Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 90

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 90

Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 90


قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina pls banda kiran waya,bana amsa shi,Just message za'ayi mun ta whatsapp in sha Allah zan amsa,don bana shariya indai ina online 08103884440❤Masu kirana ƙarfe goma na dare kuna son jamun wlh😡_

Cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi"na..am yaya haroon" raba ta yayi daga jikinshi tare da sanya hannayenshi ya tallabo fuskarta,daƙyar take iya buɗe idanunta waɗanda ke jike sharkaf da hawaye,zuba mata ido yayi yana kalllonta,fuskarta duk ta kumbura tayi haske,gashi ta ɗan yi rama wannan ya tabbatar mashi da cewar tana cikin matsananciyar damuwa,yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana idonshi ya sauka akan hannunta,kanula ya gani,a ruɗe yace"Amrish!Wannan fa?faɗa mun meya faru?Kinyi rashin lafiya ne"?

   daƙyar ta iya buɗe baki tace"Poison nasha,Saboda na gaji da zaman duniyar nan,Mommy ta 6atamun rai,ba ta sona ba ta damu dani ba......".

  Bata ƙarasa maganar ba,yaja hannunta izuwa wurin motarshi,buɗe mata motar yayi ta shiga back seat ta zauna sannan shima ya shiga mazaunin driver,shiga cikin Hotel ɗin ya ƙarasa shiga da ita,bayan yayi parking ɗin Motar ya fito ya buɗe wurin da amrish take ya shiga daga ciki,

   Cikin sanyin Murya yace"faɗamun abunda ya faru tsakanin ki da ita"?

  Nan ta labarta mashi abunda ya faru tsakaninta da mommynta tun daga farko har ƙarshe,

     "Amrish!ashe baki da hankali?saboda kawai ta gaya maki wannan ƴar maganar sai ki nemi kashe kan ki?suwa kika yi ma asara?

  Shiru tayi yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,

    "So kike narasa ki ko"?da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a,

  1. Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 87
  2. Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 88
  3. Abban Sojoji Takun Karshe Chapter 89

   "Bazan ƙara ba,yaya haroon mommy ce ta 6ata mun rai,kuma ni bansan zama wurinta,Na tsaneta bata kwanta mun araina ba,dan Allah kada ka mayar dani wurinta,ka kaini gidanku kawai in zauna tare daku,"

  Waro idonshi ya ɗan yi kafin yace"gidan mu!in kaiki a matsayin wa?so kike kija mun?yayyena fa gaba ɗayansu maza ne kuma sojoji ne,bazaiyiwu ba ki zauna acan,"

  Fuskarta tamkar zata yi kuka tace"Ya kake so nayi da rayuwata ne?ni babu wurin da nake jin daɗin zama,Ka kaini kawai gidan ku in zauna,idan ina ganinka sai hankalina yafi kwanciya,amma ni bazan koma wurin mommy ba,in ba so kake ka rasa ni ba gaba ɗaya,"tayi maganar aɗan shagwa6e,

   Shiru ya ɗan yi yana tunanin mafita,don kuwa ya santa da baƙar zuciyar nan ta gado,in har yaƙi yi mata abunda take so to tabbas zata aikata abunda ta faɗa ne,

   Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallonta yace"It's Okey,zan kai ki gidan mu amma kafin nan,Ki fara zama a wurina,Ni abunda ya ɗaure mun kai,taya ya har kika gano inda nake?"

  Sae lokacin ta ɗan saki murmushi akan fuskarta,kafin tace"Ae nasan duk wani wuri da kake zuwa,kaine baka sani ba....".  

   "Wato bibiyata kikeyi ko"? Dariya tayi,tana ɗaga mashi gira,

    "Zanyi maganinki,mai ɗan kumatu,"

  Sosai ya shiga zolayarta,har sai da yaga farin ciki akan fuskarta,atare suka fito daga cikin Motar hannunshi acikin nata,wucewa yayi da ita VIP,inda room ɗinsa daya kama a hotel ɗin yake,bayan sun shiga ciki wanka ya sanyata tayi sannan ya daukko mata kayan da zata sanya ajikinta,dama ɗakin nasa na sharholiyarsa ne,akwai duk wani abu da mace zata buƙata,tunda nan yake kawo ƴan matansa da samarinsa duka dae,bayan ta kammala shirya kanta,order ya bada na abincin da zataci,

  Bayan an kawo mata abincin,taci ta ƙoshi,sannan yace ta kwanta ta huta,Cikin ƙankanin lokaci bacci ya ɗauke ta asaman gadonshi,

  Safa da marwa ya shiga yi acikin ɗakin tunanin shi,taya za'ae yakai amrish gidansu!?Yasan cewa ba wani abun tashin hankali bane,kuma in ya kaita zasu kar6eta hannu bibbiyu,amma bazai bari su ganshi ba da sunan wanda ya kawota,in ba haka ba zai zama abun zargi a wurin ƴan uwansu,

Download >>>> Daudar Gora book 2 complete Document

Download >>> A Rubuce Take (K'addarata) book 2 complete Document.


