Auren Wata Uku Page 44 Complete by Sameena Aleeyou -Abokiyar Hira Novels

*AUREN WATA UKU..!*

*44*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Sun d’auki lokaci sosai  a haka Har saida kukan nata Ya tsagaita yayinda Haidar yaci gaba da Shafa kanta zuwa bayanta a hankali cikin k’ok’arinsa na calming dinta. 

D’akin yai shiru tana nan kamo cikin k’irjinsa sai zukatansu dake bugawa kusan a tare.

Bata San dalili amma sosai ta samu natsuwa da kwanciyar hankali tattareda shi. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Nayi kewarsu..! Nayi kewarsu sosai..?”

Ya kuma shigar da ita k’irjinsa. Ba ra’ayinsa bane bin diddigin matsalolin mutane. Baisan dalili ba amma sai yaji yana son jin nata matsalan “Su waye kikayi kewarsu.?”

A hankali take furta “Abba.. Umma.. Khulsum.. Da sauran ‘yanuwana..!” Ta k’arashe wani kukan na zuwa mata. 

Haidar yaci gaba da Shafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali. D’akin yai shiru har kaman bazai ce komai ba sai kuma yace “Then… give them a call..”

Shiru bata ce komai ba.. Shima saida yai maganar ya tuna duk zamansu shidai bai tab’a ganinta da waya ba sann bai tab’a ganin ta kira kowa ba. Ya d’an kamo arms dinta Ya d’ago ta  kad’an “Where is your cell phone… Do you have one..?” 

Shiru kaman bazata ce komai ba sai kuma ta girgiza kai a hankali.

Mamaki Ya cika Haidar. ‘Ta Ya za’a ce mutum baida wayar salula. Is this even possible.?’ Ya dan girgiza kai kad’an, Kasancewar shi kansa mutum ne da bai cika son magana da bin diddigin al’amari ba yasa shi jinjina Kai a hankali. Sai Ya mik’a hannun Ya d’auki nasa wayar. Sai gani Ummul tai yana mik’a mata nasa wayar.

“Here..! You…. can use mine.. If that’s.. ok with you..” Ya k’arashe yana dubanta sosai.


Ta dubesa sai ta dubi wayar. Jikinta ya kuma yin sanyi sakamakon tunowa da kalaman Umma ‘Kar ki neme mu koda a waya ne har sai kin cika watanni uku a gidan aurenki . Sai ta girgiza kai a hankali. Cikin rawar murya tace “Ban rik’e lambobinsu akai na ba..”


Wann karon ma da mamaki yake dubanta sosai. Dukda shima bai tab’a damuwa ya kiyaye lambobin ahalinsa ba tin yaranta yasan hakan nada alak’a da rashin jituwa da k’alubale da ya fuskanta da iyayensa tin yarinta. Amma ita tanada alak’a mai kyau da iyayenta ga dukkan alamu, musamman mahaifinta dan bai mance ta sanar dashi sabida shi ta amince da aurensa. Amma sai bai ce komai ba ya jinjina Kai a hankali. 


Kallonta ya kuma yi dan shidai baisan wani aba lallashi ba a rayuwarsa sann bai iya ta ba. Sai ya

kamo hannunta cikin nasa ya kuma kwantar da ita gefen kafad’arsa, yatsun hannunta cikin nasa. Calmly yake fad’in “You know, I’m not used to seeing you like this.. Murmushi yafi Miki kyau.” Ya k’arashe kaman ba daga bakinsa maganar ya fito ba. 


Sai taji Murmushin ya kufce mata out of nowhere. tai saurin kare fuskarta da tafukan hannayenta. 


Hannu yasa ya d’ago fuskanta kad’an suna duban juna. Ya tsareta sosai da ido kafin yace “Do you feel better now..?” Ya tambaya fuskarta tallafe cikin tafukan hannayensa.


D’an lumshe idanunta tai kafin ta jinjina masa kai a hankali.


Shima ya jinjina nasa kan. Su duka biyun murmushi ne saman fuskokinsu.


**

Anisa ta shigo a guje tana nuna ma  Mommy Pages na different professional event planners. Ta murmusa tace “Yauwa Mommy ya kikaga wann. The event should be grand and super elegant. Ya kamata ayi komai to perfection. I’ll be the coordinator.. And trust me, it will definitely be a sight to behold.!” Ta k’arashe tana juyi gaban Mommy had’ida juya ido. Cikin zuciyarta kuwa cewa take ‘Dan na miki alkawari Mommy, akwai abubuwa da dama da zasu faru a wann rana Wanda idaniya bazasu tab’a mancewa ba.’ 


