*AUREN WATA UKU..!*
*43*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Inna Dije ta jinjina kai “K’warai kuwa kaman yanda kika ji.”
Wata ‘yar bazawarar dariya Mama Tani tai irin Wanda bai kai ko ina ba “Haba haba Dije. Dani dake munsan Suwaiba.. Koda ace shashasha ce lamba d’aya bazata tab’a abinda kike fad’a mun ba. Koda ace mafarkin Suwaiba da cikan burinta shine taga Ummul dinta a d’akin aure ko wane iri ne. Dije munsan Suwaiba bazata tab’a gigin jefa ‘yarta a halak’a Har haka ba.!”
Asshe ta murmusa tana duban Tani “K’warai kuwa da saninta bazata jefa ‘yarta a auren halak’a kaman yanda tayi ba. Burin Suwaiba shine ‘yarta Ummul tayi aure ko ta halin k’ak’a ko wani iri ne matuk’a sunansa Aure. Tabbas da ace Suwaiba tasan wani irin Aure ta jefa ‘yarta ciki da nadaman da zatayi sai tafi wanda take ciki yanzu.” Ta numfasa kafin taci gaba “A Yarjejeniyar da mukai da nida Suwaiba shine ‘yarta Ummulkhair Auren Kwangila tayi mai k’ayyadadden wa’adi Wanda wa’adinsa watanni uku ne. Sam ban sanar da Suwaiba ga asalin sahihin manufar Auren ba. Hasalima ban sanar da kowa bayan ‘Yaruwata da muka shirya Auren tare sai ku da Ya zama dole na bude maku cikina dan bazan iya wann yak’in ni kad’ai ba. A halin yanzu Babu abinda nake so kaman Ummul ta fice daga rayuwar ‘Yaruwata tinda na kula Ummul ta riga tayi tasiri a zuciyarta. Ba haka na shirya abun ba.. Domin kuwa a halin yanzu ‘Yaruwata mahaifiyar mijin Ummul Auren gaskiya take son D’anta yayi da Ummulkhair ba AUREN WATA UKU kaman yanda muka faro daga farko ba.”
Tani ta dubeta da mamaki sai ta girgiza kai “Toh mai kike so muyi a nan.? Ta yaya zamu raba auren da bamu muka k’ulla ba.?”
Inna Dije ta murmusa “Mu kad’ai ne zamu iya datsen Auren sabida mu keda kusanci da Ummul da kuma Mahaifyarta Suwaiba. Hajiya Asshe batada abokin tarayya domin kuwa ‘yaruwar tata da tai komai domin ita asirin Suwaiba yayi tasiri akanta tinda gashi ta makance da soyayyar Ummul ma d’anta. A halin yanzu Suwaiba ta aminta da mu Tani. Da wann aminci mu kuma zamu yi amfani mu tsinke Auren ‘yarta sann mu d’au fansar duk wasu abubuwan da tai mana.!”
Tani tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta girgiza kai kad’an “Amma idan Har Ummulkhair Auren mutuwa tayi mai zai hana mu kyaleta ta Mutu cikin wann aure kinga Babu babban fansa da zamu d’auka kan Suwaiba tamkar ta rasa ‘yarta da ta k’wallafa rai akanta tin haihuwarta. Musamman ma ke da kika rasa tilon D’anki ta dalilin bak’in k’addararta.”