  Sae faman zirga zirga yakeyi acikin ɗakin,lokaci zuwa lokaci yakan ɗan juya ya kalli amrish dake kwance saman gadon nashi,hankalinta kwance sae sharar bacci take yi,bai ta6a ganin yarinyar da ta yarda dashi ba kamar amrish,kwata kwata ba ta jin tsoranshi don ta rungumeshi,ba wani abu bane a wurinta,duk da shi ya koya mata hakan,har kwana saman gado ɗaya suna yi da ita,amma wani abu bai ta6a shiga tsakaninsu ba,sae dai ƙawayenta su Zeenatu,babu wadda bai yi lalata da ita ba acikinsu,kuma har yanzu yana tare da kowaccensu,duk in ya buƙace su zasu kawo mashi kansu ne,


❤🤍❤


After La'asar,


Tsaye take agaban dressing mirror tana ƙare ma kanta kallo yadda kasan wadda za ta je gasar Kyawun duniya,Wedding gown ce a jikinta  fara ƙal,tabi shape ɗin jikinta,hips ɗinta ya fito sosai kamar zai fasa rigar haka daga saman rigar net ne,sosai fatar ƙirjinta ta fito mai matuƙar jan hankali,Daga bayan Rigar lace tattoo ne wanda ya ƙara fito da kyawun rigar,fuskarta na ɗauke da light makeup,ta shafa jan baki red colour,Hannunta na sanye da haɗaɗɗiyar wrist watch ta diamond da Aunty azeeema ta saka mata,mai haɗe da ring da kuma chain ƴar ziririya fara,ga earrings ɗinta,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fitowa daga jikinta Kamar wadda aka tsamo daga cikin ƙogin turare,gaba ɗaya bedroom ɗin nasu Ƙamshin turarenta ne ya karaɗe ko'ina,ƙafarta na sanye da stilleto,matsiyacin high heels ne mai shegen tsini,shima launin rigar jikinta ne,ƙafafunta sun fito ɗass acikinsa,


   "Wow masha Allah,Tabarakallahu Ahsanul khaliƙin!"hajiya azeema ce ta ambaci hakan,jahad kuwa hannunta na ɗauke da Wayar sehrish ta shiga Camera sae video take yi mata,ita ma hosana hannunta na ruqe da wayar hajiya azeema I phone 13,Sun taru sai video suke ɗaukar sehrish,

Ƙoƙarin juyowa tayi da sauri hajiya azeema ta dakatar da ita"Kada ki juyo yanzu,bari na aza maki net ɗin nan asaman kanki zai ƙara maki kyau sosai,Bayan ta kammala sanya mata mayafin sannan tace"Sannu a hankali zaki juyo ba da sauri ba," a natse Sehrish  ta soma juyowa a wani slow,Hosana na kallonta ta cikin camera sai faman sakin Murmushi take yi,

  Hajiya azeema tace"Yawwa My photographers ku ɗaukarmun ita da kyau,ta fito sosai acikin Video ɗin,yadda zanji daɗin ɗaurawa a status ɗina,

  Ƙarasa juyowa sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da ƙayataccen Murmushi,ita kanta tasan tayi kyau over,Zuciyarta cike fal da farin ciki,kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna,dama hannunta akwai zanen jan lallen da akayi masu na walima,yana nan raɗau a hannunta bai goge ba,ta ruƙe yar purse ɗinta a hannunta,

  Tun daga ƙasa Hosana ta fara ɗaukarta ta cikin camera ɗin har izuwa saman fuskarta,

   "Turn ur back,yadda zasu ji daɗin ɗaukarki da kyau,"acewar Azeema,

  Juyawa sehrish tayi a hankali suka ɗauki bayan,sannan ta sake juyowa,Jahad sae faman zuzuta ta take yi tana cewa"wlh yadda kasan Amaryar Gaske,Sehrish kinyi kyau sosai kamar dollars"

  Dariya hajiya azeema tayi jin abunda jahad tace,

  tace"Wato kuɗi sune suka fi komai kyau kenan?shiyasa ake kwantanta su da mutumin da yayi kyau ko"?tayi maganar tana kallon Jahad dariya sukayi gaba ɗayansu,

  Suna cikin rahar nan wayar hajiya azeema tayi ringing,sunan Abba ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,da sauri hosana ta miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar bayan ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnanta,

   Tun kafin tayi sallama taji muryar abba yace"Azeema kina ina ne"?

   "Ina a ɗakinsu sehrish ne yanzu haka,na kammala yi mata kwalliya ne harma ta sanya rigar amaren...."

  Katse ta yayi da cewa"Karki kuskura,kice zaki kai yarinyar nan ɗakin Rafayet!".  

