo a zuciyarta majinyaci irin Haidar ka iya mak’alewa gefen kujera har yayi bacci irin haka ba.
Ta yunk’ura a tsorace zata tashi sai ta sinkayo muryarsa yana sakin ‘yar k’ara had’ida rik’e gefen hak’ark’arinsa. Su duka biyu duban juna suke kasancewar akwai hasken dim-night cikin d’akin.
Tai saurin mik’ewa tsaye daga kan kujerar tana kuma kallonsa.
Ganin da gaske na cikin pain dan har lokacin bai daina tamke ido yana dafe hakarkarinsa ya sanyata saurin duk’awa gabansa tana tambayarsa “Da zafi ne.? Na bige maka ciwo ko.? Dan Allah kai hak’uri wllhi ban kula bane.!” Ta k’arashe maganar kaman mai shirin kuka.
Sai Ya daina tamke idon da yake yana Ware idanunsa a hankali yana kallon yanda take magana kaman itace cikin pain d’in.
Ta d’an saci kallonsa “Kai hakuri zan tabbata na taho da abin rufuwa yau in sha Allah.”
Ya tsareta sosai da ido kafin ya girgiza kai kad’an had’ida lumshe idonsa “It’s fine..” Ya fad’i a tak’aice.
Ya mik’e a hankali yana fadin “I.. Will use the bathroom.. It’s subh prayer time already..”
Ta jinjina masa Kai a hankali “Kana buk’atan taimako na.?”
“No I.. Can manage.” Ya fad’i yana dingisawa har ya nufi hanyar bathroom din.
Yana shigewa ta zauna had’ida sauk’e deep breath. Hannunta na rawa ta janyo mayafin da ya rufesu dashi. Sai ta runtse idonta da sauri wai yau ita Ummul ke bacci mayafi guda da Haidar.. Kunya ne.? Damuwa ne? tsoro ne? Duk sai ta ma rasa mai ke mata yawo cikin zuciyarta.
A b’angaren Haidar Shima haka nan ya lumshe idonsa a bathroom abubuwa fal zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake tuhumar kansa ‘What’s wrong with you Haidar.? Why are you so soft with her..?’ Take zuciyarsa ta shiga tuno kalaman mahaifiyarsa garesa ‘Ka ba ma kanka dama da Ummulkhair.. Kamin wann Haidar koda shine abu na k’arshe da zan buk’ata wajenka.’
A fili yake furta “Sabida Mommy. You are doing it for Mommy and because of Mommy.. Kaman yanda ta buk’ata.”
Da safe kuwa su duka biyun yanayinsu ya dan sauya bayan baccin da sukayi tare musamman ma Ummul wacce ta kasa had’a ido dashi. Gaisuwa ma k’asa k’asa tai masa. Haidar nata karantarta.
Sassafe take shirin tafiya gida dan ta samu ta kintsa kanta kafin ta dawo. Zata fice ta sinkayo muryarsa “Khairy.!” Cak ta tsaya tana sauraron sunan da ya kirata dashi.
Haidar yaci gaba “Don’t take long.. And.. kar ki sake ki zo da wani abin rufuwa asibitin nan.”
Sai ta dubesa da mamaki “Amma maiyasa.?”
Ya tab’e baki kad’an “Hospital rules.!”
Ta jinjina Kai a hankali tace “Shikenan bazan zo dashi ba”
Haidar ya jinjina mata Kai sihirtaccen murmushi saman labb’ansa. (Kunji wani salon wayo wajen Haidar. Wai asibiti ta hana zuwa da abin rufuwa daga gida.)
Ita dai Ummul Haka ta fice tana mamakin wann wane irin asibiti ne masu tarin dokoki da k’a’idodi.
Bayan ficewar ta da kad’an Anisa tai knocking a k’ofa. Duk a tunaninsa Ummul ce ta dawo. Kai tsaye ya bada izinin shigowa.