Dije tai ‘yar bazawarar dariya wann karon “Idan dan wann ne da na jima dayi Tani. Idan kashe jinin Suwaiba shine fansar ran Fa’izu ai Khulsum tana nan gabana da tuni na b’atar da ita. Kar ki mance ‘ya’yan Suwaiba duk yanda naje nazo ‘ya’ya na ne.. Sann ai mutuwar Ummul bazai mata ciwo ba musamman idan a gidan Aurenta ta Mutu. Hakan na nufin burin Suwaiba na aurar da Ummul Ya cika kenan. Ai bari kiji Tani Ummul ta dawo gida sann tasan duk wani badak’ala da mahaifiyarta ta tafka da sunan Aurar da ita sai yafi komai yi ma Suwaiba ciwo. Dik randa Ummulkhairi tasan cewa Mahaifiyarta ta siyar da ita ne domin ta zamto makarin asiri da sunan Aure zata tsani Suwaiba, zatayi danasanin kasancewarta mahaifyarta sann zatayi nadaman duk wani biyayya da ta jima tana mata. Ba a nan kawai ba, Mijinki Yayana zai tsani Suwaiba zai guje ta Ya rabu da ita rabuwa ta Har abada kai kowa nata sai Ya guje ta. Dan babu Wanda zaiji abinda Suwaiba ta tapka bai kyamaceta ba. Yanzu kin fahimci manufata.?” Ta k’arashe tana tsare Tani da ido.
Makirin Murmushi Tani ta saki irin Wanda ta jima batayi ba tin kafin a gark’ame ta a gidan gyaran hali “Lallai dole na jinjina Miki Dije. Wann shiri naki Ya shiryu Ya kumayi daidai da fansar da na jima ina so na daukan kan Suwaiba amanata da taji ta aure min miji bayan na aminta da ita.! Har na hango idon Suwaiba a lokacin da Malam zaiji cewa Matar sonsa Suwaiba ta mik’a yarsa mafi soyuwa ayi tsafi da ita.!” Ta kece da wata iriyar muguwar dariya Dije na tayata.
Asshe ta dubesu tana murmushi “Toh ni babu abinda zance sai hamdala tinda dukkanmu mun samu matsaya guda shine mukai Suwaiba k’asa warwas. Abinda zamu maida hankali yanzu akai shine ku kuje kuci gaba da shashantar da Suwiaba kuna nuna mata cewa Lallai kuna tareda ita dan taji dadin sakin jiki daku ta yarda cewa tuba na gaskiya kukayi. Nima kuma zan maida hankali ga ‘Yaruwata da shirye shiryen da take na tariyar Ummul da Haidar da zaran an sallami Haidar d’in daga asibiti. Bazamu bari ayi wann bikin tariyar ba. A daidai wann lokacin zamu k’addamar da duk wani shirin mu sann mu lalata komai. Zan raba D’an ‘Yaruwata da zuri’ata da annobar da na kawo mana cikin zuri’a. Sann ku kuma zaku d’auki fansar ku akan Suwaiba. Duk kun amince da haka.?”
Gaba d’aya suka jinjina kai suna masu jaddada k’udirorinsu.
**
Abuja…
A hankali yake takowa cikin parlorn bayan kiran da Ya samu daga Hajiya Kwaise Maitama cewa tana nemansa. Koda Hisham yaji sak’on nemansa da Hajiya kwaise keyi baiji ko d’ar ba cikin zuciyarsa sann baiyi k’asa a gwiwa ba ya amsa gayyatar nata.
Cak Ya tsaya tsakiyar katafaren parlorn na alfarma bayan one of the maids ta masa iso. Wann shine ya kamata ace Ya kasance rayuwarsa amma Hajiya Kwaise ta masa denying. Ta koresa a gidan mahaifinsa tin yana ciki baizo duniya ba. Ya d’aga kai yana kallon wani hoton Haidar da ba’a jima da kafawa a parlorn ba. Shi kansa Haidar baisan da hoton ba dan yana asibiti Mommy tasa aka saka hoton. A Office aka masa hoton bayan ya gama gudanar da wani presentation. Yayi kyau sosai k’warjininsa sosai ya bayyana cikin hoton. Wani irin k’atutun bak’in ciki ya tokari Hisham. Wann duka rayuwarsa ne amma ta sace komai daga gare shi ta baiwa D’anta shi kad’ai. Ya tsane su gaba d’aya. Kuma babu Wanda zai ragar masa cikinsu.