Mommy ta tab’e baki tana dubanta sama da k’asa “Toh ce Miki akayi shiririta zaayi wajen ne.? Bani son shashashan cin nan naki.”


Anisa ta turo baki kad’an “Haba Mommy.. I’m just being concerned here… Kuma kinsan abu idan aka ce biki toh a nan wayota da basirata Ya k’are.. Mommy kinsan bazaki iya dealing da wani headache na event a yanzu ba. Kuma Haidar cousin dina ne Ummul kuma I consider her friend. Ni ce yafi cancanta na shirya shagalinsu Mommy. Just assign me to do the work please.. Please Mommy. And kuma kinsan abu na zamani sai d’an zamani.. Gwara a shirya komai daidai da zamani da yayi.” Ta k’arashe tana juya ido da rangwad’a Wanda d’abi’ar ta ce. 


Mommy ta kuma girgiza kai yayinda Anisa taci gaba da mata magiya tana fad’in ta dank’a mata ragamar shirya shagalin. 


Murmushi Mommy tayi had’ida girgiza kai kad’an “Fine, naji Anisa.. Amma kinsan bani so a samu wani mishkila.”


Anisa harda ‘yar tsallenta tana fad’in baza’a samu mishkila ba, kama daga shirya wajen taro, live entertainments har zuwa guests list. 


Mommy ta murmusa tana duban Anisa tana jin dadin yanda kowa ke marmarin biki. Batai k’asa a gwiwa ba taci gaba da kiran k’awayenta da matan abokan kasuwancin Daddy tana sanar dasu. Sann hakan wani dama ne da zai goge scandal din da yai erupting kwanakin baya. Labarin da wani gidan jarida ya wallafa cewa Engr Aliyu Maitama yayi ma d’ansa auren sirri da ba’asan ko wacece Amaryar ba. A wann rana zata gabatar da Ummulkhair matsayin matar D’ansu Haidar ga duk abokan alk’allarsu dama sauran jama’a gaba d’aya. 


Anisa kaman ta zuba ruwa a k’asa ta sha dan murna. Haka ta kirawo Hisham tana sanar dashi plan dinsu Ya tafi yanda suka tsara. Mommy dai ta dank’a mata ragamar jagorancin shagalin bikin. Sann Gidan Haidar da Hisham ke renovating nan ne venue kaman yanda Mommy ta buk’ata . Hisham yai muguwar murmushi yace komai Ya tafi daidai.. A ranar wann shagalin zasu striking plan d’in su. Ranan da Kwaise Maitama take tunanin farin cikin ahalinsu zai soma wann ranar komai zai wargaje. 


A haka ko wani b’angare suka ci gaba da gudanar da shirye shirye yahinda b’angaren Haidar da Ummul sabo da shak’uwa ke dad’a shiga tsakaninsu. 


A b’angaren su Tani ma suna nan suna nasu tanadin dan Hajiya Asshe ta sanar dasu ‘yaruwarta Hajiya Kwaise na shirya gagarumin bikin tariyar Ummul da Haidar Wanda suma a nasu shirin wann ranar zasu k’addamar da shirinsu. Zasu fayyace ma Ummul komai gameda mahaifiyarta da wulak’antaccen auren da tai mata. Zasu jefa rayuwar Suwaiba cikin garari a wann ranar. Zasu d’auki duk wani fansarsu dake kan Suwaiba. 


A b’angaren Ummul dad’i da k’arin sakin jikinta da Haidar yanada alak’a da tsananin farin ciki da take ciki. Watanni uku Sun kusa cika zataga ahalin ta kaman yanda ta d’aukar ma mahaifiyarta alk’awari cewa bazata waiwayesu ba har sai ta cika watanni uku da aure kaman yanda mahaifiyar tata ta buk’ata daga gareta. 


 Shi kuwa Haidar dukda shiryawa da yai da mahaifiyarsa saidai har kawo wann lokacin bai saka mahaifinsa a idonsa ba. Daddy bai kuma dawowa asibiti ya dubasa ba. Abun bai basa mamaki ba tinda yasan shidai tsakaninsa da mahaifinsa Babu komai face tsangwama tsana da kuma kyara. Amma saidai a wann lokacin abun bai masa ciwo sosai kaman a lokutan baya sanin cewa da yai ko Babu komai a halin yanzu yana tareda soyayyar mahaifiyarsa da k’aunarta. Uwa uba idan Ya kalli Ummul sai yaji duk wani k’unci dake zuciyarsa ke ciki ya yaye.. Bai sani ba ko tsananin sabon da sukayi a yanzu ne ke haifar masa da hakan Wanda a baya idan aka ce zai zauna da ita under same roof zai musa. Sai gashi a halin yanzu Har bacci suke cikin mayafi guda. Ya lumshe idanunsa a hankali murmushi na kufce masa.