Ga mamakin sa Anisa ya gani rik’eda jakan kaya. Ya tsareta sosai da ido alamun yana jiran ba’asi tinda yasan ya mata iyaka da asibitin.
Ta k’ak’aro murmushi tana masa gaisuwar da bata samu amsa ba.
“What are you doing here? I thought I made it clear to you…” Saurin katsesa tai ta hanyar d’ago masa jakar Kayan “Kayan Ummul… Mommy ce ta Aiko ni na kawo..” Sai ta d’an saci kallonsa “And.., I…wanted to check how you’ve been holding up.. Laifi ne hakan..? After all, we are cousins.”
Katseta yai “I just don’t want you here.. Don’t you get it”
Kuka ta fashe dashi tana mai barin d’akin. Ta rasa mai tai ma Haidar yake mata irin wann kiyayya.. Toh kodai ya fahimci da saka hannunta ne a had’arin da ya samesa.? Dole ta nemi Hisham su san ta yanda zasu bullo ma al’amarin.
**
Hisham ya dubeta sai kuma ya girgiza Kai yana murmushi “Kar ki bani dariya mana Neesa. Quite alright Haidar na zargin had’arin mota da ya samu shiryayyen abu ne.. Amma ina mai tabbatar Miki ba kece yake zargi ba.”
Anisa ta dubesa ta d’an girgiza kai “Ta Ya ka tabbatar da haka.? Sann waye yake zargi.?”
Hisham Ya murmusa “Wani hujja yakeda shi da zai zargeki.?”
Shiru bata basa amsa ba.
Hisham yaci gaba “A kalaman Haidar cewa yayi yana zargin wani ne dake boyayyen agenda akansa. Waye keda dalilin ganin bayansa.?”
Shiru bata amsa ba.
“Dareen.! Ita ce kawai takeda motive na hallak’a Haidar tinda ta rasa shi bazata bari wata ta same shi ba. Haka ne.?”
A hankali Anisa ke jinjina kai.
Hisham yaci gaba da murmusawa “Which is why dole na cimma Dareen kafin Haidar Ya cimmata..” Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Duk abinda nakeyi.. Everything is calculated. Ki bar mun komai kaman yanda na fad’a.. Aikinki kawai shine ki saka ido akan Haidar da kuma Ummul.”
Ta rausayar da ido “But it is not as easy as it seems. Haidar is making it difficult.”
Ya kurbi drink dake hannunsa had’ida d’age kafad’unsa kad’an ya tabe baki “You must do it. You don’t have a choice. Find a way to keep an eye on those two”
Ta shiga jinjina kai a hankali tana furzar da huci.
Basu ida maganar ba wayar Hisham tai ruri Haidar ke kiransa.
Ya murmusa yana duban wayar “Speak of the devil… he shows.!” Ya furta a fili kafin ya d’aga kiran.
Bayan Sun gaisa irinta abokai Haidar yace “I sent you an email.. Since you can’t come to visit.”
Ya murmusa “Haba abokina ba haka bane.. Kasan asibitin naku ne na turawa. Komai d’an k’aida.. And work’s been too demanding lately.. Musamman da yake baka nan. On the other hand ga neman Dareen da nake. Kasan bazan tab’a barinta ba sai na nemota ta biya abinda ta aikata ma abokina.
“Speaking of Dareen. Are you free?”
Shiru kaman bazai amsa ba Ya soma yan kame kame Haidar Ya katse sa “You know me. I don’t take no as an answer. Ina jiranka.” Daga haka katse kiran yai.
Duban Anisa yai yana huci. Cikin zuciyarsa yake ayyana Ya tsani yanda Haidar keyi kaman wani boss d’insa bayan cewa ko a haife ne shine gaba da Haidar d’in..
Anisa ta katse shirun da fad’in “See Kai gashi yana nemanka amma ni cewa yake anyi restricting zuwan visitors.”
Hisham Ya furzar da huci “Kinsan meye matsalar?”
Anisa ta girgiza kai alamun a’a.