Yana nan tsaye wata maid din ta k’araso ta k’araso ta cika centre table da kayan motsa baki. Ta kuma tanbayesa ko yana son tea ko coffe. Ya girgiza mata kai had’ida fad’in kar ta damu abinda ta kawo ya wadatar. Tai excusing kanta ta fice. Har lokacin Hisham na nan tsaye gaban hoton Haidar ya had’e hannayensa ta baya yana kallon hoton.
Sallaman Mommy yasa shi kaikaitowa yana dubanta.
Kaman ko yaushe Hajiya Kwaise Maitama ta sauk’o zuwa parlorn cikin shigarta ta alfarma. A da saidai ka hango izza da isa a tattare da ita amma a halin yanzu annuri fari’a da walwala kake hangowa a kyakkyawar fuskarta.
A sanda take takowar nan Hisham kaw cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kece sila.. Kece silar komai.. Baki cancanci yafiyana ba Kwaise Maitama.’
Ta k’araso da murmushinta tana nuna ma Hisham wajen zama “Bismillah zauna mana.”
Shid’inma murmushi ne saman fuskarsa ga kwantar da kai da yake irinta girmamawa Wanda zaka ranste Har cikin ransa ne. Saida ya duk’a Har k’asa ya gaida Mommy cikeda risinawa da girmamawa Wanda hakan sosai ya kuma birge Mommy ta kuma jin ta aminta sosai da tarayyarsa da D’anta.
Ta amsa da sakin fuska tana fad’in Ya tashi ya hau kujera ya zauna.
Hisham yai yanda Mommy tace cikeda girmamawa ba.
Mommy ta dubesa bayan ta tambayarsa mutanen gida da aiki. Hisham yace “Kowa lafiya Mommy. Aiki kuma mun gode Allah.” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa.
Mommy ta murmusa tana fad’in Masha Allah.
Dak’ik’a ya dan gifta kafin tace “Arc. Hisham ko.?”
Hisham ya murmusa “Hisham d’in dai Mommy.”
Itama murmushin tayi “A’a gwara dai na baka title dinka. I heard that you are one of our best architects a nan M&M Builders.” Cikin raha da k’ok’arin sako barkwanci take maganar wanda a baya ba d’abi’arta bace.
Hisham Ya dan murmusa “K’ok’ari kawai muke Hajiya.”
Itama ta murmusa “Toh ma sha Allah. Allah ya taimaka.”
Hisham Ya amsa da Ameen.
Mommy ta dan gyara zama kafin tace “Hisham wata ‘yar alfarma nake buk’ata daga wajenka.”
Ya d’ago Ya d’an dubeta sai Ya girgiza Kai “Alfarma kuma Mommy.. Wace iri kenan.?”
Wani folder ta dauko gefenta ta mik’a masa tana fad’in ya duba ya gani.
Hisham ya saka hannu biyu ya amsa.
Mommy taci gaba a sanda yake warware folder d’in “Plan ne na gida. Ina so ka duba kai nazari akai.”
Hisham Ya ida warware folder d’in yana dage takardun yana gani.
Mommy taci gaba “I want to surprise your friend.. My son.”
Hisham ya dago ya dubeta “You mean Haidar.?”
Mommy ta jinjina masa kai “He’s my only son.. Our only son nida mahaifinsa.” Tai maganar da murmushi saman fuskarta Wanda yake nuni da tsananin k’aunar da take ma D’an nata.
A cikin zuciyarsa Hisham yace ‘Sabida kinyi sanadin raba d’ayan d’ansa da ahalinsa.’ Amma a fili sai Ya murmusa “Okay.. And mai za’ayi da wann.?”
“Nasan kanada masaniyar cewa tsawon lokaci alak’an Haidar da halinsa akwai babban tangarda ciki since you are his best friend and possibly his only friend nasan kanada masaniya kan wann.”
Hisham ya jinjina kai a hankali “Haka ne Mommy.. And believe me burina shine Haidar ya shirya da ahalinsa.”