A reception wani staff na asibitin Ya bata wani shud’in folder mai d’aukeda logo na Maitama Builders daga fuskarsa.  cewa wani abokin aikin Haidar d’in ne ya bari a bashi. Ita dai ta amsa folder d’in ta nufi d’aki dashi. Hisham Wanda shine ya kawo folder d’in yana lab’e yana kallon Ummul Har ta shige da folder d’in. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Saura kad’an.. Saura kad’an na d’aukeki Ummul.. Saura kad’an mu kasance tare.. Saura kad’an ki kasance da masoyinki na gaskiya.’ Yana ida fad’in haka yaja Pcap d’in dake kansa ya kuma rufe face dinsa dashi kafin ya fice daga asibitin. 



Haidar yai zaune yana duban folder d’in Wanda ke k’unshe da wasu bayanai da wani waje na rattaba hannu gameda babban aikin da suke gab da farawa da zaran ya fito daga asibiti. Long awaited project dinsu. Project d’in da yai alwashin kai mahaifinsa k’asa warwas dashi. Project d’in da yai niyyan ruguza Maitama Builders dashi. Project d’in da Ya jima yana tanadin duk wani fansa nasa kan iyayensa musamman mahaifinsa Wanda Har kawo wann lokacin basu fuskanci juna ba. 


Shiru yai yana juya folder d’in cikin hannunsa a hankali yake furta “You deserve this Daddy.. You deserve this.. I can’t backdown now.. Ka cancanci haka Daddy.!”


Ummul ta dubesa da d’an mamaki ganin irin hucin da yake. Ga wani yanayi da Ya shiga tinda ta kawo masa wann folder d’in Wanda ta jima bata gansa cikin irin yanayin ba. Tai k’ok’arin zama gefensa a d’arare. Ta dubesa kaman mai tsoron magana “Lafiya kake..? Kaman naji magana kake.? Ko.. Akwai abinda zan iya taimakawa  dashi.?” Tai maganar a sanyaye. 


Kallonta yayi, wann karon irin kallon da yake mata a baya kafin su saba da juna . Ya kafeta sosai da ido sosai Wanda Ya soma bama Ummul tsoro Har saida taji dama bata tambayesa ba. 


Jiki a sanyaye tace “Kai.. Hak’uri.. Ba nufi bane nai maka shishigi a almarinka..” 


Tana k’ok’arin mik’ewa taji ya kamo hannunta. Ta lumshe idanunta cikin k’ok’arin saita kanta. Bugun zuciyarta na sassauta a hankali.


Ya dawo da ita Ya zaunar kafin ya kuma d’ago folder d’in yana gani. Idonsa na kan folder d’in yake furta “He sees me as a failure.” Yai murmushi da za’a iya kira da murmushin takaici “That I create a circus out of his business life.” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “I’ve been planning.. To take him down.. To take Aliyu Maitama down.. To ruin him.. To bankrupt his business.. The business he valued all his life more than his own son..” Fuskarsa tai jazir haka idanuwansa sanda yake maganar.


Ya d’ago yana duban Ummul dake dubansa cikin wane irin yanayi mai kama da tausayi. 


Haidar yai murmushi yana juya folder d’in, irin murmushin nan da ake kira da murmushin takaici “He values this more  than everyone around him. Tell me, shin nayi laifi idan nace zan kaishi k’asa.?”


Sai Ummul ta shiga jinjina kai tana dubansa “K’warai kuwa.. Ka tapka kuskure. Kuskure mai muni. Dik yanda kaje kazo shine mahaifinka… Wanda kasancewarsa hakan Ya haramta maka fad’a dashi..”


Katseta yai da fad’in “You don’t know anything.!” Ya sassauta murya  “If only you knew the kind of hell he made me went through tin daga yarinta na, har kawo girma na.. Har zuwa aiki da nayi a k’ark’ashin kampaninsa. Ki yarda dani wann aikin da zanyi shine zai zamo aikina na k’arshe k’ark’ashin kampanin sa. Sann shine fansar duk wani wulak’anci da cin zarafi da na fuskanta a wann kampanin.!” Ya k’arashe yana kuma tamke folder d’in cikin hannunsa. 


“Kar ka bari fushi yai maka jagora..” Bata Kai aya ba ya dakatar da ita. 