“Bazai yuwu Ummul ta ganni wajen Haidar ba all our plans zasu lalace ne. No Ummul bazata ganni wajen Haidar ba. It will be a disaster.”
Anisa ta murmusa “But this is the perfect time da ya kamata ka visiting Haidar because Ummul bata wajensa ta tafi gida. I believe ma Shiyasa ya samu chance na kiranka.
Hisham yace “You sure.?”
“Hundred percent.!” Ta basa amsa tana mai jinjina kai.
“Perfect! Yanzu abinda zaayi kiyi maza ki tafi gida ki rik’eta ki hanata barin gida Har sai nayi alerting naki. Ma’ana sai na bar wajen Haidar.”
Anisa tace “An gama Barinyi sauri na tafi kafin ta fito nasan sai ta tsaya tayi wanka tayi wasu abubuwan.”
Daga haka sukai sallama da Hisham. Shi Ya nufi asibiti wajen Haidar ita kuma ta nufi gida wajen Ummul.
A can gida kuwa Mommy sai nan nan da Ummul take tana fad’in maza maza ta gama shiryawa driver ya maidata. Mijinta majinyaci ne bai kamata ta barosa shi kad’ai ba. Asshe kanta sai mamaki take ganin yanda Mommy keyida Ummul. Lallai Anisa tayi gaskiya da tace idon Mommy ya rufe akan Ummul. Gani take kaman an canza mata ‘yaruwar tata da gaske ne. Gaba d’aya Mommy ta tashi daga Aunty Kwaise da ta sani ta koma wata abu daban. Ita kanta Asshe lamarin tsoro Ya fara bata. Ta zuba ma sarautar Allah ido ta kasa katab’us.
A haka Anisa ta iso gidan ta taddasu sai karantar Mommy take tana ganin yanda take ingiza Ummul tayi ta tafi wajen mijinta. Makirin Murmushi Anisa tai tana jinjina kai dan har ta hasasho ta yanda zata tarwatsa Auren Haidar da Ummul. Muddin ta fayyace ma Ummul komai zata fahimci Hajiya Kwaise Maitama azzalumar mace ce ba soyayyan gaskiya take nuna mata ba. Kawai tana mata duk abubuwan da take ne don amfanin kanta da D’anta. Tabbas Ummul zata tsani Kwaise da tsinann auren da tai ma da d’anta Wanda boka Ya had’a. Ta k’arashe tunanin tana mai kecewa da Makirin murmushi.
A k’ofan fita daga sashen Mommy Anisa ta cimma Ummul. Suka sakar ma juna murmushi had’ida gaisuwa.
Anisa ta k’arada “Ba dai har zaki wuce ba.?” Kafin Ummul ta kaiga bata amsa ta kuma sakin murmushi tana mai dafa kafad’an Ummul d’in “It’s fine, Ya kamata ki tafi kin baro mijinki shi kad’ai… I Miss having you around Ummul.. Kinsan bahaushe yace sabo turken wawa”
Suka murmusa a tare kafin Anisa ta mik’a mata jakan hannunta “Ga wann kar na rik’eki da surutu.”
Ummul ta d’an girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta “Ta mecece.?”
“Kayanki ne a ciki. Nayi tunanin na kai miki su asibiti sanin cewa zaki buk’ata amma sai mijinki Ya koreni dasu.. Kamar dai ko yaushe.” Ta k’arashe tana mai k’ak’aro murmushi.
Jikin Ummul Ya d’anyi sanyi “Kiyi hak’uri Anisa…”
Saurin dakatar da ita Anisar tai “No no.. You don’t have to apologise for his behaviour. Kar ki samu damuwa.. Nasan Haidar since childhood.. He’s rude, arrogant, short tempered.. and sometimes unpleasant to be around.. Ki yarda dani, idan da sabo na saba da halin d’anuwana..”