Mommy ta kuma jinjina kai “Hakan yasa na gayyato ka domin ka min wann aikin. After all, layinka ne.”
Hisham Ya kuma jinjina kai kafin Mommy taci gaba “Wann plan na gidan da na dank’a maka shine gidan da muka fara zama cikinsa nida Mahaifin Haidar wato Engr Aliyu Maitama a lokacin da muka dawo Abuja.. Ina so Haidar da matarsa Ummul su tare a wann gidan da zaran an sallamesa daga asibiti. Na dank’a maka ragamar komai duk wasu gyare gyare da sauye sauye Wanda yayi daidai da ra’ayin Haidar ayisu kafin bikin tariyarsu da zaran an sallamesa daga asibiti. Kai abokinsa ne nasan kasan ra’ayinsa tsare tsarensa. Inaso ayi komai to his taste ta yanda zaiji dadin bazatan. Duk wani abinda ake buk’ata don’t hesitate to let me know. Kar ka mance na sanar da kai wann din Bazata ne. So ko Boss dinka a Office ina nufin Mahaifin Haidar banso ya sani.. Is our little secret for your dearest friend.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
K’ak’aro murmushi Hisham yai dukda mutuwar zaune da yai yana sauraron Hajiya Kwaise kafin ya shiga jinjina kai “Bakida matsala Mommy. Haidar tamkar D’anuwa na d’aukesa ba aboki kawai ba. Zanyi komai to the best of my ability in sha Allah.”
Mommy ta murmusa tana dubansa. Yanda yace D’anuwa Ya d’auki Haidar ba aboki kawai ba sosai Ya hakan Ya haifar mata da sanyin jiki. Bata san dalili ba amma sai taji tunanin Fannah da abinda ke cikinta yazo mata. Watak’ila da ace Fannah ta haife abinda ke cikinta idan Ya fito namiji da yanzu Sun taso tare haka da D’anuwansa Haidar tamkar dai abokan. Sai ta tsinci kanta da addu’an Allah Ya bayyana mata Fannah Ya kuma sa ta haifi abinda ke cikinta ko Haidar d’inta zai samu D’anuwa ko ‘yar uwa. Daga bisani mik’ewa tai tana ce ma Hisham Ya saki jikinsa kaman a gida yake Yaci abubuwan da aka kawo masa. A haka Mommy ta bar parlorn duk jikinta a mace sakamakon tuno Fannah da abindake cikinta da tayi.
Yayinda Hisham yai mutuwar zaune yana jin shirin Kwaise Maitama. Wai shi Hisham shine zai gyara ma Haidar gidan da zai zaman aure da Ummul d’insa sann gidan ma ba ko wane gida ba. Gidan Mahaifinsa da ya fara zama ciki lokacin da yazo garin. Idan akwai Wanda yafi kowa cancanta da zaman aure tareda Ummul a wann gidan ba kowa bane face shi. Shine babban d’an mahaifinsa sann shine ya fara son Ummulkhair tun kafin Kwaise tai mata k’adararren auren nan da D’anta. She’s so selfish. Ta ya zai fara wann aikin ma.. Just how.?
Muryar Anisa yaji a kansa wacce mamaki ya cika sai waige waige take “What are you doing here.? Who invited you.?”
Duban Anisa yai sai Ya murmusa “Mu gaisa mana kafin duka wad’ann..”
Anisa taci gaba da ‘yan waige waige kafin tai k’asa da murya tace “Is this also part of your games.?”
CCTV camera dake mak’ale a parlorn Ya kalla sai Ya murmusa Yace “Neesa long time no see. Ko dan dik rashin lafiyar abokina ne ya b’oyeki kema..?”
Mamaki Ya cika Anisa tana duban Hisham dake kurb’an drink din dake hannunsa. Lokaci guda Ya mik’e yai k’asa da murya “Zan iya samun rakiyarki..? To my ride.?”