   Hankalinta atashe tace"Saboda me Yaya hossein"?tun daga kan muryar Abba ta tabbatar da cewar yana cikin matsananciyar damuwa,

   "Tun farko sai da na faɗa maki cewar wannan auren na sirri ne,kuma na faɗa maki dalilin dayasa ya aureta ba don yana sonta ba fa ce don tayi mashi aiki,.." a ɗan ruɗe hajiya azeema ta dago tana kallon Sehrish,jikinta ne yayi wani irin sanyi har cikin zuciyarta taji babu daɗi,

  Da sauri tace masu"Ina zuwa" tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,a nan cikin corridor din ta tsaya,Muryarta asanyaye tace"Yanzu yaya kana nufin cewa yarinyar nan bazata tare aɗakin Mijinta ba!"

   "Azeema so nake ki fahimce ni,!ki natsu ki saurare ni,!rafayet wani irin bauɗaɗɗan mutunne mai wuyar sha'ani,Wlh bazai bari yarinyar nan ta zauna a part ɗinsa ba,da sunan amaryarshi,Yanzu haka zancen da nake yi maki,Ya hana uban kowa ya ɗauki hoto tare dashi!gaba ɗaya babu wanda ranshi bai 6aci ba saboda rafayet!"

   Muryar hajiya azeema tamkar zatayi kuka tace"Amma ba'ayi ma yarinyar nan adalci ba!Meyasa tun farko ba'a shawarce ta ba?kafin a ɗaura mata aure dashi!yakamata ace tasan da zancen auren da za'ayi mata da kuma dalilin yin auren!me kuke tunanin zai faru idan har yarinyar nan taji cewar an aurar da ita ne don tayi aiki kawai a ƙarkashinsa"?

  Shiru Abba yayi batare daya ce mata komai ba,

  Jinjina kai kawai hajiya azeema tayi tare da cewa "Shikenan kawai,Zansa ta cire rigar dana sanya mata,Amma dae banji daɗi ba,Kuma in sha Allah rafayet sai yayi danasanin yin hakan da yayi!"tana kai ƙarshen maganarta,tayi rejecting kiran,Tuni idanunta sun cicciko da kwalla,Ranta yayi mugun 6aci,

    "Aunty azeema!"hosana ce ta ambaci sunanta,da sauri takai idanunta ƙopar ɗakin nasu,tsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Munata jiranki,Kince zamu je kai amarya,"

   "Kada ki damu hosana,Yanzu zan shigo ciki,"

  Amsa mata tayi da toh,sannan ta koma cikin ɗakin,Kusan 15 mins hajiya azeema tana tsaye batare da ta motsa ba,sae da zuciyarta ta lafa,sannan ta wuce cikin ɗakin nasu,

    A tsaitsaye ta samesu suna jiran dawowarta,gaba ɗaya duk sai taji ba daɗi,Musamman yadda taga Sehrish sae faman sakin Murmushi takeyi,tsananin tausayinta ne ya kamata,Shin wata irin rayuwa yarinyar zatayi a ƙarƙashin Sgr?mutumin da baisan Soyayya ba,Tabbas zata sha wahala a hannunshi,Domin kuwa zai mayar da ita tamkar baiwarshi ne,su yaya hossein sunyi kuskuren aura mashi ita,da sunan tayi mashi aiki,wannan tamkar ƙasƙanci ne,kuma yarinyar bazata ji daɗi ba,ranta zai 6aci sosai idan ta gano cewar aure akayi mata,auren ma na sirri,tamkar wata mara gata,babu walima babu wani party,babu taron mutane,babu wedding pics,dole abun ya ta6a Zuciyarta,na biyu da sa hannun iyayenta suka aura mata shi da sunan tayi aiki a ƙarƙashinsa ba matsayin matarshi ba,tabbas an gama cutar da ita,


    Mamaki abun ya ba su Jahad ganin hajiya azeema tayi tsaye agabansu,kuma ta ƙurawa sehrish ido tana kallonta,Kamar mai nazarin wani abu,

   Jahad ce ta ambaci sunanta"Aunty azeema,"

  Firgita tayi lokaci guda ta ɗan saki murmushin yaƙe tare da cewa"Am sorry fa,wlh na shafa'a ne,Yanzu mai ya rage mana muyi"?

   Hosana tace"Kai amarya mana,ki faɗa mana a ina zamu kai rishi ɗin,"

   Hajiya azeema tace"Ae wannan shirin drama ne!ba dagaske ba,A nan zakuyi wasan ga wayata ma idan kuna buƙatar yin hotuna,Ni yanzu inaso zan wuce ciki ne,"

  Da sauri Hosana ta kar6i wayar daga hannun hajiya azeeman,sallama tayi masu da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,

  "Kamar yanayinta ya canza ko"?jahad ce tayi maganar tana kallon sehrish,

   "Nima na lura da hakan,Hosana wanene ya kira ta a waya nasan kinga sunan daya bayyana akan screen ɗin,Zai iya yiwuwa wani abu aka sanar da ita wanda ya 6ata mata rai,"acewar sehrish,

   Hosana tace"Ni dai naga Sunan Yaya hossein,amma bansan wanene ba,"

  "Sunan Abbansu Junaid ne,Allah yasa dae ba wani abu ya faru ba,"sehrish tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,

  "Kodai naje najiyo mana abunda ke faruwa cikin gidan"?Hosanar tayi tambayar tana kallonsu,

  Jahad tace"A'a,babu ruwanki,tunda ba kiran mu akayi ba,"


Cigaba da ɗaukar hotuna sukayi acikin ɗakin,Shigowa junaid yayi fuskar nan tashi ɗauke da murmushi,Suna ganinshi suka haɗa baki wurin cewa"Baby Junaid!"