“O c’mon Khairy.!Stop minimising the issue here. Don’t act like I’m making a big deal out of it.!” Yaci Ya k’arashe maganar a zafafe. 


Dukda zuciyarta dake bugu hakan bai hanata k’ok’arin tattaro courage dinta ba, ta d’aura hannunta saman nasa, tana dubansa da fuskarta mai cikeda rauni “Duk abinda Ya faru dakai a baya. Na d’auka mun riga mun wuce wann. Na d’auka ka goge duk wani k’unci na rayuwar da ka fuskanta a baya da yafiya.. Su d’in iyayenka ne ba ma’asumai ba. Girman hakkinsu akanka Ya shige ka nemi fansa akansu..”


Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa “You always talk about hakkinsu.. Have you ever bothered talking about hakkin ‘ya’ya. Shin su basuda hakki ne kan mutanen da suka zamto sanadin tsintar kansu a wann duniyar..?”


Shiru tai tana dubansa. 


“Answer me. Basuda hakki.?”


“Eh.. Su.. su..”


Katseta yai “Why are you stuttering now..? Kin kasa furta kalma d’aya sabida kinsan gaskiya nake fad’a. Sunada hakki and they will be questioned kan wann hakki na yaransu.” Yaci gaba da jinjina kai “Shin kinsan most of children da suka tsinci kansu a yanayi na Allah wadai are victims of circumstance. Wasu sun fuskanci abuse and  negligence from their own parents. And don’t you think this can cause behavioural issue in the children later in life.?” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Idan kayi shuka zaka bashi ruwa zaka kula dashi Har wann shukan ya girma ka girbi amfaninsa. Kaman haka idan kayi shuka baka kula dashi ba zaka samu akasin amfani mai kyau. Kaman misalin haka ne tsakanin ‘ya’ya da iyayensu.” Ya dan rage girman idanunsa yana dubanta “Wait a minute, do you really think you can change the dynamic of this family.?”


Ummul ta jinjina kai a hankali “Bank’i maka duk abinda kace ba. Shiyasa na sanar dakai tin daga farko. Iyayenmu ma suna kuskure. Sann kuma idan akwai wad’anda zamu fi ma uzuri sune Iyaye.” Ta d’an gyara zamanta “Jinin Daddy shike yawo through your veins tun a fari.. Sann daga baya da ka samu had’ari ka rasa jininka jininsa ke yawo cikin jikinka a karo na biyu..!” Ya kaikaito yana dubanta da mamaki. Ummul taci gaba da jinjina Kai tana sakin murmushi. Lokaci guda taci gaba “Zan sanar dakai wani sirri da baka sani ba. Sabida tsananin k’aunarka da yake Ya zab’i a ajiye hakan matsayin sirri a wajenka harma da Mommy. Bai zab’i ka sani ba, sabida yayi ne don soyayyar da yake maka.”


“What do you mean.? What secret are you talking about.?” Ya tambaya cikin rashin fahimta.


Ummul taci gaba “A lokacin da mukayi accident Daddy ne ya bada jininsa aka k’ara maka. Cikin yardar Ubangiji, You are alive today sabida jinin Daddy na yawo through your veins.” Ta k’arashe murmushi had’eda k’walla tab idanunta. 


Haidar ya shiga girgiza kai “No. no, no way… No, this can’t be… You must have got this wrong.. Tsakanina da mahaifina babu komai face k’iyayya, kyara da hantara.. I’m the last person da Daddy zai baima jininsa. Na sani bazai tab’a ba koda mutuwa zanyi.. Ta Ya mutumin da ko zuwa Ya dubani baiba zai bani jini. I almost lost my life amma.. Bai damu yazo Ya dubani ba. Ta Ya zai bani jininsa.?” 


“Amma yayi hakan. Idan Har hakan na cikin wani hakkoki naka akansa toh ka tabbata Ya cika wann hakkin. Kana iya karb’an hospital report d’in and see for yourself.” Cewar Ummul.


Haidar ya girgiza Kai “Well I don’t need his blood.! Knowing my Dad.. Akwai manufar da yasa yai hakan.! Watak’ila to throw it own my face cewa ya bani jini.. I’m alive sabida jininsa dake yawo through my veins.!” Ya k’arashe yana huci. 


Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali “Bazai tab’a zama haka ba sabida Daddy bai zab’i wani daga cikin ahalinsa yasan hakan ba. Musamman ma kai.” Batai k’asa a gwiwa ba ta kuma daidaita zamanta “Dalili shine Ina zaune lambun can na shak’atawa dake bayan offices din likitocin kwanakin baya. Nan na tsinci zancen likitan da abokin aikinsa yana sanar dashi kwanaki da suka rasa jini kala kaza a asibitin mahaifin patient d’in shi  Ya bada jininsa kuma ya zab’i hakan Ya zama sirri tsakanin ahalinsa. Sunan hamshak’in D’an Kasuwa Engr Aliyu Maitama da suka ambata yasa na fahimci kai suke nufi.” Ta d’an numfasa “Ba nufi bane naji zancensu. Sann banso ka sani ba tinda Daddy ya zab’i ya zama sirri. Amma idan hakan zai kawo maslaha cikin ahalin banida zab’i da Ya shige na sanar dakai.!”


Jikin Haidar Ya d’anyi  sanyi Dikda k’ok’arin b’oye hakan da yaketayi, yayinda Ummul ta kuma daura tafukan hannunta bisa nasa “Daddy yana sonka.. Yana matuk’ar k’aunarka.. Dan Allah ka janye duk wata maganar fad’a da d’aukan fansa akansa.. Shid’in mahaifinka ne… Idan baka zamto jigo na hab’aka masa kasuwancinsa ba bazaka tarwatsa ba. Kar ka mance mutane da yawa Sun dogara da aikin da suke a wann Kampanin dasu da iyalansu. Kai tunani idan ka tarwatsa Kampanin mutane nawa zai affecting.? Mutane nawa zasu rasa ayyukansu sakamakon durk’usar da Kampanin da kayi. Mutane nawa zasu koma basuda aiki basuda abinda zasu rufa asirin kansu da iyalansu dashi. Tin daga shugaban Kampanin Wanda Ya kasance mahaifinka Wanda yake da girman hakki akanka matsayinsa na mahaifinka koda bai kasance ahugabanka wajen aiki ba. Sauran manyan ma’aikata masu hannun jari Har zuwa kan k’anan ma’aikata… Ina zaka kai girman hakkokinsu.?”


Ya d’ago Ya dubeta cikin yanayin da zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba. 


A hankali taci gaba “Nasan kai mutum ne  mai saka sharri da alkhairi. Wanda duk yanda Ya zauna Ya tashi alkhairansa bazasu gushe ba. Jajirtacce Wanda jajircewarsa takanyi  tasiri cikin duk abinda yasa gabansa. Mai taimakon Al’umma ba mai durk’usar da ita ba.”


“What if duk abinda kika fad’a akaina ba haka bane.! What if na aikata kudirina da abinda na jima ina shiryawa.?! Kina tunanin zaki iya dakatar dani.! Just Who do you think you are.?!” Ya k’arashe yana mai tsareta da ido.


Cikin zuciyarta tace ‘I call you sweet monster for a reason. You are not like other monsters out there.’ A fili kuwa cewa tayi “Kanada zuciya mai kyau. Inada yak’inin kyakkyawar zuciyarka bazata bari ka aikata akasin abinda na fad’a ba.”


Haidar Ya kuma d’agowa ya dubeta. Sai Ya dan lumshe idonsa kadan “Khairy please get out now. I need to be alone.!” 


“Amma…”


“I said leave.!” Ya katseta a zafafe


A hankali ta mik’e, ta d’an dubesa kafin ta soma tafiya cikin sanyin jiki.


Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Just.. go home. I don’t need you here.!” Ya k’arashe ba tareda ya dubeta ba.


Ta juyo ta dubesa a sanyaye sai ta jinjina kai a hankali. Lokaci guda tasa kai ta fice cikin sanyin jiki. 


Bayanta yabi da kallo Har ta fice kafin ya maida dubansa ga folder d’in kalamanta yaketa k’ok’arin yakishewa ganin basuyi tasiri cikin zuciyarsa ba. Ya d’ago hannunsa yana juywa yana bin veins d’insa da sukai rud’u rud’u sukai kore shar yana tuna kalamanta sanda take sanar dashi Daddy ya basa jini. Jinin Daddy ke yawo through his veins. A hankali Ya lumshe idanunsa hoton abubuwan da mahaifinsa Ya jima yana masa na yawo a kwanyarsa, zuciyarsa da kuma lumsassun idanunsa. 


Koda dare yai Haidar kasa bacci yai sabida rashin Ummul. Baisan yayi sabo da ita Har haka ba. Room nurse din dake kula dashi kuwa cewa yai ya fice ya bar masa d’aki he can take care of himself. Gaba d’aya gani yake room nurse baisan komai ba bai iya komai kaman ita ba. Abubuwa ne da dama fal zuciyarsa. Koda yazo bacci haka yaita juyi yana tunaninta. Yakai dubansa ga kujerar da suka kwana tare ranar farko da ya farka. Ya lumshe idanunsa. A fili yake furta “I’m not the type that share his problems with others.. I don’t know how I do it with you.” Ya d’anyi shiru still yana duban wajen. A hankali ya furta “It feels so empty to go to bed without you.!” Ya rasa haushinta ne ko haushin kansa ko kewarta yake.