Da mamaki Ummul ke dubanta dan ko ba auren soyya sukai da Haidar ba sosai taji zafin kalaman da take fad’i kansa. Amma sai ta danni zuciyarta ta murmusa “Baki tunanin kalaman da kike sunfi kama da cin fuska.?”
Shiru Anisa batace da ita komai ba.
Ummul ta murmusa had’ida dafa kafad’ar Anisa “Kar ki damu banyi fushi ba. Dan dik abinda kika lissafo gameda shi kwalliya na d’aukesu. Domin kaw sosai suke k’ara masa k’warjini da birgewa.” Ta k’arashe murmushin nan nata dake tunzura Anisa saman fuskarta.
Murmushin da yafi kama da yak’e Anisa ta k’ak’aro “Of course. Haka ne.. Let me walk you to the car..” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Ummul d’in suka nufi mota.
A hanya Anisa ke ci gaba da fad’in “Mutanen gidan nan sunyi kama da mutanen kirki koda ahalin ya kasance birkitaccen ahali mai tarin gib’i.. Haka ne.?”
Ummul ta dubeta cikin rashin fahimta.
Anisa ta murmusa “Ko wani d’an adam yanada sirrikansa.. Amma akwai wasu abubuwan da sirri baida muhalli cikinsu. Kamar dai Aure. Haka ne.?”
Ummul ta kuma girgiza kai tana karantar yanayin Anisa. Tana danganta maganganun Anisa da tunanin kodai Anisa tana so ta sanar da ita cewa tasan yanda akayi aurenta ne.? Amma batada wani sirri da ta b’oye ma Haidar gameda aurensu face iyaka da Umma tai mata da d’aukacin ahalinta Har na tsawon watanni uku ciki harda mahaifinta dake kwance yana jinya. Bata Ida tunanin ba ta kuma sinkayo muryar Anisa daidai sanda suka isa jikin mota.
“Kina tunanin kinsan ahalin gidan nan ne Ummul.? Ko kina tunanin kinsan mijin da aka aura Miki ne.? Ina shawartar ki kar ki zak’e da yawa.. Don’t get too attached. Be warned.!” Cikeda gargadi tai maganar kafin ta murmusa “Akwai abubuwa da dama dake cikin duhu. Ina fatan a lokacin da duhun nan zai yaye miki Ummul bazaki sameni cikin wad’anda suka ci amanarki ba. And you can count on me dan ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.” Ta k’arshe tana murmushi had’ida bud’e mata marfin mota “A cikin gidan nan trust no one but yourself Ummulkhair. Tabbas Wani Auren nasara ne. Amma Wani Auren halak’a zai kaika.! Allah Ya tsare hanya.” Ta k’arashe da murmushi. Tana ida fad’in haka ta juya ta shige cikin gida zuciyarta na mata fari k’al. Dan ta tabbata ko ba komai ta cika shakku cikin zuciyar Ummul. Wani abu ma sai randa k’wai Ya fashe gaba d’aya.
Tabbas Anisa tayi nasaran jefa mata waswasi da shakku cikin zuciyarta. Shin da gaske ne ita d’in ta zak’e da yawa.? Batasan mai Anisa take son sanar da ita ba. Sann koda wann auren tun usul bata tsammaci farin ciki ko wani abunda yai kama da wann cikinsa tun farko ba. ta tsinci kanta cikin tsananin shakku da rud’ani Wanda bataji irinsa a baya ba. Sann sosai taji tana buk’atan sanin mai Anisa take son sanar da ita musamman gameda mijinta Haidar. Haka har ta isa asibiti tunanin da take kenan jikinta duk a sanyaye.