  Ɗaure fuskarshi yayi tare da ɗan turo bakinshi ashagwa6e yace"Ni ku daina Kirana da sunan baby,In ba haka ba,ran kowa zai 6aci a wurin nan,"ya ƙarasa maganar tare da aza idanunshi kan Sehrish dake tsaye tasha Kwalliya abunta,sakin baki yayi galala yana kallonta,a ruɗe ya ambaci sunanta"Reesh,"

  Murmushi Sehrish ta sakar mashi,tare da yi mashi fari da ido,sannan tace"Na'am,Junaid ya kaga wankan nawa,"?

   daƙyar ya iya cewa"reesh,yanzu kina sane aka ɗaura maki aure da babban yayan mu bayan kinsan da cewar Ina sonki"?

  Gabanta ne ya faɗi rassss!!Ba ita ba hatta su Jahad da hosana a ruɗe suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma,da Babban yayan mu!"

  Shi kanshi junaid ɗin sae da gabanshi ya faɗi,tunani ya shiga yi anya Sehrish tasan da auren kuwa?Yanayin yadda ya ga ta razana ya tabbatar mashi da cewar batasan da zancen auren ba!acikin ranshi yace"meke faruwa ne?Mommy batasan da auren babban yaya ba,kuma itama rishi dasu jahad basu san da auren ba!Abba ya 6oye masu kenan!aikuwa saina tona masu asiri kowa yaji,dama ya 6ata mun raina yau,duk irin amanar dake tsakanina da Abba ya rasa dame zai sakamun sai da wannan,"

  "Junaid dan Allah kayi mana bayani dalla dalla yadda zamu fahimta!"acewar jahad,

   Kallon fuskar sehrish yayi ganin ta zuba mashi ido tana kallonshi,kalmar daya furta masu ce take ta maimaitawa acikin zuciyarta

   "nidai baza aji mutuwar sarki abakina ba,Abba yace kar na faɗama kowa cewa an ɗaura aurensu,"yayi maganar tare da sanya hannu ya toshe bakinshi,

  Hankali atashe suka shiga kallon juna atsakaninsu,

   "Don Allah junaid ka faɗamun auren wa aka ɗaura"? muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,

   "Sehrish kiyi haƙuri bazan iya sanar dake ba,Amma idan kina son samun ƙarin bayani,kije wurin Uncle ki tambayeshi,


  Jiki na rawa sehrish ta kama hanyar fita da sauri Hosana tabi bayanta,suka fita atare,

    Matsawa yayi kusa da jahad,tare da ruƙo hannayenta yace"Jahad!Albishirinki"?

"Goro,"ta bashi amsa fuskarta ɗauke da murmushi,

"Fari ko Ja"? Wurga ido ta ɗan yi sama kafin tace"Fari,"

    "Uncle ya bani aurenki,"jin wannan maganar yasa hankalin jahad ya tashi,lokaci guda ta ɗaure fuskarta,tare da fisge hannunta daga cikin nashi,

   Gabansa ne ya faɗi,ganin yadda ta canza mashi lokaci guda tsoranshi kada ace jahad ba son shi take yi ba,

  "Jahad baki sona?bakison ki aure ni ko"?

  Shiru jahad tayi tana ƙare mashi kallo daga ƙasa har sama,

   Tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,fargabarshi wata amsa jahad zata bashi,in har bata amince ba shikenan zai rasa damar da yake da ita,na mayar da gurbin rishi ɗinsa daya rasa,

   Motsi ta soma yi da la66anta daƙyar ta iya cewa"Junaid!dagaske kake mun ko wasa?tell me the truth pls,i know u are just teasing me,'

    Girgiza kai yayi tare da cewa"Am serious jahad,Bazan 6oye maki ba,da farko sehrish nake so sosai,in har ba zaki manta ba,lokacin dana ɗauko ki a school matsayin sehrish,idan zaki iya tunawa sunanta nake ambata a matsayin ke,nayi tunanin itace shiya sanya na sanar dake abunda ke acikin zuciyata,Amma yau batare da sani na ba,A masallaci naji sanarwar ɗaurin Auren Sehrish da babban yayan mu,har sai da na kusa zaucewa ƙarshe a masallacin na yanke jiki na fa....."

  A razane jahad ta katse shi da cewa"Wai dagaske an ɗaura auren Sehrish!kuma da babban yayan mu!?