**


A b’angaren Ummul kuwa Mommy taso ta fahimci wani abu musamman da taga Ummul d’in bata koma asibiti wajen Haidar ba . 


Washe gari da safe koda Ummul ta shigo gaida Mommy sai Mommy ta dakatar da ita bayan Sun gaisa. Ta nuna ma Ummul d’in gefenta saman kujera “K’araso nan ki zauna daughter, magana nake so muyi.”


Ummul ta jinjina Kai had’ida amsawa kana tai yanda Mommy tace.


Anisa dake k’ok’arin saukowa downstairs nan ta sinkayo zancensu. Ba shiri ta lab’e jikin staircase tana sauraronsu. 


Mommy taci gaba yayinda kan Ummul ke kife k’asa “Bana so na zamto irin iyayen nan masu kutsa Kai a al’amari gidan ‘ya’yansu. But when it comes to Haidar you and I are team. Haka ne.?”


Ummul ta jinjina Kai a hankali.


Mommy taci gaba “Kuma zamuci gaba da zama team wajen ceto rayuwarsa daga halak’a. Tinda ni mahaifiyarsa ce ke kuma matarsa. Mu duka d’in yanada matuk’ar mahimmanci a wajenmu. Haka ne.?”


Nan ma jinjina Kai ta kumayi a hankali.


Wann karon sai Mommy ta d’aura hannu saman nata “Ummulkhair.!”


Ummul ta d’ago a raunane tana duban Mommy.


Mommy taci gaba “Nasan kina hak’uri da Haidar. Amma dan Allah ki k’ara. I have this strong feeling, with you by his side, Haidar zai mending ways d’insa. Kuma mun fara ganin hakan cikin ikon Allah..” Ta dan numfasa “Bazan tambayeki mai ya hadaku ba dan wann ba hurumi na bane. Sann dik hukuncin da kika zartar har kawo zuwa lokacin da zaki sauk’o bazan tak’ura miki ba. And always remember kina tareda yarda da kuma k’aunata a gidan nan. Tashi kije, Allah shi muku albarka gaba d’aya.”


Ummul ta jinjina kai a sanyaye kafin ta mik’e ta fice jiki ba laka. 


Anisa da ta gama nad’e komai murmusawa tai. Cikin zuciyarta take furta ‘You are so selfish Mommy. Kedai kawai d’anki. Toh bari dai mu gani idan hak’arki zai cimma ruwa.’


Da dare ta iske Ummul a sashenta. Anisa ta saki murmushi tana duban Ummul “Da alama jikin D’anuwana kuma mijinki da sauk’i sosai tinda gashi har kin rigashi dawowa.” Tai maganar tana murmushi sai kuma ta k’arada “Kodai kema koroki yai kamar dai yanda ya koroni.?” Ta k’arashe tana d’aga gira d’aya.


Tinda Anisa ta soma magana k’irjin Ummul ke bugu. 


Anisa ta kuma murmusawa “Saidai kuma nasan mahaifiyarsa zatai iya k’ok’arinta ta kuma maida masa ke koda kuwa korarki yayi. Sabida ita d’in kanta kawai ta sani. She’s so selfish.”


Ummul ta dubi Anisa da idonta da tuni sun kad’a. Murmushin ne dai saman fuskar Anisa. Ta matso dab kusan Ummul ta dafa kafad’arta “Hajiya Kwaise Maitama bata tab’a son talaka ba sann bazata tab’a so ba, ita d’in mace ce da bata so wani talaka ya rabeta balle har ta aura ma D’anta. Ki yarda dani, she’s just toying with you Ummul. She’s using you. Ki yarda dani amfani dake kawai take dan ki toshe gibin da ta jima da bud’ewa cikin ahalinta da kanta.” Anisa tai maganar babu ko alamun d’ar tattareda ita. 