*
Asshe bata iya kwanaki garin ba ta tarkasa ta dawo Kano dan sosai ta firgita da lamarin ‘yaruwarta dole ta dawo gida ta samu ta shawo kan matsalar kafin komai Ya ida kwance mata musamman da idonta ya tabbatar mata idan ‘yarta Anisa bata k’arashi rayuwarta gidan yari ba toh kuwa ba shakka zata k’are a turu ganin irin abinda take wanda yafi kama da hauka tuburan duk dan akan Haidar. Da fari ta saka ma Ummulkhair guba a turare sann ta d’aura alhakin kan Mommy har ta tafi jail tai kwanaki dik akan haka. Yanzu ga had’arin mota da ta shirya ma Haidar wanda k’iris bai rasa ransa ciki ba. Lallai ya zama dole tasan abinyi.. Dole ta raba wann jarabebben aure na Ummulkhair da Haidar wanda ta zamto silarsa a farko ko dan ta ceto ‘yarta Anisa.
*
Kano..
Sun had’e su uku a parlorn Hajiya Asshe. Mama Tani wacce bata jima da shak’an iskan ‘yanci ba, Inna Dije sai kaw Uwar gayya Hajiya Asshe.
Tani ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Inna Dije “Dije kina nufin kice wann matar ita tayi belina ba sirakan Suwaiba ba.? Sann so kike kice mun duk zaman dad’I da naga kinayi da Suwaiba a halin yanzu dama ba na gaskiya bane.? Dije wai meke faruwa ne.?”
Inna Dije ta murmusa tana duban Tani “Tani banda abinki.. Wann ma ai sirkar Suwaiba ce. Kuma ke a tunaninki ni Tani zan tab’a yafe ma Suwaiba da ‘yarta Ummulkhair ne. Kar ki mance a dalilin bak’in k’addarar Ummulkhairi na rasa tilon D’ana Fa’izu.! Kuma ke kinfi kowa sani Tani. Dije bata yafiya sai d’aukar fansa.! Yau d’in nan zan sanar dake wace kalan Aure Suwaiba taima ‘yar D’anuwana dake kwance yana jinya wanda zai zamto Miki makami da zaki kori Suwaiba da Auren cin amana da tai miki. Tani na san komai Suwaiba zata Miki a halin yanzu. Duk wani halacci na k’arya da zata Miki bazaki tab’a mance bak’in cin amana da ta miki na aure Miki miji bayan kin aminta da ita da tayi ba. Haka ne?!”
Tani tai shiru tana duban Inna Dije wacce ke sakin huci.
Tani sai ta girgiza kai a hankali “A’a Dije. Yo ni a halin yanzu wani makami nakeda shi Wanda zan yak’i Suwaiba dashi bayan yarana da a kullum nake goranta mata cewa sunyi aure suna d’akin mazajensu gasu nan duka sun dawo gida daga wacce miji Ya koroto sai wacce miji Ya gudu Ya barta. K’arewa ma Suwaibar ke kula dasu a lokacin da nake gark’ame gidan gyaran hali. Na sani abinda Suwaiba ta min bazan tab’a yafe mata ba ko mutuwa Malam yayi amma a halin yanzu banida abinda zan yak’i Suwaiba dashi kina gani yarana ma sun koma k’ark’ashin tutar Suwaiba.. Toh mai yai saura.?”
“Malam Isubu Yayana shine kad’ai ya miki saura Tani. Dan Dikda kasncewarki ‘yar ta’adda mai saida hakkin miji da ransa da sunan gado ta’addacin da Suwaiba tayi yafi naki kuma dik randa D’anuwana yasan mai Suwaiba ta aikata a lokacin da yake kwance ya rabu da ita kenan rabuwa ta Har abada.. Kuma idan mutuwar auren yaranki ne Ya tsaya Miki ki taya Suwaiba sharan d’aki yanda Ummul zata zauna dan nan da wata d’aya jal Ummul zata dawo gida ta jone da naki yaran.!”
Tani ta girgiza kai “ban fahimceki ba Dije.? Mai kike nufi.? Wane irin Aure Suwaiba taima Ummul.?”
Carab Asshe ta cab’e “Auren mutuwa.! Auren warware sihiri.! Auren WATA UKU.!”
Take Tani ta mik’e a zabure tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Tani. Auren mutuwa..?!”
SameenaAleeyou