   ɗaga mata kai yayi alamar eh,kafin ya ɗaura da cewa"Ni kaina bansan da zancen auren nasu ba sae a masallaci dana ji ana sanarwar,abun ba ƙaramin ta6a zuciyata yayi ba,na shaqu sosai da sehrish,

  Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,jin zancen auren Sehrish da Sgr,ta rasa gane a wane yanayi take ciki,farin ciki ko kuwa akasin hakan!babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda aka 6oye masu ba'a sanar dasu ba,Ko meyasa?Yanzu shikenan an ɗaura auren rishi ɗinsu?ta zama married woman?

   Runtse idanuwanta tayi tare da sanya hannu ɗaya ta dafe gefen goshinta,a hankali ta furta"Ya salaam,"

   "Jahad,inason naji amsar tambayar da nayi maki"?muryarshi a kasalance yayi maganar,don ya qagara yaji amsar da zata bashi,

   A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar junaid,tana kallonshi tace"junaid Daddy da kanshi ya baka aure na?kuma ya tabbatar maka da cewar bada wasa yake maka ba"?

   Bubbuga ƙafafunshi yayi saboda hasalar da yayi,a ƙule yace"eh mana,shi da kanshi ya mallaka mun ke agaban kowa da kowa,yaji tausayina ne saboda halin dana shiga,"

.....fuskarta aɗaure tace"Meyasa daddy zai yi mun haka?nace mashi ina sonka ne?kuma ya rasa ma wazai ba aure na sai kai?junaid kayi mun ƙanƙanta!Ni bazan iya zaman aure dakai ba,nafison namijin daya mallaki hankalinshi ba shagwa6a66e ba sangartacce irinka...."tun kafin takai ƙarshen maganarta,hawaye suka fara wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka yace"au haka ma zaki ce jahad?shikenan babu komai,"da sauri junaid ya juya tare da nufar kopar ɗakin nasu gwanin ban tausayi,

  Yana ƙoƙarin kai hannu ya buɗe ƙopar,da gudu jahad ta faɗa bayanshi tare da rungumoshi sosai tana dariya,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya junaid ya sauke,kwantar da kanta tayi asaman bayanshi,magana ta soma yi mashi anatse"junaid,ko da yake yanzu na canza maka suna,Ka tashi daga junaid ka koma Babyn jahad,Ina fata hakan yayi maka,"

  Tafin hannayenshi ya sanya tare da share hawayenshi,wani irin sanyi ne ya ratsa cikin zuciyarshi,Calmly ya ambaci sunanta"Jahad,Kin amince da aure na?a yadda nake?zaki iya haƙuri dani?ki zauna dani amatsayin Mijin ki uban ƴa'ƴanki kuma"?

  Lumshe idanunta tayi yayin da hancinta ke shinshinar ƙamshin turaren jikinshi,

   "I accept ur love junaid,I love u so much,nayi farin ciki sosai da daddy ya baka aurena,a ashirye nake dana baka kulawar daya dace junaid,"

  Saboda tsabar farin ciki bakin junaid yaƙi rufuwa,hannunta ya ruƙo tare da zagayo da ita,ta dawo gabanshi suna facing ɗin junansu,zuba ma juna ido sukayi na wani lokaci,batare da sun sha Wahala ba,Sun amince ma junansu kowa ya samu abunda zuciyarshi ke muradi,janyota yayi ta faɗa asaman ƙirjinshi,zagayo da hannayenshi yayi ta bayanta,sosai ya rungumeta,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,lokaci guda suka kamu da tsananin son kasancewa da junansu,

  


*Boss Bature*


  ❤🤍❤

  


"Rafayet!Ka 6ata mun rai!ka ƙuntatamun!Amma kai ko ajikin ka?meyasa zakayi mun haka"?Abbansu ne yayi maganar a yayin da yake tsaye acikin bedroom ɗin Sgr,Idanuwanshi sun cika tab da hawaye,

  "Abba,don me zaka tashi hankalin ka akan auren nan!You know the reason why I married her,Saboda inaso taci gaba dayin aiki a ƙarƙashina,ni ban shirya yin rayuwar aure ba,Babu wannan a tsari na," yana magana huci na fita a bakinshi,saboda tsabar 6acin ran da ya ke ciki,ji yake gaba ɗaya sun takura rayuwarshi,ba don komai ba sai don saboda sun nemi Alfarmar ya taimaka yayi koda hoto ɗaya ne shi da Sehrish don su ajiye na tarihi,

  Gyaɗa kai Abbansu yayi tare da cewa"A haka kakeso kai ayi maka biyayya,bayan Ni ban isa na sanya ka abu kayi mun ba,narasa gane kai wani irin mutunne!ka ce yarinya bazata zauna a part ɗinka ba!kuma ba zaka ɗauki hoto ba atare da ita,nasan meyasa kayi hakan!saboda kada hotonku ya shiga duniya a dinga nunata a matsayin matarka!saboda kai a wurinka wannan ƙasƙancine aganta a matsayin matarka,saboda ka fi ƙarfin ta ko"?