Anisa ta murmusa ta biye wasan Hisham “Sure.. Of course.”
Hisham ya nuna mata hanya “After you.”
Sa kai sukai suka fice a tare. Suna isa jikin motar Hisham yace “Get in.”
Ta dubesa da mamaki “Ban gane ba.. Are you a kidnapper now.?”
“Just get in Neesa.. We need to talk.. Somewhere else.”
Ba musu ta bud’e motar ta shige kafin Hisham ya shige mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan.
Tinda suka fice daga Hisham ke zabga gudu saman kwalta zuciyarsa na tafarfasa musamman idan Ya tuna aikin da Kwaise Maitama ta basa wai shi Hisham sai zai renovating gidan da Haidar da Ummul d’insa wai zasu zauna.
Anisa ganin gudu ba na k’arau ba Hisham na yunk’urin hallak’asu cikin motar ta soma k’ok’arin dakatar dashi “Ka dakata Hisham.! Wai meke faruwa ne.? Why are you so furious.? Where are you taking me to.?!”
A harzuk’e ya buga kan steering wheel ya dubeta yace “I don’t know Neesa.! I just don’t know maybe to hell.!”
Yanda Yai maganar yana huci gashi bai daina gudu ba yasa Anisa kuma razana ga wata mota gaba garesu Wanda k’iris Ya rage Hisham bai daki bayan motar ba “Hishaamm.!” Ta k’arashe tana daka masa tsawa daidai sanda Hisham ke taka birki a tsakiyar titi. Rufin asirin Allah Babu wata mota bayansu.
Ya d’ago yana dubanta cikin huci. Itama d’in hucin take tana dubansa “Just what do you think you are doing.? What’s gotten into you.? Are you trying to kill us or something.?! Meye haka.? Kaga saidai tafi hell d’inka kai kad’ai but I won’t allow you to take me with you..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin fincikar marfin motar.
Hisham Ya furzar da huci kad’an yace “All right.. I’m sorry..”
Ta juyo tana dubansa fuska a tamke.
Parking yai gefen hanya kafin ya shafi fuskarsa yace “I can’t stand your Aunt Neesa. I just can’t.!”
“Mai tai..? Mai ma ya kaika gidan in the first place. I thought your friend is still in the hospital. So why were you there anyway.?”
Ya dubeta sosai “Kirana tayi ta bani wani aiki.. Aikin da zaifi mun ciwo sama da ko wani aiki a rayuwata.!”
Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Aiki.? Wane irin aiki kuma..? For all I know my Aunt doesn’t take part a ayyukan company.”
Folder din dake hannunsa ya mik’a mata.
Anisa ta girgiza kai “Meye wann.?”
“Karba ki gani.”
Ta karba ta shiga bud’ewa “Dukda ba Layina bane amma Wann ai kaman plan ne na gida.? Mai hakan yake nufi.?”
“Hakan yana nufin ni ne mutumin da Kwaise Maitama ta d’aura ma alhakin gyaran gidan da Haidar zai angwance da Ummul d’ita ciki.!”
Anisa ta zaro ido tana dubansa “No you can’t be serious.? You know you are such a joker.”
Hisham ya dubeta sosai “I’m being serious here Neesa. Hajiya Kwaise Maitama ta d’aura alhakin gyaran gidan hannun aminin D’anta.! Ya gyara zamansa kadan yana jinjina kai “Hakan na nufin zanyi mastering ko wani lungu da sak’o na cikin gidan a saukake. Idan naso na d’auke Ummul d’ita na gudu da ita a randa aka kai masa ita wann gidan.. Sann kuma na cinna ma gidan wuta your beloved Haidar na ciki bayan na gudu da abar k’aunata. Kwaise Maitama zata hadiye ranta da zaran ta rasa tilon D’anta. Haka ne.?!” Ya k’arashe yana fashewa da dariya.