Ta d’ago idanunta masu cikeda k’walla tana duban Anisa. Sai Anisa ta karkad’a yatsa a saman fuskar Ummul d’in “No, I’ll do the talk today because, ni keda abin cewa.” Taci gaba da murmushi tana duban Ummul “Mommy is a very dangerous woman who’s capable of doing anything to protect her interest. She brought you into her son’s life not because she loves you for him. But because, she wants you to do what she couldn’t do.” Taci gaba da jinjina kai alamun tabbatar da kalamanta “She wants you to do the job for her. To knock some sense into her son. She brought you into his life to cleanup her mess. Ki nutsu kiyi tunani Ummul a koda yaushe Mommy zancen Haidar take miki. Ya za’ai ki shawo mata kan Haidar. Shin ta tab’a tambayarki idan kina cutuwa a zaman da kike da D’anta.? Ko ta tab’a tambayarki menene naki damuwar.? Shin ta tab’a tambayarki ko kinada wata damuwa da ya danganci ahalinki.? Bata tab’a ba. Koda yaushe maganar d’aya ce ‘Haidar.’ Haka ne.?”


Izuwa lokacin idanun Ummul sun soma zubda ruwa.


Anisa ta dafata kad’an “Kar ki bari Mommy tayi amfani dake dan cimma wata manufa nata. Ke macece mai k’ima. Kar ki bari wann matar ta watsar dake gaban D’anta.” Ta kuma dafa Ummul “Kiyi weighing maganganun da na fad’a miki sai ki tantance. Abu guda nakeda tabbaci akai shine ban tab’a miki k’arya ba.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai zata fice. Har ta Kai k’ofa ta kuma juyowa “Save yourself while you still can. Run as fast as you can.. Ki ceci kanki daga wann auren da da baida tabbatacciyar makoma.” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice tana sakin murmushi.


A hankali Ummul ta silale k’asa kukan da taketa k’ok’arin dannewa na zuwa mata gadan gadan. Meyasa takejin zuciyarta ta gamsu da duk abubuwan da Anisa ta fad’a. Meyasa takeji kamar dai itace ta b’ace cikin k’ok’arin lalumo ma Haidar hanyarsa. Meyasa takeji kamar dai kowa amfani da damarsa yake akanta.? Ba auren soyayya tayi ba sann bata tsammaci wani abu mai kama da farin ciki cikin auren ba. Musamman idan ta tuna yanda akayi auren Wanda sadakin auren Ya kasance kudin jinyar mahaifinta. Koda ace Mommy ba har zuciya take nuna mata so ba, koda ace manufar Mommy shine ta shigo rayuwar Haidar dan tai guiding d’insa bata jin Mommy tanada wani laifin cikin hakan tinda tin farko ga yanda akai auren. Sann A d’an zaman da sukai da Haidar kai tsaye bazata ce ta kamu da soyayyarsa ba. Amma tana jin damuwarsa Har cikin ranta. Saidai dukda wad’ann tunani can k’asan zuciyarta tana jin sosai take so ta gano manufar Anisa dan ta tabbata idan Babu wani boyayyan al’amari Anisa bazata samu k’warin gwiwa irin haka ba. Ta d’au d’amarar gano bakin zaren komai cikin ikon Allah. 


A ‘yan kwanakin Mommy ke zuwa wajen Haidar ta yini dashi sann ko zancen bata kumayi ma Ummul ba. Iyaka damuwa Haidar yakai k’ololuwa. He misses her so much. Baisan ta yanda zai sanar da Mommy ba. Ya kula ma kaman Mommy punishing d’insa take da rashin Ummul d’in. 


Da Haidar yaga abin ba na k’are ba Har ana shirin sallamarsa batazo ba dole ya tambayi Mommy Ina take mai take gida.? 


Mommy ta dubesa a dan tsare “Hutawa take gida, ka kyale nurse room dinka ya kula dakai. After all, aikinsa ne. An biyasa domin yayi hakan.”


“But Mommy he doesn’t do anything right.. And I don’t want him touching my things.” Ya k’arashe fuskarsa duk a dame. 


“Oh kasan da haka kai mata mugun hali.?” Mommy tace a dake.


Sai Ya d’ago a d’an firgice “Mommy mugun hali kuma.? ita tace Miki na mata wani abin.?” 


Yanda yai tambayar ya tabbatar ma Mommy D’anta Ya fara nitso a tekun soyayya bai sani ba. Ta kifa kai ta murmusa kafin ta kuma d’agowa a tsare ta dubesa “Nasan ka mata wani abin ne amma wann ji da kan naka bazai bari ka amince kayi ba.”


Ya lumshe idonsa kadan had’ida furzar da huci “Mommy I didn’t mean to hurt her feelings.. Believe me.” 


Dakatar dashi tai “Ba ba’asi na nema ba.” Sai ta kuma dubansa wann karon a d’an sanyaye “Haidar, ni na haifeka nasan halinka tun k’uruciya. Nasan abubuwan da kai going through a rayuwa. Tin kana yaro baka bari a gane lagonka dukda tarin k’alubale da ka fuskanta. Jarumtarka baya bari a gane raunin ka. Amma ka sani even the strong people need help sometimes.” 