  Yayi maganar ranshi a 6ace,Sgr kuwa ko ajikinshi,yana daga tsaye agaban dressing mirror ɗinshi ya juya ma Abbansu baya,har lokacin bai canza kayan jikinshi ba,babu wanda baizo yayi mashi magana ba akan ya amince da buƙatar mahaifinsu amma yaƙi yarda,hatta Ishaq da Abbas sunyi sunyi har sun gaji sun ƙyale shi,haka Marshal Omar sunyi barambaram dashi,saboda ya 6ata masu rai,

  "Zan tafi na bar maka ɗakin ka,Amma inaso na ƙara tunasar dakai cewa Abusufyan ya baka tsawon wata ɗaya kacal akan ka canza ra'ayinka game da auren yarjejeniyar nan,Zaka iya soke shi in har kana so acikin ƴan kwanakin nan,Amma idan har ka bari wata ɗaya ya wuce baka canza ra'ayin ka ba,duk abunda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa ka kuka da kanka!kuma babu ruwana Na zame hannu na aciki,

  A fusace Sgr ya juyo tare da kallon Abban nasu yace"bazan ta6a canza ra'ayi na ba akan hakan!Idan ma yana tunanin hakan to ya daina!Bana buƙatar wani time nayin tunani!wata uku na cika zan sallame ta ne!

  Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,ta wutsiyar idonshi ya hango mutun atsaye,a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,

  Sehrish ce atsaye tana kallonsu,gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa,domin kuwa taji duk abunda suka ce kaf acikin kunnanta,Jikinta har kerma yakeyi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa akan fuskarta,

  Jin shessheƙar kukanta yasa Sgr Juyawa tare dakai idanunshi wurin da take tsaye a ƙopar ɗakin nashi,tun daga ƙasa har sama yabita da kallo,

  A hankali Abbansu ya ambaci sunanta"Sehrish!"

  Juyawa tayi da gudun gaske tabar ƙopar ɗakin nashi,gaba ɗaya tabar part ɗin nashi,saukkowa tayi downstairs,Su fawan ne tsaitsaye acikin babban falon,koda suka ji shessheƙar kukanta sae hankalinsu ya koma akanta,kowa ya shiga tambayarta lafiya,

  Bata tsaya sauraronsu ba,da gudu ta wuce bedroom ɗinsu,tana shiga ciki ta samu junaid da jahad azaune gefen gadonsu suna shan soyayya,jin shigowarta yasa suka mike tsaye hankali atashe suka shiga tambayarta Lafiya,

  Bata basu amsa ba,kai tsaye ta nufi toilet ta buɗe ƙopar ta shige ciki,da ƙarfi ta datse ƙopar,sannan ta tsugunna ƙasa tana kuka tamkar ranta zai fita,


Gaba ɗaya Jahad da Junaid suka nufi ƙopar,Suna kwankwasawa suna kiran sunanta"Sehrish!Sehrish!dan Allah Rishi ki buɗe mana kopa!

  Turo kopar ɗakin nasu akayi,Abusufyan ne tare da hajiya azeema suka shigo ciki hankalinsu atashe,basu jima da shigowa ba,sai ga Abbansu junaid,dama tunda yaga ta watsa aguje tana kuka ya biyo bayanta,

  A bakin kopar shiga toilet ɗin suka tsaitsaya cirko cirko

   "Dama nasan abunda zai biyo baya kenan!"acewar hajiya azeema,

  Abusufyan yace"Ni bansan waya faɗa mata ba,Naso ace ni na fara sanar da ita,"

  Fuskar Abba a yamutse yace"wlh bansan da ita ba!Yanzun nan fa naganta a ɗakin Rafayet,muna cikin magana dashi akan zancen auren nasu,kawai naji shessheƙar kukanta,ashe duk taji abunda muka ce,"

   Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,musamman Abusufyan har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata,

   Ƙoƙarin lallashinta suka shiga yi amma ina,Sehrish taƙi sauraron kowa kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita,tana jin muryoyinsu a waje sai faman yi mata magiya sukeyi akan ta buɗe masu ƙopar,

   Junaid duk yabi ya ruɗe sam baisan cewa abun zai ta6a zuciyarta ba har haka,Ita kanta jahad ba ƙaramin tausayin Sehrish taji ba,kowa sai da yasha jinin jikinshi,babban abunda suke ji ma tsoro kada ta illata kanta,


Bakomai ne ya ƙona mata rai ba,Fa ce abunda kunnuwanta suka jiyo mata,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,komai ya fita aranta,tabbas tana son Sgr sosai har cikin ranta,kuma babu abunda ya canza acikin zuciyarta,tayi farin ciki mara misaltuwa na kasancewarta matarshi,wannan babbar kyauta ce agareta,sae dai kash bataso ya aureta batare da yana sonta ba!Sam bata ta6a ra'ayin hakan ba,tafi son ta auri wanda take so kuma yake sonta,bawai wanda takeso ba,Shi baya sonta,bugu da ƙari kuma ya aureta ne don taci gaba da aiki a ƙarkashinshi na wata uku kacal!