Anisa ta girgiza kai “You are insane Hisham. Kar ka mance a Yarjejeniyarmu Babu cutar da both parties ina nufin Haidar da Ummul. Rabasu shine agenda d’in haka ne.?”
Ya murmusa kad’an “Just kidding sweetheart. Ki kwantar da hankalinki Haidar dinki is safe matuk’ar Ummul dita tana lafiya. Abun shine Hajiya Kwaise ta kawo mun hanya mafi sauki ne da zan d’auke kayata na gudu. Idan Har na kasance Wanda zai renovating wann gidan ke kuma ya kamata ki zamto event planner. Baki tunanin abin zai k’ayatar.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda.
Shiru tai kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai “Yes. K’warai ka kawo shawari. Idan Har zaka kasance mai gyara gidan da zasu zauna ni yafi cancanta na zamto wacce zata shirya shagulgulan bikin tariyar. Kaga a sauk’ak’e zamu rufta komai mu lalata komai.. Duk shirin Mommy na ganin Ummul da Haidar sun tabbata ma’aurata zamu lalata shi. Ko wannenmu ya kasance da abun k’aunarsa haka ne.?”
Hisham Ya kuma murmusawa “Perfect.! Ni yanzu aiki na ya shigo hannu saura kiyi naki k’ok’arin ta dank’a Miki ragamar jagorancin shagalin bikin tariyar.”
Anisa ta murmusa kafin tace “Bikin da Aunty Kwaise Maitama bazata tab’a mancewa dashi ba. Bukin da zamu gayyat manyan bak’i ciki harda Dareen.. Tsohuwar sirkar ta da basu tab’a had’uwa ba.!”
Suka kece da dariya suna ci gaba da ayanna manufofinsu.
**
Hospital..
Haidar ya dubeta dan ya kula yanayinta a kwanakin ya d’an sauya gashi in less than 2weeks za’a musu sallama.
Ta k’araso ta bashi magungunansa fuskarta Babu wani walwala. Zata mik’e Ya kamo hannunta.
Ta juyo ta dubesa still babu wani walwala tattareda ita.
Ganin Ya tsareta da ido ya sata sauk’ar da idonta kad’an.
“Khairy…!” Ya ambato sunanta a hankali.
Still bata d’ago ta kallesa ba saima hawaye da taji na yunk’urin zuwa mata. Zuciyarta cike yake da tarin abubuwa. Ga maganganun Anisa Wanda ta sanar da ita kwanakin can ga kewar ahalinta da ta baro gida da ya addabeta. Tana nan tana lissafin watannin da Umma ta d’ibar mata ta waiwayi gida wato watanni uku bayan aurenta. Dukda cewa bai shige sauran sati biyu watannin su cika ba ji take kaman bazasu cika ba. Majinyacin Mahaifinta da bata san wani hali yake ciki ba. ‘Yanuwanta musamman ‘yaruwarta Ummukhulsum da ko bacci bai rabasu a baya sann da ita kanta Umman koda itace ta bata wann sharad’in. Tayi kewarsu gaba d’aya sann ta k’agu ta gansu taji daga garesu.
“Look up Khairy.. Kalleni..” Yai maganar softly.
Sai ta d’ago ta dubeshi.
Hawaye Ya hango kwance cikin idonta.
“Are you crying.?” Ya tambaya yana k’ok’arin kai hannunsa had’ida d’ago hab’arta kad’an.
Baisan Ya akai ba saiji yai hannun nasa a kasan idonta . Gently ya shiga share mata hawayen dake mak’ale cikin idonta Wanda tuni sun ziraro k’asa. Ai kaw kaman wacce ke jiran dalili sai ta soma kuka maras sauti.
Haidar yai mata k’uri yana kallonta.
A hankali Ya furta “Come here.” Ya janyota zuwa b’angaren jikinsa. Kaman wacce ke jira nan ta soma kuka sosai kanta cikin k’irjinsa.
SameenaAleeyou📚