Sai ya dubi Mommy a d’an sanyaye wann karon. 



Mommy taci gaba da jinjina kai “I know your psychological wounds are much deeper.. But I believe they’ll heel in time with Ummulkhair by your side.” Haidar ya kuma duban Mommy without saying a word.


Mommy taci gaba “Ba gazawa bane to Own up to your mistakes and apologies when necessary. Even if it hurts..” Ta murmusa tana dubansa “Kana so matarka ta dawo wajenka.?”


Sai ya dubi Mommy har lokacin baice komai ba. Saima kaikaitar da fuskarsa da yai. 


“Shikenan zan sa driver ya kawota. But I have my conditions.” 


Yai saurin duban Mommy “Mommy conditions kuma.? You.. just call her my wife fah.”


Dariya Ya kusa kufce ma Mommy tai k’ok’arin gimtsewa “Toh so kake na kawo maka ita ka wulak’anta ta. Ai dai naga ni na biya sadakin ba Kai ba.”


Ta kuma gyara zamanta “Conditions dina sune Bazaka sakata fushi ba. And you must kill that prideful behaviour of yours. Kayi alkawari.?”


Ya marairaice fuska “Mommy do I have to promise.?”


“Aw! Toh kaga ni saida safe.. Room nurse d’inka na jira.” Ta mik’e tana k’ok’arin d’aukar jaka.


Saurin kamo hannunta yai “Ok, fine. I promise.” Ya fad’i kaman Wanda aka masa dole. 


Mommy ta k’unshe dariyarta dan sosai draman Haidar d’in Ya bata dariya. Ga abu kana so amma ka kasa fitowa kai tsaye ka furta. Wani abun sai Aliyunta. Ta tuna da fari da kyar Ya amince Ummul ta zauna wajensa sai gashi yanzu da kanshi yake nemanta. ‘Sannu a hankali ma zaka kawo kanka wajen Ummul d’ita Haidar.’ Mommy tace a zuciyarta. 


Ba Mommy ce ta maida ma Haidar matarsa ba sai ana gobe sallamarsa. Dan so take ta wana Haidar kad’an yanda idan ta mayarsa da Ummul zai shiga taitayinsa. Sa’arsa d’aya ma dan jinya yake. 


*

Yana nan kishingid’e saman gado  yana duban yanda taketa fito da  kayayyakin daga hospital wardrobe d’in tana shiryawa cikin suitcase. Fuskarta babu yabo babu fallasa. Dan tinda ta dawo bata yarda sun koma kaman da ba musamman idan ta tuna maganganun Anisa. Ta k’udiri niyyan gano koma menene ke b’oye da izinin Allah tinda tasan a shashanci irin na Anisa haka kawai bazata shirya zance irin haka ba face tanada k’wakk’waran hujja.


Ta dan saci kallonsa tana linke Kayan. Nan taga ya kafe ta da ido. Tai saurin janye idonta. 


Mik’ewa yai Ya soma takowa a hankali. Ta bayanta ya tsaya had’ida rungumota, Ya rik’e hannunta da kayan cikin nasa. Ummul ta lumshe idonta a hankali jin hannunta saman nasa. A hankali yake k’ok’arin linke kayan ba tareda ya saki hannunta ba. Har lokacin idanun Ummul a lumshe suke tana jin kwalla na k’ok’arin ciko idonta. A hankali Ya d’aura hab’arsa saman wuyarta had’ida lumshe idanunsa. Wasu abubuwa yake mata Wanda k’afafuwansu ke barazanar gaza d’aukarsu. Rigar dake cikin hannunsu Ya silale Ya fad’i k’asa… Ta soma k’ok’arin cire jikinta daga nasa amma saiji tai ya rik’eta tsam. Murya can k’asa yake furta “I wanted to hate you.. I tried to hate you.. But I couldn’t..!” Ya d’anyi fasali yana mai ci gaba da sinsina wuyarta. K’amshinta da yai missing. Har lokacin idanun Haidar a lumshe suke. Yayinda hawayen da Ummul ke k’ok’arin makalewa suka shiga zarya. 

“I can’t get you out of my mind Khairy… Please stay.. right here..And don’t let go.!” 


Hawaye shar suka soma ambaliya a fuskarta. Ta shiga cikin rud’ani matuk’a. Ta rasa da waye zata yarda cikin ukun. Mommy ce, ko Anisa ce ko kuwa Haidar ne. 




SameenaAleeyou📚


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post