    "Idan ba damuwa inaso ku ɗan bani wuri in shawo kanta,"hajiya azeema ce tayi maganar,

   Abusufyan yace"kina ganin zaki iya shawo kanta kuwa?

  "Ku je kawai,Ni nasan yadda zanyi da ita,ku ɗan bamu wuri,"

  Kama hanya sukayi gaba ɗayansu hadasu jahad suka bata wuri,kamar yadda ta bukaci su fita daga dakin,

  Zuƙunnawa hajiya azeema tayi abakin ƙopar toilet ɗin,Saboda ranta ya bata cewar sehrish tana zuƙunne a ƙasa,ta gane hakan ne ta hanyar sautin kukan nata,

  Cikin lallami ta ambaci sunanta"Sehrish,"

  Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"

  "Inason magana dake!dan Allah ki bani haɗin kai,kada ki bani kunya,inaso kizo ki buɗe mun ƙopar nan!,"

   Miƙewa sehrish tayi,jikinta sai faman kerma yake yi,daƙyar ta iya sanya hannu ta buɗe kopar toilet ɗin,

  Sauke ajiyar zuciya hajiya azeema tayi tare da mikewa tsaye tana kallonta,fuskar nan tayi suntum da ita,gaja gaja da hawaye,idanun sun kumbura,janbakin da ta shafa duk ya 6ata mata fuskarta,mascara ɗin da aka shafa mata asaman eye lashes ɗinta,duk ya jike sharkaf da hawayenta ya 6ata fuskar da baƙin,kayan jikinta ne kawai basu 6aci ba,

  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita daga gefen gadon nasu,itama ta zauna suna fuskantar juna,

"Haba amaryar babban yaya,kuka bana ki bane,Farin ciki ya kamata na gani akan fuskarki,"cike da zolaya hajiya azeema tayi mata maganar hada jan kumatunta,

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shesshekar kuka tace"Am...amma..Aunty azeema..meyasa za'ayi mun haka?saboda me za'a ɗaura mun aure tare da babban yayanmu batare da an sanar dani ba?Nasan cewa sun isa dani!Amma yakamata ayi mun adalci,Auren wata uku fa?kawai saboda buƙatar kanshi"?

  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi cikin sanyin murya tace"Inaso na tambayeki wani abu,amsa ɗaya kawai nakeso ki bani,kuma ki faɗamun gaskiya,'

Dakatawa sehrish tayi da yin kukan tare da mayar da hankalinta kan Aunty azeema tana sauraronta,

   "Inaso ki faɗamun gaskiya,Shin kina son Sgr ko bakya son shi ne"?

Kun Karanta wadannan jerin Littafan?

  Shiru sehrish tayi yayin da idanunta ke akan yatsun hannunta da ta harɗesu wuri guda tana murzasu,

  "Kinyi shiru baki ban amsa ba"?

ƙasa kasa tayi da muryarta tare da cewa"bazan 6oye maki ba Aunty azeema,ina son Yaya rafayet sosai,fiye da yadda nake son kaina,"

   Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi,dama saida ranta ya bata cewar tana sonshi,

  "In har dagaske kina son shi bai kamata kiyi kuka ba don an ɗaura maki aure dashi,"

  "Aunty azeema ba baƙin ciki nake yi ba,bakomai ne ya 6ata mun rai ba fa ce irin auren da akayi mun dashi,Saboda kawai nayi  aiki a ƙarƙashinshi,na tsawon wata uku?meyasa za'ayi mun haka?idan aka barni ma zan iya yin aiki a ƙarkashinshi ba sai ansa ya aure ni ba,ba bisa son ranshi ba,tunda ba sona yake yi ba,ni kaɗaice nake ɗawainiya da son shi tun kafin nasan wanene shi,Wahala kawai zansha a hannunshi,Ni ban ta6a son na aureshi ba batare da yana Sona ba,"

  Jinjina kai hajiya azeema tayi tare da cewa"hakane kin faɗi gaskiya,ba'ayi maki adalci ba,Ni kaina bansan dalilin yin auren ba sai daga baya nake ji a wurin Abbanku,Amma kiyi haƙuri dan Allah kada hakan yasa ki bijire ma iyayenki,kiyi masu biyayya in sha Allah zaki ci ribar yin hakan,"

  Batare da musu ba Sehrish tace'Shikenan,in sha Allah zanyi masu biyayya,kamar yadda kika ce,kuma koda baki faɗamun haka ba,Ni bazan yi kuskuren bijire masu ba,"

  Murmushi hajiya azeema tayi tare da sanya hannunta ta shafa gefen fuskar sehrish,

   "Good girl,Naji daɗi sosai da kika amince zakiyi masu biyayya,Ni kuma nayi maki alƙwarin cewa atare zamu yaƙi sgr,acikin waɗannan watannin guda uku kacal,Zamu canza mashi ra'ayinshi,don ya gane kuskurenshi,kinsan ance DUK ƘYAN TAKALMI ƘAFA CE KE TAKASHI,So nake ki take mun wannan tsadaddan takalmin da ƙafafun nan naki ya taku sosae,"

Sae lokacin Sehrish ta fashe da dariya,har hakoranta suka bayyana,maganar da hajiya azeema tayi mata ta ƙarshen nan ba ƙaramin dariya ta bata ba,


Cigaba da magana hajiya azeema tayi"domin aikin mu yayi kyau muna buƙatar mu shirya plan A da kuma plan b zuwa c,zamu fara jaraba plan A,idan har akaci nasara akan shi kinga basai mun buƙaci plan B ba,Abunda nakeso dake yanzu shine muna buƙatar satar amsa,kuma ke kaɗae ce zaki iya samo mana wannan satar amsar da muke buƙata a wurinshi,

  A tsorace sehrish tace"Ni kuma!"hajiya azeema tace"kwarai kuwa,ba wani abun tashin hankali bane,just akwai bukatar musan me yake so da kuma abunda baya so don mu kiyayesu,Ni dae a iya sanina Sgr mutunne maison abi umarninshi ba'ayi mashi musu,yafi so ayi mashi biyayya abishi sau da ƙafa,sannan mutunne shi mai tsaftar gaske,ya tsani ƙazanta,bayan haka kuma Yana son abinci mai daɗi,shiyasa yake cin girkin azmee saboda tana da tsafta kuma ta iya girki,yakama ki koyi kalar girke girkenta,"

  "Ae na fara koyo a wurinta,Kuma na iya waɗansu,amma zanyi mata magana akan ta ƙara koyamun wanda ban iyaba,"

  "Yawwa haka nakeson ji,ki dage sosai,Nidae ta 6angarena zan baki gudummuwa sosai,""  

  Sun jima suna fira atsakinsu tamkar ba uwa da ƴa ba,har sae da aka fara kiran sallar Magrib,sannan aunty azeema tayi mata sallama,

  Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta samu ƙwarin guiwa sosai a wurin Hajiya azeema kuma taci alwashin zata ɗaura ɗamarar zama da sgr,har na tsawon wata ukun


*Boss Bature*


Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana a tsaye cikin ɗakinsu,sae faman zagaye zagaye takeyi,tana jiran dawowar Sgr,tun bayan sallar isha'e bai dawo cikin gidan ba,har lokacin wedding gown ɗince a jikinta,ta gyara kwalliyar fuskarta,sannan ta daure gashin kanta da ribbom,

  Jahad da hosana sun jima da yin bacci ita kaɗae ta rage batayi bacci ba,zuciyarta cike take da damuwa,sam tagaza samun natsuwa babban abunda takeyi ma fargaba shine taya zata fara tunkarar SGR a matsayin Mijinta?shin zata iya jure zama dashi?tasan cewa dole ta fuskanci ƙalubale dayawa a wurinshi,

  Tana cikin wannan zancen zucin taji shigowar motocinsu,ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa gefen gadonsu ta zauna tana jiran su ƙarasa shigowa cikin gidan,

  Almost 30 mins,sannan ta miƙe tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito waje,babu kowa kai tsaye ta nufi kitchen,batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi dinner ɗinshi a saman ƙayataccen tray ta ruƙo shi da hannayenta,a hankali take tafiya saboda tsinin takalman dake a ƙafafunta,bata saba tafiya da irinshi ba,babu kowa a main palour ɗin hakan yasa ta wuce upstairs part ɗinsa,

   Da sallama abakinta tashiga falon,babu kowa aciki sae dae kamshin turaren nan nashi,kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi tayi,a bakin ƙopar ta tsaya tare da yin sallama"Assalamu alaikum"

  "Who's there"abunda taji yace kenan,

daƙyar ta iya cewa"Ni ce"

  "Okey,Come in"

 A hankali ta zura ƙafarta cikin ɗakin nashi,samun shi tayin kwance asaman katafaren gadon nan nashi na mulki,ko takalman ƙafarshi bai cire ba,still shaddar ce ajikinshi,

   Ƙarasa shiga ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,kamar wata mara gaskiya ta juya zata kama hanyar fita daga ɗakin muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Baki iya gaisuwa bane?"

  dakatawa tayi tare da ɗan juyo ta saci kallon fuskarshi,A lumshe ta samu idanunshi tamkar maijin bacci,

   Muryarta na rawa tace"Ina yini"

 Ta6e la66ansa yayi tare da cewa'zonan""

Jiki asanyaye ta tunkareshi,da hannu ya nuna mata gaban gadon nashi,sannan yace"kneel down"

     Tattare rigar jikinta tayi,tare da zubewa saman guiwowinta,

  "Kukan me kikeyi ɗazu?ko don saboda kinji abunda muke tattauna da Abba ne?"

  Girgixa kai tayi'a'a ba haka bane,""

   "Okey,"

Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yaci gaba da magana"Na aureki ne saboda inaso ki cigaba da aiki a ƙarƙashin ikona!Idan har bakya ra'ayin hakan zan iya sakin ki,"Ya ɗan dakata da yin maganar yana jiran jin amsarta,


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post